Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

A biya ma'aikata albashin watan Mayu yanzu - Zulum

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da annobar korona da ma wasu karin batutuwa da ke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshe wannan shiri na kawo muku bayanai kai tsaye. Mun gode

  2. Tarayyar Turai za ta taka wa Isra'ila burki kan Falasdinawa

    Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta yi kokarin hana Isra'ila abin da ta kira yiwuwar mamaye wasu bangarori na gabar yamma da kogin Jordan.

    Babban jami'i mai kula da harkokin kasashen waje na tarayyar Josep Borell ya ce tarayyar za ta yi amfani da karfin diplomasiyya don hana Israila yin gaban kanta wajen daukar duk wani mataki.

    Shirin zaman lafiya da Shugaban Amurka Donald Trump ya tsara ya nuna cewa Israila tana da damar fadada yankin da ta mamaye.

    Falasdinawa sun yi mummunar suka ga tsarin

  3. Tarayyar Turai da Burtaniya ba su cimma matsaya ba kan ficewar kasar daga tarayyar

    Taryyar Turai da Birtaniya sun ce babu wani ci gaba na a zo a gani a tattaunawar baya-bayan nan kan makomar dangantakarsu bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

    Babban mai shiga tsakani na Turai Michel Baneir ya ce ba shi da kwarin gwiwar cewa za a cimma yarjejeniya kan cinikayya.

    Ya yi kira ga Birtaniya ta ringa duba abin da zai yiwu. A bangarensa, mai shiga tsakani na Birtaniya Davir Frost ya zargi Turai da kokarin kakaba tsarin nahiyar a kan Birtaniya.

    Ya ce tarayyar ta bijiro da wasu tsare- tsare da suka karkata wani bangare, wadanda za su daure Birtaniya da jijiyar jikinta.

  4. Trump ya bayyana shirin samar da riga-kafin korona

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wani shiri na gaggauta samar da allurar riga-kafin cutar korona.

    Ya ce manufar shirin da ya kira "Operation Warp Speed" shi ne samarwa da rarraba riga-kafin da aka amince da shi cikin gaggawa.

    Shugaba Trump ya ce yana fatan ganin an samar da riga-kafin zuwa karshen shekarar nan, to amma kwararru sun nuna hakan da kamar wuya.

    Ya ce shirin shi ne mafi girma da gwamantin Amurka ta yi, tun bayan samar da makaman kare dangi na nukiliya.

  5. Coronavirus ta sa Minista ya yi murabus a Brazil saboda sabani da gwamnati

    Ministan lafiyar Brazil Nelson Teich ya yi ritaya kasa da wata guda bayan nada shi, sakamakon samun sabani kan yadda gwamnati ke tafiyar da yaki da cutar korona.

    Fiye da mutum dari bakwai ne suka mutu a makon da ya gabata a Brazil, abin da ya sa kasar ta zama ta biyu da aka fi samun mace-mace a duniya bayan Amurka.

    Sai dai Shugaba Jair Bolsonaro na ci gaba da nuna adawa da matakin kulle, yana mai cewa babu yadda za a yi a hana cutar yaduwa.

    A baya-bayan nan Mista Nelson ya soki dokar da shugaban kasa ya kafa ta bude wuraren motsa jiki da na gyaran jiki.

  6. Zulum ya bada umarnin biyan albashin watan Mayu a Borno

    Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da a biya albashin watan Mayu da kuma fansho domin ba ma'aikata damar yin shirye-shiryen sallah.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a ta hannun mai taimaka masa kan watsa labarai Isa Gusau.

    Gwamnan ya bayyana cewa biyan albashin da wuri zai ba ma'aikata damar sayen kayayyaki da wuri domin gudun hauhawar farashi a lokacin sallah.

  7. An sassauta dokar hana zuwa coci da masallaci a Ebonyi

    Jihar Ebonyi a Najeriya ta sassauta dokar da ta saka na hana zuwa coci da masallaci a jihar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai na jihar Mista Uchenna Orji ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a garin Abakaliki a ranar Juma'a.

