'Ɗaliban Najeriya ba za su zana jarabawar WAEC ta 2020 ba'

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge, Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokaci muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau.:

    • Sama da dala miliyan daya ta yi batan dabo a babban bakin Mauritania
    • Masu korona sun haura miliyan uku a Amurka
    • An koma zirga-zirgar jiragen sama a yau a Najeriya
    • Majalisar dattawa ta mayar da wa'adin babban sufeton 'yan sanda shekara 4
    • An umarci makarantu a Kenya da su mayarwa da iyaye kudin 2020
    • Yawan masu korona ya haura 500,000 a Afrika
    • Hong Kong ta hana dalibai magana kan duk abin da ya shafi siyasa
    • Hare-haren 'yan bindiga ya sa mutane sun faɗa cikin kogi a Sokoto
    • Burkina Faso: An gano gawarwaki 180 a wani ƙabari

    Ku duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da wasu muhimmai...

  2. Labarai da dumi-dumi, Firai ministan Ivory Coast ya rasu bayan taron majalisar zartarwa

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Firai ministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

    Shugaban ƙasar Alassane Ouattara ne ya tabbatar da hakan inda ya ce marigayin ya fara rashin lafiyar ne lokacin da ake tsakiyar taron majalisar zartarwa ta ƙasar wanda daga nan ne aka kai shi asibiti kuma ya rasu a can.

    Kafin rasuwarsa, Mista Coulibaly ne aka sa ran cewa zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar RDR mai mulki a watan Oktoba.

    Marigayin kuma ya rasu ne makon guda bayan ya dawo daga ƙasar Faransa inda ya shafe watanni biyu yana jinya sakamakon matsala da ta danganci ciwon zuciya.

    Ya kuma shafe shekaru uku kan kujerarsa ta Firaiminista.

  3. Labarai da dumi-dumi, 'Ɗaliban Najeriya ba za su zana jarabawar WAEC ta 2020 ba'

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/ADAMU ADAMU

    Rahotanni daga Najeriya na cewa ɗaliban ƙasar waɗanda suke ajin ƙarshe na sakandire ba za su zana jarabawar WAEC ba.

    Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa ministan ilimi na ƙasar Malam Adamu Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan taron Majalisar Zartarwa na Tarayya.

    Ya kuma bayyana cewa har yanzu babu ranar komawa makaranta.

    Ministan ya kuma bayyana cewa ya gwammace ɗaliban su zauna shekara ɗaya gida da ya saka rayuwarsu cikin haɗari.

  4. Burkina Faso: An gano gawarwaki 180 a wani ƙabari

    BURKINA24/HRW

    Asalin hoton, BURKINA24/HRW

    Akalla gawarwaki 180 ne aka gano a wani ƙabari a arewacin Burkia Faso inda a nan ne sojoji ke yaƙi da 'yan tayar da ƙayar baya, in ji ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rigts Watch.

    "Hujjojin da muke da su sun nuna cewa jami'an gwamnati na da hannu kan kisa ba bisa ƙa'ida ba," in ji Human Rights Watch.

    Sama da watanni bakwai, an zube gawarwakin ne kusa da garin Djibo a rukuni daban-daban kafin mazauna yankin suka binne su.

    Ministan tsaro na ƙasar ya bayyana cewa ya kamata a ɗora alhakin hakan ga masu tayar da ƙayar baya.

  5. Coronavirus a Ghana: Ghana ta yi atamfar korona

    Atamfar Korona

    Asalin hoton, Ghana Textile

    Wani kamfanin yin atamfofi na Ghana ya ƙaddamar da sabbin samfuri na atamfofi da ke nuna irin matakai da kuma halin da aka shiga lokacin annobar cutar korona.

    Sabbin atamfofin na da alamomi kamar ƙwado da mukullai da jirgin sama, waɗanda duka matakai ne da aka ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar.

    Ana yawan saka atamfofi na Afrika a Ghana, kuma ma'aikata da dama na saka su a ranar Juma'a.

    An saka dokar kulle a manyan biranen ƙasar biyu a watan Afrilu - kuma a faɗin ƙasar, an saka dokar hana taruwar jama'a da kuma kulle iyakoki.

    An sassauta dokar kulle da daɗewa- duk da cewa akwai dokar bayar da tazara musamman a coci-coci - kuma rashin saka takunkumi a bainar jama'a babban laifi ne a ƙasar.

    Ƙasar da ke yammacin Afrika ta bayar da rahoton sama da mutum 20,000 da suka kamu da cutar korona inda kuma a kalla mutum 129 suka mutu daga cutar.

  6. Tsoffin gwamnoni hudu da Magu ya daure

    Tsoffin gwamnoni hudu da Magu ya daure

    Asalin hoton, Other

    Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'anati Ibrahim Magu ya tashi daga wanda yake farautar wasu zuwa wanda ake farautarsa.

