Atiku ya soki gwamnatin Najeriya kan dakatar da jarrabawar WAEC

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:

    • Za a bar shugaban Ivory Coast ya yi mulki wa'adi uku
    • Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020
    • Karnuka na 'haƙo gawarwakin ƙananan yara' a Mozambique
    • Cutar korona: Birtaniya ta yi sassauci kan masu son shiga kasar
    • An hana ƴan Najeriya neman aiki a Dubai
    • Ƴan sandan Malasia sun yi wa ƴan jaridar Al-Jazeera tambayoy
    • Hagia Sophia: An mayar da shahararren gidan tarihin Istanbul zuwa masallaci
    • Gwamnatin Sudan ta haramta kaciyar mata

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai..

  2. Waiwaye kan rayuwar Firaministan Ivory Coast da ya yi mutuwar fuju'a

    Bayanan bidiyo, Waiwaye kan rayuwar Firaministan Ivory Coast da ya yi mutuwar fuju'a

    Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

    Wannan bidiyo ne da ke waiwaye kan rayuwar Firaministan Ivory Coast da ya yi mutuwar fuju'a.

    A ranar Laraba 8 ga watan Yuli ne Firaminista Amadou Gon Coulibaly ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya a wajen taron majalisar ministocin ƙasar.

    Shugaban ƙasar Alassane Ouattara ne ya tabbatar da hakan inda ya ce marigayin ya fara rashin lafiyar ne lokacin da ake tsakiyar taron majalisar zartarwa, kuma daga nan ne aka kai shi asibiti inda ya rasu a can.

  3. Adadin waɗanda suka kamu da korona a duniya ya ƙaru – WHO

    Yawan mutanen da suka kamu da korona a faɗin duniya ya ƙaru, inda mutum 228,102 suka kamu a sa'o'i 24 da suka gabata, in ji Hukumar Lafiya Ta Duniya.

    Hukumar ta bayyana cewa adadi mafi yawa da yaƙaru ya fito ne daga Amurka da Brazil da Indiya da kuma Afirka Ta Kudu.

    Adadin da hukumar ta fitar a ranar 4 ga watan Yuli na waɗanda suka kamu da cutar shi ne 212,326.

    Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayar da rahoton cewa mutum miliyan 12.1 suka kamu da cutar. Ƙididdigar Jami'ar Johns Hopkins kuma ta bayyana cewa adadin ya kai miliyan 12.3.

  4. Atiku ya soki gwamnatin Najeriya kan dakatar da jarrabawar WAEC

    ..

    Asalin hoton, @atiku

    Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya nuna rashin jin daɗinsa bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da gudanar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a ƙasar.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai hanyoyin da gwamnatin za ta iya bi wurin gudanar da jarrabawar ba wai ta dakatar da ita baki ɗaya ba.

    Cikin hanyoyin da ya lissafo akwai batun amfani da manyan ɗakunan taro na ƙasar da makarantun firamare da filayen wasanni da sauran wurare domin amfani da su wurin gudanar da jarrabawar.

    Ya bayyana cewa dama tuni sauran ƙasashen Afirka suka bar Najeriya a baya a fannin ilimi, ya kuma ce wannan yunƙurin na dakatar da jarrabawar zai iya jawo rikici a ɓangaren ilimi a ƙasar.

    Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnatin ƙasar ba ta bari an gudanar da jarrabawar ba, dubban mutane za su ƙetara maƙwafta domin zana jarrabawar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Ana ci gaba da zanga-zangar yanke ƙauna ga shugaban Mali

    .

    Asalin hoton, AFP

    Dubban mutane na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Bamako babban birnin ƙasar Mali inda suke kira da Shugaban ƙasar Boubacar Keita ya yi murabus.

    Wannan ce zanga-zanga ta uku da aka yi ta nuna rashin goyon baya kan cin hanci da rahsawa da rashin shugabanci nagari da maguɗin zabe da kuma gazawar gwamnatin ƙasar ta kasa shawo kan rikicin ƙabilu da kuma na masu iƙirarin jihadi.

    .

    Asalin hoton, AFP

    Wata sabuwar gamayya ce ke jagorantar wannan zanga-zanga ƙarƙashin jagorancin Mahmoud Dicko.

  6. Gwamnatin Sudan ta haramta kaciyar mata

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Sudan ta kafa dokar da ta mayar da yi wa mata kaciya a ƙasar laifi.

    Majalisar Ƙoli ta ƙasar ce ta amince da wannan dokar, watanni biyu bayan da gwamnatin ƙasar ta fitar da ƙudirin wannan doka tare da neman hukunta waɗanda suka aikata wannan laifi da su shafe shekaru uku a gidan yari.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kashi 90 cikin 100 na 'yan mata da ke tsakanin shekaru 14 zuwa 49 an yi musu kaciya a ƙasar.

