Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Lauya a Legas

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Abdullahi Bello Diginza and Halima Umar Saleh

  1. Rufewa

    Masu bin wannan shafi na BBC Hausa a nan muke muku sallama tare da fatan haduwa gobe don ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a duniya, kai tsaye.

    Mu kwan lafiya.

  2. 'An sace kusan mutum 200 a ƙauyukan Sokoto cikin mako uku'

    Mazauna kauyuka da yawa a gabashin jihar Sakkwato sun ce matsalar satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga sai kara kamari take a kwanakkin baya-bayan nan.

    Wasu daga cikinsu da suka zanta da BBC sun ce wadanda aka sace daga kauyukan a cikin makonni uku zuwa wata dayan da ya wuce suna iya kai mutum 200.

    Sai dai kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da hakan ba.

    Lamarin dai ya fi kamari ne yanzu a kauyukan yankin karamar hukumar Goroyo kamar su Takakume da Gorau da Goronyo da Balakozo da Kwakwazo da Kojiyo da Kagara da Shinaka da makamantansu.

    Wani mazaunin gari Kwakwazo ya ce lamarin baya-bayan nan nan ya faru ne jiya da daddare a Kagara da Shinaka.

    Yayin da yake wa BBC karin bayani kan yadda suke kwana a tsaye suna arangama da maharan, Malam Shiitu Ibrahim Takakume, ya ce duk da haka mutanen da aka sace kawo yanzu za su iya kai 200 bisa kiyasi.

    Shi ma wannan mazaunin garin Gorau da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun rasa mutum uku a cikin wata arangama da suka yi da maharan da tsakar dare.

    Sai dai kokarin da muka yi na jin ta bakin hukumomin tsaro a jihar dangane da wannan ikrarin bai yi nasara ba.

    Yankin na gabashin Sakkwato dai na daga cikin wuraren da a yanzu yan fashin daji suka mayar kamar mashekarinsu inda suke bulla idan aka fatattake a makwabciyar jihar Zamfara.

  3. Ana ci gaba da gasar kokawar gargajiya a Jamhuriyar Nijar

    A yau ne aka shiga yini na hudu na kokowar gargajiya da ake yi Diffa ta Jamhuriyar Nijar a karo na 43.

    Kawo yanzu dai ƴan kokowa 65 ne suka riga suka fadi tun zagaye na farko na kokowa tsakanin jihohin kasar.

    Tuni dai aka fitar da Diffa mai masauƙin baƙi daga gwagwarmayar neman takobin na bana.

  4. An kashe mutum 60 a wani rikici na kwana hudu a Sudan ta Kudu

    An kashe kimanin mutum 60 sakamakon wani tashin hankali na tsawon kwanaki hudu a Sudan ta Kudu.

    Jami'ai a jihar Jonglei sun ce wasu matasa ne na al'ummar Nuer suka kai farmaki a kauyukan 'yan kabilar Murle.

    Kusan dukkan wadanda aka kashen yan kabilar ta Nuer ne.

    Rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Sudan ta Kudu a baya-baya nan ta kara tsaurara ayyukan sintiri a yankin, inda ta yi gargadin cewa matan na Nuer na shirin far wa 'yan kabilar Murle.

    Hare-haren ramuwar gayya masu nasaba da kabilanci da kuma tashin hankali kan shanu abubuwa ne da suka zama ruwan dare a Sudan ta Kudu.

  5. Ƴan sanda sun fadi sunan jami’insu da ake zargi da harbe wata lauya ranar Kirstimati a Lagos

    Ƴan sanda a jihar Lagos ta Najeriya sun sanar da sunan jami’insu da ake zargi da harbe wata lauya har lahira a birnin Legas din ranar Kirstimati.

    Mrs Omobolanle Raheem ta gamu da ajalinta ne a unguwar Ajah yayin da take kan hanyarta ta komawa gida daga addu’o’in zagayowar ranar ta Kirtimeti.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin ‘yan sanda a jihar SP Benjamin Hundeyin ya ce wanda ya harbe matar shi ne Drambi Vandi wanda kuma tuni aka kama shi kuma aka garkame.

    SP Hundeyin ya ce an kuma mika jami‘in mai mukamin mataimakin sufurtanda wato ASP ga sashen binciken miyagu laifuka na rundunar, kana ya yi alkawalin cewa ba za a bata lokaci ba wajen binciken kisan matar.

