Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Biden ya lashe Michigan, kuma ya ce ya kusan lashe zaɓen Amurka

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Ana ci gaba da dakon sakamakon zaɓe

    Jama'ar Amurka da na wasu ƙasashen duniya na nan sun zura ido sun kuma kasa kunne domin gani da jin wanda zai samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar Amurka.

    A yanzu dai Joe Biden ne a kan gaba da ƙuri'u 227 sai kuma Donald Trump da ƙuri'u 214.

    A ƙa'ida, duk wanda adadin ƙuri'unsa suka fara kai 270, shi ne ya ci zaɓen.

    Har yanzu dai akwai sauran jihohin da ba a kammala tattara sakamakon zabensu ba.

  3. Labarai da dumi-dumi, 'Joe biden ya lashe Jihar Wisconsin'

    Rahotanni daga Amurka na cewa Joe Biden na Jam'iyyar Democrat ya lashe jihar Wisconsin.

    Kafofin yaɗa labarai na CNN DA CBS DA Fox da kuma kamfanin dillancin labarai na AFP duk sun ruwaito hakan.

    Ana dai ci gaba da fafatawa da Donald Trump da Joe Biden inda dukan ɓangarorin biyu kowa ke ikirarin ya ci zaɓen.

    A sakamakon da ake samu, babu wata tazara sosai tsakanin 'yan takarar biyu, za a iya cewa ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta ƙare.

  4. 'Yar Najeriya ta lashe kujerar Majalisar Wakilan Amurka

    Wata 'yar Najeriya da ke zaune a Amurka, Esther Agbaje, ta lashe kujerar Majalisar Wakilai ta Amurka, a zaɓen ƙasar na 2020.

    Jaridar The Punch a Najeriya ta ruwaito cewa Agbaje ta kayar da abokin hamayyarta, Alan Shilepsky a zaɓen.

    Ta samu kuri'u 17,396, wanda hakan ke nufin ta samu kashi 74.6 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Shilepsky na Jam'iyyar Republican ya samu ƙuri'u 4,128, wanda hakan ke nufin ya samu kashi 17.7 cikin 100 na ƙuri'un da aka jefa.

    Ms Agbaje wacce ta karanci ilimin shari'a a Jami'ar Harvard da kuma digiri na biyu a Jami'ar Pennsylvania, ta yi aiki a ofishin harakokin wajen Amurka.

  5. Bidiyo: Dalilan da suka sa zaɓen Amurka na 2020 ya yi kama da zaɓukan Afirka

    A wannan bidiyon, Bilkisu Babangida ta BBC Hausa, ta yi mana duba kan hanyoyin da zaɓen Amurka na 2020 ya yi kama da zaɓukan da aka saba yi a Afirka.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:

  6. MINTI ƊAYA DA BBC - LABARAN YAMMA 04/11/2020

  7. Trump ya yi zargin an yi masa maguɗin zaɓe

    Duk da cewa akwai miliyoyin ƙuri'un da ba a kammala ƙidayawa ba a zaɓen Amurka, Shugaba Donald Trump ya yi da'awar lashe zaɓe ba tare da wata hujja ba.

    Ya kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi tare da ha'intar ƙasarsa ta Amurka.

    Don haka ya ce zai garzaya Kotun Ƙoli don ƙalubalantar sakamakon.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:

  8. Sakamakon zaɓen zuwa yanzu

  9. Gwamnan Pennsylvania: "Ba lallai mu san sakamakon zaɓe a yau ba"

    Gwamnan jihar Pennsylvania, Tom Wolf, ya bayyana cewa ba lallai a samu sakamakon jihar ba a yau, a zaben shugaban ƙasar da aka gudanar.

    "Ba lallai a samu sakamakon zaɓen ba a yau, sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne za a samu sakamako mai inganci, ko da sakamakon ya ɗauki lokaci bai fito ba," kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

    Sakataren harkokin wajen jihar Kathy Boockvar, ya ce kusan kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka jefa ta akwatin gidan waya an ƙirga su, inda ya ƙara da cewa wannan ne zaɓe mafi inganci da ya taɓa gani.

    Mista Trump ya bayyana cewa "abu ne mai wuya" Biden ya kamo shi a yawan ƙuri'u a Pennsylvania, wadda ita ce jihar da ya samu nasara da ƙuri'u 44,000 a 2016.

    Jihar na da kwamitocin masu zaɓen shugaban ƙasa 20.

  10. Kwamitin kamfe na Trump ya gana da manema labarai

    Rahotanni na cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya kira taron manema labarai don shaida musu cewa ''muna da ƙwarin gwiwa'' na samun ƙuri'u 270 na kwamitocin masu zaɓen shugaban ƙasa.

    Sun bayyana cewa akwai yiwuwar sake ƙirga ƙuri'un jihar Wisconsin, kuma sun ce suna kyautata zaton "Trump zai ci gaba da bada wuta" a tsakanin marasa rinjaye a Pennsylvania.