    A ranar Litinin 6 ga watan Yunin 2020 ne Magu ya bayyana gaban wani kwamiti a fadar shugaban kasa bisa zargin sa da aikata ba daidai ba.

    Rahotanni sun ce Magu ya shafe daren ranar a hannun jami'an tsaro saboda kwamitin bai gama tuhumarsa ba.

    Kafin yanzu dai Magu shi ne mai tuhumar mutane kan zargin almundahana tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi shugabancin EFCC a 2015.

    Ya sha tsare manyan 'yan siyasar Najeriya har ma ya yi nasarar tura wasun su gidan yari bayan da kotu ta tabbatar da cewa lallai sun saci kudin kasa.

    Ku karanta jerin wasu manyan 'yan siyasa da Magu ya tura gidan yari a zamanin shugabancinsa ta hanyar latsa nan.

  7. Hare-haren 'yan bindiga ya sa mutane sun faɗa cikin kogi a Sokoto

    A Najeriya mutane a kalla 10 sun rasa rayukansu a yankin jihar Sokoto kusa da iyakar jihar da ta Zamfara, a wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a daren jiya zuwa safiyar Laraba.

    Da dama daga cikin mutanen yankin kuma sun fada kogi, da zuwa yanzu ba a gan su ba ba a kuma samu gawawwakin su ba ko ruwa ya ci su.

    Lamarin sace-sace ta hanyar kai hare –hare sun zama ruwan dare a wannan yanki.

    Ga rahoton Abdou Halilou kan batun:

    Bayanan sautiRahoton Abdou Halilou kan hare-haren Sokoto da Zamfara
  8. Mutum 980 sun kamu da kwalara a Kamaru

    A lokacin da hukumomin kiwon lafiya suke yaki da annobar cutar korona, annobar kwalara ita ma ta kunna kai ta karu inda ta shafi larduna hudu na Jamhuriyyar Kamaru.

    An kiyasta cewa mutum 980 ne annobar ta shafa, a yayin da ta yi ajalin mutum 45. Masana na dora alhakin zama annoba da wannan cutar ta yi a kan rashin kula da tsaftar muhalli, da rashin samun tsaftaceccen ruwan sha, ga kuma rashin ingantaccen makewayi.

    Ga rahoton Mohaman Babalala ya aiko mana daga Yaounde.

    Bayanan sautiRahoton Babalala kan barkewar kwalara a Kamaru
  9. Fafaroma Francis ya soki cibiyoyin tsare 'yan cirani da ke Libya

    Fafaroma Francis

    Asalin hoton, EPA

    Fafaroma Francis ya soki cibiyoyin tsare 'yan cirani da ke Libya, inda yace 'yan ciranin na samun kansu cikin mummunan matsi a wadannan wurare.

    Ya ce a hakan ma duniya ba ta gama sanin irin bala'in da wadannan bayin Allah ke tsintar kansu ba a cibiyoyin.

    'Yan cirani sun bayyana cewa ana musu fyade da azabtar da su, kuma yunwa ta kama 'ya'yansu.

    Akwai rahotannin da ke cewa baya ga cibiyoyin tsare 'yan ciranin na hukumomi, akwai na bayan fage da masu safarar mutane ke tafiyar da su.

    Dama Tarayyar Turai na taimaka wa masu aikin ceto a Libya don hana su ketarawa kasashensu.

  10. Hong Kong ta hana dalibai magana kan duk abin da ya shafi siyasa

    Daliban Hong Kong

    Asalin hoton, Reuters

    Hong Kong ta ba da umurnin hana dalibai magana kan duk wani abu da ya shafi siyasa, 'yan sa'ao'i bayan China ta bude ofishin da zai kula da sabuwar dokar tsaro a yankin.

    Daga yanzu za a fara fada wa 'yan makaranta cewa kar su kara zancen siyasa ko wani abu mai kama da dimokradiyya.

    Wakilin BBC ya ce ''A duka zanga-zangar neman 'yancin dimokradiyya da aka gudanar bara a Hong Kong dalibai na ciki dumu-dumu. To amma yanzu kwamishinan ilimi ya ce an haramta musu haka.''

    A yanzu ofishin da Chinar ta bude zai rika sa ido wurin ganin an bi dokokin da gwamnatin a Beijing ta kakaba.

    Shugaban da zai jagoranci ofishin ya ce za su bi doka wurin gudanar da aikinsu.

  11. Janar Haftar ya 'shirya sa hannu kan yarejeniyar zaman lafiya'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayar da rahoton cewa Janar Khalifa Haftar na Libiya ya shirya domin saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Janar Haftar dai ya daɗe da zama ɗan tawaye ga gwamnatin Libiya.

    Mista Lavrov ya ce yana sa ran cewa Turkiyya za ta iya shawo kan gwamnatin Libiya da ke da goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da hakan.

