An kama hodar cocaine ta kimanin $8.7m a Jamhuriyar Nijar

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Sai ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni da suka shafi rayuwarku.

    Mu kwana lafiya.

  2. An gano jaririn da aka jefar a bandakin cikin jirgi

    Jariri

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatan filin jirgin saman Mauritius sun gano wani jariri sabon haihuwa da aka jefar da shi a cikin sharar da ke ban-dakin cikin jirgi.

    An tsare wata mace mai shekara 20 'yar kasar Madagascar, wadda aka yi zargi ta haifi jaririn a cikin jirgin.

    Jirgin na kamfanin Air Mauritius, wanda ya isa kasar daga Madagascar, ya sauka a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sir Seewoosagur Ramgoolam International ranar 1 ga watan Janairu.

    Ma'aikatan jirgin sun gano jaririn ne lokacin da suke bduba jirgin kamar yadda ake yi a ko da yaushe.

    Daga nan suka garzaya da jaririn asibiti domin a kula da lafiyarsa.

    Matar da ake zargi da haihuwar jaririn, wadda da farko ta musanta haihuwarsa, an gudanar da gwaje-gwaje a kanta wadanda suka tabbatar da cewa ita ta haife shi.

  3. Dole a hukunta Trump bisa kisan Soleimani - Raisi

    Raisi

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya ce dole a hukunta tsohon shugaban Amurka Donald Trump bisa kisan babban janar din sojin kasar Qassem Soleimani shekaru biyu da suka wuce, idan ba haka Iran za ta yi ramuwar gayya.

    A wani jawabi da ya gabatar ta gidan talbijin ranar Litinin, shugaban shugaban kasar ta Iran ya ce “babban mai laifi kuma makashi” wanda ya bayar da umarnin kai hari da jirgi maras matuki a kan jerin gwanon motocin Soleimani a Iraq, Trump dole ne ya fuskanci “shari'ar Allah” sannan ya fuskanci “qisas”, wanda a Musulunce yake nufin ramuwar gayya.

    Raisi ya yi kira a kafa “kotun adalci” wadda Trump, da tsohon Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo da sauran jami'an kasar za su gurfana a gabanta sannan a hukunta su.

  4. An kama hodar cocaine ta kimanin $8.7m a Jamhuriyar Nijar

    Bazoum

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar 'yan sandan Jamhuriyar Nijar ta kama hodar cocaine mai nauyin fiye da kilogiram 200 wadda kudinta ya kusa $8.7m a cikin motar wani magajin gari, a cewar wasu majiyoyin 'yan sanda.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda ya rawaito wannan labari ranar Litinin, ya kara da cewa an kama magajin garin da direbansa, wadanda suke cikin motar, da kulli 199 na hodar cocaine a wani wajen binciken ababen hawa da ke wajen birnin Agadez ranar Lahadi.

    Wata sanarwa da ta fito daga ofishin da ke yaki da miyagun kwayoyi na kasar ya tabbatar da kama fiye da kilogiram 200 na cocaine a Agadez, kodayake bai yi karin bayani ba.

    Wasu kasashen Yammacin Afirka sun kasance hanyar da ake bi wajen safarar miyagun kwayoyi daga Kudancin Amurka zuwa Turai, kuma a 'yan shekarun nan an samu karuwar kama miyagun kwayoyi a yankin.

  5. Hauhawar farashi ta yi ƙaruwa mafi girma cikin 20 a Turkiyya

    Hauhawar farashin kayayyaki na shekara-shekara a Turkiyya ya yi karuwa mafi girma cikin shekara 20 wanda galibi wasu manufofin tattalin arziki na Shugaba Recep Tayyip Erdogan suka haifar.

    Farashin sufuri ya karu da fiye da rabi yayin da farashin kayan masarufi suka karu da sama da kashi 40 cikin 100.

    Bisa tsari, bankuna suna kara yawan kudin ruwa domin magance hauhawar farashin kayayyaki amma sun rage kudin ruwan tsawon wata hudu a jere saboda matsin lamba daga shugaban kasa.

    Mista Erdogan ya bayyana kudin ruwa a matsayin abu maras kyau yana mai nuni da koyarwar addinin Musulunci da ya yi hani a kansa.

  6. Ɗan Kuwait zai maye gurbin ɗan Najeriya Barkindo a shugabancin ƙungiyar OPEC

    OPEC

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC) ta sanar da naɗa Haitham Al-Ghais a matsayin sabon babban sakatarenta.

    Ɗan ƙasar Kuwait ɗin zai maye gurbin ɗan Najeriya Muhammad Barkindo, wanda ya shafe kusan shekara shida a matsayin.

    Zaɓen nasa ya zo ne a jajiberin taron ƙungiyar da ƙawayenta na wata-wata game da ƙalubalen da ƙasashen ke fuskanta na yawan ɗanyen fetur ɗin da suke kaiwa kasuwar duniya.

    Kazalika, man fetur ɗin ya samu tagomashi a ranakun farko na sabuwar shekara, inda farashinsa ya ƙaru zuwa dala 78.34 kan ganga ɗaya.