    Sai dai a sharudan sabuwar dokar, babu wurin bautar da za a tara fiye da mutum 50, haka zalika dole a wanke hannu tare da bayar da tazara tsakanin juna da kuma saka takunkumin rufe fuska.

    A wannan makon dai wasu jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Borno da Adamawa da Gombe da Jigawa suka sassauta dokar da ta haramta yin taruka ciki har da na addini kuma yanzu mazauna yankunan za su iya zuwa masallatan Juma'a da majami'u.

  8. Shugaban Brazil ya yi rashin ministan lafiya karo na biyu cikin kwana 60

    Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya yi rashin ministan lafiya karo na biyu ciki wata biyu.

    Nelson Teich ya aje aikin da ya fara cikin kasa da wata daya, wanda ya maye gurbin Luiz Henrique Mandetta da aka kora.

    A ranar Litinin ne shugaba Bolsonaro ya bayyana gidajen motsa jiki da wajen gyaran gashi a matsayin wuraren da suka zama dole abarsu a bude duk da sake barkewar cutar korona, ba tare da tuntubar ministan lafiya Nelson Teich ba.

    Kafafen yada labarai na Brazil sun ce abu na gaba da Bolsonaro yayi, shi ne goyon bayan amfani da maganin chloroquine, duk da cewa babu wata shaida a kimiyance.

    Kasar ita ce wadda cutar ta fi mugun tasiri a nahiyar Latin Amurka, inda aka tabbatar da sama da mutum dubu 200 na dauke da cutar kuma kimanin 14,000 suka mutu, tun bayan barkewar cutar, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta bayyana.

  9. Me kuka sani game da ciwon siga da cutar korona?

    Daya bisa hudu na marasa lafiyar da suka mutu a asibiti sakamakon cutar korona a Ingila na da ciwon siga, matsalar da ke janyo sikarin da ke jikin dan adam ya yi sama sosai.

    A Burtaniya kimanin kashi 90 cikin 100 na dattijan kasar na fama da ciwon siga nau'in type 2. Karin kiba na haifar da hadarin kamuwa da wannan nau'in ciwon sigan, kuma yana kara hadarin kamuwa da cutar korona.

    Saboda me? Saboda yawan kitsen da jikinka ke shi, karancin aikin da huhunka da zuciyarka za su yi. Kitsen zai iya haifar da ciwon jiki da zai janyo garkuwar jikinka ta yi rauni.

    Wasu karin hadarin da ke tattare da nau'in ciwon siga na type 2 - kamar hawan jini da kuma fitowa daga jinsin bakaken fata ko Asia ko kabilun da basu da rinjaye - duka nada alaka da hadarin kamuwa da mummunar rashin lafiya daga korona.

    Haka kuma masana na cewa hadarin kamuwa da cutar ga 'yan kasa da shekara 40 ba shi da yawa, ana ta kiraye-kirayen bukatar neman taimako ga mutanen da ke fama da ciwon siga nau'in type 2, musamman idan ba a gida suke aiki ba.

  10. 'Yar Ethiopia ta zama minista ta farko a Isra'ila

    Isra'ila na daf da samun minista da ba 'yar kasa ba a karon farko cikin tarihi, wacce aka shigar da ita kasar a boye a 1980.

    An zabi Pnina Tamano-Shata ta zama mataimakiyar Firaiminista Benny Gantz, wanda ke kokarin kafa kwamnatin hadaka da Firaiminista Benjamin Netanyahu.

    Ana sa ran za a rantsar da sabuwar gwamnatin a ranar Lahadi - bayan dan jinkirin da aka samu wajen nada ministoci.

    Yahudawan habasha da ke zaune a Isra'ila na kuka game da fuskantar wariya.

    Matsaloli irin na su 'yan sanda na amfani da karfi da ya wuce iko kan 'yan Isra'ila da ke zaune a yankunan 'yan Habasha - cikin har da harbe-harbe - wanda ya janyo zanga-zanga a kan tituna da ta janyo rikici a baya-bayan nan.

    Al'ummar da yawansu ya kai 140,000 na cikin wadanda suka fi kowa talauci a kasar, kuma suke fama da rashin aikin yi.

