Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya zama gwarzon UEFA 2022
Wannan shafin zai kawo muku halin da ake ciki kai tsaye a Istanbul game da raba rukunan gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge
Wanne rukuni ne zai fi zafi a wannan gasar
Rukunin A:Ajax, LIVERPOOL, Napoli, RANGERS.
Rukunin B:Porto, Atletico, Leverkusen, Club Bruges.
Rukunin C:Bayern, Barcelona, Inter, Viktoria Plzen.
Rukunin D:Frankfurt, TOTTENHAM, Sporting, Marseille.
Rukunin E:AC Milan, CHELSEA, Salzburg, Dinamo Zagreb.
Rukunin F:Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, CELTIC.
Rukunin G:MANCHESTER CITY, Sevilla, Dortmund, Copenhagen.
Rukunin H:PSG, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa.
Robert zai koma gida ba jimawa
Bayan hadewar da suka yi a rukuni guda, Barcelona za ta sake fafatawa da Bayern Munich a wasannin rukuni.
Magoya baya za su so ganin yadda fafatawar za ta kasance, ganin cewa dan wasan gaban Bayern, Robert Lewandowski sai koma Allianz Arena amma a wannan karon a matsayin wanda zai fafata da kungiyar.
A wasannin da suka gabata dai Barcelona ta fi shan kashi a hannun Bayern, amma a wannan karon da ake ganin Barcelona karfinta ya kawo ana ganin labarin zai iya sauyawa.
Labarai da dumi-dumi, Benzema ya lashe kyautar gwarzon dan wasan UEFA na bana
Karo na biyar kenan da dan wasan ke lashe gasar Champions tare da Madrid.
Shi ne ya fi kowa cin kwallo a bana a gasar, inda ya ci kwallo 15.
Ancelotti ya ce Karim ba kawai kyaftin din kungiyar ba ne, shugaba ne mai tafiyar da tawaga.
Benzema ya doke Thibaut Courtois da Kevin de Bruyne wadanda suka fafata tare.
Wiegman ta lashe kyautar koci ta mata ta bana
Abin birgewa!
Kocin Ingila da ta lashe gasar Euro ta mata ta 2022 Sarina Wiegman ita ce ta zama kocin da ta fi kowacce kokari a bana.
Ancelotti ya lashe kyautar kocin da ya fi kowanne
Carlo Ancelotti shi ne kocin da ya fi kowanne kokari a nahiyar Turai.
Kocin ya lashe gasar Champions sau hudu a tarihi.
Shiu ne ya lashe kofin a bara bayan doke Liverpool da ya yi da ci daya mai ban haushi.
Yanzu kowa ya san matsayinsa a Champions League
Ko wacce kungiya ta san wanda za ta fafata da shi ya zuwa yanzu.
An kuma shiga raba kyautuka.
Rukunin C
Bayern
Barcelona
Inter
Plzeň
Rukunin B shi ma ya cika
Porto
Atlético
Leverkusen
Club Brugge
Rukunin A
Ajax
Liverpool
Napoli
Rangers
Rukunin E
AC Milan
Chelsea
Salzburg
GNK Dinamo
Rukunin G ya cika
Manchester City
Sevilla
Dortmund
FC Copenhagen
Rukunin D ya cika
Frankfurt
Tottenham
Sporting CP
Marseille
Rukunin F ya cika
Real Madrid
Leipzig
Shakhtar
Celtic
Rukunin C
Bayern Munich
Barcelona
Inter
Rukunin F
Real Madrid
Leipzig
Shakhtar
Rukunin D
Frankfurt
Tottenham
Sporting Club
Rukunin B
FC Porto
Atletico Madrid
Bayern Leverkusen
Rukunin G
Manchester City
Sevilla
Dortmund
Rukunin H
P S G
Juventus
Benfica