Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/05/2024
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 26 ga watan Mayun, 2024.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Aisha Shariff Bappa
Yara biyu sun mutu sakamakon rushewar masallaci a Legas
Yara mata biyu sun rasu yayin da wasu mutum biyar suka samu raunuka a yau Lahadi sanadiyyar rushewar wani masallaci a unguwar Papa Ajao da ke birnin Legas.
Daya daga cikin manyan jami’an Hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas, Olatunde Akinsanya, ya bayyana wa manema labaru cewa daya daga cikin yaran da suka rasu ta rasa ranta ne nan take a inda lamarin ya faru yayin da dayar ta rasu a lokacin da aka isa da ita asibiti.
Masallacin mai hawa biyu ya rufta ne bayan wata motar rushe gine-gine da ke aikin fadada titi ta tokare shi bisa kuskure.
Hukumar Lasema ta tabbatar wa BBC cewa mutum bakwai ne aka zakulo daga cikin baraguzan masallacin.
Babbar jam'iyyar adawa a Afirka ta Kudu ta zargi jam'iyya mai mulki da gazawa a aiki
Babbar jam'iyar adawa ta Afrika ta Kudu Democratic Alliance ta gabatar da yaƙin neman zaɓen ta na ƙarshe gabanin babban zaɓen ƙasar da za a yi a ranar Laraba.
Shugabannin Jam'iyar sun soki jam'iyya mai mulki ta ANC da gazawa wajen cika alƙawurran da ta yi wa al'ummar ƙasar na samar da ayyukan yi da gidaje.
Rahotanni na cewa yawancin magoya bayan jam'iyar adawa ta DA sun fito ne daga tsirarun al'ummar ƙasar da ake nunawa wariyar launin fata.
Southampton ta samu tikitin shiga Premier League ta 2024/25
Asalin hoton, Getty Images
Southampton ta samu gurbi na uku na shiga Premier League a badi, bayan da ta ci Leeds United 1-0 a wasan cike gurbi ranar Lahadi a Wembley.
Minti na 21 da take leda ne Southapton ta ci kwallo ta hannun Adam Armstrong, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye a Championship a bana.
Ana buga karawar cike gurbi tsakanin wadda ta yi ta uku a kakar wato Leeds United mai maki 90 da wadda ta yi ta hudun teburi Southampton mai maki 87.
Da wannan sakamakon Southampton ta samu gurbi na uku, bayan da ta lashe kofin cike gurbi ranar Lahadi.
Leicester City ta lashe kofin Championship na bana, wadda ta kare a matakin farko da maki 97, sai Ipswich Town ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani da ƙungiyar King Power.
Tun farko ƙungiyoyi uku ne daga Premier League a bana suka bar gasar da suka hada da Luton Town da Burnley da kuma Sheffield United.
Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano a Kotu
Asalin hoton, OTHER
Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano kwamared Aminu Abdulsalam a gaban kotu bisa zargin ɓata masa suna.
A ranar Asabar ne mataimakin gwamnan ya zargi Nuhu Ribadu ya shirya mayar da Alhaji Aminu Ado Bayero, zuwa Kano bayan gwamnan jihar ya sanar da matakin tuɓe shi.
Aminu Abdulsalam, ya zargi Nuhu Ribadun da samar wa Alhaji Aminu Ado Bayero jirage guda biyu domin su kai shi Kano.
To sai dai tun a jiyan Nuhu Ribadu ya musanta zargin kamar yadda mai magana da yawunsa ya shaida wa BBC.
A cikin wata wasiƙa da lauyoyinsa suka aike wa mataimakin gwamnan sun buƙace shi ya nemi afuwar Ribadun cikin sa'o'i 24.
Lauyoyin sun kuma buƙaci mataimakin ya fito ya nemi afuwar Ribadun a cikin manyan jaridun ƙasar biyar da fitattun kafafen sada zumunta ko kuma su gurfanar da shi a gaban kotu.
Matasa sun yi zanga zanga a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, 'Yan sanda
Wata sabuwar zanga zanga ta barke a Kano a daidai lokacin da ake cikin jayayya a kan sarautar a jihar.
