Ƙwazon Ronaldo a Saudi Arabia da na Messi a Amurka

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku irin abubuwan dake faruwa a fagen wasanni a fadin duniya a ranar irin ta Talata 28 ga watan Mayun 2024

Taƙaitattu

  • Ƙwazon Ronaldo a Saudi da na Messi a Amurka
  • Anthony Martial zai bar Man United
  • Ko Southampton za ta taka rawar gani a Premier?
  • Maresca na son karbar aikin horar da Chelsea

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan za ku tara ranar Laraba, domin wani shirin.

    Sunana Mohammed Abdu, Mamman Skepper Tw.

    Sai ku kasance a shirin Labaran wasanni a daren nan da na Hantsi a gobe Laraba.

  2. Ronaldo na fatan taka rawar gani a Euro 2024

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Cristiano Ronaldo na fatan ya taka rawar gani a Euro 2024 da za a gudanar a Jamus tsakanin Yuni zuwa Yuli.

    Za buga babbar gasar tamaula ta duniya ta 11 a karon farko bayan da ya fara buga Euro 2004

    Mai shekara 39 ya ci ƙwallo 128 a wasa 206 da ya buga wa Portugal.

    Zai taka leda a gurbin da ya hada da ɗan wwasan Paris Saint-Germain, Goncalo Ramos da tsohon ɗan ƙwwallon, Barcelona da Chelsea, Joao Felix da na Liverpool, Diogo Jota da na AC Milan, Rafael Leao.

  3. Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan da Cristiano Ronaldo ya lashe takalmin zinare a matakin wanda yafi cin ƙwallaye a gasar tamaula a Saudi Pro League, ya zama na farko da ya lashe irin wannan ƙyautar a gasa hudu da ban a lik.

    Ya lashe takalmin zinare a 2007-08 a Premier League a Manchester United.

    A Real Madrid, Ronaldo ya dauki Pichichi Trophy karo uku.

    Haka kuma ya lashe kyautar a Serie A da ake kira ta Paolo Rossi Award a 2020-21.

  4. De Bruyne da Doku suna cikin tawagar Belgium zuwa Euro 2024

  5. Ronaldo na taka rawar gani a Saudi Arabi

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin cin ƙwallo a Saudi Pro League bayan da ya ci wa Al-Nassr biyu a karawar da ta doke Al-Ittihad, kenan ya zura 35 a raga.

    Mai shekara 39 ya haura yawan na Abderrazak Hamdallah mai 34 a kakar 2018-19.

    Kenan Ronaldo ya ci ƙwallo 64 a wasa 69 a Al-Nassr a dukkan fafatawa tun bayan da ya koma kungiyar cikin Janairun 2023 bayan da ya bar Manchester United.

  6. McKenna zai sa hannu kan sabuwar yarjejeniya a Ipswich Town

    McKeana

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran Kieran McKenna zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar da zai ci gaba da jan ragamar Ipswich Town, wadda za ta buga Premier League a badi.

    Mai shekara 38 yana cikin wadanda Chelsea ta so ɗauka, domin ya maye gurbin Mauricio Pochettino an kuma alakanta shi da aikin jan ragamar Brighton.

    Shi ne gwwarzon koci da aka zaba a bana, bayan da ya dawo da Ipswich Town babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan shekara 22 rabonta da gasar.

  7. Tawagar Serbia ta sanar da ƴan wasan da za ta je da su Euro 2024

    Serbia

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Serbia, Dragan Stojkovic ya sanar da ƴan wwasa 26 da zai je da su Euros 2024.

    Cikin wadanda ya bayyana har da golan Chelsea, Dorde Petrovic da ɗan wasan Fulham, Sasa Lukic har datsohon ɗan ƙwallon Fulham, Aleksandar Mitrovic da na Juventus, Dusan Vlahvoic.

    Za ta fara wasan farko da Ingila ranar 16 ga watan Yuni a Gelsenkirchen.

    Masu tsaron raga: Rajkovic, Milinkovic-Savic, Petrovic

    Masu tsaron baya: Gudelj, Milinkovic, Pavlovic, Mladenovic, Veljkovic, Spajic, Babic, Stojic

    Masu buga tsakiya: Tadic, Kostic, Milinkovic-Savic, Maksimovic, Zivkovic, Gacinovic, Ilic, Mijailovic, Samardzic, Birmancevic

    Masu cin ƙwallo: Mitrovic, Jovic, Vlahovic, Ratkov

  8. Belgium ta bayyana ƴan wasa 25 da za ta je da su Euro 2024

    Romelu Lukaku

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne da Jeremy Doku suna cikin tawagar Belgium da za ta je da su Euro 2024, amma ba golan Real Madrid, Thibaut Courtois a ciki.

    Cikin ƴan wasa 25 da aka bayyana yawancinsu suna buga Premier League da ya hada da na Arsenal, Leandro Trossard da na Aston Villa, Youri Tielemans.

    Sauran sun hada da na Everton, Amadou Onana da na Leicester City, Wout Faes da kuma na Fulham, Timothy Castagne.

