Rufewa
Nan muka kawo karshe shirin namu. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Mun gode.
Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.
Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail
Nan muka kawo karshe shirin namu. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Mun gode.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar harkokin addinin musulunci a Saudiyya ta gargadi limamai a ƙasar da kada su gudanar da Sallar Idi, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Ministan harkokin addinin musulunci, Sheik Abdullatif Al-Asheikh ne ya umarci yin hakan a wata sanarwa da ma'aikatarsa ta fitar.
Wannan wani yunƙuri ne na dakatar da taruwa a masallatai kamar yadda ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta bada umarni domin daƙile yaduwar cutar korona.
'Yan tawayen Houthi a Yemen sun musanta zargin da ake yi musu na yi wa wasu masu cutar korona allurar mutuwa.
Marasa lafiyar dai na zaune ne a yankin da 'yan tawayen na Houthi ke da iko.
'Yan tawayen sun musunta zargin ne bayan wani minista a ƙasar Yemen ya wallafa wani saƙo a shafin Twitter inda ya zarge su da kashe masu cutar korona.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci coci-coci a ƙasar da su buɗe domin a ci gaba da bautar ubangiji.
Ya bayyana cewa Amurka na buƙatar addu'a matuƙa a wannan lokacin, haka zalika ya caccaki gwamnonin ƙasar da suka bar gidajen siyar da barasa suka buɗe.
Kiran na Shugaba Trump na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Amurka ta fitar da sharuɗa kan yadda coci-coci za su buɗe a ƙasar.

Asalin hoton, KNSG
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fita sallar Juma'a a masallacin Juma'a da ke gidan gwamnati.
Kamar yadda ake gani, an bayar da tazara kamar yadda masana harkar lafiya suka yi umarni.
To ko sauran jama'ar gari sun bayar da irin wannan tazara? Duba yadda suka yi tasu a nan
Wasu na nuna kyama ga masu dauke da cutar korona, inda wasu ke ganin cewa ba a iya warkewa daga cutar. Wannan ba gaskiya ba ne.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa ana iya warkewa ras daga cutar.

Asalin hoton, @HaramainInfo
Gwamnatin Saudiyya ta ce sai ranar Lahadi za a gudanar da Idin Salla karama sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a ranar Juma'a.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shafin masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce ba a ga jaririn watan Shawwal ba a yammacin ranar Juma'a bayan duban tsanaki.
Ana dai fara duban watan Shawwal ne a yayin da watan Azumin Ramadana ke cika 29 galibi, a wasu lokutan kuma idan ya kai kwana 30.
Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da masana ilimin taurari suka tabbatar da ba za a ga watan Sallar ranar Juma'a ba.
Jaridar Saudi Gazetteta ruwaito hasashen da suka yi na nuna cewa wata zai riga rana faɗuwa ranar Juma'a, saboda haka ranar Idi ita ce Lahadi 24 ga watan Mayu, yayin da za a yi azumi 30.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, IRMCT
Wani mai gabatar da kararraki kan laifukan yaki na majalisar dinkin duniya ya tabbatar da rasuwar wani kasurgumin mutumin da ake zargi da laifukan yaki a kasar Rwanda.
Wani bayani da aka fitar ya nuna cewa gwaje-gwajen kwayar halittar gado da aka yi sun nuna cewa wata gawar da aka samu a cikin wani kabari a kasar jamhuriyar Congo, ta Augustin Bizimana ce. Kuma ana tunanin cewa ya mutu ne a shekara ta 2000.
Mista Augustin Bizimana, shi ne ministan tsaro a shekara ta 1994, inda wata kotun kasa-da-kasa ta tuhume shi da laifuka 13, ciki har da na laifukan da suka hada da kisan kiyashi, da kisan kai, da fyade, da kuma gallaza wa mutane ukuba.
Wannan sanarwa dai ta biyo bayan damƙe wani hamshakin attajiri Felicien Kabuga a birnin Paris, wanda ya yi ɓatan-dabo tun bayan zargin na kisan gilla.

An gudanar da sallar Juma'a karo na farko cikin wata biyu a masallatan da ke yankin Gaza, biyo bayan sassauta dokokin da aka sanya domin dakile yaduwar cutar korona.
Mutane sun kuma rinka yin tururuwa zuwa manyan kantuna sayar da kayan masarufi domin sayen kayan abinci a shirye-shiryen da ake yi na bukukuwan karamar sallah bayan karewar azumin watan Ramadan.
Sabbin masu kamuwa da cutar ta korona dai a yankin na ci gaba da kara yawa a cikin wannan mako, wakilin BBC ya ce akwai fargabar cewa karin cakuduwar mutane da ake samu zai iya tazzara al'amura.

Dubban mutane ne suka halarci sallar Juma'a a birnin Kano da kewaye, ranar farko kenan da aka buɗe masallata bayan kusan mako biyar sakamakon annobar korona.

