Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 a jihar Edo

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Tukur

  1. Rufewa

    A nan za mu yi bankwana da ku a wannan shafin.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe Juma'a inda za mu ci gaba da kawo maku labarai daga Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

  2. Duke Na Edinburgh Philip zai yi kwanansa na uku a asibiti

    Ana sa rai Duke na Edinburgh zai yi kwana na uku a asibiti bayan da aka kwantar da shi ranar Talata.

    Zamansa a asibiti ba shi da alaƙa da cutar korona kuma wata majiyar fadar ta ce Duke din da kansa ya taka ya shiga asibiti.

    Ana sa rai zai zauna a asibiti tsawon kwanaki don a duba shi kuma ya samu hutu.

    Sarauniyar mai shekaru 94 ta kasance a Windsoe Castle.

    A watan jiya ne aka sanar cewa Sarauniya Elizabeth da mijinta Philip sun yi allurar riga kafin cutar korona a fadarsu ta Windsor.

  3. An kama babbar mota maƙil da magungunan bogi a Kano

    Hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki ta jihar Kano (KCPC) ta kama wata babbar mota trailer ɗauke da magungunan bogi da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 50 a jihar Kano.

    Wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakin hukumar Nabilusi Abubakar K/Na'isa ta ce an kama motar ne da misalin karfe 3:30 na tsakar daren Alhamis aunguwar sabon gari.

    Haka kuma tsanarwar ta ce direban motar da masu motar sun tsere sun bar motar a nan bayan da jami'an hukumar suka kama su.

    Sanarwar ta ce muƙaddashin shugaban hukumar, Alhaji Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana cewa sun kama motar ne bayan da suka samu bayanan sirri dangane da safarar magungunan.

  4. EFCC ta gano wata makarantar koyon zamba ta intanet a Abuja

    Hukumar EFCC ta gano wata cibiyar horon masu zamba ta intanet a unguwar Mpape da ke Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta Najeriya ta ruwaito.

    Jami'an EFCC ɗin sun gano cibiyar ne bayan da suka samu bayanan sirri sannan suka far wa wurin ranar Alhamis suka kama mutane 27.

    Wannan na zuwa ne ƴan makonni bayan hukumar ta gano wata makarantar koyon aikin zamba ta intanet a yankin Bwari a Abuja inda mutum 10 ke koyon yadda ake damfarar mutane ta shafukan intanet.

    Wata sanarwa da kakakin EFCC Wilson Uwujaren ya fitar ta bayyana cewa cibiyar ta Mpape na ƙarkashin kulawar wani Emmanuel Clement ne mai shekaru 30 kuma mafi yawa ɗalibansa matasa ne da suka kammala karatun sakandire da shekarunsu ba su haura 25 ba.

    An gano wayoyin hannu na salula 30 da komfuta 1 da mota kirar toyota venza ɗaya a cibiyar.

  5. Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 a jihar Edo

    Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum bakwai a jihar Edo a Najeriya ranar Laraba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da manoma a Ugboke da Oshodi da Okokodo da Ariyan da Yoruba Camp a ƙaramar hukumar Ovia North-East a jihar.

    Wata ganau Misis Janet Ighodaro ta bayyana cewa ƴan bindigar waɗa ake zargi makiyayay ne sun fara aiwatar da hare-haren nasu ne a unguwar Yoruba Camp.

    Ta ce mutum huɗu cikin wanda aka kashe suna hnayarsu ta dawowa ne daga gona lokacin da maharan suka harbe su.

    Ta ce ita kanta sa'a ta yi ta tsira inda yanzu take birnin Benin a wajen ƴan uwanta.

    Jami'in hulda da jama'a na jihar SP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce suna gudanar da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin.

  6. Babban hafsan sojin Uganda ya nemi afuwa kan cin zarafin ƴan jarida da jami'an tsaro suka yi

    Babban hafsan sojin Uganda ya nemi afuwa kan cin zarafin ƴan jarida da dama da jami'an tsaro suka yi lokacin da suke daukar rahoto a wani taro da ƴan adawa suka shirya.

