Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An yi saukar Kur'ani da addu’o’i miliyan 41 kan Boko Haram a Borno

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe Idan Allah ya kai inda za mu shafe yinin Litinin muna kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da suka shafe ku.

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a yinin Lahadi.

  2. Ganduje ya nemi Jami’ar Amurka ta hukunta wanda ya ba shi farfesan bogi

    Rikici ya kaure tsakanin tsakanin gwamnatin Kano da kuma Jami'ar East Carolina da ke Amurka kan batun ba gwamnan jihar matsayin Farfesa.

    Gwamnatin Kano ta nemi jami'ar ta bayar hakuri kan musanta ba gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje matsayin Farfesa inda ta ce ranta ya ɓaci kan naɗin farfesan da ya so kunyata gwamnan.

    A makon da ya gabata ne sakataren watsa labarai na jihar Kano, Abba Anwar ya fitar da wata sanarwa da ke cewa Jami'ar East Carolina a Amurka ta ba Ganduje matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira "ƙwarewarsa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al'umma".

    Kuma a cewar sanarwar, matsayin Farfesan na gwamnan ya shafi bayar da shawarwari ga ɗalibai masu digiri na uku, da kuma ƙananan malamai.

    Sai dai daga baya jami'ar ta Amurka ta musanta cewa ta bai wa Gwamnan na Kano matsayin farfesa da kuma aikin koyarwa a jami'ar, bayan bin diddigi da Jaridar Premium Times ta yi.

    Jami'ar ta ce wasikar da wani ma'aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta samu amincewar mahukuntar jami'ar ba.

    Wata sanarwar daga sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji, gwamnatin Kano ta buƙaci jami'ar ta hukunta jami'in jami'ar da ya aiko wa gwamnan da takardar tabbatar masa da matsayin Farfesa domin ya nemi ya ƙunyata gwamnan da kuma al'ummar jihar Kano.

    Sanarwar ta kuma ce gwamnan ba shi ya nemi matsayin a jami'ar ba.

  3. An yi saukar Kur'ani da addu’o’i miliyan 41 kan Boko Haram a Borno

    Mutanen Borno sun yi addu’oi sama da miliyan 41 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya domin neman kawo ƙarshen masifar da mayakan kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.

    Wata ƙungiya ce mai suna Borno Concerned Citizen wato ƴan jihar da suka damu da halin da take ciki ta jagoranci taron addu’o’in a ranar Lahadi.

    Barista Zahra Maiduguri ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci addu’o’in ta ce an yi saukar Al ƙur’ani da kuma addu’oi 41, 837,016 domin neman sauƙin masifar da jihar take ciki.

    Daga cikin addu’o’in har da “Istigifari” miliyan 13,669,000 da “Ya Laɗifu” miliyan 10,688,00.

    An kuma yi “Ya Kahharu” fiye da miliyan ɗaya da salatin Annabi da kuma salatil fati.

    Baya ga addu’u’oin an kuma yanka dabbobin shanu da nufin yin sadaka domin Allah ya biya buƙata.

    Ƙungiyar ta kunshi shugabanni na siyasa da na gargajiya da malaman addini da malaman Boko a jihar Borno.

    Mayakan Boko Haram sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

    Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane da kana suka raba miliyoyin jama'a da gidajensu.

    Harin Zabarmari inda ƙungiyar ta yi wa manoma yankan rago shi ne hari na baya-bayan nan mafi muni da Boko Haram ta kai a jihar Borno.

  4. Daular larabawa ta ce tana fuskantar hare-hare ta intanet bayan ƙulla alaƙa da Isra’ila

    Gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce ta fi fuskantar hare-hare ta intanetbayan ƙulla alaƙar da ta yi da Isra’ila a watan Satumba.

    Muhammad Hamad al-Kuwaiti babban jami’in kula da tsaro ta Intanet na Daular Larabawa ne ya bayyana haka a Dubai a wani taron tsaro da ƙasashen yankin ke gudanarwa.

    Ya ce ƙulla alaƙa da ƙasarsa ta yi da Isra’ila ya jefa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa cikin fuskantar barazanar daga mahara.

    Sai dai jami’in bai yi cikakken bayani ba game da hare-haren, ko an gano masu kutsen.

  5. Shugabannin Yarabawa sun yi taron ƙara haɗin kansu

    An kammala taro game da ƙara hadin kan Yarbawa da kuma kawo ci gaban matasa a wannan shiryar kudu maso yammaci.