    A ranar Lahadi dai ne aka harbe Mrs Bolanle Raheem a unguwar Ajah lokacin da take kan hanyarta ta dawowa daga majami’a a kan idon mijinta da ‘ya’yanta da kuma kanuwarta.

    Bayanai sun ce dan sandan ya harbi motar da suke tafiya a ciki wadda mai gidanta ke tukawa ne lokacin da suke juyawa a karkashin gadar Ajah bayan da ‘yansandan da ke sintiri a wajen suka bukaci da su tsaya.

    Rahotannin suka ce dansanda ya yi kokarin arcewa bayan yin harbin amma sai abokan aikinsa suka damke shi.

    Daga nan an garzaya da marigayiyar zuwa asibiti inda aka tabbatar da rai ya yi halinsa.

    Tun daga lokacin faruwar zuwan yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da yin Allah-wadai da lamarin tare da yin ta’aziyya ga iyalan lauyar, da kuma kiran a hukunta wanda ya yi Harbin.

    Daga cikin wadanda suka yi ta'aziyyar har da gwamna jihar Babajide Sanwo -Olu da babban sufetan ‘yansandan kasar IGP Usman Alkali Baba da kuma manyan ‘yan takarar shugabancin kasar uku wato Atiku Abubakar da Bola Tinubi da kuma Peter Obi.

    A cikin wata sanarwa, babban sufetan ‘yan sandan ya ce abin jami’in ‘yan sandan ya yi baya kan ka’ida a tsarin aikin dansandan Najeriya ya kuma bayar da umarnin gaggauta bincike da kuma gurfanar duk wadanda ke da hannu a lamarin gaban shari’a.

  6. Sojojin Nijar sun kashe ƴan bindiga 50

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce dakarun sojin sun kashe 'yan bindiga kusan 50 a makon da ya gabata.

    Akasarin wadanda aka kashe din an kashe su ne a garin Banibangou inda jirgin yakin sojin kasar ya musu ruwan wuta.

    Sannan kuma a yankin Tafkin Chadi aka yi gaba da gaba da dakarun kasar da ƴan bindiga inda aka kashe a kalla ƴan bindiga 10 aka kama wasu da dama.

  7. Mutum 20 sun mutu a haɗuran mota biyu a Najeriya

    Akalla mutum 20 ne suka mutu a wasu haɗuran mota biyu da suka auku a wurare biyu a Najeriya.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta ƙasar Bisi Kazeem ya sanya wa hannu ya ce daya daga cikin haɗuran biyu ya auku ne a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, yayin da ɗayan kuma ya auku a hanyar Mokwa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa mutum 10 ne suka mutu a haɗarin hanyar Ibadan yayin da shida suka jikkata.

    Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa wasu mutum 10 sun mutu a haɗarin da ya auku a hanyar Mokwa, tara nan take ɗaya kuma bayan an kai shi asibiti.

    Sanarwar ta ambato muƙaddashin shugaban hukumar Dauda Biu na kokawa game da saɓa wa dokokin gudun wuce kima da mafi yawan direbin ƙasar ke yi, musamman a lokutan bukuwan Kirsimeti,

    Mista Biu ya gargadi direbobin da ke da wannan ɗabi'a da su tsayar da wannan hali nasu, ko su fuskanci fushin jami'an hukumar matuƙar suka je hannu.

    A Najeriya ana samun yawaitar haɗuran mota a kan titunan ƙasar da ake yawan alaƙantawa da lalacewar htitunan ƙasar da kuma kauce wa dokokin tuƙi ciki har da gudun wuce kima da ma fi yawan direbobin ƙasar ke yi.

  8. Taiwan za ta tsawaita aikin sojinta zuwa shekara guda

    Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen ta ce ƙasar za ta tsawaita aikin soji na tilas daga wata huɗu zuwa shekara guda.

    Matakin na zuwa ne bayan da aka samu ƙaruwar takun-saƙa tsakaninta da China, wacce ke kallon tsibirin a matsayin wani yanki na ƙasarta.

    Yayin da take magana a taron manema labarai, shugaba Tsai ta bayyana matakin da cewa zai ƙarfafa tsaron Taiwan domin kare kanta daga hare-haren China.