  7. Libiya za ta ci gaba da sayar da mai bayan watanni 6

    ..

    Babban kamfanin mai na ƙasar Libiya ya bayyana cewa ƙasar za ta ci gaba da fitar da man fetur bayan an shafe kusan watanni shida ba a fitar da shi.

    Hakan ya faru ne sakamakon yawan rikici da kuma tayar da zaune tsaye da ake samu a ƙasar ta Libiya.

    Tuni dai tankar mai ta farko ta fara lodi a gabashin tashar ruwa da ke Es-Sider.

    A baya dai dakaru masu goyon bayan Janar Khalifa Haftar ne suka toshe hanyoyin samar da mai a yankin.

    Man fetur dai shi ne ƙashin bayan tattalin arziƙin Libiya, kuma kuɗaɗen da ƙasar ta yi asara sakamakon dakatar da fitar da man sun kai biliyan $6.

  8. Yawan masu korona na ƙaruwa a Rasha a kullum

    Rahotanni daga ƙasar Rasha na cewa mutum 6,635 suka kamu da cutar a rana guda, in ji hukumomi a ƙasar.

    Wannan ne ya kawo yawan masu ɗauke da cutar ta korona a ƙasar zuwa 713,936.

    Haka zalika an sake samun mutum 174 da suka mutu sakamakon cutar wanda hakan ya sa yawan waɗanda suka mutu sakamakon cutar a ƙasar ya kai 11,017.

    Hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta bayyana cewa sama da mutum 18,375 suka mutu a ƙasar, inda aka ce kusan 7,444 a ciki na da alaƙa da cutar korona.

    • Hagia Sophia: An mayar da shahararren gidan tarihin Istanbul zuwa masallaci

      The Hagia Sophia has huge significance as a religious and as a political symbol

      Asalin hoton, Getty Images

      Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanya hannu kan wata doka da ta mayar da wani tsohon gidan tarihi da ke Istanbul mai suna Hagia Sophia zuwa masallaci.

      Tun da farko wata babbar kotun kasar ta soke dokar da ta mayar da wurin gidan tarihi kuma wurin da miliyoyin mutane kan ziyara a kowace shekara.

      An fara gina coci ne a wurin shekara 1,500 da ta gabata, amma an mayar da shi Masallacin Hagia Sophia yayin mulkin Daular Ottoman. A 1934 kuma aka sauya shi ya koma gidan tarihi.

      Masu kishin Islama a Turkiyya sun dade suna kiraye-kiraye ga gwamnatin kasar ta mayar da wurin masallaci, amma masu adawa da matakin daga cikin ƴan majalisar kasar sun rika sukar yin haka.

      Wasu shugabannin addinai na duniya ma sun rika sukar shawarar mayar da ginin zuwa masallaci.

      Shugaban Cocin Eastern Orthodox Church da kasar Girka na cikin wadanda suke adawa da daukar wannan matakin. Akwai miliyoyin mabiya darikar cocin Eastern Orthodox Church a kasar Girka.

      Dokar ta Mista Erdogan ta mika masallacin Ayasofya - sunan da ake kiransa da Turkiyanci - ga hukumar da ke kula da harkokin addini domin a fara yin ibada cikinsa.

    • Ƴan sandan Malasia sun yi wa ƴan jaridar Al-Jazeera tambayoyi

      Rundunar `yan sanda Malasia na yi wa wasu `yan jarida su shida na gidan talabijin na Al-Jazeera tambayoyi dangane da wani shirin musamman da suka yi a kan yadda jami`an tsaron kasar suka dinga tsare wasu ma`aikata da suka shiga kasar ba bisa ka`ida ba, lokacin da kasar ta kafa dokar kulle.

      Mahukunta sun akwai kura-kurai a cikin rahoton da `yan jaridar suka hada, kuma yana iya ruda mutane.

      Babban sifetan `yan sandan kasar, Abdul Hamid Badur ya bayyana cewa suna gudanar da bincike ne game da zargin cewa `yan jaridar sun aikata laifukan da suka shafi tunzura jama`a da shafa wa gwamnati kashin-kaji.

      Amma mahukuntan gidan talabijin na Al-Jazeera sun musanta zargin, suna kuma nuna damuwa game da halin da `yan jaridar suke ciki.

      Ana kokawa game da wasu matakai da gwamnatin Malesiya ke dauka na takura wa kafafen yada labarai, bayan ta karbi mulkin kasar a watan Maris din da ya wuce.

