Kwamatin Tsaro na MDD zai yi zaman gaggawa kan harin Isra'ila a Rafah
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 28 ga watan Mayun, 2024.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail, Haruna Kakangi and A'isha Babangida
Rufewa
To jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa wanda muke kawo muku labarai kai tsaye, a nan za mu dakata, yau Talata.
Sai kuma gobe Laraba 29 ga watan Mayu, 2024, idan Allah Ya kai mu lafiya za mu sake dawowa tun da safe.
Kafin sannan a madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad, nake mana fatan alheri mu kwana lafiya.
Ga wani karin magana mu ƙaru da shi - Mahauta biyu mai raba hankalin ƙuda
'Rashin kuɗi ne ya hana Shugaba Tinubu naɗa sababbin jakadu'
Asalin hoton, AMB. YUSUF TUGGAR/TWITTER
Ministan harkokin waje na Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce rashin isasshen kuɗi ne ya haifar da jinkiri wajen naɗa jakadun ƙasar a ƙasashe.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron bayanin ayyukan ma'aikatun gwamnatin ƙasar a yau Talata a Abuja, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fuskantar babbar matsalar kuɗi da ta tattalin arziƙi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tun bayan da shugaban ƙasar ya mayar da dukkanin jakadun ƙasar na waje a ranar 2 ga watan Satumban 2023, bai naɗa wasu sababbi ba.
Wannan ne ya sa ake nuna damuwa kan tafiyar da harkokin ofisoshin jakadancin na Najeriya a ƙasashen duniya.
Ministan ya ce babu amfanin a tura jakadun ba tare da samar musu kudaden tafiyar da ayyukansu da kuma ofisoshin ba.
Sai dai Amabassada Tuggar ya ce gwamnati na aiki kan matsalar kuma za a magance ta nan da wani lokaci.
'Dalilin da ya sa muka yi watsi da naira dubu 60 albashi mafi ƙanƙanta'
A Najeriya, manyan ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar, wato NLC da TUC, sun yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin
tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.
A ranar Talatar nan ne dai ƙungiyoyin biyu suka yi wani zama da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.
Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku
a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.
Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a
matsayin albashi mafi ƙanƙanta.
Kwamared Kabiru
Ado Minjibir, mataimakin shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar, wato
NLC, ya yi ƙarin bayani game da yadda taron ɓangaren gwamnatin da na ƴan ƙwadagon ya kaya, a hirarsa da AbdusSalam Ibrahim Ahmed.
Isra'ila ta ce makaman da aka ɓoye ne suka haddasa wutar sansanin Falasɗinawa
Asalin hoton, Reuters
Sojojin Isra'ila sun ce binciken da suka yi ya nuna cewa wutar da ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar Rafah a ranar Lahadi, ta tashi ne saboda makaman da aka boye a wajen.
Gomman Falasdinawa ne suka mutu a harin wanda ya janyo ce-ce-ku-ce daga ƙasashen duniya.
Kakakin Sojin Isra'ila Daniel Hagari ya ce 'yan makaman da suka harba sun yi ƙanƙanta su tayar da wannan wutar da ta tashi.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa kan wannan lamari.
Tashar jirgin ruwa ta wucin-gadi ta kai tallafi Gaza ta lalace
Asalin hoton, Reuters
Jami'an Amurka sun ce igiyar ruwa ta lalata tashar bakin ruwan da aka samar ta wucin-gadi domin shigar da kayan agaji Gaza.
An ambato wasu jami'ai na cewa zai ɗauki aƙalla mako biyu kafin a gyara gadar da ba ta fi mako biyu da fara aiki ba.
An dakata da aikin agaji kwana biyu da suka gabata, lokacin da Falasdinawa da ke cikin matsananciyar buƙata suka sa wawa kan kayan da ake rabawa.
Shugaba Biden ne ya bayar da umarnin a gina gadar a watan Maris, a matsayin wata hanya ta daban da za a rika shigar wa Gaza da kayan taimako.
Shugaban Faransa ya nemi a ba Ukraine damar kai hari cikin Rasha
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ya kamata a bai wa Ukraine damar kai hari sansanin sojin Rasha matukar aka yi amfani da su aka harba makami mai linzami zuwa kan iyakarta.
Mafi yawan ƙasashen da suke bai wa Ukraine makamai, suna gindaya mata sharaɗin kada ta kai hari cikin Rasha da makaman.
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Yens Shtoltenburg ya nemi a cire sharudan da aka sanya wa Ukraine kan amfani da makaman.
Haka kuma Macron ya nuna goyon bayansa kan wannan shawara.
