Bankwana
Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai riƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ahmad Tijjani Bawage and Buhari Muhammad Fagge
Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na yau.
Hukumomi a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo sun ce adadkin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa ya kai 176.
Gwmannan Kudancin Kivu ya ce har yanzu akwai ƙarin mutanen da ba a ƙirga ba, waɗanda ake fargabar sun nutse a cikin ƙasa.
Ƙauyukan Bushushu da Nyamukubi sun tafi babu komai a cikinsu, sakamakon kogunan da suka cika suka batse a yankin gabashin ƙasar.
An samu rahoton zabtarewar ƙasa da ta lalata gidaje da gine-gine masu yawa.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun rawaito cewa sama da kashi uku na wani ƙauye ya ruhse ciki har da makarantu da kuma cibiyoyin lafiya.
Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya bayyana rashin jin daɗin sa game da sakamakon da jam`iyyar sa ta Conservative Party ta samu a zaɓen ƙananan hukumomi.
Ya ce sakamakon da aka samu yanzu ya yi wuri, amma zai ci gaba gabatar da abubuwan da jama’a suka sa a gaba, kamar rage hauhawar farashin kayayyaki da haɓɓaka tattalin arziƙi da rage bashi da kuma dakatar da jiragen ruwa masu shigowa da ƴan cirani.
Zaɓen ya kasance na farko kuma gwaji ga mista Sunak wanda ya zama Firamanista a watan Oktoban bara.
Jam`iyyun Labour da Liberal masu adawa sun yi nasara a zaɓen wajen samun mafi yawan kujerun majalisar.
An kama wani mutum ɗan ƙasar Kanada a yankin da ake kira British Columbia, bayan ya buɗe kantin tafi-da-gidanka na sayar da hodar iblis da kokino da sauran miyagun ƙwayoyi.
Jerry Martin, mai shekara 51, ya ce zai ƙalubalanci kamun da 'yan sanda suka yi masa a kotu.
'Yan sandan Vancouver sun ce sun kama mutumin ne bisa zargin "alaƙa da fasa-ƙwaurin ƙwaya da kuma haramtaccen shagon sayar da ƙwayoyi" ko da yake ba su shigar da tuhume-tuhume a hukumance ba.
Kama Jerry Martin a ranar Alhamis na zuwa ne kwana daya, bayan ya bude shagonsa na kayan maye.
Ya fara sayar da ƙwaya ne ranar Laraba a wani shago da ya buɗe a bayan motar tirela a Downtown Eastside da ke Vancouver, wata unguwar talakawa da ake samun masu yawan amfani da ƙwaya da kuma yawan cibiyoyin hana shan ƙwaya fiye da kima.
Mista Martin wanda wani ɗan'uwansa ya mutu sanadin shan ƙwaya fiye da kima ya ce ya yi niyyar buɗe shagonsa ne bayan hukumomin Kanada sun soke haramci a kan mallakar miyagun ƙwayoyi 'yan kaɗan a lardin Birtish Columbia farkon wannan shekara.
Matakin wani ɓangare ne na wani shirin gwajin dafi na tsawon shekara uku.
An ɓullo da matakin kare lafiyar al'ummar ne don mayar da martani kan ƙaruwar mace-macen masu shan ƙwaya fiye da kima sanadin kayan mayen da ake haɗawa da ƙwayar fentanyl a yammacin Kanada.
A shekara ta 2022, mutane sama da 2,720 ne suka mutu sanadin shan ƙwaya fiye da kima a yankin na ƙasar Kanada- abin da ke nufin kusan a kullum ana samun mutuwar mutum bakwai.
Mata aƙalla 400 ne suka shiga mako na biyu suna yajin cin abinci a wani gidan yari mai matsanancin tsaro da ke Bagadaza, babban birnin ƙasar Iraƙi.
BBC ta fahimci cewa an garƙame matan ne saboda kasancewarsu 'ya'yan ƙungiyar IS, bayan abin da suka ce shari'ar rashin adalci da aka yi musu.
An ce ƙungiyar tana da wakilai 'yan ƙasashen waje daga Rasha da Turkiyya da Azerbaijan da Ukraine da Syria da Faransa da Jamus da kuma Amurka.
Kuma ana jin cewa akwai ƙananan yara kimanin 100 da su ma ake tsare da su a gidan yarin.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa Umaru 'Yar'adua a matsayin shugaba maras son zuciya.
Ya bayyana haka ne a wani ɓangare na ranar cika shekara 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar na Najeriya.
Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa Yar’Adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma'a, Jonathan ya rubuta cewa, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, ƙasarmu ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.
Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya.
“Muna waiwaye baya don nuna godiya ga Allah saboda rayuwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga ƙasarmu.
“Shugaba Yar’Adua, jagora ne abin misali, wanda ya rayu ba tare da nuna bambancin ƙabilanci ko na addini ba. Kuma gudunmawarsa a fagen aikin gwamnati ta zaburas da mutane da yawa kan hanyar alheri.
“A yau, muna tuna shi da kuma hidimar da ya yi a rayuwarsa da jajircewa da duƙufa wajen tabbatar da dunƙulalliyar ƙasa daya mai bunƙasar arziƙi.