    "Zaman lafiya ba zai sauko mana kawai daga sama ba, Taiwan na ƙoƙarin kare kanta daga mamaya'', in ji shugabar ƙasar

    Shugaba Tsai ta ce za a ƙara bai wa dakarun ƙasar horon soji, inda ta ce za su aro wasu kayyakin horon daga Amurka da wasu ƙasashen da ke da ƙarfin soji.

    Ta ƙara da cewa ƙarfin tsaron tsibirin a yanzu ba zai iya kare ƙasar daga farmakin China ba, wacce ke ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya ƙarfin soji a duniya.

  9. Jam'iyyar Labour ta naɗa sabon daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa

    Kwamintin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour ya naɗa Akin Osuntoku a matsayin sabon daraktan kwamitin.

    Naɗin mista Osuntokun na zuwa ne bayan murabus ɗin tsohon daraktan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar Dakta Doyin Okupe bayan da aka same shi da laifin ɓarnatar da kuɗi.

    Yayin da yake bayyana naɗin, shugaban jam'iyyar na ƙasa Barista Julius Abure ya ce naɗin ya zama wajibi ne bayan murabus ɗin mista Okupe.

    Murabus ɗin Okupe na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin ƙasar ta same shi da laifin karɓar sama da naira miliyan 200 daga hannun tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.

    Mista Osuntokun wanda tsohon daraktan kamfanin dillancin labarai na Najeriya ne, ya taɓa rike muƙamin mai bai wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo shawara kan kan harkokin mulki, ya kuma taɓa riƙe muƙamin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a shekarar 2011.

  10. Darajar kuɗin Iran ta yi mummunar faɗuwa

    Darajar kuɗin ta ci gaba da faɗuwa, lamarin da hukumomi ke cewa ta wani ɓangare yana da alaƙa da dubban zanga-zangar da ake yi a wasu sassan ƙasar sama da watannin uku da suka gabata.

    A ranar Litinin darajar kuɗin ƙasar ta yi faɗuwar da ba a taɓa ganin irin ta ba tun bayan fara zanga-zangar.

    Waɗanda ke da hali a cikin 'yan ƙasar suna ta sayen daloli da gwala-gwalai a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun rage asara, yayin da ake ta samun hauhawar farashin kaya a ƙasar.

    Hukumar da ke sa-ido kan kafafen yaɗa labarai a ƙasar ta gargaɗi wasu gidajen yaɗa labaran ƙasar da su san irin labaran da za su riƙa bayarwa kan wannan batu.

  11. Buhari ya yi Allah wadai da kisan Lauya a Legas

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da abin da ya kira 'kisan rashin hankali'' da wasu 'yan sanda da ke bakin aiki suka yi wa wata lauya mai suna Omobolanle Raheem ranar Kirsimeti.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin kashe lauyar,.

    Sannan kuma shugaban ya umarci hukumomin 'yan sanda da su ɗauki tsattsauran mataki kan waɗanda suka aikata wannan ta'asa.

    A wata mai kama da wannan ita ma hukumar kula da aikin 'yan sanda ta Najeriya ta yi Allah wadai da kisan lauyar.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke sa hannun shugaban sashen hulɗa da jama'a na hukumar Ikechukwu Ani, hukumar ta ce tana buƙatar rahoto kan kisan daga hukumar 'yan sandan, da kuma kiran bayar da horo ga 'yan sanda kan yadda za a riƙe makamai.

  12. 'Yan sandan Ghana sun haramta hasashen abubuwan da za su faru a sabuwar shekara

    'Yan sandan Ghana sun gargaɗi shugabannin addinai game da al'adar hasashen abubuwan da za su faru a sabuwar shekara, wanda ke janyo fargaba da rikici har ma da mace-mace a ƙasar.

    A wata sanarwa da 'yan sandan ƙasar ta fitar ta ce bai kamata 'yancin addini ya saɓa wa 'yancin wasu ba.

    Masu suka dai na ganin wannan sabuwar doka a matsayin wacce ta saɓa wa 'yancin addini wanda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar, dan haka dokar ba ta kan ƙa'ida.

    Miliyoyin kiristoci ne dai ke taruwa a majami'u domin sauraron hasashen abubuwan da za su faru a shekara mai kamawa daga bakunan fastocinsu.