Masallacin Umar Ibn Khattab da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a birnin Kano na ɗaya daga cikin masallatan da jama'a suka yi wa tsinke.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa walkilin BBC cewa sun ji daɗin buɗe masallatan.

Wakilin BBC Mansur Abubakar ya ce kasancewar wannan ce Juma'a ta ƙarshe a watan Ramadana, hakan ya ƙara jawo cikar jama'a a masallatan.

Kazalika ya tarar da 'yan agaji a ƙofar masallacin, inda akasarin waɗanda ke sanye da takunkumi suke cikin masallaci, waɗanda ba su sanya ba kuma suke waje.

Asalin hoton, AFP
Malaman makaranta a Zimbabwe sun nuna adawarsu ga sake buɗe makarantu, suna masu cewa ba a ɗauki matakan kare yaɗuwar cutar korona ba, a cewar jaridar Herald ta gwamanti.
An ambato shugaban ƙungiyar malaman, Sifiso Ndlovu, yana cewa idan gwammnati ta ci gaba da shirin nata malaman za su tsunduma yajin aiki.
A 'yan kwanakin da suka gabata ma'aikatar ilimin ƙasar ta sanar da shirinta na sake buɗe makarantun, inda za a fara da 'yan shekarar ƙarshe domin ba su damar rubuta jarrabawarsu da za a fara ranar 29 ga watan Yuni.
"Ɗalibai ba sa cikin hayyacinsu da za su iya rubuta jarrabawa a yanzu," in ji Ndlovu. Sannan ya roki gwamnati da ta soke jarrabawar.
Shugaban Najeriya Muhammadu ya ce shi da iyalinsa za su yi Sallah Idi a gida.
A sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma'a, ya ambato Shugaba Buhari yana cewa zai yi Sallar Idi a gidan ne domin yin biyayya ga dokar hana fita da aka sanya a Abuja da kuma umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar cewa kowa ya yi sallar Idi a gida.
"Na dauki matakin ne bisa umarnin da Sultan na Sokoto kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayar na dakatar da yin sallar Idi a kasa baki daya, " a cewar Shugaba Buhari.
Ya kara da cewa wannan salar Shugaba Buhari ba zai karbi bakoncin jami'an gwamnati ba - wadanda sukan kai masa gaisuwar Sallah - kamar yadda aka saba a al'adance.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Dubban mazauna birnin Moscow na ƙasar Rasha sun koka kan yadda suka ce ana cin tararsu bisa kuskure sakamakon amfani da manhajar bin sawun cutar korona a ƙasar.
Ofishin magajin garin ne ya ƙirƙiro da amfani da manhajar a watan Maris.
Fiye da mutum 60,000 ne suka yi rajistar amfani da manhajar da ke sa ido kan yin nesa-nesa da juna kuma take da ikon gano inda mai amfani da ita yake tare da umartarsa da ya ɗauki hoton selfie masu yawa a kowacce rana.
An ci tarar kusan kashi 30% na masu amfani da ita rouble 4,000 - kwatankwancin dala 55 (kusan naira 21,000) saboda sun gaza bin umarninta.
Wasu sun ce an yi ta cin tararsu har kusan rouble 50,000.

Asalin hoton, FACEBOOK/MARAYA
Malamai sun ce bisa nassi an fara Zakkar Fidda-kai bayan hijirar Annabi Muhammad SAW da shekara biyu, wato a shekarar da aka wajabta Azumin Ramadan, saboda haka Sunna ce mai karfi da ke da nufin wanzar da zaman lafiya tsakanin al'ummar Musulmai.
Tasirin Zakkar Fidda-kai guda uku tsakanin musulmi:
BBC ta tattauna da wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Malam Halliru Maraya kan Zakkar Fidda-kai da tasirinta a tsakanin musulmai.
Malamin ya lissafa wasu abubuwa guda uku a matsayin tasirin da Zakkar Fidda-kai ke yi a tsakanin musulmi:

Asalin hoton, @AsisatOshoala
Tauraruwar 'yar kwallon Najeriya kuma ta ƙungiyar mata ta Barcelona, Asisat Oshoala ta bayyana abin da take ji game da kasancewar yau Juma'a a matsayin ranar azumin Ramadana 29.
Kamar yadda kuke gani, Oshoala ta wallafa a Twitter cewa: "Na 29....#Ramadan".
Sai dai BBC ba ta iya fahimtar me 'yar kwallon ke nufi ba; murna ce ko alhinin rabuwa da Ramadana.
Amma muna fatan ku za ku iya fahimta - musamman ma waɗanda korona ta haramta wa ganawa da abar ƙaunarsu ƙwallon ƙafa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Shugabar hukumar zaɓe ta ƙasar Malawi ta yi murabus daga muƙaminta wata ɗaya kafin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu.
Kotu ce ta yi umarni da sake zaɓen bayan ta soke na shekarar da ta gabata, wanda ya bai wa Shugaba Peter Mutharika damar mulki karo na biyu.
Masu zanga-zanga sun yi ta kira ga Jane Ansah da ta sauka, suna masu cewa ta gaza a zaɓen farko, inda aka yi amfani da tawadar gyara a jikin takardun kaɗa ƙuri'a.
Sai dai, a wata hira da gidan talabijin ɗin ƙasar ta musanta cewa tana shirin yin murabus.
Za a yi zaɓen ranar 23 ga watan Yuni.