Shugaban Vladmir Putin na Rasha ya gargadi ƙananan ƙasashe kan tsoma baki cikin wannan lamari.
Shugaba Putin ya ce wakilan kasashen NATO na Turai musamman ƙananan ƙasashe,za su shiga ɗanɗana kuɗarsu kan abin da suke neman wasa da shi.
A cewar shugaban Rasha ba kanwar lasa ba ce.
Jam'iyyun Netherlands sun tsayar da mai adawa da Musulunci takarar Firaminista
Asalin hoton, EPA
Jam'iyyun siyasa a Netherlands sun zaɓi mutumin da suke son ya zama sabon Firaministan kasar a nan gaba.
Dick Schoof shi ne tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar, kuma yanzu yana cikin manyan jami'an ma'aikatar shari'a ta Netherlands.
An zaɓe shi ne a matsayin dan takarar sasanci, bayan jam'iyyun haɗaka sun ƙi amincewa da shugaban masu ra'ayin riƙau a matsayin dan takararsu.
Jam'iyyarsa ta PVV mai ƙin addinin Ismala ita ce ta zo ta ɗaya a zaɓen da aka yi a watan Nuwamba.
Mista Schoof ya ce zai yi aiki ga duka mutanen Netherlands idan aka zaɓe shi.
Zelensky ya nemi Biden ya halarci taron ƙolin Ukraine
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya nemi shugaban Amurka, Joe Biden da ya halarci taron ƙolin zaman lafiya da za a yi a ƙasar Switzerland a tsakiyar Yuni.
Mista Zelensky ya ce rashin halartar babban abokinsa zai zama abin dariya ga Vladimir Putin na Rasha.
Rahotanni na cewa akwai yiwuwar shugaba Biden da mataimakiyarsa, Kamala Haris ba za su halarci taron ƙolin ba .
Duk da dai ana sa ran samun wakilci daga Amurka, amma rashin halartar shugaban za ta kasance wani abin da zai cusguna wa Ukraine.
Taron dai wanda aka daɗe ana tsarawa, za a yi shi ne a wani otal ɗin alfarma na Burgenstock. Wannan na zuwa ne bayan da Mista Zelensky ya shawarci tsohon shugaban ƙasar Switzerland, Alain Berset cewa ƙasar ta Switzerland wadda 'yar ba-ruwanmu ce ita ya kamata ta karɓi baƙuncin taron.
Ronaldo na fatan taka rawar gani a Euro 2024
Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo na fatan ya taka rawar gani a Euro 2024 da za a gudanar a Jamus tsakanin Yuni zuwa Yuli.
Za buga babbar gasar tamaula ta duniya ta 11 a karon farko bayan da ya fara buga Euro 2004
Mai shekara 39 ya ci ƙwallo 128 a wasa 206 da ya buga wa Portugal.
Zai taka leda a gurbin da ya hada da ɗan wwasan Paris Saint-Germain, Goncalo Ramos da tsohon ɗan ƙwwallon, Barcelona da Chelsea, Joao Felix da na Liverpool, Diogo Jota da na AC Milan, Rafael Leao.
Ƙwazon Ronaldo a Saudi Arabia da Messi a Amurka
Asalin hoton, gett
Cristiano Ronaldo ya ci ƙwallo 64 a wasa 69 tun bayan da ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia a Janairun 2023, wanda ya ɗora a kan sana'arsa ta tamaula tun daga Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus.
Bayan da ya bar Old Trafford wata 16 da ta gabata, haka kuma watanni tsakani ƙyaftin ɗin tawagar Argentina, Lionel Messi ya bar Paris St Germain zuwa Inter Miami mai buga Major League Soccer.
To sai dai tun bayan da dukkansu suka bar tamaula a nahiyar Turai, yaya ƙwazon Ronaldo yake a Saudi da na Messi a Amurka?
Kamar yadda Ronaldo ya ci ƙwallo matsakaici 0.93 a kowanne wasa, haka shima Messi ke taka rawar gani, wanda ya zura 27 a Inter Miami, kenan yana cin 0.85 a duk wasa. Labaran wasanni kai tsaye
Fafaroma Francis ya nemi afuwa ga masu neman jinsi guda
Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Francis ya nemi afuwa sakamakon wasu rahotanni da suka alaƙanta shi da yin amfani da kakkausan harshe ga masu neman jinsi guda.
A wata sanarwa da daga fadar Vatican, Fafaroman ya ce ba shi da nufin cin zarafin wani ko wata sannan ya nemi afuwar waɗanda ' kalaman nasa suka ɓata wa rai".
Rahotanni dai sun rawaito yadda Fafaroman, a yayin wani taron fada-fada da aka yi a Italiya, ya ce ba za a bar 'yan luwaɗi su shiga sahun waɗanda za a horar domin zama limaman coci.
