Matar da ke amfani da abinci wajen yin zane-zane
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon:
Haneefah Adam ta ce ta fara kirkirar abubuwa tana sawa a Instagram, sai mutane suka fara so saboda haka ta ci gaba sannan yin hakan yana sa ta jin dadi.
Ta ce ta kan yi tunanin wane labarin take so ta bayar, sai ta dauki abinci ta kirkiri aikin.