    • Kashi 90 na masu aiki a ma'aikatar ilimin Ghana sun kamu da cutar korona

      Ministan ilimi na Ghana Matthew Opoku Prempeh ya ce kashi 90 cikin 100 na masu aiki a ma'aikatar ilimi sun kamu da cutar korona.

      A wata sanarwa da aka fitar ta wata tashar rediyo, ministan ya ce yawancin ma'aikatan sun killace kansu a gidajensu.

      Shi ma ministan kwanan nan aka sallame shi daga asibiti bayan gwajin da aka yi ma sa mako biyu da ya gabata ya tabbatar yana dauke da cutar.

      Yawan wadanda suka harbu da cutar korona a Ghana ya zarce 23,000, inda hukumomin kiwon lafiya na kasar suka ce mutum 641 ne suka kamu da cutar cikin awa 24 kacal.

      coronavirus
    • An hana ƴan Najeriya neman aiki a Dubai

      Ƴan Najeriya na bayyana fushinsu a shafukan sada zumunta bayan da aka wallafa wani tallan neman ma'aikata a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda a ciki aka fito karara ana cewa ba a bukatar ƴan Najeriya su nemi aikin.

      Tallan da kamfanin Shirley Recruitment Consultants ya wallafa a shafinsa na intanet ya sanar da masu neman aiki cewa ana neman wadanda za su iya aikin tallan turare ne a Dubai, kuma ana bukatar su kasance masu kwarewa kan harkar kasuwanci na a kalla shekara uku.

      Tallan ya kuma ce "ƴan Afirka maza ko mata na iya neman aikin amma ban da ƴan Najeriya."

      Joblinks

      Wani dan Najeriya da ya soki tallan a dandalin sada zumunta na Twitter: "Hana ƴan Najeriya kawai su nemi aiki da wata kasa ta yi nuna bambanci ne kuma ya taka dokokin kasa-da-kasa."

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

      Wasu ƴan Najeriya da suka yi tsokaci kan batun a shafukan sada zumunta na da ra'ayi cewa kamun da aka yi wa wasu ƴan Najeriya masu damfarar mutane da a halin yanzu suna hannun hukumomin Amurka na da nasaba da wannan matakin da kamfanin ya dauka.

    • Cutar korona: Birtaniya ta yi sassauci kan masu son shiga kasar

      Passenger at Heathrow international arrivals

      Asalin hoton, AFP

      Birtaniya ta sassauta dokar shiga kasar daga kasa 75 ciki har da wasu yankunan da ke karkashin ikonta.

      Sai dai ma'aikatar harkokin waje ta ƙasar ta ce hanin tafiya hutu bisa manyan jiragen ruwa na nan ga ƴan kasar.

      Daga safiyar Juma'a, matafiyan da suka isa Birtaniya daga Faransa da Italiya da Belgium da Jamus da kuma wasu gomman ƙasashe na iya shiga ƙasar kai tsaye ba tare da an killace su na mako biyu ba.

      Amma wannan bai shafi duk matafiyan da suka isa ƙasar ba cikin mako biyun da ya gabata - su sai sun kammala kwanakin killacewar da suka rage mu su.

      Kasar Scotland kuwa ta sanar da aniyarta ta ci gaba da killace matafiyan da suka isa ƙasar daga ƙasashen da cutar korona ke yaduwa fiye da na ƙasar ta Scotland.

      Yayin da aka fara yin sassauci kan dokar shige da fice ta Birtaniya, ma'aikatar harkokin waje ta ƙasar ta gargadi ƴan kasar da su kiyayi tafiya hutu cikin katafaren jiragen ruwa.

      Wani kakakin ma'aikatar ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki da hanin saboda "ya yi daidai da shawarar da ma'aikatar kiwon lafiya ta Ingila ta bayar."

    • Karnuka na 'haƙo gawarwakin ƙananan yara' a Mozambique

      Karnuka a ƙasar Mozambique sun fara haƙe gomman kaburburan ƙananan yara a birnin Chimoio, kamar yadda mazauna birnin suka sanar da tashar talabijin na Miramar.

      Wata mata ta ce kwanaki kaɗan bayan ta binne ɗanta, ta koma domin tsaftace kabarin, amma ta taras karnukan tuni sun haƙe kabarin har ma sun cinye gawar.

      Rahoton ya nuna tsummokara da sauran ƙasusuwa da naman mutum a harabar kabarin. Idan iyali ba sa iya sayen akwati saboda talauci, sukan naɗe gawarwakin mamatansu a bargo ko leda mai faɗi gabanin binne su.

      Ɗan jaridar tashar Miramar da ya haɗa rahoton ya shaida wa BBC cewa cikin mako guda kawai karnukan sun haƙe kaburbura 343 a maƙabartar.