An dai yi taron ne a ɓoye to amma kuma kafafen watsa labarai sun kwwarmata shi.
Sanarwar ta fadar Vatican ta ce Fafaroma Francis yana sane da labaran da suke fitowa dangane da tattaunawar da ya yi da fada-fada...a ɓoye,".
Da farko dai wata jaridar ƙasar Italiya ce ta intanet mai suna Dagospia ta fara buga labarin kafin daga bisani sauran jaridun ƙasar da kamfanonin dillancin labarai su ɗauka.
Aƙalla mutum 64 sun jikkata a harin Rafah na yau
Bayanai da ke fitowa daga Rafah na cewa harin da Isra'ila ta kai birnin a yau da rana ya yi sanadin mutuwar mutum 21 sannan 64 sun jikkata a kudancin birnin Gaza, in ji ma'aikatar lafiya.
Mai magana da yawun shugaban Falasɗinawa, Nabil Abu Rudeineh ya yi magana dangane da hare-haren na yau a Rafah, inda ya bayyana shi da "kisan gilla" kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya rawaito.
Harin Rafah yana da matuƙar tayar da hankali - Cameron
Ministan harkokin waje kuma tsohon firaiministan Burtaniya, David Cameron ya ce harin da aka kai Rafah ranar Lahadi na da tayar da hankali.
"Muna kira da a yi bincike da gaggawa," Cameron ya shaida wa 'yan jarida, inda ya ƙara da cewa su kansu 'yan Isra'ila "sun amince cewa babban kuskure ne".
Cameron ya ƙara da cewa suna son su ga an samu tsagaita wuta sannan a saki waɗanda ake garkuwa da su a kuma tabbatar da shigar kayan agaji zuwa Gaza.
Ya ƙara da cewa yana goyon bayan tsarin ƙasashe biyu wato na Falasdinawa da Isra'ila a matsayin hanyar warware taƙaddamar amma kuma ya ce ba wannan ne ya kamata ya zo a farkon al'amarin ba.
Kotu ta yi gargaɗi kan cusgunawa Sarki Muhammdu Sanusi II
Asalin hoton, Kano EMirate Council
Wata babbar kotun jihar Kano ta yai gargaɗi kwamishinan 'yan sandan jihar da Sifeto janar na 'yan sandan Najeriya da darektan jam'ian tsaro na DSS da hafsan hafsoshin Najeriya da kuma sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da su guji cusgunawa Sarkin kano Muhammadu Sanusi II.
Takardar kotun mai ɗauke da sa-hannun rijistarar kotun, Umar Mustapha, ta yi ƙarin bayani kan abin da take nufi da cusgunawa da ta haɗa da ƙoƙarin fitar da Sarki Sanusi daga gidan Rumfa ko ƙwace tagwayen masu ko kuma duk wani abun da zai janyo wulaƙanci ga Sarkin.
Asalin hoton, Kano court
Asalin hoton, Kano court
China ta koka kan hare-haren da 'yan Houthi ke kai wa jiragen ruwa
Asalin hoton, Reuters
China ta yi kira a kawo ƙarshen hare-haren da 'yan tawayen ƙungiyar Houthi ke kai wa jiragen dakon kaya a Tekun Maliya.
Ministan harkokin wajen kasar da ta fi fitar da kayan abinci a duniya, Wang Yi, ya tattauna da takwaransa na gwamnatin Yemen da ke yaki da 'yan tawayen.
Ya ce Beijing na son taka rawar gani wajen tabbatar da aminci a duka mashigun da ke tekun na Maliya.
Ƙungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran, ita ke da iko da mafi yawan yankunan ƙasar ta Yemen.
Tun a watan Nuwamba ta fara kai wa jiragen dakon kayayyaki hare-hare a matsayin martani kan yakin da ake yi a Gaza.
Labarai da dumi-dumi, Majalisar Dattawan Najeriya ta janye dakatarwar da ta yi wa Abdul Ningi
Asalin hoton, Nigerian Senate
Majalisar Dattawan Najeriya ta yafe wa Sanata Abdul Ahmed Ningi tare da janye dakatarwar da ta yi masa tun daga ranar 12 ga watan Maris.
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan Sanata Abba Moro ya gabatar da ƙudirin neman afuwarta a madadinsa kuma "ya ɗauki alhakin dukkan" abin da ya faru a zaman da suka yi yau Talata.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya siffanta Ningi a matsayin "mai hazaƙa" kuma ya ce sun ɗauki matakin ne "ba tare da nuna ɓangaranci ba".