    "Muna so mu tabbatar an ƙirga duka ingantattun kuri'un da aka jefa," in ji babban mai ba shi shawara kan harkokin yaƙin neman zabe, Jason Miller.

    "Muna kuma so mu tabbatar da cewa duk wata ƙuri'ar da aka jefa ba bisa ƙa'ida ba, ba a ƙirga ta ba."

  11. Zaɓen Amurka ya ɗau zafi a daidai loacin da ake jiran sakamako

    A yanzu dai, ana kusan kan-kan-kan tsakanin Mista Trump da Joe Biden inda Mista Biden din ya tsere wa Donald Trump da ƙuri'u kaɗan.

    Masu goyon bayan Joe Biden dai na cewa alamu sun fara nuna cewa sakamakon zaɓen da ke fitowa na nuni da alamun nasara a garesu.

    Sai dai Mista Trump na Jam'iyyar Republican, ya yi iƙirarin lashe zaɓen kuma ya sha alwashin kai ƙara Kotun Ƙoli domin ƙalubalantar zaɓen.

    A yanzu dai akwai miliyoyin ƙuri'u waɗanda ba a ƙidaya ba, kuma babu wani ɗan takara da zai iya iƙirarin lashe zaɓen.

  12. Sakamakon zaɓen Amurka "ba zai sauya manufofin Iran ba - Khamenei

    Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya jaddada cewa sakamakon zaɓen Amurka 'ba zai sauya' manufofin Iran ba kan Amurka.

    "Manufarmu... a bayyane take. Sauyin wani ba zai sauya komi ba," in ji shi. "Ba ruwanmu da wanda zai zo ko zai tafi."

    Donald Trump ya yi "matsin lamba" ga Iran a yaƙin neman zaɓensa tun yin watsi da yarjejeniyar nukiliya a 2018.

    Abokin hamayyarsa, Joe Biden, ya ce zai iya dawo da yarjejeniyar.

    Ga cikakken labarin nan:

  13. Shekara 120 rabon da asamu adadin ƙuri'ar da aka jefa bana a Amurka

    Sama da Amurkawa miliyan 160 suka fito jefa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, wannan adadi shi ne mafi yawa na 'yan ƙasar da suka fito jefa ƙuri'a a shekaru 120 da suka gabata, kamar yadda aka ƙididdige yayin zaɓen.

    A 1900, Shugaban Amurka ɗan Jam'iyyar Republican William McKinley ya kayar da abokin karawarsa na Jam'iyyar Democrat William Jennings Bryan inda aka samu kashi 73.7 cikin 100 na masu zaɓe suka fito jefa ƙuir'a.

    A wannan shekarar kuma kashi 66.9 cikin 100 na masu zaɓe ne suka fito don jefa ƙuri'a.

    A bana dai, masu sa ido kan zaɓe sun yi hasashen za a samu mutane da yawa da za su fito jefa ƙuri'a tun bayan da aka sanar da cewa wasu za su yi zaɓe ta hanyar aika wasiƙa ta akwatin gidan waya sakamakon annobar korona.

  14. Ana ci gaba da kirga kuri'un zaben 'yan majalisa

    Ana cigaba da kirgen kuri'u a zaben sanatoci a Amurka, inda ake sa ran fitar da sakamakon karshe na zaben nan gaba a yau.

    Sai dai da alama 'yan Democrat na sha da kyar a kokarinsu na samun rinjaye a Majalisar Dattawan.

    Ya zuwa yanzu, sun lashe kujera guda a Colorado kuma kafafen yada labarai a Amurkan na hasashen jam'iyyar za ta yi nasara a Arizona.

    'Yan Republican kuma sun lashe kujerarsu a Alabama. Ana sa ran Majalisar Wakilan za ta ci gaba da zama a karkashin 'yan Democrat.

    Bayan zaben 'yan majalisar, Amurkawa kuma na zaben sabbin gwamnoni a jiha 11.

    Gwamnan Vermont ya ce wannan ne zaben da aka fi fitowa a tarihin Amurka.

    "Ba wai an samu rashin fitowar jama'a ba ne kuma hakan na iya damun mu kamar yadda aka yi a 2016," in ji shi.

  15. Babu dokar da ta ce sai an bayyana sakamako a daren ranar zaɓe

    A zaɓen shugaban Amurka, babu wata doka da ta ce lallai sai an bayyana sakamako a daren ranar da aka gama kaɗa ƙuri'a.

    Kodayake ba haka aka saba gani ba, amma hakan ta faru a baya-bayan nan, inda a zaɓen 2000 sai da aka shafe fiye da wata ɗaya kafin a san haƙiƙanin wanda ya lashe zaɓen tsakanin Mista Gore da kuma Bush sakamakon ƙarar da aka shigar a Kotun Ƙoli.

    Akasari kafafen yaɗa labaran Amukr ne ke bayyana wanda ya lashe zaɓen tun kafin a sanar da shi a hukumance.