    Sakonnin kan kunshi bushara kan abubuwa na farin ciki da garɗari kan munanan abubuwa.

    'Yan sandan sun sanya wannan doka ne bayan a shekarar da ta gabata aka yi hasashen samun yawan mace-mace da bala'o'i masu yawa a ƙasar.

  13. Dakarun Sabiya na cikin shirin ko-ta kwana kan fargabar hari daga Kosovo

    Rundunar sojin Sabiya ta ce ta sanyan dakarunta cikin 'shirin ko-ta-kwana', bayan da aka kwashe makonni ana samun ƙaruwar rikici tsakaninta da Kosovo.

    Shugaban ƙasar Aleksandar Vucic ya ce zai ɗauki ''duka matakan da suka dace don kare mutanen Sabiya''.

    Rundunar sojin ƙasar na cikin shirin ne sakamakon ikirarin da kafofin yada labarai a ƙasar ke yi na cewa Kosovo na shirin ƙaddamar da hari kan ƙabilar Serb da ke arewacin ƙasar.

    Kawo yanzu dai gwamnatin kosovo ba ta ce komai ba game da wannan ikirari.

    To amma a baya ta sha zargin shugaban Sabiya da neman tayar da hargitse tsakanin ƙasashen biyu.

    Ƙasar Kosovo dai ta ɓalle ne daga Sabiya bayan wani yaƙi a shekarar 1998 zuwa 1999.

    Kuma har yanzu Sabiya ba ta amince da cin gashin ƙasar Kosovo ba, haka kuma tana kallon 'yan ƙabilar Serb da ke zaune a arewacin Kosovo a matsayin 'yan ƙasarta.

    Ita dai Sabiya na zargin Kosovo da shirya ta'addanci kan 'yan ƙabilar Serbs kusan dubu 50 da ke zaune a wasu yankunan arewacin ƙasar.

    A wani martani da ta mayar Kosovo ta zargi Sabiya da shirya wasu jami'an tsaro da suka saka shingayen bincike a mafi yawan sassan arewacin Kosovo cikin wannan wata na Disamba.

    Ƙungiyar tarayyar Turai ta sha yunƙurin shiga tsakanin ƙasashen biyu. Yayin da take kira ga ƙasashen biyu da shugabanninsu da su taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin.

  14. Dakarun Jamhuriyar Nijar sun kashe 'yan ta'adda 49

    Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce dakarun kasar sun kashe 'yan ta'adda akalla 49 yayin samame a wurare daban-daban da ke kasar.

    A sanarwar da take fitarwa mako-mako, rundunar sojin kasa ta kasar ta ce an kashe 'yan bindiga akalla 36 a yammacin kasar.

    Bayanai sun ce an kashe 25 daga cikinsu ne sakamakon hari ta sama da aka kai a garin Banibangou, an kashe daya a Samira, yayin da kuma aka kashe biyu bayan an yi wa motarsu kwanton-bauna a lardin Tangounga.

    A tsakiyar kasar, an kashe 'yan bindiga uku a samamen da aka kai Chara.

    A lardin Tafkin Lake Chadi, an kashe 'yan bindiga 10 sannan aka kama wasu da dama.

    An kashe soja daya sannan aka jikkata shida a samamen.

  15. Jam'iyya mai mulki a Jamhuriyar Nijar PNDS-Tarayya ta zabi sabon shugaba

    Jam'iyyar Party for Democracy and Socialism PNDS-Tarayya da ke mulki a Jamhuriyar Nijar ta zabi Foumakoye Gado a matsayin sabon shugabanta.

    An gudanar da zaben ne ranar Lahadin da ta gabata, bayan an kwashe kwana biyu ana taron jam'iyyar a Tahoua.

    Foumakoye Gado ya maye gurbin Mohamed Bazoum, wanda shi ke shugabancinta kafin ya zama shugaban kasar.

    Tsohon ministan ya zama shugaba na uku na jam'iyyar PNDS bayan tsohon Mahamadou Issoufou da shugaban shugaban kasa mai-ci.

    Foumakoye Gado ya rike mukamin mataimakin shugaban jam'iyyar tun daga 2013.

  16. Bala'in sanyi ya sa mutane sun kasa fita daga motocinsu a Amurka

    Akalla mutum 28 sun mutu a Jihar New York yawancinsu a garin Buffalo, a yayin da mahaukaciyar iska mai dauke da jaura take ci gaba da mamaye Arewacin Amurka.