    Wakilin BBC Umar Shehu Elleman ya ce taron wanda aka gudanar ranar Lahadi ya ƙunshi har da shugabannin Hausawa da Fulani mazauna yankin domin neman ƙara haɗin kansu ga samar da tsaro da zaman lafiya a yankin na Yarabawa

    Al'ummar Owu wadanda suka shirya taron sun tabbatar da cewa dole a tafi da matasa in har ana neman kawo ci gaba a al'umma.

    Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da gwamnan jihar Osun Adegboyega Oyetola da Basarake Oba Adekunle Hammed Makama wanda ya kira taron sun nemi a raya harkokin al'adu da na matasa.

    Sauran mahalarta taron sun hada da Sarkin Fulani na jihar Legas, Alhaji Muhammad Abubakar Bambado II.

  6. Yariman Saudiyya Turki Al-Faisal ya caccaki Isra’ila

    Yariman Saudiyya Turki Al-Faisal bin Abdulziz al-Saud, kuma tsohon shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar ya caccaki Isra’ila inda ya kira ta babbar mai mulkin mallaka da ke amfani da ƙarfi da rusa matsugunin Falasɗinawa.

    Yarima Turki al Faisal ya yi waɗannan kalaman ne a wani taron tsaro ta intanet da Bahrain ke jagoranta a Manama a ranar Lahadi wanda ya samu halartar ministan harakokin wajen Isra’ila Gabi Ashkenazi wanda ya yi watsi da kalaman.

    Al-Faisal ya ƙara da cewa “Isra’ila tana rusa gidaje yadda ta ga dama kuma tana kashe duk wanda take so.”

    Amma a martaninsa, ministan harakokin wajen Isra’ila ya ce ya tausayawa kalaman da suka fito daga yariman.

    Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa “zargin karya da jami’in Saudiyya ya yi a taron Manama ba ya nuna gaskiya ko asalin canjin da yankin ke ciki."

    Zafafan kalaman da suka fito daga Yarima Turki al Faisal a wajen taron Manama ya nuna girman ƙalubalen duk wata yarjejeniya da ake son cimma tsakanin ƙasashen Larabawa da Isra’ila muddin babu batun cin gashin kan Faladinawa.

    Kuma wannan na faruwa ne a yayin da manyan ƙasashen Larabawa kamar Bahrain da Daular Larabawa suka yi maraba da Isra’ila a wajen taron bayan daidaita hulɗarsu da Isra’ila da gwamnatin Trump ta jagoranta.

  7. Amsoshin Takardunku: Abin da ke jawo haɓo

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tamabaya game da dalilin da yake jawo haɓo wato zubar jini daga hancin mutum.

    Nabeela Muktar Uba ce ta gabatar da shirin.

  8. Shugaban Ghana Akufo-Addo zai yi wa 'yan ƙasa jawabi a yau

    Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana zai yi wa 'yan ƙasar jawabi nan gaba a yau Lahadi, yayin da ake shirin kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasa gobe Litinin.

    Shugaban zai yi jawabin ne da ƙarfe 8:00 agogon Ghana - 9:00 agogon Najeriya da Nijar.

    Kazalika, ita ma hukumar zaɓen ƙasar GCE za ta yi wa 'yan jarida bayani game da shirye-shiryenta gabanin zaɓen na gobe.

    Tun ranar Talata masu ayyuka na musamman suka kaɗa ƙuri'unsu, inda ake sa ran mutum 109,577 da suka yi rajista daga cikinsu sun yi zaɓen. 'Yan sanda da 'yan jarida da masu tuƙa motar ɗaukar marasa lafiya na cikin waɗanda suka jefa ƙuri'ar.

  9. Kwale-kwale ya kife da 'yan sandan Najeriya shida

    An tabbatar da mutuwar 'yan sandan Najeriya guda shida bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife a Ƙaramar Hukumar Kudancin Ijaw ta Jihar Bayelsa.

    'Yan sandan na kan hanyarsu ta zuwa yankin ne a jajibarin ranar zaɓen cike gurbi na 'yan majalisa, wanda aka gudanar a jiya Asabar a mazaɓar sanata uku da ke jihar.

    Mai magana da yawun rundunar 'yah sandan jihar, Asinim Butswat, ya tabbatar wa da kafar Channels TV rasuwar tasu a yau Lahadi, yana mai cewa an gano gawarwakin 'yan sandan shida.

    'Yan sanda 11 ne a cikin kwale-kwalen a lokacin da tsautsayin ya faru.

    Hukumnar zaɓe ta INEC ta gudanar da zaɓukan cike gurbi a jiha 11 a faɗin Najeriya, waɗanda suka haɗa da zaɓen sanata guda shida da kuma na 'yan majalisar jiha guda tara.

    Daga cikin jihohin da aka gudanar da zaɓen akwai Zamfara da Bauchi da Cross River da Filato da Legas da Imo.