    Al'amarin da aka naɗa a hotunan bidiyo ya faru ne a wajen ginin Ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD lokacin da dan adawar nan kuma mawaki Bobi Wine ke gabatar da korafi kan cin zarafi.

    An jikkata yan jarida shida bayan lakadamusu duka da sanduna. Janar David Muhoozi ya ce babu hujjar aikata irin wannan cin zarafi kan yan jaridar don haka sojojin za su biya kudin magunguna da kula da su a asibiti.

    MDD ta yi Allah-wadai da faruwar lamarin tare da bukatar daukan matakan hukunci.

  7. Mece ce mafita ga matsalar tu'ammali da ƙwayoyi a Najeriya?

    A Najeriya, matsalar tu'ammali da miyagu ƙwayoyi sai karuwa ta ke yi.

    Sai dai an saba cewa gwamnatoci ne ke daukar matakan kawar da wannan matsala da kawo yanzu ta zama karfen kafa ga al'umomin arewacin kasar.

    Amma wasu kungiyoyin matasan arewacin Najeriyar sun gudanar da wani taro a Abuja, babban birnin kasar, inda su ka hada kan hukumomin gwamnati kamar Hukumar da ke kula da Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA, da Majalisar Dinkin Duniya, da gwanatocin jihohi da hadakar kungiyoyin matasan arewacin kasar domin samar da sabbin dabarun magance wannan da ke son gagarar .

    Sani Aliyu ya halarci taron, ga kuma rahotonsa

  8. Kallon da ƴan Nijar ke yi wa shugabancin Muhammadu Isoufu na shekara 10

    Yayin da ake shirin gudanar da zaben sabon shugaban kasa a Jumhuriyyar Nijar, shi kuma Shugaba Muhammadu Isoufu na shirin sauka daga kan karaga, bayan ya shafe shekara goma yana mulkin kasar.

    Sai dai ra'ayi ya bambanta dangane da yadda al'ummar kasar ke kallon zamanin nasa, kasancewar wasu ƴan kasar na cewa an ci gajiya, wasu kuma na ganin akasin haka.

    A watan Afrilun 2011 ne Shugaba Muhammadu Isufu ya fara wa'adin mulkinsa na farko a matsayin shugaban kasar Nijar a karkashin tutar jam'iyyar PNDS Tarayya, har zuwa shekara ta 2016 inda ya samu wa'adin mulki na biyu.

    Ga shi yanzu ana maganar zai kammala cika shekara 10 yana mulkin Nijar a watan Afrilu mai zuwa.

    Duk da cewa kowa da yadda yake kallon tafiyar gwamnatin, amma jam`iyyarsa ta PNDS na cewa Nijar ta samu gagarumin ci gaba a zamanin Shugaba Muhammadu Isoufu.

    Amma babbar jam'iyyar hamayya ta RDR Tchanji cewa ta yi ba ta ga wata nasara ko gajiyar da mulkin shugaba mai barin gadon ya tsinana ba.

    Hon Abdurrahim Balarabe shi ne kakakin jam'iyyar a jihar Damagaram.

    Haka dai ake samun irin wannan bambancin ra'ayin a tsakanin al'ummar Nijar.

    A watan Afrilu mai zuwa ne Shugaba Muhammadu Isofu zai kammala wa'adin mulkinsa, wanda ko ba komai jam'iyyarsa ta PNDS na jinjina masa, saboda shi ne ya jagorance ta har ta kafa gwamnati a karon farko a jamhuriyyar.

  9. Masu ɗinki na son a hana shigar da kayan gwanjo Afirka

    Wani ƙiyasi da aka yi ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na kayan gwanjo da ake bayar wa don a raba yawanci Afirka ake kawo su.

    Kuma an shafe gomman shekaru mutane a faɗin nahiyar na maraba da waɗannan kayayyaki da yawanci ake shigar da su daga Amurka ko Turai.

    Sun zama gata da abin tunƙaho ga waɗanda ba sa iya sayen sabbin kaya.

    “Mutane sun fi son kayan gwanjo, saboda sun fi sababbi araha,” a cewar Grace Nsonga, wata mai sana’ar sayar da kaya a Lilongwe, Malawi.