Dakatarwar da aka yi wa sanatan mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya ta tsawon wata ta jawo cecekuce a majalisar da ma faɗin ƙasar a watan Maris.
Ƙudirin da majalisar ta zartar a lokacin ya zargi Abdul Ningi da "zubar da ƙimar majalisa" bayan ya zargi shugabanninta da sake yin wani kasafin kuɗi na 2024 bayan wanda 'yan majalisar suka amince da shi a bainar jama'a.
Dalilin da ya sa majalisa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi
Ireland, Sifaniya, Norway sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance
Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Ireland ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda ta bi sawun Sifaniya da Norway, waɗanda suka yi hakan a safiyar yau.
"Gwamnati ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci da kuma cin gashin kanta, kuma mun yarda za mu ƙulla alaƙar difilomasiyya tsakanin Dublin da Ramallah," a cewar wata sanarwa.
Za a tura jakadan Ireland zuwa Falasɗinu "tare da cikakken Ofishin Jakadancin Ireland a Ramallah," in ji sanarwar.
Ita ma Norway ta yabi matakin da ta ɗauka a matsayin "rana ta musamman", inda Ministan Harkokin Waje Espen Barth Eide ya ce ƙasarsa na cikin waɗanda suka fi goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinawa sama da shekara 30".
"Irin wannan rana da Norway ta amince da ƙasar Falasɗinawa a hukumance ta musamman ce a alaƙar ƙasashen," a cewar Eide, yana mai cewa "abin takaici ne yadda gwamnatin Isra'ila ta gaza wajen nuna kyakkyawar niyya" wajen cimma ƙasa biyu.
Sifaniya kuwa ta amince da Falasɗinu ne bayan majalisar ministoci ta amince da hakan, in ji mai magana da yawun gwamnatin ƙasar.
Pilar Alegria ta ƙara da cewa majalisar "ta amince da mataki mai muhimmanci na amincewa da ƙasar Falasɗinu, wanda ke da manufa ɗaya tilo: don taimaka wa yunƙurin zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila".
Firaministan Sifaniya Pedro Sanchez ya faɗa kafin ya gana da majalisar tasa cewa "amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba abin tarihi ba ne kawai...sharaɗi ne na cimma zaman lafiya".
Firaministan Ireland Simon Harris ya ce kafa ƙasa biyu ta Isra'ila da Falasɗinawa "ita ce hanya ɗaya da Isra'ila da Falasɗinawa za su rayu kafaɗa da kafaɗa cikin aminci".
Da safiyar yau Talata ya ce akwai wani sabon salo "abin ƙyama kuma maras daɗin ji" inda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kwatanta kisan Falasɗinawa da "'tsautsayi'".
Harris na magana ne kan harin Isra'ila a sansanin gudun hijira da ya kashe aƙalla mutum 45 ranar Lahadi.
An zaɓi Sheikh Maher Al Muaiqly wanda zai yi huɗubar Arafa ta bana
Asalin hoton, Inside Haramain
Hukumar kula da Masallatan Harami a Saudiyya ta sanar da sunan limamin da zai jagoranci huɗubar aikin Hajji na bana.
Kafar yaɗa labarai ta Inside Haramain ta ruwaito cewa limamin Harami Sheikh Maher Al Muaiqly ne zai jagoranci huɗubar, wadda za a gudanar ranar 9 ga watan Zul Hijjah na kalandar Musulunci.
Sai dai ba za a tabbatar da ranar da za a hau Arafa ba har sai an ga watan na Zul Hijjah.
Makarantar gwamnati da iyaye ke ɗaukar malamai aiki a Kano
Ireland ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance
Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Ireland ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda ta bi sawun Sifaniya da Norway, waɗanda suka yi hakan a safiyar yau.
"Gwamnati ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci da kuma cin gashin kanta, kuma mun yarda za mu ƙulla alaƙar difilomasiyya tsakanin Dbulin da Ramallah," a cewar wata sanarwa.
Za a tura jakadan Ireland zuwa Falasɗinu "tare da cikakken Ofishin Jakadancin Ireland a Ramallah," in ji ta.
Firaministan Ireland Simon Harris ya ce kafa ƙasa biyu ta Isra'ila da Falasɗinawa "ita ce hanya ɗaya da Isra'ila da Falasɗinawa za su rayu kafaɗa da kafaɗa cikin aminci".
Da safiyar yau Talata ya ce akwai wani sabon salo "abin ƙyama kuma maras daɗin ji" inda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kwatanta kisan Falasɗinawa da "'tsautsayi'".
Harris na magana ne kan harin Isra'ila a kan sansanin gudun hijira da ya kashe aƙalla mutum 45 ranar Lahadi.