Masu aikin ceto suna ta ƙoƙarin tserar da fiye da motoci 1,000 da suka maƙale a kan wani babban titi tsawon kwana biyu bayan zubar dusar ƙanƙara a Japan.
Hukumomi sun rarraba abinci da man fetur da barguna ga direbobin a kan titin na Kanetsu, wanda ya haɗa babban birnin ƙasar Tokyo da kuma Niigata da ke arewaci.
Dusar ƙanƙarar da ta fara zuba ranar Laraba, ta jawo cushewar ababen hawa a kan titin.
Lamarin ya sa fiye da gidaje 10,000 a arewa da yammacin ƙasar sun rasa wutar lantarki.
Kafar yaɗa labarai ta Kyodo ta ruwaito cewa an samu cunkoso a ɓangarori daban-daban na babban titin Kanetsun.
Cunkoson ya fara ne bayan da wata babbar mota ta maƙale a cikin dusar ƙanƙarar ranar Laraba da daddare.
Wasu kafofin sun ce cunkoson ababen hawan ya kai har tsawon kilomita 16.5km a kan titin.
Jami'ai sun yi ta amfani da na'urori da dama don ciro motocin da suka maƙale ɗaya bayan ɗaya, amma kusan motoci 1,000 har yanzu suna nan maƙale a kan titin har zuwa ranar Juma'a da rana.