Goodluck Jonathan ya ce: “Za mu ci gaba da tunawa da shi saboda gagarumin ci gaban da ya kawo da kuma himmarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya”.
Shugaban Serbia Aleksandar Vucic, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen bazuwar makamai tsakanin al`ummar ƙasar bayan tagwayen harin bindiga na kan mai uwa da wabi.
Ya kuma ce zai karɓe dubban makamai da suke hannun al`umma ba bisa ƙa`ida ba.
Mista Vucic ya yi Alla-wadai da hari na biyu da ya auku a ranar Alhamis bayan ayyana shi a matsayin ayyukan ta`addanci.
Mutumin da ake zargi da kashe mutane takwas ɗin ya harbe su ne daga cikin motarsa a kusa da Belgrade.
Shugaban ƙasar ya ce za a tura ƴan sanda makarantun ƙasar sakamakon harin farko inda ɗalibi ya tsara abokan karatunsa da bindiga.
Ƙasar Serbia dai ta tsaurara matakai kafin mutum ya mallaki bindiga.
Shugaban Kungiyar sojan Haya ta Rasha watau Wagner Yevgeny Prigozhin, ya sanar da shirin janye dakarun sa daga birnin Bakhmut a ranar Laraba.
Moscow ta kwashe watanni tana yunkurin karɓe ikon Gabashin Ukraine ta hanyar amfani da sojojin na Wagner don samun nasara, to sai dai mista Prigozhin ya yi ƙorafin rashin isassun harsasai.
Mataimakiyar ministan tsaron Ukraine Hanna Malya ta bayyana cewa kungiyar mayaƙan Wagner sun canza hanya ne amma karɓe birnin na Bakhmut shi ne burinsu.
Shugaban Kungiyar ta Wagner ya kware wajen kai mummunan hari fitattun wurare, kungiyar ta naɗa Janar Mikhail Mizintev a matsayin mataimakin kwamanda bayan korarsa daga aiki.
Jami'an gwamnatin mulkin soji a Mali sun sanar da 18 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar zaɓen raba gardama kan daftarin tsarin mulki.
Kakakin gwamnatin ƙasar, Kanar Abdoulaye Maïga ya ce jami’an tsaro za su kaɗa kuri’a mako guda kafin nan, kamar yadda ya bayyana a gidan talabijin na ƙasar ranar Juma’a.
Sojoji da ke mulkin ƙasar sun sanya zaɓen raba gardama kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin ƙasar a ranar 19 ga Maris, kafin a ɗage zaɓen.
Sabon kundin tsarin mulkin na ɗaya daga cikin muhimman matakan da aka shimfida kafin a mai do da gwamnatin farar hula, bayan hamɓarar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita a shekara ta 2020.
A watan Fabrairun shekara ta 2024 ne dai za a gudanar da zaɓe.
Ƙasar Mali dai na fuskantar matsalar tsaro, inda kungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke ci gaba da kai hare-hare.
Kotun tsarin mulki a Uganda ta soke dokar da ta haramta amfani da muggan kwayoyi, irin su tabar-wiwi da ganyen khat.
Hakan dai ya biyo bayan kalubalen da kungiyar manoman ganyen khat ta soma yi na tsawon shekaru shida da suka gabata a matsayin martani ga dokar shekarar 2015.
Yanzu dai an soke dokar baki-ɗaya bayan da kotu ta ce an zartas da shi ba tare da samun rinjaye ƴan maajlisa da ake bukata a majalisar.
Kafin a yi muhawara da kuma zartar da doka a majalisar dokokin Uganda, dole ne akalla kashi ɗaya bisa uku na dukkan mambobin da ke da hakkin kaɗa kuri'a su kasance a majalisar.
Ko da yake an soke dokar a yanzu, duk da haka akwai haɗarin cewa za a kama masu noma da sha ko kuma sayar da haramtattun kwayoyi a ƙarƙashin wasu dokokin Uganda.
A Uganda, jami’an tsaro sun kasance suna kai samame tare da ƙona gonakin da ake nome tabar-wiwi ko kuma ganyen khat.
A duk faɗin Afirka, ƙasashe suna yin yunƙuri don halatta kasuwanci da kuma fitar da tabar wiwi.
Wata babbar kotu da ke zama a jihar Nasarawa ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 29 mai suna Gwom Yusuf-Ali ɗaurin shekara 13 a gida yari saboda samunsa da laifin fashi da makami.
Matashin wanda ya fito daga karamar hukumar Barkin Ladi na jihar Filato yana tsare ne a gidan gyaran hali tun watan Nuwamban 2020 bayan da ƴan sanda suka kama shi da laifin fashi a garin Gunki-Marmara da ke karamar hukumar Nasarawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma samu matashin da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.
Lauya mai gabatar da kara, R.D.K Adagba Esq, ya ce wanda ake zargin ya amsa lafin aikata fashi kan wani mai achaba ta hanyar nuna masa bindiga, inda ya kwashe masa kuɗaɗe da kuma tafiya da babur ɗin sa.