  10. An kama mutum 19 bisa zargin safarar mutane zuwa Turai

    ‘Yan sanda a Italiya sun kama mutum 19 da ake zargi da gudanar da wata kungiyar safarar baƙin haure zuwa Nahiyar Turai.

    Ana zargin sun yi jigilar mutane daga ƙasashe ciki har da Afghanistan da Iraƙi da Pakistan zuwa Italiya sannan suka wuce zuwa arewacin Turai.

    Wakiliyan BBC ta ce 'yan sanda sun ce wadanda aka kama sun hada da ‘yan Italiya da Kurdawan Iraƙi da kuma ‘yan Afghanistan, sannan 'yan ciranin sun biya sama da dala 8,00 don a tsallaka da su.

    Binciken da aka yi shekara biyu da suka gabata ya alaƙanta waɗanda ake zargin da wasu masu safarar a ƙasashen Turkiyya da Girka.

    Mutanen kan tsallakar da 'yan cirani ta ruwa ta hanyar amfani da jiragen ruwa na haya ko na sata.

  11. An kashe masu garkuwa da mutane, an kama 'yan fashi a Jihar Sokoto

    'Yan sandan Jihar Sokoto sun kashe 'yan fashi biyu a garin Sanyinna na Ƙaramar Hukumar Tambuwal yayin wata musayar wuta.

    Yayin da yake bayani ga manema labarai ranar Asabar, Kwamishinan 'Yan Sandan Sokoto Ibrahim Sani Ka’oje ya ce an samu ƙaruwar sace-sacen mutane a jihar.

    Ya ƙara da cewa wani harin fashi da makami da wasu suka kai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya a kwanan nan.

    "Mun kwana biyu muna bin sawunsu. Mako biyu da suka wuce, an kai wani hari a Sanyinna, inda sojoji suka je dajin amma ba su iya shiga ba saboda wurin yana buƙatar shiri sosai," in ji shi, a cikin rahoton Channels TV.

    A cewarsa, an kama ɗaya daga cikin waɗanda suka kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum mako biyun da suka wuce.

    Kazalika, an kama mutum huɗu da zargin fashi da makami da kuma wasu takwas da ake zargi da garkuwa da mutane, sannan an ƙwace bindigar AK-47 daga hannunsu.

  12. Zaɓen Ghana: Masu zaɓe za su iya kaɗa ƙuri'a ko da katin zaɓensu ya ɓata

    Masu zaɓe a Ghana za su iya kaɗa ƙuri'arsu a gobe Litinin ko da kuwa katin zaɓensu ya ɓata, a cewar hukumar zaɓen ƙasar ta Ghana Electoral Commission (GEC).

    Hukumar zaɓen ta ce mutum zai je rumfar zaɓensa ne kawai ya faɗi sunan da ya yi rajista da shi, inda su kuma ma'aikatan zaɓe za su duba.

    A gefe guda kuma, GEC ta ce za ta yi amfani da na'urar tantance masu zaɓe mai suna Biometric Verification Devices (BVD) a ranar kaɗa ƙuri'a.

    Na'urar BVD na ɗauke da shaidar yatsa da kuma hoton fuskar kowane mai katin zaɓe, ta yadda idan an kasa tantance yatsan mutum sai a yi amfani da fuskarsa.

    Kazalika, duk wanda ba shi da takunkumi ba zai shiga wurin kaɗa ƙuri'a ba, in ji GEC.

    A gobe Litinin ne za a fafata tsakanin Shugaba Ƙasa Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP da kuma tsohon Shugaba John Mahama na jam'iyyar NDC.

    Jam'iyya 27 ne za su shiga zaɓen amma zai fi zafi ne tsakanin NPP da NDC.

  13. An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a Faransa

    An yi mummunar arangama a Paris babban birnin Faransa tsakanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga-zanga.

    'Yan zanga-zangar sun taru a karo na biyu a ƙarshen mako domin nuna adawa da daftarin dokar da ke kare 'yan sandan Faransa daga ɗaukarsu a bidiyo ko hoto yayin da suke bakin aiki.

    Mutanen sun riƙa fasa shaguna tare da lalata motocin jama'a kafin 'yan sanda su harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

    Wakilin BBC ya ce gwamnatin ƙasar ta yi alƙawarin yin gyara musamman a sashen dokar da ke neman hana yaɗawa ko wallafa hotunan 'yan sanda a jaridu da shafukan Internet.

    Sai dai hakan bai ishi masu suka da ke neman ganin an yi watsi da dokar ba baki ɗaya.

    Rahotanni sun ce zanga-zangar na ci gaba da tumbatsa.