    Sai dai rabi kayan da ake aika wa don sadakarwar ana sayar da su ne ga mutane maimakon ba su kyauta.

    Mcau ɗinki da masu tallar kayan ƙawa sun ce rububin kayan gwanjo da mutane ke yi yana kashe musu kasuwa.

    Shi ya sa da yawansu ke son a haramta shigar da kayan gwanjon, ko kuma a taƙaita.

  10. Wani matashi ya kashe kansa a Kano

    Rundunar ƴan sandan jihar Kanon Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani mutum Sabi’u Aminu mai shekara 60 da ake zargin ya rataye kansa a gidansa a Kano.

    Rudunar ƴan sanda ta ce bayan samun labarin faruwar al’amarin ne suka isa gida kuma suka tafi da shi zuwa asibitin Sir Muhammad Sanusi, inda likitoci suka tabbatar musu da cewar ya rasu.

    Ƴan sandan dai daga bayanan da suka tattara sun nuna cewa marigayin na sana'ar gyaran tayar mota da babur, a unguwar da yake da zama.

    Ku latsa alamar lasifikar da ke ƙasa don sauraron rahoton Khalifa Shehu Dokaji daga Kano:

  11. Matsakaicin shekarun da mutane ke yi a Amurka ya ragu da shekara guda

    Matsakaicin shekarun da mutane ke yi a Amurka ya ragu da shekara guda a watanni shida na shekarar 2020, raguwar da ba a taɓa gani ba tun yaƙin duniya na biyu.

    Kididdigar wucin gadi da gwamnati ta fitar ta nuna cewa lamarin ya fi shafar tsirarun ƙabilu, inda Amurkawa bakaken fata suke asarar kusan shekara uku, ƴan latin Amurka kuma ke rasa shekara biyu na matsakaicin shekarunsu.

    Kwararu na danganta sauyin da ake gani da annobar cutar korona, da kuma ƙaruwar mace-mace da ake samu sakamakon tu’ammali da ƙwayoyi, bugun zuciya da cututtukan da annobar cutar korona ta zo da su.

  12. Yunwa na addabar mutanen Syria

    Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce sabbin alƙaluma sun nuna yadda ake samun ƙaruwar wadanda ke shiga cikin matsanancin yunwa a Syria.

    Sama da mutum miliyan 12 - kaso 60 cikin 100 na ƴan kasar - na fuskantar ƙarancin abinci.

    Wakilin BBC ya ce hukumar ta ce bayan shekara 10 ana yaƙi, iyalai sun ƙarar da ajiyarsu, sannan sun shiga yanayi mai wahala na tsadar rayuwa.

    Tsadar abincin da zai ciyar da iyalai a wata guda ya zarta matsakaicin kudin shigarsu.

  13. Sanatoci sun yi kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta kafa dokar ta-ɓaci kan tsaro

    Majalisar Dattijan Najeriya ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta kafa dokar ta-ɓaci a ɓangaren tsaro bayan sace ɗalibai da malaman kwalejin Kagara.

    Ta yi wannan kira ne bayan wani ƙuduri da Sanata Muhammad Sani Musa mai wakiltar Neja ta Gabas ya gabatar a zaman majalisar na jiya Laraba.

    Ya bayyana kyakkyawan fata ga ƙoƙarin jami'an tsaro na kuɓutar da ɗaliban Kagara, inda ya ƙara da cewa jazaman ne kuma sai hukumomi sun ɗauki ƙwararan matakai don murƙushe ayyukan ƴan fashin daji cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

  14. Rikicin manoma da makiyaya ya lafa a Chadi

    Yanayin rikici da ya yi zafi tsakanin manoma da makiyaya a kudancin Kasar Chadi ya fara sanyaya bayan Hukumomi sun aika jami’an tsaro domin shiga tsakanin bangarorin.

    Rikicin na bana ya ɓarke ne a lokacin da jami’an ma’aikatar kiwo tare da kansilolin jihohin kasar ke halartar wani taro domin tattauna matsalolin da sana’ar kiwo ke fuskanta a Kasar Chadi.

