Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da jana'izar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Mustapha Musa Kaita and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa game da jana'izar Sarauniya Elizabeth ll, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan kuna iya ziyartar shafinmu na BBC Hausacom domin karanta labaran da muke wallafa muku a kowanne lokaci.

    Haka kuma za ku iya ziyartar shafinmu naFacebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

    Amma yanzu a madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An binne gawar Sarauniya - Iyalanta

    Iyalan gidan Sarautar Birtaniya sun ce sun binne gawar Sarauniya Elizabeth ll a wata kebantacciyar jana'izar da suka gudanar a fadarta da ke Windsor.

    A wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na yanar gizo, sun ce sun binne ta ne tare da mijinta Yarima Philip, a hubbaren 'King George VI Memorial' da ke cocin St George

    'Yayanta da jikokinta ne kadai suka halarci binne gawar tata.

    A wannan cocin ne dai aka binne mahaifinta Sarki George VI, da mahaifiyarta, da kuma kanwarta gimbiya Margaret

  3. 'Yan Canada sun yi bankwanan karshe ga Sarauniya a kasarsu

    Al'umar Canada sun yi bikin bankwana ga Sarauniya Elizabeth II, ta hanyar gudanar da taron addu'o'in girmamawa ga Sarauniyar da kuma faretin soji a babban birnin kasar

    Sojojin fadar masarautar Canada ne suka jagoranci faretin sojin, kamar yadda sojojin ruwan fadar Birtaniya suka jagorancin faretin jana'izar Sarauniyar da aka gudanar a birnin Landan.

    Taron dai ya samu halartar manyan baki daga ko'ina a fadin kasar

  4. Hotunan rayuwar Sarauniya a fadar Windsor

    A yau ne aka gudanar da jana'izar Sarauniya Elizabeth II da yammacin ranar Litinin a cocin St George da ke fadar Windsor - wurin da Sarauniyar ta fi so a a lokacin da take raye.

    Sarauniyar tare da kanwarta Gimbiya Margaret sun kwashe shekaru masu yawa a fadar lokacin da ake cikin yanayin yake-yake, daga baya kuma Sarauniyar ta zauna a wujen tare da 'ya'yanta.

    Haka kuma ta karbi bakuncin manyan mutane a fadar, kama daga Ronald Reagan zuwa Mikhail Gorbachev, kuma tana yawan ziyartar fadar domin halartar taron bikin wasan doki.

    Ko a lokacin annobar cutar Corona ma, fadar Windsor Sarauniyar ta koma da zama, kuma daga can ta aiko da sakonta na 'sai mun sake haduwa' zuwa ga 'yan kasar

  5. Wadanne Sarakuna aka binne a cocin St George?

    Tuni aka saka gawar Sarauniya a cikin taskar adana gawa a cikin cocin St George, gabanin yi mata jana'izar karshe da iyalan gidanta za su yi mata.

    Sarki Edward IV ne aka fara binnewa a cocin na fadar Windsor, wanda ya kasance a karkashin ikon gidan Sarautar na kusan shekara 1,000.

    Tsoffin Sarakuna da yawa aka binne a cocin, wadanda suka hada da Sarki George IV da George III, wanda a zamanin mulkinsa ne Amurka ta samu 'yancin kai daga daular Birtaniya.

    Sarakuna da dama ne dai aka binne tare da taskancewa a wurare daban-daban cikin cocin

    Za a binne Sarauniyar tare da mijinta Yarima Philip, a cocin inda a nan ne aka binne mahaifinta Sarki George VI, da mahaifiyarta, da kuma kanwarta gimbiya Margaret

  6. 'Yan gidan sarauta ne kadai za su binne Sarauniya

    Nan gaba kadan ne da maraicen nan iyalan gidan sarautar Birtaniya za su binne gawar Sarauniya Elizabeth ll, tare da mijinta Yarima Philip Duke na Edinburgh, a wani daki da ake kira 'King George VI', wanda ke cikin cocin St George

    Za kuma a rubuta ELIZABETH II 1926-2022 a kan kabarinta, domin nuna tsawon lokacin da ta rayu a duniya

    A dazu ne dai aka gudanar da jana'izar kasar ga Sarauniyar, wadda shugabannin kasashen duniya daban-daban suka halarta.

  7. Mutane da sun kalli jana'izar Sarauniya ta allunan majigi

    A yayin da mutane da dama suka yi kokarin shiga fadar Windsor Castle domin shaida jana'izar Sarauniya Elizabeth ll, wasu kuma sun kasance a gaban allunan majigi da ke tsakiyar birnin Landan domin kallon jana'izar kai-tseye.

    Lloney da matarsa Elvira Monono, sun yi jiran sa'o'i da dama a gaban allunan majigi tare da 'ya'yansu domin shaida jana'izar Sarauniyar, kuma yanzu kamar sauran wadanda suka halarci jana'izar suma sun tafi gida.

    Lloney ya ce ''abu ne na tarihi, ita ce Sarauniya daya tilo da na sani a tsawon rayuwata, ta yi mulki tsawon shekara 70, mafi kankantar abin da za mu yi mata shi ne mu zo nan domin kallon jana'izarta, don nuna girmamawa a gareta''.

  8. Sarki Charles III ya bar cocin St George bayan kammala jana'izar Sarauniya

    Sarki Charles lll tare da matarsa Camilla sun bar cocin St George da ke fadar Windsor bayan kammala jana'izar Sarauniya Elizabeth ll

    Sarki Charles III ya yi magana da shugaban cocin Ingila da manyan jami'an cocin a wajen cocin yayin da suke suke barin cocin shi da matarsa.

