Coronavirus: Karnukan da aka horas don su gano cutar korona
Ku latsa hoton da sama don kallon bidiyon:
An kai karnukan da suka kware wajen sinsina abu wadanda aka yi wa horo don gano cutar Covid-19 filin jirgin sama na Helsinki-Vantaa domin taimaka wa wajen yaki da annobar.
Ana yi wa fasinjoji gwajin ne bisa ra'ayin kansu.
Mai binciken da ke jagorantar shirin ya ce gwajin ya nuna cewa za a samu sakamako mai kyau amma har yanzu ba a tabbatar da kwarewar karnukan ba, kuma wasu kwararrun masana lafiya suna da ja kan shirin.