Sarki Muhammadu Sanusi na II da kuma Alhaji Aminu Bayero da aka cire dukkanninsu na fafutukar ganin sun ci gaba da kasancewa a kan sarautar.
Dazu bayan Sallar la’asar , wasu matasa suka bi titunan jihar Kano inda suke bukatar a dawo da sarkin da aka cire.
Wasu daga cikinsu na kona tayoyi a kan manyan titunan jihar a yayin da suke maci suna rera wakokin habaici ga gwamnatin jihar.
Bayanai sun ce akwai jami’an ‘yan sanda a kasa amma kuma ba su yi wani yunkuri na tarwatsa masu zanga zangar ba.
A waje daya kuma Sarki Sanusi na ci gaba da zama a fada inda jama’a ke ci gaba da zuwa domin yi masa mubaya’a.
A daya bangaren kuma an girke motocin ‘yan şanda a kofar gidan şarkı da ke Nasarawa inda Alhaji Aminu Ado Bayero yake na shi zaman fadan
Isra'ila ta kashe fararen hula da dama a kudancin Lebanon
Kafar yada labaran Lebanon ta rawaito cewa fararen hula da dama ne aka kashe yayin da wasu kuma suka jikkata a wasu hare hare da jirage marassa matuka da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe 'yan kungiyar Hezbollah da dama a yankin Naqoura da kuma wasu a kan iyakar kauyen.
Kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ta ce ta kaddamar da wasu hare haren roka da na atilari a kan sojojin Isra'ila da ke yankin arewacin kasar.
Isra'ila da kuma Hezbollah wadda ke goyon bayan Hamas na musayar wuta tun bayan da aka fara yakin Gaza a watan Oktoban da ya gabata.
Sarakunan arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan halin da ake ciki a Kano
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar sarakunan arewacin Najeriya ƙarƙashin mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar lll, ta nuna damuwarta kan halin da ake ciki a Kano kan rikicin sarauta.
Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin hadin kan sarakunan arewacin ƙasar, wanda kuma shi ne sarkin Gummi, Alhaji Lawal Hassan Gummi, ta ce rikicin ka iya shafar tsarin sarauta a yankin.
''Majalisarmu na kira ga duka ɓangarorin su dubi masalahar zaman lafiya da kwanciyar hankali, su kai zuciya nesa, kasancewar batun na gaban kotu, don haka a kwantar da hankali'', in ji sanarwar.
Haka kuma Majalisar ta yi addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, a jihar Kanon.
A ranar Alhamis ne gwamnan jihar ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi ll kan karagar sarautar Kano bayan majalisar dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar kwaskwarima.
Sai kuma wata kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin sauraron shari'ar.
To amma ranar Juma'a sai gwamnan jihar ya miƙa wa Muhammadu Sanusi ll takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano.
Sai kuma kwatsam! A ranar Asabar aka wayi gari da wani turka-turka, bayan da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shi ne sarki kafin gyaran dokar, ya koma birnin tare da shiga gidan sarki da ke unguwar Nassarawa, bayan da Muhammadu Sanusi ll ya shiga fadar sarkin da ke Ƙofar Kudu.
Da safiyar Asabar ɗin ne dai gwamnan jihar ya umarci kwamishinan 'yan sandan Kano ya kama Alhaji Aminu Ado bisa zargin yunƙurin tayar da tarzoma a jihar.
To sai dai kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar 'yan sanda tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro za su yi biyayya ga umarnin kotu.
Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 26/05/24
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Real Madrid ta yi wa Kroos ban kwana a Santiago Bernabeu
MDD na fargabar ƙasa ta rufta wa mutum 670 a Papua New Guinea
Asalin hoton, Reuters
Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum 670 ne ƙasa ta binne sakamakon zaftarewar ƙasa da ta auku a ƙasar Papua New Guinea
Shugaban Hukumar Kula da 'yan Gudum Hijira na MDD a Papua New Guinea, Serhan Aktoprak, ya ce ɓarnar da zaftarewar ƙasar da ta auku ranar Juma'a a lardin Enga na ƙasar, ya zarta yadda ake tunani.