  9. An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa

    An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa, gabanin binne ta

    Daga nan sai babba sarkin yakin fadar wato Garter King of Arms, ya ambaci salo da sarautun da ake kiran Sarauniyar lokacin mulkinta.

  10. Shugaban cocin Ingila ya sanya wa gawar Sarauniya albarka

    Shugaban cocin Ingila Justin Welby, ya sanya wa gawar Sarauniya Elizabeth ll albarka.

    A lokacin da aka ajiye ta domin addu'ar karshe shugaban cocin ya ce ''Kin koma ga mahaliccinki cikin salama, kin zama mai kwarin gwiwwa, kin yi riko da daidai, kin rike wa kowa da amana, kin taimaka wa gajiyayyu, kin agaza wa masu rauni, kin mutunta mutane, kin nuna soyayya da kauna ka mutane, ina miki fatan samun salama da albarkar ubangiji a gareki''

  11. Hotuna daga cikin cocin St George inda aka ajiye gawar sarauniya domin addu'o'in karshe

  12. Shugabanni da manyan mutane 500 ne suka halarci jana'izar Sarauniya

    Manyan mutane 500 ciki har da shugabannin kasashe da firaiministoci da kuma sarakuna a fadin duniya ne suka halarci addu'ar da aka yi wa Sarauniya a majami'ar Westminister Abbey

    Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaba Biden da mai dakin shugaban Ukraine Olena Zelenska da shugabannin Jamus da Faransa da Afirka ta Kudu da India da kuma mataimakin shugaban China.

    Kasashe kalilan ne aka cire su daga zuwa jana'izar ciki har da Rasha da kuma Belarus, saboda yakin da ake yi a Ukraine. Syria da Myanmar da Afghnaistan da kuma Venezuela ma ba su halarci taron ba

  13. Ana jin ƙarar harbin bindiga duk minti guda yayin da ake jiran isowar gawar Sarauniya Windsor

    Ana jin ƙarar harba bindiga kowane minti da kuma ƙarar kaɗa ƙaraurawa a lokacin da ake isowa da gawar Sarauniya.

    Nan ba da daɗewa ba ake sa ran binne ta. Mutanen na sa ran cewa nan ba da jimawa ba za su ga wucewar gawar a yayin da suke jin kaɗeɗe da bushe-bushe.

    Iyaye da dama sun ɗauki yaransu bisa kafaɗa domin su ga wucewar.

  14. Jama'a na jiran isowar Sarauniya Fadar Windsor

    Gawar Sarauniya Elizabeth na hanyar zuwa Windsor inda mutane da dama ke ci gaba da taruwa a cikin rana wasu kuma suna kallo a talabijin.

    Tafiyar Sarauniya ta ƙarshe ta soma ne ɗaruruwan kilomitoci tun daga Fadar Balmoral inda a nan ne Allah ya yi mata rasuwa zuwa Fadar Windsor da ke garin Berkshire.

    Ga Basant Sehra mai shekara 22 da mahaifinta Bahadur, wannan lokaci ne mai muhimmanci kallon jana'izar Sarauniya.

    Basant ta taɓa haɗuwa da Sarauniya a lokacin da ta ziyarci garinsu wato Hayes da ke Yammacin London a lokacin da take makarantar Firamare.

  15. Hotunan yadda dubban mutane ke ci gaba da bankwana ga Sarauniya

    Dubban mutane na ci gaba da kafa layi inda suke jiran wucewar Gawar Sarauniya Elizabeth II a yayin da ake tafiya da ita zuwa Fadar Windsor.

    Mutane da dama na jefa furanni ga motar Sarauniyar a yayin da ake hanyar kai ta Fadar Windsor.

    Idan anjima ne ake sa ran za a binne Sarauniyar a Fadar ta Windsor.

  16. Ma'aikatan Fadar Buckingham sun taru domin bankwana da Gawar Sarauniya

    Ma'aikatan Fadar Buckingham sun taru a gaban fadar a lokacin da ake wucewa da Gawar Sarauniya a karo na ƙarshe ta gaban gunkin tunawa da Sarauniya Victoria.

    An kafa gunkin ne tun a 1901 domin tunawa da rasuwar kakar-kakar Sarauniya Elizabeth II wato Sarauniya Victoria.

  17. Wasu daga cikin muhimman lokuta a jana'izar Sarauniya Elizabeth II

  18. Jama'a da dama sun kafa layi domin bankwanan ƙarshe yayin da ake tafiya da Gawar Sarauniya

    Jama'a da dama sun taru domin kallon tafiya da Gawar Sarauniya Elizabeth II.

    Jama'a na ci gaba da fitowa inda suke taruwa a kan tituna domin bankwana da Gawar Sarauniya.

  19. Gawar Sarauniya na barin Westminster Abbey

    An gudanar da taken Birtaniya - a daidai lokacin da aka kammala addu'o'i na jana'izar Sarauniya.

    Za dai ku iya ci gaba da kallon jana'izar Sarauniya Elizabeth II da kuma yadda za a kai ta Wellington Arch ta hanyar danna hoton da ke saman wannan shafin na kai tsaye.

  20. Ana gudanar da jawaban godiya da addu'o'i ga Sarauniya

    Jerin shugabannin coci na gudanar da addu'o'i a halin yanzu a wurin jana'izar.

    Babban limamin Cocon Scotland Iain Greenshields ya soma ne da godiya ga Sarauniya kan irin mulkin da ta yi a Birtaniya.