Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zelensky ya caccaki Nato kan hana shawagin jirage
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau
Liverpool 1-0 West Ham United: Liverpool na jiran Man City ta yi ɓari
Liverpool ta datse yawan makin da ke tsakaninta da Manchester City zuwa maki uku bayan doke West Ham a Anfield.
Zelensky ya caccaki Nato kan hana shawagin jirage
Shugaban Ukraine ya caccaki shugabannin kungiyar tsaro ta NATO saboda ƙin aiwatar da hana shawagin jirage a ƙasarsa.
A cikin wani kakkausan jawabi, Volodymyr Zelensky ya ce jan ƙafar da ƙasashen yammaci ke yi na shiga tsakani ya ba Rasha “ƙarfin guiwa” na ci gaba da kai hare-hare a garuruwa da kauyukan Ukraine.
Nato ta ce matakin hana shawagin zai haifar da fito na fito da Rasha.
A ranar Asabar ɗin nan shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya yi gargaɗin cewa ɗaukar mataki irin haka zai kasance a matsayin “amincewa da shiga yaƙi ne da ƙasar ta yi.”
Dangane da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha, shugaban na Rasha ya ce “matakin ya yi kama da tallar yaƙi, amma sai godiyar Allah hakan ba ta faru ba.
A cikin jawabinsa daga Kyiv, Mista Zelensky ya ce bai amince da cewa ɗaukar matakin kai tsaye zai iya haifar da wuce gona da iri kan kungiyar tsaro ta Nato ba. A cikin fushi kuma ya bayyana cewa “ra’ayin ƙasashen yammaci ya nuna cewa ba su ɗauki gwagwarmayar neman ƴanci ba a matsayin burin farko na ƙungiyarsu ba.
"Mutanen za su mutu tun daga wannan rana saboda ku, saboda rauninku, saboda rashin hadin kan ku," in ji Mista Zelensky.
Saudiyya ta ɗage haramcin hana ƴan Najeriya shiga ƙasarta
Gwamnatin Saudiyya ta ɗage haramcin hanawa ƴan Najeriya shiga ƙasarta saboda annobar korona.
Matakin ya shafi ƙasashen Afghanistan da Afirka Ta Kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar da Angola da Seychelles da Comoros da kuma Ethiopia, kamar yadda shafin hukumomin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina ya bayyana.
Wannan na zuwa bayan sanar da ɗage dakatar da Umrah, shekara biyu bayan dakatar da aikin Ibadar saboda annobar korona
Firaministan Isra’ila ya gana da Putin
Firaministan Isra'ila Naftali Bennett ya gana da shugaba Putin a birnin Moscow inda suka tattauna batun yakin Ukraine.
Naftali Bennett, bayan tattaunawa da Vladimir Putin a Moscow tsawon sa'a biyu, ya kuma kira shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky kan ganawar da ya yi da shugaban na Rasha, kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana.
Ofishinsa ya ce Bennett zai nufi Berlin, inda zai tattauna da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz.
Israel na shiga tsakani ne a madadin Amurka da Jamus da Faransa.
Isra'ila babbarƙawar Amurka ce kuma ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi.
Amma kuma ta yi tayin yin sulhu tsakanin Moscow da Kyiv. Haka kuma Isra'ila ta damu da tattaunawar nukiliyar Iran batun da ya shafi Rasha.
Chelsea ta lallasa Burnley
Chelsea ta lallasa Burnley inda ta ci ƙwallo huɗu cikin kusan minti 23 a karawar farko bayan Roman Abramovich ya sanar da sayar da ƙungiyar.
Sojojin Rasha sun ƙwace ikon asibitin mahaukata a Ukraine
Rahotanni daga Ukraine na cewa dakarun Rasha sun karɓe ikon asibitin mahaukata da ke nisan kilomita 60 da arewa maso yammacin Kyiv.
Rahotannin sun ce marar lafiya 670 ke cikin asibitin.
Kafar yaɗa labaran Ukraine ta Hromadske ta ce gwamnan yankin ya tabbatar da kwace ikon asibitin da ke Borodyanka
"Yau mun kasa fahimtar yadda za mu kwace waɗannan mutanen, ko yadda za mu taimake su ba," in ji Oleksiy Kuleba.
"Suna fama da matsalar ruwa da magani, suna buƙatar taimako"
Wasu masu son zama shugaban ƙasa ya kamata a ce suna gidan yari – Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce wasu masu burin zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya kamata a ce suna gidan yari idan da hukumomin da ke yaƙi da rashawa a Najeriya suna aikinsu yadda ya dace.
Tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani babban taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abeokuta jihar Ogun domin bikin cikarsa shekara 85 da haihuwa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
“Na kalli wasu daga cikin mutanen da ke yawo da kuma wadanda mutane ke yawo da su. Idan da EFCC da ICPC za su yi aikinsu yadda ya kamata da kuma goyon bayan ɓangaren shari’a, da yawancinsu suna gidan yari.”