    Al-Ghais zai kama aiki a watan Agusta na tsawon shekara uku idan wa'adin Barkindo ya ƙare a watan Yuli mai zuwa.

  7. An harbo jirage ɗauke da makamai a Iraƙi da suka nufi sansanin sojan Amurka

    Rahotanni daga Iraƙi na cewa jami'an tsaro sun harbo wasu jirgi biyu marasa matuka ɗauke da makamai yayin da suka nufi wani sansanin sojin Amurka da ke kusa da babban filin jirgin sama na birnin Bagadaza.

    Wasu majiyoyin tsaro a Iraki sun ce babu wanda ya jikkata.

    Yunkurin kai harin na zuwa ne daidai lokacin da aka cika shekara biyu da kisan hafsan sojin Iran, Qassem Soleimani, a wani harin jirgin Amurka maras matuki a Bagadaza.

    Tsohon shugaban Amurka na wancan lokaci, Donald Trump, ne ya ba da umarnin kai harin.

    Janar ɗin mai shekara 62 ya jagoranci ayyukan sojojin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin shugaban runduna ta musamman.

  8. Shugaba Buhari ya yi alhinin rasuwar Bashir Tofa

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa ta'aziyyar rasuwar tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar Bashir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al'ummar Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin "cikakken ɗan kishin ƙasa".

    "Ha zuwa lokacin rasuwarsa, cikakken ɗan kishin ƙasa ne. Ya nemi kafa ingantacciyar Najeriya ga kowa da kowa," a cewar Buhari cikin sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya ji ƙansa sannan ya bai wa iyalai da abokansa haƙurin rashinsa. "Muna addu'ar aƙidarsa ba za ta gushe tare da shi ba," in ji Buhari.

    Kazalika, Buhari ya tura tawagar ta'aziyya zuwa Jihar Kano da ta ƙunshi jami'an gwamnati da suka haɗa da ministan tsaro, ministan harkokin ruwa, babban akanta na ƙasa, da kuma Garba Shehu kakakin fadar shugaban ƙasa.

    Bashir Othman Tofa ya rasu da asubahin Litinin yana da shekara 74 bayan ya sha fama da jinya kuma an yi jana'izarsa a birnin Kano.

    • Bashir Tofa: Hotunan jana'izar tsohon dan takarar shugaban Najeriya
  9. Farashin man fetur ya ƙaru a kasuwar duniya

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen man fetur ya ƙaru da kashi 0.27 cikin 100 zuwa dala 78.34 kan ganga ɗaya gabanin taron ƙungiyar ƙasashe masu arzikin fetur da ƙawayenta ta Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC+) ranar Talata.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an samu ƙaruwar ce a yau Litinin yayin da aka mayar da hankali kan yawan man da ƙasashe za su ci gaba da fitarwa a sabuwar shekarar 2022.

    Rahoton ya nuna cewa farashin samfurin Brent ya ƙaru da 0.72 zuwa 78.34.

    Ana kyautata zaton ƙungiyar OPEC+ za ta ba da shawarar ƙara ganga 400,000 na mai da ake kaiwa kasuwa a kullum a watan Fabarairu, a cewar wasu majiyoyi.

    Ana alaƙanta ƙaruwar farashin da raguwar fitar da mai daga Libya.

  10. Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan zai kai ziyara Saudiyya

    Erdogan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ce zai kai ziyara Saudiyya a watan Fabarairu mai zuwa.

    Da yake amsa tambayoyin wata mace game da wahalhalun shiga da kaya ƙasar daga Saudiyya, Mista Erdogan ya ce za su jira nan da Fabarairu.

    "Bari mu gani, nan da Fabarairu. Ya yi mani alƙawari kuma zan je Saudiyya a Fabarairun," in ji shi.

    Zauren masu hada-hadar shiga da kaya Turkiyya daga Saudiyya ne suka shirya taron da zimmar gano bakin zaren sauƙaƙa harkokin nasu.

  11. Harin mayaƙan Al-Shabab ya kashe mutum shida a Kenya

    Al-Shabab

    Asalin hoton, AFP

    Mutum shida ne suka rasu sannan aka lalata gidaje sakamakon wani hari da mayaƙan ƙungiyar Al-Shabab suka kai a wani gari a Kenya da ke da iyaka da Somalia, a cewar 'yan sanda.

    An yanke kan mutum ɗaya sannan aka harbe ko kuma ƙona wasu biyar a harin da aka kai gundumar Lamu mai nisan kilomita 420 daga birnin Nairobi.

    "Jami'an tsaronmu na bin sawunsu sannan muna neman agaji daga mutanen gari saboda idan muka yi aiki tare za mu fi yin nasara," kamar yadda Kwamashinan 'Yan Sandan Lamu Irungu Macharia ya faɗa wa AFP.

    'Yan sanda sun ce maharan sun caka wa wani shugaba a yankin wuƙa sannan suka cire masa kai tare da ƙona gidansa, kazalika suka harbe wani mutum da aka tsinci gawarsa a gefen titi.