    Zaɓe biyar da suka gabata, CNN ta sanar da waɗanda suka yi nasara a lokuta kamar haka:

    • 2016: An sanar da Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙarfe 2:47 agogon Amurka
    • 2012: An sanar da Barack Obama a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙarfe 11:18 agogon Amurka
    • 2008: An sanar da Barack Obama da ƙarfe 11:00 agogon Amurka
    • 2004: Ba a iya tabbatar da wanda ya yi nasara ba saboda an yi kankankan, sai da John Kerry ya amsa shan kaye da tazarar ƙuri'a 100,000 a Jihar Ohio
    • 2000: Ba a iya samun wanda ya yi nasara ba sai da aka je Kotun Ƙoli
  16. Jihohin da take ƙasa tana dabo

    Har yanzu fafatwa ake a matsayin kankankan a wannan zaɓe, abin da ya sa ba za a iya bayyana wanda ya yi nasara ba.

    Trump ya lashe jihohi masu mahimmanci kamar Florida da Ohio da Texas amma yana buƙatar ya lashe ƙarin jihohi masu mahimmanci domin samun nasara.

    Har yanzu Biden na da hanyoyin da zai bi domin kaiwa ga gaci, amma fa dukkaninsu babu tabbas.

    Jihohin da har yanzu ba su bayyana sakamako ba:

    • Arizona
    • Navada
    • Georgia
    • Michigan
    • Pennsylvania
    • Wisconsin
  17. Yadda Trump zai lashe Florida

    'Yan Democrat sun so su kawo wa Trump tsaiko a yunƙurinsa na lashe Jihar Florida.

    Amma bayan ƙirga kusan dukkanin ƙuri'un, ana ganin Trump ne zai lashe jihar da aka fafata sosai, da kashi 51 cikin 100 na ƙuri'un idan aka kwatanta da 48 na Biden.

    Shugaban ya samu maki biyu ƙari a kan na nasarar da ya samu a 2016. A gefe guda kuma, Biden ya gaza samun sama da abin da Hillary Clinton ta samu a zaɓen 2016 a jihar.

  18. Jihohi ƙalilan ake jira yanzu kafin samun sakamako

    Har yanzu ba za mu iya sanin sanin wanda ya yi nasara ba a zaɓen shugaban ƙasar Amurka, yayin da ake jiran sakamakon jiha tara daga cikin 50 na ƙasar.

    Amma abin da muka sani zuwa yanzu shi ne, Shugaba Trump ya taka rawar gani sosai fiye da yadda ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta bayyana.

    Ƙuri'un ra'ayin jama'a na cibiyar Real Clear Politics sun bai wa Biden nasara da +0.9 a Jihar Florida, jihar da za a fafata wadda kuma ake tsammanin Trump ne zai lashe ta.

    Wasu daga cikin ra'ayoyin sun zarta na zaɓen 2016. Yayin da Amurkawa ke jiran sakamakon zaɓe na wannan shekarar, masu aiwatar da ƙuri'un jin ra'ayoyin jama'a na ƙorafi.

    Tsohon shugaban ma'aikata na Trump, Mick Mulvaney ya faɗa wa BBC cewa "ƙuri'un ba na gaskiya ba ne" a jihohi kamar Texas.

  19. Joe Biden ne kan gaba a Jihar Wisconsin mai mahimmanci

    Bayan ƙirga kashi 99 cikin 100 na ƙuri'u, ɗan takarar Democrat Joe Biden ya tserewa Donald Trump da tazara ƙalilan (20,000 zuwa yanzu) a Jihar Wisconsin da aka ƙwallafawa.

    Trump ya doke Hillary Clinton a Wisconsin da tazarar fiye da 30,000 a 2016 a wani yanayi da ba a saba gani ba.

    Duk da tazarar da Biden ya bayar, ba za a iya bayyana wanda ya yi nasara ba saboda sakamakon ya yi kankankan da yawa.

    Wisconsin na da matuƙar mahimmanci wurin fayyace wanda zai yi nasarar shiga Fadar White House.

  20. Dalilin da ya sa ake kankankan a Jihar Michigan

    Babban daliln da ya sa aka yi kankankan tsakanin Trump da Biden a Jihar Michigan ya ta'allaƙa ne ga Gundumar Wayne, inda Detroit da sauran unguwanni suke, a cewar wakilin CNN Phil Mattingly.

    Michigan na ɗaya daga cikin jihohin da aka fi fafatawa tsakanin 'yan takarar kuma har yanzu babu tabbas game da wanda zai lashe ta.

    "Hakan na nuna irin tasirin da unguwannin da Democrat ke da rinjaye waɗanda ƙuri'un da ba a ƙirga ba a cikinsu ke yawa," in ji shi.

    Gundumar Wayne wadda ita ce mafi girma a Michigan, tana da kashi 18 cikin 100 na dukkanin ƙuri'un jihar.

    "Da yawa daga cikin ƙuri'un an kaɗa su ne ta hanyar akwatin gidan waya. 'Yan Democrat sun jefa ƙuri'a ta gidan waya sosai. Abin da nake so a gane shi ne, Trump yana kan gaba da ƙuri'a 212,000 'yan awanni da suka wuce, yanzu tazarar 64,000 kawai ya bayar."