    Rikicin ya haifar da mutuwar mutum 35 daga ɓangarorin biyu tare da soja ɗaya.

    Latsa hotonda ke ƙasa don ku saurari rahoton Mahaman Babalala:

  15. 'Yan bindiga sun sake kai hare-hare a Jihar Neja

    Ƙasa da kwana ɗaya bayan sace mutum 42 a makarantar sakandare ta Kagara da ke Jihar Neja, 'yan bindiga sun sake kai wa mazauna yankin Shiroro hare-hare.

    Rahotanni na cewa an kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu, inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, a cewar Sani Abubakar Yusuf Kokki, shugaban ƙungiyar matasan Shiroro.

    Shugaban matasan ya faɗa wa BBC cewa maharan sun shiga ƙauyukan Kokki da Gurmana da Bakin Kogi a daren Laraba suna harbi kan mutane.

    "Mun ga mutum uku da aka harba da bindiga, ciki har da wata mace da aka harba a ido, da wani kuma kafaɗa, sai kuma wani da aka kai shi babban asibiti na birnin Minna saboda tsananin raunin da aka ji masa," a cewarsa.

    Ya ƙara da cewa akasarin waɗanda abin ya ritsa da su 'yan gudun hijira ne da suka fita neman abinci a ƙauyukan da ke tsallaken kogin Shiroro.

    Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya da ta Neja ke tattaunawa da 'yan fashin da suka yi garkuwa da ɗalibai da malaman makarantar sakandare ta Kagara da aka sace a daren Talata.

  16. Jihar Sokoto na shirin kafa hukumar Hisbah

    Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta amince da ƙudirin dokar kafa hukumar Hisbah a jihar.

    Matakin ya biyo bayan yarjewa da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin addini da taimakon na kare haƙƙi yayin zamanta na yau Alhamis.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ambato Honarabul Abubakar Yabo, shugaban kwamitin, na cewa sai da suka nemi shawarwari daga masu ruwa da tsaki kafin su cimma matsaya.

    Kafatanin 'yan majalisar ne suka amince da ƙudirin bayan sun jefa ƙuri'a da muryoyinsu.

    Jihohin arewacin Najeriya irinsu Kano da Jigawa da Zamfara na da hukumomin Hisbah, wadda ke tabbatar da bin dokokin Shari'ar Musulunci.

  17. An cafke wasu ‘yan Malawi kan naɗe furannin a cikin takardun kudin kasar

    ‘Yansanda a kasar Malawi sun cafke mutane hudu sakamakon kama su da aikata laifin amfani da takardun kudi wajen kawata damen furannin kallo na ranar masoya wato ‘Valentine’s Day’.

    Hotunan furannin kallon da aka nade a cikin takardun 2,000 na kudin kasar kwaca – kwatankwacin sama da dala biyu da rabi sun mamaye dandalin WhatsApp a kasar ranar Lahadi.

    Babban jami’i a sashen bincike na babban bankin kasar ta Malawi Emmanuel Malasa ya ce ofishinsa ya gudanar da binciken hadin gwiwa tare da jami’an ‘yansanda wajen cafke mutanen saboda lalata wulakantawa da lalata takardun kudin kasar.

    A baya dai babban bankin ya ce maye gurbin takardun kudin da suka lalace na da matukar tsada.

    ‘Yansanda sun ce ana zargin wadanda aka cafke a dandalin Blantyre da aikata laifin ‘’amfani da kudin kasar ta haramtacciyar hanya’’ kuma akwai yiwuwar a ci tarar su kwaca biliyan biyar kwatankwacin dala miliyan shida da kusan rabi idan aka same su dumu-dumu da aikata laifin.

    Duka mutanen hudu dai bas u amince cewa sun aikata laifin ba.