Duk wanda da ba ya da gaskiya a ƙananan abubuwa ba zai iya gaskiya ba manyan abubuwa,” in ji Obasanjo.
Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ce babu wani ɗan takara a yanzu da yake goyon baya, duk da ya ce wasu daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa sun kai masa ziyara suna neman goyon bayansa.
Obasanjo ya kuma ƙaryata rahotannin da suka lissafa wasu ƴan takara a yankin kudu da yake marawa baya.
“A irin wannan hali da muke ciki, ba zan yi gaggawar faɗin sunaye, ba tare da tuntuɓa ba da kuma tabbatar da ingantattun ka'idoji da matakai ba,” in ji shi.
Ana ci gaba da gwabza faɗa a Ukraine
Ana ci gaba da gwabza fada a wasu yankuna da dama na kasar Ukraine.
An kai harin bama-bamai da yawa a Irpin – birnin da ke arewa maso yammaci da Kyiv inda sojojin Rasha ke kokarin kutsawa.
Jama'a da dama sun yi ta tserewa ta hanyar wata gadar ta wucin gadi da ta ratsa kogi, yayin da gadar titin ta lalace.
Putin ya ce duk ƙasar da ta hana shawagin jirage yana nufin ta shiga yaƙin Ukraine
A wani ɓangare na jawabinsa, shugaba Vladimir Putin ya yi gargaɗi ga duniya cewa duk ƙasar da ta saka dokar hana shawagin jirage, yana nufin ta shiga yaƙin Ukraine.
Shugaban na Rasha ya ce "Za mu ɗauki duk wani mataki da aka ɗauka ta wannan hanyar a matsayin shiga cikin yaƙi a kasar."
A ɓangaren soji, dokar hana shawagin jirage na nufin babu wani jirgi da zai shiga ko ratsawa ta yankin da ake yaƙi. Duk jirgin da ya ratsa za a iya harbo shi.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya caccaki Nato kan rashin ayyana hana shawagin jirage, yana mai cewa wannan "rauni ne da rashin haɗin kai."
Nato a nata ɓangaren ta ce wannan zai iya rura wutar yaƙin zuwa wasu ƙasashe.
Birtaniya ta tara wa Ukraine fam miliyan 85 na taimako
An tara sama da fam miliyan 85 a Birtaniya don taimakawa Ukraine.
Kwamitin Gaggawa na Bala'o’i (DEC) - wanda ya ƙunshi ƙungiyoyin agaji na Birtaniya 15 da suka haɗa da Red Cross da Oxfam - sun gode wa duk wanda ya ba da gudummawa tun lokacin da aka kaddamar da gidauniyar a ranar Alhamis domin tallafawa Ukraine
Kwamitin ya ce an tara kuɗin bayan kiran da Sarauniya da Yariman Wales, da Duke na Cambridge, da kuma dubban jama'a suka yi.
Jimillar kuɗin sun ƙunshi fam miliyan 25 da gwamnatin Birtaniya ta bayar.
An kuma yi kira ga al’ummar ƙasar su ci gaba da bayar da agaji, inda kwamitin ya yi gargaɗin cewa za a fi buƙatar taimakon nan watanni zuwa shekaru masu zuwa.
Gwamnatin Legas na bincike kan waɗanda suka raba man fetur a wurin biki
Gwamnatin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarakuna a matsayin kyautar halartar biki.
Kwamashinan Yaɗa Labarai na Legas, Gbenga Omotoso, ya ce "shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi".
A 'yan awannin da suka gabata ne bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarakunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. Daily Trust ta ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar naɗa ta a matsayin Erelu Okin.
Yanzu haka 'yan Najeriya na fama da ƙarancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka.
Labarai da dumi-dumi, Shugaba Putin ya ce ba shi da niyyar saka dokar soja a ƙasar
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce ba shi da niyyar saka dokar soja a ƙasarsa.
Da yake ganawa da ma'aikatan kamfanin jirgi na Aeroflot, shugaban ya ce za a ɗauki wannan matakin ne kawai "idan aka kawo hari daga ƙasar waje ta hanyar soja".
An yi ta yaɗa jita-jita cewa Putin zai saka dokar soja ko kuma marshal law a Turance - inda za a dakatar da duk wata dokar farar hula ko kuma sojoji su karɓe mulki.
Ya ƙara da cewa akwai sauran hanyoyi da za a iya amfani da su wajen "hari daga ƙasar waje", amma duk da haka ba shi da niyyar saka dokar.
Mai kuɗin duniya na fuskantar matsi don ya toshe kafofin labaran Rasha
Ma kuɗin duniya Elon Musk ya ce kamfaninsa Sterlink mai samar da layin intanet ba zai toshe kafofin yaɗa labarai na Rasha ba duk da matsin lambar da yake fuskanta daga wasu ƙasashe.
Mista Musk ya ce wasu ƙasashe sun neme shi da ya yi hakan, amma ban da Ukraine a cikinsu.
"Wasu gwamnatoci sun faɗa wa [kamfanin] Sterlink (ban da ta Ukraine) ya rufe kafofin yaɗa labarai na Rasha," in ji attajirin. "Ba za mu yi haka ba sai an saka mana bindiga."