  12. Jam'iyyun siyasa a Mali sun yi watsi da shirin sojoji na ci gaba da mulki

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar haɗakar jam'iyyu a Mali ta yi watsi da shirin sojoji na shafe shekara biyar riƙe da mulki kafin a gudanar da zaɓe.

    Sojoji a Malin sun yi juyin mulki a watan Agustan 2020, inda suka yi alƙawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun 2021.

    Ita ma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta yi barazanar takunkumi mai tsauri ga gwamnatin sojin kan karya alkawarin gudanar da zaben.

    Sai dai sojin sun ce sun ɗauki matakin ne lura da yadda tsaro ke daɗa tabarbarewa a kasar.

  13. Matakan da gwamnati ke ɗauka kan matsalar tsaro sun yi kaɗan - Bashir Tofa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli hira da fittacen dan siyasa Bashir Othman Tofa

    Cikin wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a 2020, Marigayi Bashir Othman Tofa ya ce ya kamata gwamnati ta sauya salon yadda take tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya.

    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce "lokacin matasa ne, su ne ya kamata su yi (zanga-zanga)".

    A cewarsa: "Ba wai cewa muke gwamnati ba ta yin komai ba game da tsaro, muna cewa ne matakan da ake ɗauka sun yi kaɗan, a sauya wasu."

  14. An binne Bashir Tofa a kusa da mahaifansa

    Bash Tofa
    Bayanan hoto, An binne shi a tsakiyar ƙabarin mahaifansa

    An binne Bashir Tofa a kusa da mahaifinsa Zanna Alhaji Othsman Tofa da mahaifiyarsa Hajiya Riqaayya (Inna) da ke maƙabartar da ke kan Titin Katsina.

    An yi jana'izarsa ne a birnin Kano bayan ya rasu ranar Litinin a Asibitin Malam Aminu Kano yana da shekara 74.

    Kano

    Wasu makusantansa sun tabbatar da cewa tsohon dan siyasar ya yi fama da jinya.

    Shi ne tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar 1993 ƙarƙashin jam'iyyar National Republican Convention (NRC).

    A makon jiya ne aka yi ta watsa labarin da ke cewa Bashir Tofa ya rasu, amma daga bisani aka tabbatar bai rasu ba.

    Sarkin Kano
    Bayanan hoto, Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izarsa akwai Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
  15. Duk wanda zai shiga fadar Buhari sai an masa gwajin korona

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Daga yanzu masu kai ziyara Fadar Shugaban Najeriya sai sun yi rigakafin korona kafin a ba su damar shiga fadar mulkin ta Aso Rock Villa da ke Abuja.

    A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, wajibi ne a yi wa duk mai ziyara gwajin a kyauta a bakin ƙofa.

    Cikin waɗanda dokar ta shafa har da gwamnoni da sauran manyan ƙasa sannan kuma ba waɗanda za su ga shugaban ƙasa ba kawai.

    Sai dai ya ce akwai wasu shugabannin ƙasar waje ba lallai sai an yi musu ba "duk da cewa su ma ana ba su shawarar su yi gwajin".

    "Kyauta ake yin gwajin saboda haka babu wanda zai biya ko ƙwandala...duk wani mai ziyara, ba masu ganin shugaban ƙasa kaɗai ba, dole ne ya yi gwajin gaggawa a bakin ƙofa."

  16. Korona ta kashe ƙarin mutum shida a Najeriya

    Mutum shida ne suka rasu a Najeriya ranar Lahadi sakamakon cutar korona, a cewar alƙaluman hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Rahoton da NCDC ta wallafa ya nuna cewa ƙarin wasu mutum 573 sun harbu da cutar.

    Mutanen sun fito ne daga jiha bakwai na ƙasar. Su ne:

    • Legas (281)
    • Benue (202)
    • Kano (61),
    • Borno (20)
    • Jigawa (5)
    • Edo (2)
    • Oyo (2)

    Ya zuwa yanzu jumillar mutum 243,450 ne suka kamu da cutar a Najeriya yayin da ta yi ajalin mutum 3,039.

  17. Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus

    Abdalla Hamdok

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Sudan ya yi murabus mako shida bayan sojojin sun mayar da shi kan mulki.

    A wani jawabi da ya yi kai-tsaye ta kafar talabijin, Abdalla Hamdouk ya ce akwai bukatar a sake zama don lalubo wasu hanyoyin tabbatar da cewa Sudan ta dawo tantagaryar demokuradiyya.

    Ya ce ya yi iya kokarinsa na ganin kasarsa ba ta fada rikici ba, amma ga alama hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

    Jawabin Mista Hamdouk na zuwa a daidai lokacin da rahotanni suka tabbatar da cewa jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga biyu a Oumdurman.

    Wakilin BBC ya ce kawo yanzu zanga-zangar da ake ta yi a Sudan ta yi sanadin kisan akalla mutum 56.

  18. Assalamu Alaikum

    Fatan kun shigo shafin rahotanni kai-tsaye tare da Umar Mikail.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.