    Wani jami'in gwamnatin jihar ya ce lamarin ya rutsa da mutane da dama inda wasu suka kwashe fiye da kwana biyu a cikin motocinsu a yanayin iskar sanyi mafi muni a tarihi.

    Kankarar da ke sauka ta kai santi mita 23, kamar yadda masana suka yi hasashe.

    Mahaukaciyar iskar mai bala'in sanyi ta somo ne daga Canada zuwa kan iyakar Mexico inda ta kashe akalla mutum 56.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana dokar ta-baci inda ya amince a bayar da tallafi na musamman ga jihar New York.

    "Ina jajanta wa mutanen da suka yi asarar 'yan uwansu a wannan lokaci da ake hutun karshen shekara," in ji shugaban kasar a wani sako da ya wallafa a Tuwita.

  17. Koriya ta Kudu za ta inganta ayyukan leƙen asiri

    Shugaban Koriya ta Kudu ya ce zai ƙara inganta sojoji da ayyukan leƙen asiri a ƙasar bayan jirage marasa matuƙa biyar na Koriya Ta Arewa sun yi musu kutse.

    Yoon Suk Yeol ya ce wannan lamari da ya faru ya nuna gazawa a irin shirin da sojojin ƙasarsa ke da shi.

    Ya bayyana cewa Koriya Ta Kudu za ta samar da wani sashe na musamman na jirage marasa matuƙa.

    Bayan kutsen da Koriya Ta Arewar ta yi da jiragen a jiya, sai takwararta Koriya Ta Kudu ta mayar da martani ta hanyar tashin jiragen yaƙi da masu saukar ungulu domin tunkarar jirage marasa matuƙan.

    Sai dai rahotanni sun ce jiragen yaƙin sun yi harbi sama da sau 100 kan jirage marasa matuƙan Koriya Ta Arewa amma sun kasa kaɓo ko guda ɗaya.

  18. China za ta bai wa matafiya damar shiga kasar daga watan gobe

    China za ta daina killace matafiya daga ranar 8 ga watan Janairu lamarin da zai kawo gagarumin sauyi kan matakinta na yaki da annobar korona, a cewar jami'ain gwamnatin kasar.

    Bayan ta shafe kusan shekaru uku iyakokinta a kulle, yanzu za a bai wa masu bisar aiki da karatu da kuma wadanda ke son ziyartar iyalansu damar shiga kasar.

    Wannan sauyi na zuwa ne a daidai lokacin da China take fama da karin yaduwar cutar korona bayan ta janye takunkumin da ta sanya wa 'yan kasar na kulle.

    Rahotanni sun ce asibitoci sun cika makil da marasa lafiya kuma tsofaffi na ta mutuwa.

    A halin yanzu ba a san adadin mutanen da ke mutuwa sanadin cutar a kullum ba saboda an daina sanar da alkaluman wadanda suke mutuwa.

    A makon jiya Beijing ta bayar da rahoton cewa kusan mutum 4,000 ke kamuwa da cutar Covid a kullum kuma ana samun mutuwa nan da can.

  19. Masu so su yi amfani da karfin gwamnatin tarayya don murde zabe ba za su yi nasara ba - Bala Mohammed

    Gwamnan Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya Bala Mohammed ya yi zargin cewa ana yunkurin yi masa magudi a zaben gwamnan da za a gudanar a 2023.

    Ya bayyana haka ne ranar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Bauchi yayin da kungiyar Kiristoci ta jihar ta kai masa ziyarar bikin Kirsimeti.

    Gidan talbijin na Channels TV ya ambato Gwamna Bala Mohammed yana cewa mutanen da suke yunkurin yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin yin magudin zabe ba za su yi nasara ba domin Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bari hakarsu ta cimma ruwa ba.

    “Akwai mutanen da ke sayen kuri'u, da kuma wadanda suke shirin murde zabe ta hanyar amfani da karfin gwamnatin tarayya amma na sani cewa Shugaba Buhari mutum ne mai adalci, kuma tuni ya tabbatar mana cewa zai bar mutane su zabi wanda suke so,” in ji shi.

  20. Barka da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake muku barka da warhaka.

    Sannunku da sake saduwa da mu a shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku biyo mu.