      Mazauna yankin sun ce karnukan sun zama babbar matsala ga al'umma, domin a ƴan watannin nan mutane sun rage zuwa maƙabartar saboda annobar korona.

      Annobar ta haifar da wata matsalar ta daban - abin hannun yawancin masu karnuka ya ƙare - wanda ya sa ba sa iya ciyar da karnukan kamar yadda suka saba a da.

      Wani mazaunin yankin kuma ya ce rashin shinge ko katanga a maƙabartar na cikin dalilan da matsalar ke faruwa.

      Hukumomin Chimoio, wanda shi ne babban birnin lardin Manica da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Zimbabwe ba su amsa tambayoyin da aka yi mu su ba kan lamarin.

    • Labarai da dumi-dumi, Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2020

      Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kudin kasar na 2020.

      A kasafin kudin, wanda majalisun dokokin kasar suka yi wa kwaskwarima a watan jiya, za a kashe N10.8 a shekarar ta 2020.

      Mai taimaka washugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma'a.

      Sai dai bai yi cikakken bayni kan kasafin kudin ba.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Man City na son Alaba, Madrid za ta sayar da Jovic

      Alaba

      Asalin hoton, Getty Images

      Kocin Manchester City Pep Guardiola yana duba yiwuwar dauko dan wasan Bayern Munich daAustria David Alaba, mai shekara 28, a bazara.(Mirror)

      Wakilin Kevin de Bruyne ya ce dan wasan na Belgium, mai shekara 29, ba zai bar Manchester City a bazarar nan ba, ko da kuwa an tabbatar da hukuncin haramta musu buga gasar Zakarun Turai.(Sporza - in Dutch)

      Everton tana fuskantar gogayya a yunkurinta na dauko dan wasanLilledan kasar Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, bayan kungiya biyu a gasar Firimya ta nemi dauko dan wasan.(Sky Sports)

      Arsenal tana so ta ci gaba da rike golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 27, bayan ta soke shirinta na yin garambawul ga masu tsaron ragarta a bazarar nan.(Mirror).

    • Za a bar shugaban Ivory Coast ya yi mulki wa'adi uku

      Alassane Ouattara

      Asalin hoton, Getty Images

      Watakila za a bar shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya tsaya takara a wa'adi na uku bayan mutuwar fuju'a da firaiminista Amadou Gon Coulibaly ya yi ranar Laraba, a cewar wani jami'i da kamfanin dillanci labaran AFP ya ambato.

      "Muna da zabi da dama, cikinsu har da sabon wa'adin mulki ga Shugaba Ouattara," in ji shugaban jam'iyya mai mulki Adama Bictogo, a tattaunawarsa da AFP.

      An soma makokin kwana takwas a kasar kan rasuwar firaiministan wanda shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki ta RDHP a zaben shugaban kasa na watan Oktoba mai zuwa, bayan Mr Ouattara ya yanke shawarar sauka daga mulki.

      Masu sharhi sun ce zai yi matukar wahala jam'iyyar ta samu dan takara da zai yi shahara irin ta firaministan.

      Sun kara da cewa mai yiwuwa Mr Ouattara ya sake tsayawa takara ko da yake hakan ka iya kai wa ga zargin bata mulkin dimokradiyya.

      Mr Outtara ya hau mulki ne a 2011 bayan mutumin da ya gada Laurent Gbagbo, ya ki amincewa da shan kaye lamarin da ya ka ga tursasa masa sauka daga mulki.

    • Sarkin Kano ya himmatu wajen yaƙi da fyaɗe

      Aminu Ado Bayero

      Asalin hoton, Instagram/hrh_aminu_ado_bayero

      Sarkin Kano da ke arewacin Najeriya, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce masarautarsa za ta hada gwiwa da ma’aikatar harkokin mata ta jihar a yunkurin da suke yin a yaki da matsalar fyade.

      Ya bayyana haka ne lokacin da Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Malama Zahara’u Umar da tawaarta suka kai masa ziyara ranar Alhamis.

      A cewarsa, matsalar ta fyade tana bukatar hadin kan kowa domin dakile ta.

      A nata bangaren, Malama Zahara’u, ta koka game da yadda mutane suke so a rka rufa asirin mutanen da aka samu da aikata irin wadannan laifuka.

      Ta kara da cewa mutanen gari sun san masu aikata laifkan, amma sai kawai su rika cewa a "kashe maganar a cikin gida."

    • Barkanmu da Juma'a,

      Daga nan BBC Hausa muke yi muku barka da Juma'a.

      Muna fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya ta ke ciki.

      Za mu kawo mu ku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da sassan duniya.

      Kuna iya tafka muhawara a ko da yaushe a shafukamu na sada zumunta da muhawara a BBC Hausa.