  14. An yi wajerod da Kano Pillars daga gasar Zakarun Afirka

    An yi wajerod da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars daga gasar zakaru ta CAF Confederation Cup a jiya Asabar bayan ta tashi wasa 0-0 da A.S.C Jaraaf ta ƙasar Senegal.

    Masu Gida sun fice daga gasar ne sakamakon sun kasa rama 3-1 da aka ɗura musu a Senegal ranar 27 ga Nuwamba.

    An buga wasan ne a filin wasa na Ahmadu Bello da ke garin Kaduna a yammacin Asabar, inda aka doke ta 3-1 wasa gida da waje.

    Ita ma ƙungiyar Plateau United ta fice daga Gasar Zakarun Afirka ta CAF Champions League bayan ta tashi wasa 0-0 da Simba Sports Club a ƙasar Tanzania.

    A wasan farko da suka buga a Najeriya, Plateau United ta sha kashi da 0-1. An doke ta 1-0 a wasa gida da waje kenan.

    Yanzu ƙungiyar Enyimba ce kaɗai ta rage a gasar Zakarun Afirka daga Najeriya, inda ta doke Rahimo FC 2-0 wasa gida da waje.

  15. An ceto 'yan sandan Najeriya uku da aka sace

    Rundunar 'yan sandan Jihar Ogun a Najeriya ta ce ta ceto dakarunta uku cikin huɗu da 'yan daba suka yi garkuwa da su a Aba Tuntun ta Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Arewa.

    Mai magana da yawun rundunar, Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Abeokuta jiya Asabar.

    Ya ƙara da cewa har yanzu masu garkuwar na riƙe da Kurtu Emmanuel Gene.

    An kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a lamarin kuma suna bai wa 'yan sanda muhimman bayanai, a cewar Mista Oyeyemi.

    "A ranar Alhamis ne mai garin yankin ya kai wa 'yan sanda rahoton cewa wasu matasa na yawo da muggan makamai a yankin, abin da ya sa 'yan sanda suka isa wurin kuma suka ƙwace makaman," in ji shi.

    "Yayin da suke kan hanyarsu ta kai mutanen da makamansu ofishin 'yan sanda, sai wasu 'yan daba suka yi musu kwanton-ɓauna kuma suka yi garkuwa da huɗu daga cikinsu.

    "Sun harbi DPO a hannu sannan suka kuɓutar da waɗanda ake zargin. Mun ceto uku daga cikinsu amma ba mu san inda kurtun cikinsu yake ba."

  16. Cutar korona ta sake kashe mutum ɗaya a Najeriya

    Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce ƙarin mutum 310 sun kamu da cutar korona ranar Asabar.

    Haka nan wani mutum ɗaya ya rasa ransa sakamakon cutar, abin da ya sa jumillar adadin waɗanda suka mutu a Najeriya ya kai 1,180.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce an samu ƙarin mutanen ne a jiha 12 da suka haɗa da Abuja (128) da Lagos (86) da Kaduna (26) da Katsina (20).

    Sauran jihohin su ne: Rivers (19) da Oyo (7) da Benue (5) da Edo (5) da Jigawa (5) da Ogun (5) da Bayelsa (2) da kuma Kano (2).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 68,937 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya, yayin da 64,650 daga cikinsu suka warke kuma aka sallame su daga cibiyoyin killacewa.

  17. A yau za a ci gaba da tattaunawar Brexit

    Nan gaba a yau ne za a ci gaba da tattaunawar karshe tsakanin Tarayyar Turai da Birtaniyya game da ficewar ƙasar daga ƙungiyar ta EU.

    Wannan ya biyo bayan kasa cimma matsaya yayin doguwar tattaunawa ta waya da Firaministan Biritaniya Boris Johnson ya yi da Shugabar Hukumar Turai, Ursula von der Leyen.

    Shugabannin biyu sun ce har yanzu kawuna na rarrabe kan damar kamun kifi da kuma hanyoyin warware rigingimun da za a iya samu nan gaba.

    Da yake magana game da tattaunawar, Ministan Harkokin Turai na Faransa, Clement Beaune, ya dage cewa dole ne Turai ta ci gaba da samun damar kamun kifi a ruwan Birtaniya.

    Ya kara da cewa wajibi ne dukkan bangarorin su yanke shawara dangane da yiwuwar cimma yarjejeniya ko kuma Birtaniya ta fice haka nan ba tare da yarjejeniya ba.

  18. Barka da hantsin Lahadi

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye kuma zai riƙa kawo labaran abubuwan da ke faruwa ne a Najeriya da Nijar da Ghana da sauran sassan duniya.

    Umar Mikail ne zai kula da shafin a yanzu.