Rundura ƴan sanda a jihar Kano sun sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.
Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa na jihar ta Kano.
Kiyawa ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu'ammali da ƙwayoyi masu sa maye.
A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.
A jiya ne dai aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.
Shugabannin ƙasashen Afrika da dama musamman ma ƙasashen renon Ingila ta Commonwealth, suka isa birnin Landan gabanin naɗin sarautar Sarki Charles da za a yi gobe Asabar.
Cikin waɗanda suka riga suka isa Birtaniyar sun haɗa da Paul Kagame na Rwanda da Sarki Mswati na III da Lazarus Chakwera na Malawi da Hakainde Hichilema na Zambia da George Weah na Laberiya.
Shugaba Emerson Mnangagwa zai zama shugaban ƙasar Zimbabwe na farko a cikin shekaru ashirin da ya kai ziyara Landan, bayan da Birtaniya ta sanya wa ƙasar takunkumi.
Mr Mnangagwa ya ce yana cikin farin ciki da gayyatar da aka yi masa domin halartar bikin.
Sai dai wasu ƴan majalisar Birtaniya sun yi Alla-wadai da gayyatar da aka yi masa saboda irin take ƴancin ɗan adam da aka yi a ƙasarsa.
Ba a dai san cewa ko shugaban Kenya William Ruto zai halarci bikin ba, bayan zargi da ya yi a mako da ya gabata na yadda ake musgunawa shugabannin Afirka idan suka kai ziyara ƙasashen waje.
Yana magana ne kan wani lamari da aka sa shugabannin Afirka a cikin motar safa domin halartar bikin jana'izar Sarauniya Elizabeth a Burtaniya a bara.
Shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum ne zai halarci bikin naɗin sarautar daga ƙasashe masu magana da harshen Faransanci, yayin da shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara zai tura mataimakinsa Tiémoko Meyliet Koné domin wakiltarsa.
Firaministan Kamaru Joseph Dion Ngute ne zai wakilci shugaba Paul Biya a wajen taron.
Ƙasar dai ta ƙasance wadda Birtaniya da Faransa suka yi wa mulkin mallaka.
Tawagogin ceto a Guatemala da ke tsakiyar Amurka sun kwashe mutane sama da 1,000 daga ƙauyuka da ke kusa bayan aman wuta da dutsen Fuego ke yi.
Jami'ai sun buɗe cibiyoyin kwashe mutane guda huɗu a garuruwa da ke kusa, inda ake sa ran kwashe mutum 7,600.
Hukumomi sun rufe wata hanya da ke kai wa dutsen Jabal Al-Barkan, da ta haɗe garuruwa da dama a birnin Antigua.
Dutsen ya fara mana wuta ne a ranar Alhamis, inda hakaki ya turnuke sararin samaniya, abu kuma da ya jawo fargaba kan lafiyar mazauna wurin.
Shugabannin duniya na ci gaba da tururuwa zuwa birnin Landan gabanin bikin naɗin sarautar Sarki Charles da matarsa, Sarauniya Camilla a gobe Asabar.
Wakilan ƙasashe da yankuna sama da 200 ne ake sa ran za su halarci bikin naɗin sarautar a cocin Westminster Abbey.
Sarkin zai gudanar da wata liyafa a fadar Buckingham a yau Juma'a ga bakinsa na ƙasashen waje, a daidai lokacin da ake kammala shirye-shiryen na bikin.
An tsaurara matakan tsaro a faɗin Burtaniya,inda ta girke 'yan sanda sama da 29,000 a ɗaya daga cikin matakan tsaro mafi girma a tarihin a ƴan sandan London.
Masu zanga-zanga sun kewaye gidan shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan, Volker Perthes a birnin Port Sudan da ke gabashin ƙasar, domin neman a kore shi daga yankin tekun Bahar Maliya, kamar yadda tashar talabijin mai goyon bayan sojoji ta bayyana.
Mista Perthes da sauran jami'an MDD sun koma Port Sudan daga Khartoum, babban birnin kasar, kwanaki bayan ɓarkewar faɗa tsakanin dakarun RSF da kuma sojojin Sudan a ranar 15 ga Afrilu.
Tashar talabijin ta Tayba ta ruwaito cewa "Al'ummar jihar Bahar Maliya sun kewaye gidan Volker inda suka buƙaci a kore shi cikin gaggawa daga jihar."
Gidan talabijin ɗin ya nuna hotuna da faifan bidiyo na mutanen ɗauke da alluna da kuma ɗaga tutocin Sudan.
Zanga-zangar ta janyo martani daban-daban, inda wasu suka yi kira da a kori Mista Perthe yayin da wasu suka yi tir da zanga-zangar.
Kungiyoyi da ke goyon bayan sojoji da masu kishin Islama sun gudanar da zanga-zangar adawa da Mr Perthes a baya-bayan nan.
Haka kuma a kwanakin baya masu tsattsauran ra'ayi sun yi barazanar kashe shi.
Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres ya kyale ma'aikatan su koma Port Sudan amma ya ce ba za su fice daga ƙasar gabaki-ɗaya ba.