Ya ƙara da cewa kamfanin nasa "cikakken mai ba da 'yancin ra'ayi ne".
'Yan kishin ƙasa a Ukraine ne suka hana fararen hula fita daga Mariupol - Rasha
Da safiyar yau Asabar mataimakin magajin gari Mariupol ya faɗa wa BBC cewa Rasha ta ci gaba da yin luguden wuta a yankinsu duk da sanarwar tsagaita wuta da aka ce ta fara aiki da ƙarfe 7:00.
Sai dai ma'aikatar tsaron Rasha na bayyana wani abu daban da wannan.
Ta ce 'yan kishin ƙasa a Ukraine ne suka hana fararen hula ficewa daga garin, a cewar kamfanin labarai na Rasha, Ria.
Ma'aikatar ta ce an kai wa dakarun Rasha hari bayan ta ayyana tsagaita wuta don fararen hula su fita daga yankin.
BBC, CNN da kafofin labaran Yamma sun dakatar da aiki a Rasha
Gidajen talabijin na CNN da ABC da CBS da ke Amurka sun ce sun dakatar da yaɗa shirye-shirye daga Rasha yayin da aka ƙaddamar da wata doka da za ta hukunta masu yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda kamfanin labarai na Rasha TASS ya ruwaito.
Tun farko BBC ta ce ta dakatar da aiki a cikin Rasha amma za ta ci gaba da aiki daga wajen ƙasar.
"CBS ta dakatar da watsa labarai daga Rasha yayin da muke ci gaba da duba abubuwan da ke faruwa ga tawagarmu da take can saboda sabuwar dokar da aka kafa a yau," a cewar CBS.
Shi ma ABC ya ce "sakamakon sabuwar dokar tantancewa a Rasha a yau, wasu daga kafofin yaɗa labarai na Yamma ciki har da ABC sun daina yaɗa labarai daga ƙasar".
Tun farko CNN ta sanar da dakatar da yaɗa labarai daga Rasha, sai kuma kafar labarai ta Bloomberg ta ce ma'aikatanta sun dakatar da aiki a ƙasar.
Labarai da dumi-dumi, Ukraine ta ce Rasha ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Mariupol
Rahotannin da suke shigowa na cewa tsagaita wutar da aka sanar ba ta aiki a Mariupol.
"Dakarun Rasha na ci gaba da yi mana luguden wuta da makaman atilare. Abin ya ƙazanta," a cewar mataimakin magajin garin Serhiy Orlov.
"Babu wata tsagaita wuta a Mariupol har ma da duka kewayensa. Mutanenmu sun shirya don tserewa amma ba za su iya fita ba cikin wuta," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Mutum kusan 9,000 ne za su gudu daga Mariupol - Hukumomi
Mataimakin magajin garin Mariupol, Serhiy Orlov, ya faɗa wa BBC cewa suna sa ran kusan mutum 9,000 ne za su tsere daga garin idan tsagaita wuta ta ɗore.
"Tattaunawar tsagaita wuta ta gudana cikin dare, kuma mun tabbatar za ta fara aiki da ƙarfe 9:00," in ji Mista Orlov.
"Nan take muka fara shirin fitar da mutane. Mun tanadi motocin bas 50 kuma muna tunanin mutum 5,000 zuwa 6 za su iya fita zuwa Zaporizhzhia.
"Muna ganin mutane za su iya fita a motocinsu. Muna tunanin jumillar mutum dubu 7 zuwa 9,000 za su iya ficewa idan har tsagaita wutar ta ɗore.
"Babu jiragen ƙasa saboda dakarun Rasha sun lalata layukan dogo."
'Yan Ukraine 66,000 ne suka koma gida don kare ƙasarsu - Ministan tsaro
Yayin da dakarun Rasha suka ninninka na Ukraine, 'yan Ukraine ɗin mutum 66,000 ne suka koma gida don kare ƙasarsu, a cewar Ministan Tsaro Oleskii Reznikov.
Daga cikin waɗanda suka koma ɗin har da Yuriy Vernydub, kociyan tawagar ƙwallon ƙafa ta Sheriff Tiraspol mai shekara 56 wanda ya doke Real Madrid a Champions League.
Ya ce ya koma Ukraine ne bayan ɗansa ya kira shi don ya faɗa masa cewa Rasha ta kai hari.
Ƙarin 'yan Najeriya 174 daga Ukraine sun sauka a Abuja
Rukuni na biyu na 'yan Najeriya ya isa Abuja daga ƙasar Hungary bayan sun tsallaka ƙasar daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake tafkawa a can.
Mutanen waɗanda mafi yawansu ɗalibai ne, sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da misalin ƙarfe 11:50 na daren ranar 4 ga watan Maris, a cewar hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.
Najeriya ta ce tana yunƙurin kwaso 'yan ƙasarta kusan 5,000 daga ƙasashe maƙotan Ukraine, inda za a kashe aƙalla naira biliyan uku da rabi.