"Akwai gidaje fiye da 150 da aka yi ƙiyasin ƙasa ta rufe su," in ji Mista Aktoprak.
Mista Aktoprak ya ce masu aikin ceto na cikin hatsari, saboda har yanzu "ƙasar na ci gaba da zaftarewa".
Ya ƙara da cewa sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa a yankin, rayukan mutane na ci gaba da kasancewa cikin hatsari.
Akwai kimanin mutum 4,000 da ke zaune a yankunan da lamarin ya shafa.
To sai dai wata ƙungiyar agaji a yankin ta yi gargaɗin cewa adadin mutanne da lamarin zai shafa ka iya ƙaruwa saboda yawan mutanen da ke komawa yankin, don guje wa rikice-rikicen ƙabilanci a yankunansu.
EFCC na alhinin rasuwar Lamorde
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC ta nuna alhininta kan rasuwar tsohon shugabanta Ibrahim Lamorde.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kaɗu da jin labarin rasuwar Ibrahim Lamorde.
''Lamorde, wanda shi ne ya fara riƙe muƙamin daraktan ayyuka na hukumar EFCC, kuma shugaban hukumar n uku, ya kasance jajirtaccen namijin da ya yi wa Najeriya yaƙi ta hanyar EFCC,'' in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ''EFCC da Najeriya baki ɗaya sun yi rashin namiji''.
Da safiyar yau ne Ibrahim Lamorde ya rasu a Masar sakamakon wata jinya da yake yi.
Tsohon mataimakin Sifeton 'yan sandan Najeriyar, mai shekara 61, ya jagoranci hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Hamas ta harba makaman roka zuwa yankin Tel Aviv
Asalin hoton, HANDOUT
A karon farko cikin kusan wata huɗu ƙungiyar Hamas ta harba makamin roka zuwa yankin Tel Aviv da ke tsakiyar Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun ce aƙalla makaman roka takwas aka harba zuwa yankin Tel Aviv daga Rafah a kudancin Gaza, suna masu cewa sun samu nasarar kakkaɓo wasu daga ciki, sai dai babu rahoton jikkata.
Sojojin Isra'ila dai na ƙaddamar da hare-hare a Rafah.
An yi ta jin ƙarar ƙararrawar ankararwa a birane da garuruwan Isra'ila, ciki har da Herzliya da Petah Tikva.
Kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun wallafa bidiyon ɓarnar da makaman suka yi a wani gini a Herzliya. Wani bidiyon kuma ya nuna yadda wani ɗaki ya ruguje.
Wani bidiyon na daban ya nuna yadda faɗuwar wata roka ta haddasa wani ƙaton rami a wani fili a tsakiyar garin Kfar Saba.
Sashen soji na ƙungiyar Hamas 'al-Qassam' ya ɗauki alhakin abin da ya kira ''babban'' harin makami mai linzami zuwa birnin Tel Aviv a shafinta Telegram.
Birnin Tel Aviv, wanda shi ne cibiyar kasuwancin Isra'ila ya kasance birni mafi girma a ƙasar.
Hare-haren rokokin na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke ƙara zafafa hare-hare a Rafah, duk da hukuncin Kotun Duniya da ya nemi ta dakatar.
Manyan matsaloli takwas da ke addabar ƴan Afirka ta Kudu gabanin zaɓe
Rikicin Sudan: Fiye da mutum 120 sun mutu a birnin El Fasher
Ƙungiyar Likitoci ta 'Doctors Without Borders' ko MSF ta ce rikicin da ake yi a birnin El Fasher na ƙasar Sudan ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 120 tare da jikkata fiye da mutum 900, a rikicin da ya ɓarke kusan mako biyu da suka gabata.
A watan Afrilun shekarar da ta gabata ne yaƙi ya ɓarke a Sudan tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF, lamarin da ya yi sanadiyyar raba fiye da mutum miliyan takwas da muhallansu.
MSF ta ce abu ne mawuyaci a iya tantance adadin mutanen da suka mutu a El Fasher, saboda a cewarta adadin da take fitarwa na waɗanda suka mutu a asibitocin birnin ne kawai.