Asalin hoton, Getty Images
Mutum aƙalla 13 ne suka mutu sakamakon cutar kwalara tun bayan fara ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙasar Kenya.
Ma'aikatar lafiya ta ce an samu mace-macen ne a yankin arewacin ƙasar.
An bayar da samun rahoton mutum 500 da suka kamu da cutar ta amai da gudawa.
Annobar ta fara ne a garin Garissa sannan ta fantsama yankunan Wajir da Turkana da Muranga da Marsabit.
Minista Mutahi Kagwe ya alaƙanta annobar da ambaliyar ruwa, wadda ta jawo ƙarancin tsafta, yayin da masai ko kuma shadda suka gurɓata ruwan sha.
A wani bidiyo da gidan talabijin na NTV ya wallafa, Mista Kagwe ya ce ƙananan yara ne abin ya fi shafa.
Wani jirgin saman Pakistan International Airlines wanda ya taso daga Lahore ya rikito a filin jiragen saman Karachi, a cewar jami'an kula da jiragen sama.
Jirgin, wanda rahotanni suka ce yana dauke da fasinjoji 99 da ma'aikatan jirgi takwas, yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Jinnah, daya daga cikin filayen jiragen sama mafi hada-hada a Pakistan.
Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya a wurin da jirgin ya fadi da ke rukunin gidaje da ke Karachi.
Ma'aikatan agajin gaggawa sun isa wurin da jirgin ya yi hatsari, inda ya lalata gidaje.
Kakakin hukumar kula da sufurin jiragen saman Pakistan, Abdul Sattar Khokhar, ya ce: "Jirgin ya fadi a Karachi. Muna kokarin tabbatar da adadin fasinjan da ke cikinsa, amma dai bayanan da muke da su sun nuna mutum 99 da ma'aikatan jirgi tawaks a cikinsa".
Jirgin ya yi hatsari ne kwana 10 bayan gwamnatin kasar ta amince jirage su koma zirga-zirga.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY
Sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya yi kira ga gwamnonin jihohin da suka sassauta dokar kulle da su yi taka-tsan-tsan
Mr Mustapha, yayin da yake jawabi a matsayinsa na shugaban kwamitin yaki da cutar korona na gwamnatin tarayya ranar Alhamis a Abuja, ya ce matakin sassauta dokar kullen zai iya sanya mutane su yi ta kamuwa da cutar korona.
Jihohi irin su Bauchi, Kano, Adamawa, Cross River, Borno, da kuma Ebonyi suna cikin wadanda suka sassauta dokar kullen inda suka amice a gudanar da sallolin Juma'a da na Idi.
Gabilin jihohin na ci gaba da fama da karuwar masu dauke da cutar, a daidai lokacin da suke sassautar dokar ta kulle lamarin da masana harkokin lafiya suke gani a matsayin ragon azanci.
Da ma dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da soke duk wani taron jama'a, wanda ya hada da tarukan wuraren addini, a matakin dakile yaduwar cutar ta korona.
Amma duk da haka jihohin suka dauki matakin bari a gudanar da sallolin na Juma'a da Idi.
A farkon mako, Malam Garba Shehu, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin watsa labarai ya ce abin takaici ne a ce gwamnatin tarayya tana daukar matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai daga gwamnonin jihohi.
Ya ce ''ba wai zargi muke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan matsaya ba ta zo guda ba, da wuya a yi nasara a yaki da korona''.
Malam Garba Shehu, ya ce kwamitin da ke yaki da annobar na kasa na kokawa kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorin da ake samu akan annobar.
"Kamata ya yi kafin a dauki kowanne irin mataki, to a tuntubi masana domin neman shawarwari," in ji mai magana da yawun shugaba kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Brazil ta zama ƙasa ta shida da cutar korona ta kashe fiye da mutum dubu 20 a cikinsu.
An ba da rahoton mutuwar mutane kusan 1,200 jiya, adadi mafi yawa tun bayan ɓullar cutar.
Wakiliyar BBC ta ce ba ma wannan kaɗai ba, an kuma tabbatar cutar ta sake kama mutane sama da dubu goma sha takwas, annobar dai na yaɗuwa cikin sauri.
Ƙwararru sun yi gargadin cewa har yanzu akwai 'yan makwanni kafin Brazil ta kai ƙololuwar annobar, kuma rashin isassun gwaje-gwaje a ƙasar na nufin alƙaluman hukumomi ba sa nuna zahirin al'amarin.
Shugaba Jair Bolsonaro ya yi ta shashantar da barazanar annobar.
Ya ma buƙaci gwamnonin jihohi su cire matakan kulle da suka ƙaƙaba.