Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Roma ta yi kaca-kaca da Barcelona

AS Roma ta yi waje rot da Barcelona yayin da Liverpool ta fitar da Manchester City daga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana.

Rahoto kai-tsaye

Naziru Mikailu

  1. Kalli hotunan yadda ta kaya, Man City 1-2 Liverpool (1-5) Roma 3-0 Barca (4-4)

    Anan muka kawo karshen shirin na yau.

    Sai gobe inda za mu da sharhi kan Real Madrid da Juventus, da kuma Bayern Munich da Sevilla.

    Muna taya magoya bayan Roma da Liverpool murna - a kwana lafiya.

  2. Wasannin gobe, Real Madrid da Juve, Bayern Munich da Sevilla

    A gobe Laraba Real Madrid za ta kara da Juventus.

    Madrid na kan gaba da 3-0 a wasan farko.

    Bayern Munich za ta karbi bakuncin Sevilla.

    Bayern na kan gaba da ci 2-1 a karawar farko.

  3. Sakamakon wasannin yau, Roma da Liverpool sun kai labari

  4. An fitar da Barcelona, Roma 3-0 Barca (4-4)

  5. Liverpool ta fitar da City, Man City 1-2 Liverpool (1-5)

  6. An shiga karin lokaci a duk wasannin, Man City 1-2 Liverpool (1-5) Roma 3-0 Barca (4-4)

  7. Roma 3-0 Barcelona (4-4), Kostas Manolas

  8. Saura minti takwas, Man City 1-2 Liverpool (1-5)

  9. City ta ci kwallo amma an hana saboda sun yi satar gida, Man City 1-2 Liverpool (1-5)

  10. Man City 1-2 Liverpool, Firmino

    Pep Guardiola ya .dora hannu a ka

  11. An ba wa Luis Suarez katin gargadi saboda ba ta lokaci, Roma 2-0 Barca (3-4)

  12. Roma na ta kai kora, Roma 2-0 Barca (3-4)

    Roma na kara matsawa Barcelona lamba - ba kasafai ake ganin Barca a irin wannan yanayin ba.

    Idan Roma ya kara cin kwallo daya ba tare da Barcelona ta zira ko daya ba to shi ke nan an fitar da ita.

  13. Agüero ya shigo ya karbi David Silva, Man City 1-1 Liverpool (1-4)

  14. Roma 2-0 Barca (3-4), Daniele de Rossi (minti 58) fanareti

  15. Murnar kwallon Salah, Man City 1-1 Liverpool (1-4)

  16. Man City 1-1 (1-4), Mohamed Salah

  17. An dawo daga hutun rabin lokaci, Man City 1-0 Liverpool, Roma 1-0 Barca

  18. An hukunta Guardiola, Man City 1-0 Liverpool (1-3)

    An kura Pep Guardiola cikin 'yan kallo sabodsa ya yi wa alkalin wasa korafin kan kwallon da Sane ya ci wacce aka hana sabodsa satar gida.

  19. An tafi hutun rabin lokaci, Man City 1-0 Liverpool (1-3)

  20. An tafi hutun rabin lokaci, Roma 1-0 Barca (2-4)