Mazauna birnin sun ce rokoki masu yawa da mayaƙan RSF suka harba sun sa mayaƙan sun ƙwace wasu sassan yankunan yammacin birnin.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da duka ɓangarorin biyu da masu goya musu baya da su gaggauta kiran tsagaita wuta.
An zargi ƙasashen duniya da dama ciki har da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ɗaukar ɓangare a rikicin.
An zargi Rasha da taimaka wa duka ɓangarorin biyu. Tana taimaka wa RSF domin ta samu zinare.
Sannan kuma babban hafsan sojin Sudan ya ce Rasha za ta taimaka musu da makamai da harsasai domin a ba ta damar kafa sansanin kayayyakin dabarun yaƙi a tekun Maliya.
SERAP ta buƙaci Tinubu ya bayyana kadarorinsa bayan shekara guda a mulki
Asalin hoton, Bayo Onnuga/X
Ƙungiyar SERAP mai Fafutukar Yaƙi da cin Hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da bikin cikarsa shekara guda a kan mulki wajen wallafa takardun kadarorin da ya mallaka.
Cikin wata buɗaɗdiyar wasiƙa da ƙungiyar ta aike wa shugaban ƙasar, ta ce wannan dama ce da shugaban ƙasar zai nuna wa 'yan ƙasar yadda yake son ci gaba dimokraɗiyya da nuna tsantseni da rashin rufa-rufa a gwamnatinsa.
Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasar, ya umarci mataimakinsa da ministoci da gwamnonin jihohin ƙasar domin su wallafa nasu takardun kadarorin da suka mallaka.
SERAP ta ce: “Muna so ka wallafa takardun mallakar kadarorinka, sannan ka umarci sauran jami'an gwamnati su ma su yi haka, saboda hakan zai ƙarfafa samar da cikakken tsarin gwamnati maras rufa-rufa a duka matakai.''
“Yin abubuwa a bayyane ba tare da rufa-rufa ba, kamar yadda yake ƙunshe cikin takardun bayyana kadarori, zai inganta tsarin dimokraɗiyya tare da tsantseni a duka matakan gwamnati'', in ji SERAP.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci shugaban ƙasar ya gaggauta bijiro da buƙatar yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima ta yadda za a saka dokar wallafa takardun mallakar kadarorin masu riƙe da muƙamai kafin su hau mulki da kuma idan suna kan mulki da bayan saukarsu.
Tsohon shugaban EFCC Ibrahim Lamorde ya rasu
Bayanan hoto, Lamorde ya jagoranci EFCC daga 2011 zuwa 2015
Tsohon shugabana Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.
Wata majiya mai kusanci da Lamorden ta tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa a ƙasar Masar inda yake jinyar wata rashin lafiya.
Tsohon mataimakin Sifeton 'yan sandan Najeriyar, mai shekara 61, ya jagoranci hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Da farko tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya naɗa shi a matsayin shugaban riƙo na hukumar a watan Nuwamban 2011, bayan sauke Farida Waziri.
Sai kuma a watan Fabrairun 2012, Mista Jonathan ya tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban hukumar bayan amincewar majalisar dattawan ƙasar.
Ibrahim Lamorde - ɗan asalin jihar Adamawa - ya kasance mutum na uku a jerin waɗanda suka jagoranci hukumar EFCC tun bayan kafuwarta.
A shekarar 2015 ne wani kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan zargin karkatar da dala biliyan biyar, da wasu kadarori da EFCC ta ƙwato a lokacin da yake jagorantar hukumar.
To sai dai a lokacin Ibrahim Lamorde ya musanta zargin yana mai cewa shure-shure ne kawai, kasancewar a lokacin EFCC ta gurfanar da mutumin da ya yi zargin.
A watan Nuwamban 2015 ne, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sauya shi da Ibrahim Magu.
Shirin na wannan makon - da Buhari Muhammad Fagge ya gabatar - ya amsa tambayoyi kan Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC da kuma harajin VAT.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Hajji 2024: NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan jihohin Najeriya biyar
Asalin hoton, NAHCON/X.
