Bidiyon yadda mutane ke yawon shan iska a jirgi don cire kewar bulaguro
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mutane da dama sun ɗauki yin bulaguro a matsayin wani abu na ɗebe kewa kafin ɓullar annobar cutar korona, sannan suna ganin tafiya a jirgi a mstayin wata hanya ta gajarce tsayin tafiyar.
Sai dai tun bayan sanya dokar taƙaita tafiye-tafiye sakamakon ɓullar annobar, matafiya da dama ba kewar inda suke son zuwa hutu kawai suke ba, har da kewar keta hazon.
To a wannan gaɓar ne aka samu jiragen yawo ba tare da inda suka nufa fa – da ke ɗaukar mutane su yi shawgi da su a sama sai su mayar da su inda suka ɗauke su.