Coronavirus: Iyaye sun ɗau lokaci ba su ga jaririnsu na goyon ciki ba

Bayanan bidiyo, Coronavirus: Iyaye sun daɗe ba su ga jaririn da suka ba da hayar haihuwarsa ba

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Har yanzu a Ukraine ana ci gaba da kokarin sada jarirai da iyayensu, bayan matan da suka yi goyon cikinsu su, su haife.

A watan da ya gabata jami'ai sun ce wajen yara 100 ne iyayensu ba su samu ganin su ba a Kyiv, saboda matakan kullen cutar korona sun hana iyayensu na ainihi yin bulaguro a fadin duniya.

Amma a yanzu wasu kasashen sun dage takunkuman don haka iyaye na samun damar zuwa ganin 'ya'yansu.