    Rasha na daga cikin ƙasashen da ke goyon bayan Janar Haftar - ciki har da Masar da Haɗaɗiyyar Daular Larabawa.

    A cikin 'yan kwanakin nan, an samu yin galba matuƙa kan dakarun Khalifa Haftar inda gwamnatin ƙasar Libiya ce ta rinƙa afka musu tare da goyon bayan gwamnatin Turkiyya.

  12. Yawan masu korona ya haura 500,000 a Afrika

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawan masu cutar korona ya haura 500,00 a Afrika a ranar Laraba, kuma ana fargabar yawan zai karu saboda yadda ake ci gaba da samun sabbin masu kamuwa da cutar a kasashen Afrika da dama.

    Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, reshen Afrika ta fitar a ranar Laraba, inda ta kara da cewa cutar ta halaka mutum 11,959 cikin wata biyar a nahiyar, yawan da ya wuce na wadanda suka rasa ransu sakamakon cutar Ebola da aka yi fama da ita tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016 a yammacin Afrika.

    Sanarwar ta kara da cewa yawan masu cutar ya rubanya a kasashe 22 da ke nahiyar cikin wata guda da ya gabata.

    Kusan kashi biyu cikin uku na kasashen na fuskantar ci gaba da yaduwarta ne a cikin al'umma.

    Kasashen Aljeriya da Masar da Ghana da Najeriya da Afrika Ta Kudu ne ke da kashi 42 cikin 100 na masu dauke da cutar a Afrika, inda Afrika Ta Kudu kawai ke da kashi 29 cikin 100 na jumullar masu dauke da cutar a nahiyar.

  13. Man City da Juventus na son ɗauko Traore, Barca na zawarcin Ndombele

    Adama Traore

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City da Juventus sun sha gaban Barcelona a yunkurin dauko dan wasan Wolves dan kasar Sufaniya Adama Traore, mai shekara 24.(ESPN)

    Chelsea ta fi samun dama wurin dauko dan wasanBayer LeverkusenKai Havertz, mai shekara 21, saboda kungiyoyi da dama sun ce ba za su iya biyan farashin da aka sanya kan dan wasan na Jamus, wato £90m ba.(Goal)

    Barcelona ta nemi dauko 'yan wasanTottenhambiyu; dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23, kuma dan wasan Ingila Ryan Sessegnon.(Evening Standard)

    Watakila Tottenham ta bayar da aron Sessegnon a bazara a yayin da ake fargabar cewa ci gaban dan wasan mai shekara 20 na fuskantar koma-baya a hannun koci Jose Mourinho.(Telegraph)

  14. Hong Kong ta hana dalibai maganar siyasa a kasar

    EPA

    Asalin hoton, EPA

    Hong Kong ta ba da umurnin hana dalibai magana kan duk wani abu da ya shafi siyasa, yan awanni bayan China ta bude ofishin da zai kula da sabuwar dokar tsaro a yankin.

    Daga yanzu za a fara fadawa yan makaranta cewa kar su kara zancen siyasa ko wani abu mai kama da demokradiyya.

    A yanzu ofishin da China ta bude zai rika sa ido wurin ganin an bi dokokin da gwamnatin a Beijing ta ƙaƙaba.

    Shugaban da zai jagoranci ofishin ya ce za su bi doka wurin gudanar da aikinsu.

  15. An umarci makarantu a Kenya da su mayarwa da iyaye kudin 2020

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Ministan Ilimi a Kenya ya ce ko dai makarantun kasar su mayar da kudin makarantar da iyayen yara suka biya ko kuma su amince da su a matsayi na shekara mai zuwa.

    Ministan Ilimin George Magoha ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayara da martani kan damuwar da aka rika nunawa game da sanarwar da aka fitar ranar Talata cewa makarantun kasar na firaimari da sakandire ba za su bude ba sai 2021.

    Mista Magoha ya ce masu kamuwa da cutar korona akasar karuwa suke yi.

    Ministan ya ce daliban za su koma ajujuwan da suke ne lokacin da aka rufe makarantun da zarar an koma.

    Babu wadanda za su rubuta jarrabawar karshe a kasar a wannan shekara.

    Iyaye ne dai suka yi ta nuna damuwa kan kudaden makarantar da suka biya na wannan shekarar.

  16. Halin da ake ciki a Turai

    Getty

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan ce tafiyar farko da shugabar ta yi tun bayan barkewar annobar korona

    Zanga-zanga na ƙara zafi a Belgrade babban birnin Serbia bayan hukumomi sun kara ƙaƙaba dokar kulle sakamakon karuwar masu cutar korona.