    An yi mamaki da aka ji an bayyana sunan ɗan wasan Atletico Madrid, Axel Witsel, mai tsaron baya mai shekara 35, wanda ya sanar da yin ritaya a bara.

  9. Tarihin Maresca a fannin ƙwallon kafa zuwa horar da

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Enzo Maresca ya taka leda daga 1998 zuwa 2017, wanda ya taka leda a manyan ƙungiyoyin Turai ciki har da Juventus da West Brom da kuma Sampdoria.

    Maresca ya yi ritaya daga taka leda shekara bakwai da ta wuce, sannan ya fara aikin horar da tamaula a Ascoli.

    Bayan kaka ukun da ya yi a ƙungiyar Italiya sai ya koma Manchester City a matakin mai bunkasa wasannin City.

    Daga nan ya samu ci gaba bayan da City ta lashe Premier League a 2021, hakan ya sa Parma ta dauke shi aiki, koda yake daga baya ta sallame shi, bayan da ta kasa samun hawa matakin gaba.

    Daga nan ya sake komawa Etihad, amma a matakin mataimakin Pep Guardiola, haka kuma bayan da City ta lashe Premier League, sai Leicester City ta dauke shi aiki lokacin da ta fadi a bara daga babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Yanzu ya kai Leicester City gurbin Premier League da za buga a badi da lashe kofin Championship, kuma Chelsea na fatan ta bashi aiki.

  10. Ƙwazon Ronaldo a Saudi Arabia da Messi a Amurka

    Live Page

    Asalin hoton, Getty Images

    Cristiano Ronaldo ya ci ƙwallo 64 a wasa 69 tun bayan da ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia a Janairun 2023, wanda ya ɗora a kan sana'arsa ta tamaula tun daga Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus.

    Bayan da ya bar Old Trafford wata 16 da ta gabata, haka kuma watanni tsakani ƙyaftin ɗin tawagar Argentina, Lionel Messi ya bar Paris St Germain zuwa Inter Miami mai buga Major League Soccer.

    To sai dai tun bayan da dukkansu suka bar tamaula a nahiyar Turai, yaya ƙwazon Ronaldo yake a Saudi da na Messi a Amurka?

    Kamar yadda Ronaldo ya ci ƙwallo matsakaici 0.93 a kowanne wasa, haka shima Messi ke taka rawar gani, wanda ya zura 27 a Inter Miami, kenan yana cin 0.85 a duk wasa.

  11. Ƙwazon da Aston Villa ta yi a 2023/24

    Aston Villa ta kare a mataki na hudu a teburin Premier League, bayan kammala kakar bana 2023/24.

    Hakan ya sa ƙungiyar ta samu gurbin shiga Champions League a karon farko a tarihi da Unai Emery ya kai ƙungiyar.

    Ta samu nasarar ce, sakamakon wasu nasarorin da ƙungiyar da ta yi a kakar nan.

    Ciki har da canjaras a karawa da Chelsea da kuma Liverpool da yin nasara a kan Arsenal 2-0.

    Haka kuma ƙungiyar ta buga Europa Conference League a bana, inda ta kai zagayen daf da karshe, inda Olympiacos ta yi nasara 6-2 gida da waje..

  12. Emery ya yi murnar da ya kara tsawaita kwantiragi a Aston Villa

    Unai Emery

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Aston Villa, Unai Emery ya saka hannu don ci gaba da jan ragamar ƙungiyar Villa Park zuwa kaka biyar, kamar yadda mai buga Premier League ta sanar.

    Ɗan kasar Sifaniya ya kai Aston Villa mataki na hudu a teburin Premier League a bana, hakan ya sa za ta buga Champions League a badi.

    Emery ya sauya fasalin taka ledar Villa tun bayan da ya karbi horar da ƙungiyar a cikin Oktoban 2022 a lokacin da take da tazarar maki uku tsakani da ƴan ukun karshen teburi.

    Mai shekara 52, ya koma Villa da burin kai ƙungiyar gasar zakarun Turai, wanda ya lashe Europa League hudu, bayan ƙwazon da ya yi a Sevilla da Villarreal.

  13. Maresca na son komawa Chelsea

    Wasu rahotanni na cewa Chelsea za ta tattaunawa da mai horar da Leicester, Enzo Maresca, domin ya zama sabon kociyanta.

    Ɗan kasar Italiya, ya yiwa Pep Guardiola mataimaki a Manchester City, wanda ya ja ragamar Leicester City zuwa Premier League da lashe Championship a bana.

    A bara ne ƙungiyar King Power ta bar babbar gasar tamaula ta Ingila tare da Southampton da kuma Leeds United.

    Chelsea ta yaba da salon yadda kociyan ke horar da tamaula, domin ya maye gurbin Mauricio Pochettino, wanda ya yi aikin kaka daya a Stamford Bridge.

  14. Barkanmu da kasancewa a wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw, zan gabatar da muku da labarin wasanni kai tsaye a wannan shafin.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa kai tsaye a lokacin da nake gabatar da shirin kai tsaye a BBC Hausa Facebook da kuma Twitter.