Bayanan hoto, Wasu daga cikin maniyyatan jihar Kebbi
Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON, ta ce ta kammala jigilar maniyyatan jihohin ƙasar biyar a jigilar maniyytan ƙasar da take yi zuwa ƙasa mai tsarki.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ya nuna ce kawo yanzu hukumar ta kammala kwashe maniyyan jihohin Kogi da Nasarawa da Edo da Oyo da kuma jihar Ogun.
Haka kuma hukumar ta ce ta kammala kwashe maniyyatan da suka biya ta hukumar rundunar sojin ƙasar.
Hukumar ta kuma ce kawo yanzu ta yi jigilar maniyyatan ƙasar fiye da 19,700.
Nahcon ɗin ta kuma ce tana dab da kammala kwashe maniyytan jihohin Yobe da Banchi da Osun da Legas da Kebbi da Abuja.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Masu zanga-zanga a Isra'ila sun yi arangama da 'yan sanda a Tel Aviv
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na adawa da gwamnatin Netanyahu
Masu zanga-zanga sun yi arangama da 'yan sandan Isra'ila a birnin Tel Aviv a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati na neman a dawo da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya ce sun fito ne don nuna adawa ga gwamnatin Firaminista Benjamin Natanyahu.
Ya ce dukkan mu a nan muna adawa da wannan mummunar gwamnatin, muna fatan za a rugaza ta domin mu sami damar yin zaɓe mu kuma ƙarfafa dimikradiyya.
An dai gudanar da irin wannan zanga-zangar a biranen ƙasar Isra'ila da dama a daren Asabar
Sojojin mulkin Burkina Faso sun tsawaita wa'adinsu
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré
Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta sanar da tsawaita mulkinta zuwa shekaru biyar.
Kafar yaɗa labaran gwamnati ta ce shugaban gwamnatin sojin ,kyaftin Ibrahim Traore, shi ma zai iya tsayawa takara a zaɓen shugaban kasa mai zuwa.
Gwamnatin ƙasar ta ɗauki wannan mataki ne bayan da aka amince da wani kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima a babban taron na ƙasa
A ranar Asabar ne shugaban gwamnatin sojin ƙasar Kayftin Ibrahim Traore ya sanya hannu kan kundin a Wagadugu babban birnin ƙasar, inda ya tsawaita wa'adinsa kan karagar mulki fiye da watanni 21.
A lokacin da sojojin suka yi juyin mulki ƙarƙashin jagorancinsa ya yi alkawarin mayar da ƙasar kan tafarkin dimukrodiyya a tsakiyar shekarar da mu ke ciki, sai dai ga dukkan alamu sai a shekarar 2029 ne mulki zai koma hannun farar hula.
Haka kuma sauye- sauyen da aka yi wa kudin tsarin mulki sun tabbatar da Captain Ibrahim Traoré a matsayin shugaban ƙasar Burkina Faso kuma babban kwamandan dakarun ƙasar har zuwa ƙarshen wa'adin gwamnatin riƙon ƙwarya wadda zai fara aiki daga ranar 2 ga watan Yuli mai zuwa.
Mahalarta taron sun kuma amince Kyaftin Traore da firaministan ƙasar da shugaban majalisar dokokin suna da 'yancin tsayawa takara a zaɓukan da za a yi nan gaba a karshen wa'adin watanni na gwamnatin rikon ƙwaryar.
Sai dai shawarar da aka yanke a taron tuntunbar, an yi ta cikin hanzari inda wasu kafofin yaɗa labaran cikin gida suka ruwaito rashin halartar jam'yyun siyasar kasar a farkon taron.
Burkina Faso na ƙarƙashin mulkin sojoji tun shekarar 2022, kuma ƙasar na fuskantar ƙalubale wajan daƙile hare haren mayaƙa masu tayar da ƙayar baya da ake da alaƙa da kungiyoyin al - Qaeda da IS.
Kyaftin Traore ya sha gargaɗin cewa abu ne mai wuya a gudanar da zaɓe idan aka dubi matsalar tsaro da ake fuskanta a arewacin ƙasar sakamakon hare-haren mayaƙa.
A yanzu Burkina Faso ta bi sahun Mali - wadda ita ma - ta tsawaita wa'adin mukin gwamnatin sojin ƙasar.