    Ga wasu sauran labaran cikin nahiyar Tuarai:

    • A wata tafiya ta farko zuwa kasar waje tun bayan barkewar annobar korona, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nufi birnin Brussels domin tattaunawa kan yadda kungiyar Turan za ta shawo kan wannan annoba. Yayin da Kungiyar tarayyar Turai ke yunkurin tara yuro biliyan 750 don taimakawa kawayenta - wasu kasashen kungiyar kamar Netherland ba su amince da shirin ba.
    • Babban daranktan ma'aikatar lafiya ta Faransa Jérôme Salomon ya shaida wa jaridar Le Figaro cewa dole kasar ta shirya wa dawowar annobar korona a karo na biyu. "Ko wanne cikinmu dole ya rika kula da matakan kariyar da aka zayyana na tsafta da kuma ba da tazara da sanya takunkumi," in ji shi.
    • An mayar da sanya takunkumi wajibi a yankin Catalonia, musamman a bainar jama'a, Ya zuwa ranar Laraba da hukumomi ke ci gaba da ganin sun dakile bullar cutar a karo na biyu a lardin Lleida. "Munga tasirin da sassauta dokar ya haifar a baya, in ji mai magana da yawun gwamnati a yankin Meritxell Budó. " Idan muka maida ta wajibi muna da tabbacin abin da ya faru a baya ba zai kara faruwa ba"
  17. Majalisar dattawa ta mayar da wa'adin babban sufeton 'yan sanda shekara 4

    DrLawalAhmad

    Asalin hoton, DrLawalAhmad

    Majalisar dattawan Najeriya ta sauya dokar wanda ya cancanci ya rike mukamin shugaban sufeton 'yan sandan kasar zuwa shekara hudu babu daɗi babu ragi.

    Majalisar ta sauya dokar ne bayan ta yi nazari kan tsohuwar dokar 'yan sanda ta 2004 da da kuma sauya ta zuwa ta 2020.

    Da yake gabatar da rahoto kan kudurin shugaban kwamitin da ake lura da harkokin 'yan sanda na majalisar Halliru Jika cewa ya yi, mafi yawan masu ruwa da tsaki ba su goyi bayan yadda majalisar ke tabbatar da sufetocin 'yan sanda ya yin wani sauraren ra'ayi.

    "An samu rabuwar kawuna kan wannan doka da ta bukaci tabbatar da nadin ko cire babban sufeton 'yan sanda da majalisa ke yi," in ji Halliru.

    Dangane da naɗi ko kuma sake naɗa sefetocin 'yan sanda a kasar majalisar za ta ci gaba da bin doron dokar da ake da shi a kasa na 215 da aka yi bayani a kundin tsarin mulki.

  18. An koma zirga-zirgar jiragen sama a yau a Najeriya

    BBC

    A ranar Laraba ne aka sake buɗe filayen jiragen sama a Najeriya bayan dakatar da ayyukansu sama da wata uku baya.

    Tun a safiyar yau ne fasinjoji suka cika filayen jirgin da ke Legas da Abuja, wasu wakilan BBC sun zagaya filayen jirgin ga kuma wasu daga cikin hotunan da suka aiko da su.

    BBC

    Ana sa ran fasinjoji su iya filayane jirgin sa'a 3 gabanin lokacin tashinsu.

    Sanya takunkumi a cikin jirgi shi ma na daga cikin manyan ka'idojin hawa jirgin da korona ta zo da su.

    BBC

    Tabbatar da tazara da sauran ka'idojin da mahukuntan lafiya suka shimfiɗa na daga cikin dokokin da ko wanne fasinja zai bi kan hawa jirgi.

    BBC

    Za a bude sauran filayen jirgin da suka hadar da Kano da Fatakwal da Oweri da kuma Maiduguri nan da ranar 11 ga wannan watan.

  19. Labarai da dumi-dumi, Masu korona sun haura miliyan uku a Amurka

    Sama da mutum miliyan uku ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Amurka tun bayan bullar annobar, kamar yadda jaridun New York Times da NBC

    NBC ta ruwaito sama da mutum46,500 ne sabbin wadanda suka kamu da cutar ranar Talata.

    Amurka ce kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar korona a duniya baki daya.

  20. Sama da dala miliyan daya ta yi batan dabo a babban bakin Mauritania

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    An kama mutane da dama da ake zargi da hannu cikin wawure miliyoyin kudi a babban bankin Murtaniya.

    Cikin wadanda aka kama har da ma’aikatan bankin wadanda ke da hannu cikin batan dabon kudin da suka kai yuro 935,000 kwatankwacin dalar Amurka miliyan daya, daidai naira 453,000,000.

    Babbaan bankin kasar ne ya bayyana batan kudin wanda ya ce abu ne mai cike da takaici.

    Sanarwar ta dora laifin kan rashin bibiyar abubuwa a cikin gida ta kuma bukatar tsaurara matakan tsaro.

    Jami’an tsaro a kasar suna gudanar da bincike kan lamarin.