Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana
Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Wasa ya kare, Brighton 2-2 Wolves
Wolves ta ci gaba da kare gidanta, domin kuwa wasa na 11 kenan da ta buga a kakar bana ba tare da an ci ta.
Wolves ta yi canji, Brighton 2-2 Wolves
An cire Adama, inda Traore ya karbe shi.
Katin gargadi, Brighton 2-2 Wolves
An bai wa Stepens katin gargadi
, Brighton 2-2 Wolves
Wannan wasa ya kasa fidda gwani. Tun a minti na 44 da Wolves ta farke kwallo ta biyu har yanzu babu abin da ke faruwa illa fafatawa.
Idan aka tashi haka Wolves ta ci da zama a kasan Man United a mataki na shida.
Brighton 2-2 Wolves, Brighton 2-2 Wolves
Duka kocin kungiyoyin sun kasa zama kowa na neman kare matsayinsa.
Brighton 2-2 Wolves, Brighton 2-2 Wolves
Brighton na buga kwallo kamar wadanda ake ci, so take kawai ta kara kwallo domin samun mazauni a teburi.
Brighton 2-2 Wolves, Brighton 2-2 Wolves
Wolves da shirinta ta dawo, ganin cewa Manchester United ta dare wurin da take a teburin Premier, da yuyuwar Wolves ta yi duk abin da za ta iya domin ta koma matsayinta.
An dawo wasa, Brighton 2-2 Wolves
An tafi hutun rabin lokaci, Brighton 2-2 Wolves
GOAL '44, Brighton 2-2 Wolves
Wolves ta yunkuro
Ahhhhh GOAL '36, Brighton 2-1 Wolves
Propper ya kara ta biyu bayan minti 1 da dakika 32.
Babu mamaki Brighton ta karya tarihin cewa ba ta taba yin nasara ba a wasan da aka fara cin ta kwallo daya a filin wasanta mai suna The American Express Community.
Sai an tashi za mu tabbatar da hakan.
GOAL '34, Brighton 1-1 Wolves
Maupay ne ya ci wa Brighton
Wolves, Brighton 1-0 Wolves
Wolves ba ta yi rashin nasara ba a wasa 10 na baya-bayan nan (ta ci 5, ta yi canjaras 5), Liverpool ce kadai ta fi ta bajinta, inda ba a doke ta ba a wasa 33 yanzu haka.
Ita kuwa Brighton ba ta taba yin nasara ba a wasan da aka fara cin ta kwallo daya a filin wasanta mai suna The American Express Community.
GOAL '27, Brighton 0-1 Wolves
Diogo ne ya sakada ta a zare bayan Raul Jimenez ya shirya masa ita daga bangaren hagu a ciukin yadi na 18.
Raul Jimenez, Brighton 0-0 Wolves
Raul Jimenez ya kai mummunan hari na-ci sakamakon kai da ya saka wa kwallo, da kyar da yarfe gumin goshi golan Brighton Mathew Ryan ya kwakwulo ta.
Brighton 0-0 Wolves, Brighton 0-0 Wolves
Kiris ya hana Brighton ta jefa kwallo, hari biyu a lokaci daya.
Leicester ta tumurmusa Aston Villa har gida, Aston Villa 1-4 Leicester
Leicester City ta ragargaji Aston Villa har gida da ci 1-4 a wasan Premier mako na 16.
Wannan ce nasara ta takwas a jere da Leicester ta samu a Premier ta bana kuma karon farko kenan da kungiyar ke cin wasan Premier takwas a jere.
Jamie Vardy, kamar yadda aka saba, shi ne ya bude wasan da kwallon da ya ci a minti na 20 bayan ya yanke golan Villa, Tom Heaton. Ya kara ta biyu a minti na 75.
Vardy ya ci kwallo a wasa takwas a jere a kakar bana, rabon da hakan ta faru tun a 2015 lokacin da Vardy din da kansa ya ci a wasa 11 a jere - yanzu haka shi ne kan gaba wurin zira kwallaye a kakar bana da kwallo 16.
Dan Najeriya Kelechi Iheanacho ma ya ci kwallo a minti na 41 a wasan da aka fara da shi na farko a kakar bana. Ya ci kwallo hudu kenan a dukkanin wasa hudu da ya buga a bana ga Leicester City.
Jack Grealish ne ya ci wa Villa kwallo daya tilo a minti na 45+2, sai kuma Evans, wanda shi ma ya ci a minti na 49, wadda ita ce kwallonsa ta farko a kakar bana ga Leicester.
Leicester City na ci gaba da zama a matsayi na biyu da maki 38, maki takwas kenan tsakaninta da Liverpool a saman teburi.
An busa tashi, Norwich 1-2 Sheffield United
An tashi daga wasa, Newcastle 2-1 Southampton