  18. Labarai cikin minti ɗaya

    • Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta amince da fara amfani da rigakafin cutar korona ta kamafanin Oxford/AstraZeneca a ƙasar. Shugabar NAFDAC, Dr. Mojisola Adeyeye, ita ce ta bayyana hakan a yau Alhamis cikin wani jawabi da ta gabatar kai-tsaye ta talabijin.
    • Gwamnatin Jihar Neja da ta Tarayyar Najeriya sun fara tattaunawa da 'yan bindigar da suka sace ɗliban makarantar Kagara. Rahoton jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa gwamnatocin na tattaunawar ce ta hannun wasu shugabannin Fulani da tubabbun ‘yan fashin daji a matsayin masu shiga tsakani bayan sace ɗaliban a daren Talata.
    • Firaministan Australia Scott Morrison ya mayar da martini ga Facebook kan hana wa masu amfani da shi karanta labarai a shafin a cikin kasar. Ya siffanta matakin da cewa “girman kai ne” kuma “abin haushi”.
    • Anjima a yau Man United za ta fafata da Real Socieded a gasar Zakarun Turai ta Europa. Sai kuma Arsenal ta kara da Benfica, yayin da Tottenham za ta gwabza da RZ Pellets WAC.
  19. Kotu ta kori ƙarar Sheikh Abduljabbar kan ɗaurin da gwamnati ke yi masa

    Babbar Kotun Tarayya a Najeriya da ke zamanta a Kano ta kori ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar gabanta yana neman ta umarci gwamantin Kano ta cire ɗurin talalar da take yi masa.

    Mai Shari'a Lewis Alagoa ya kori ƙarar ce bayan lauyan Abduljabbar, Rabi'u Shu'aibu Abdullahi, ya gabatar da buƙatar mai ƙarar ta janye ƙorafin nasu daga gaban kotun.

    Lauyoyin da ke kare gwamnati ba su yi wata-wata ba suka amince da buƙatar kuma nan take mai shari'a ya kore ta.

    A ranar Alhamis da ta gabata ne shehin malamin ya shigar da ƙarar da zummar neman kotu ta tilasta wa gwamnati da kwamishinan 'yan sanda da shugaban tsaro na hukumar DSS a Kano da su janye jami'an su da suka girke a kofar makarantarsa da gidansa a unguwar Filin Mushe.

    Gwamnatin Kano na tsare da malamin ne a gidansa biyo bayan zarginsa da "kalaman tayar da fitina" game da lamuran Musulunci a farkon watan Fabarairu.

    Malamin ya musanta zargin sannan ya buƙaci a haɗa muƙabala tsakaninsa da sauran malamai a jihar, buƙatar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince kuma ya ce gwamnati za ta saka rana da wurin da za a gudanar da ita.

  20. Yadda za ku buɗe shafin BBC Hausa na intanet a kan Opera Mini

    A ƴan kwanakin nan masu bibiyar shafin www.bbchausa.com da dama a kan mahnajar Opera Mini a intanet ba sa iya buɗe shi, ko kuma idan sun buɗe ba sa iya ganin labaran da ke kansa.

    Wannan na faruwa ne saboda wasu matsaloli na na'ura. Sai dai BBC Hausa ta samo muku mafita dangane da hakan, ta yadda za ku iya ci gaba da buɗe shafin ba tare da wata tangarɗa ba, da samun damar ci gaba da karanta labaran da muke wallafa muku.

    Ga matakan da za ku bi dalla-dalla:

    • 1. Idan kuka sanya adireshin www.bbchausa.com a shafin Opera Mini za ku ga ya nuna fari babu komai a kai
    • 2. Sai ku je can kasan shafin inda za ku ga tambarin Opera Mini da launin ja, sai ku latsa shi
    • 3. Daga nan zai shigar da ku wajen da za ku ga "settings"
    • 4. Bayan kun shiga settings ɗin sai ku dinga duba rubutun har ku zo kan "Data Savings"
    • 5. Bayan kun shiga "Data Savings" za ku ga inda aka rubuta "automatic" sai ku latsa gefensa
    • 6. Daga nan za ku ga an sa automatic da "high" da kuma "off"
    • 7. Sai ku latsa "high" din ko "off". 7.
    • 8. Sai ku koma baya wajen ainihin shafin sannan ku sabunta shi (reload kor refresh)"
    • 9. Shi kenan za ku ga shafin www.bbchausa.com ya buɗe da labaran da aka wallafa