    Sai dai da yawa daga cikin matasan Habasha da ke zaune a Isra'ila na kara samun nasara a fadin kasar, ta yadda suke dare manyan mukamai a bangaren soji da siyasa da kuma shari'a.

  11. Abin da ya sa za mu karɓo bashin $1.2bn - Sabo Nanono

    Ministan ma'aikatar gona a Najeriya ya shaida wa BBC cewa za su karɓo bashin $1.2bn domin zamanantar da aikin noma.

    Alhaji Sabo Nanono ya ce za a yi amfani da kudin wajen inganta da aikin gona a kananan hukumomi 632 na kasar.

    A cewarsa, "Dutch Bank daga European Union su za su bayar da wani bangare na wannan bashi, sannan Development Bank na Brazil shi kuma zai bayar da wani bangare na bashin."

    Minista Nanono ya ce za a kwashe shekara goma sha biyu kafin a biya bashin, yana mai cewa Najeriya za ta biya kashi uku cikin dari na kudin ruwa a kan bashin.

    Ya kara da cewa za a sayo motocin noma da gyaransu da gina wuraren ajiye kayan feshi da magungunan kwari da makamantansu.

    Ministan ya ce ba ruwan kudi Najeriya za ta karbo ba, inda ya ce akasari za a karbo kayan aikin gona ne da kuma magungunan kwari.

    Ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraren hira da Minista Nanono:

  12. Marasa lafiya miliyan biyu sun daina zuwa asibiti a Najeriya saboda korona

    Ministan Lafiya na Najeriya ya ce kimanin kashi 50 cikin 100 na marasa lafiya masu zuwa asibitoci a duba su sun daina zuwa asibitocin.

    Dr Osagie Ehanire ya ce adadin mata masu juna biyu da ke zuwa asibiti da kuma ayyukan riga-kafi, su ma sun ragu matuka, tun daga lokacin da aka samu bullar cutar korona a kasar.

    Dr Ehanire wanda ya yi bayani a wurin taron manema labarai na kullum da kwmaitin yaƙi da cutar korona na ƙasa ke yi a Abuja, ya ce adadin marasa lafiya da ke zuwa asibitoci a matakin je-ka-ka-dawo, wato wadanda ba a kwantar da su ba, ya ragu daga mutum miliyan hudu zuwa miliyan biyu a duk rana.

    Haka nan yawan mata masu zuwa awo ko renon ciki ya ragu daga miliyan 1.3 zuwa dubu 655, yayin da ayyukan riga-kafi suka yi ƙasa ta kusan rabi.

    Adadin karɓar haihuwa da ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya ke yi, ya ragu sosai.

    Amma Ministan bai yi ƙarin haske kan dalilan da suka haifar da wannan gagarumar raguwar ba, ya yi nuni da cewa matakan takaita zirga-zirga da aka ɗauka don yaƙi da cutar korona ka iya kasancewa cikin dalilan.

    Sai dai kuma rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na nuna cewa marasa lafiya da dama sun daina zuwa asibiti saboda tsoron kamuwa da cutar korona, wasu kuma likitocinsu ke ba su shawarwarin kiwon lafiya ta waya domin rage yawan mutane a asibiti.

    Har wa yau, bayanai na nuna cewa an rufe asibitoci da dama musamman masu zaman kansu, yayin da a wasu wuraren kuma ake ɗari-ɗari da karɓar marasa lafiya, a lokacin da su kuma hukumomi hankalinsu ya fi karkata ga cutar Korona.

    Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya, Dr Francis Faduyile, ya shaida wa BBC cewa samun raguwar adadin marasa lafiya da ke zuwa asibotoci, da mata masu juna biyu, da kuma ayyukan riga-kafin da kusan kashi 50 cikn 100, ka iya ƙara jefa mata da ƙananan yara da kuma dattijai cikin haɗari.

    Amma Ministan Lafiya Dr Ehanire ya ce gwamnati na ɗaukar matakan tabbatar da an koma ga ayyukan kiwon lafiya na yau da kullum kamar yadda aka saba.

  13. Cibiyoyin gwajin korona sun zama 25 a Najeriya

    Ya zuwa yanzu akwai cibiyoyin gwajin cutar korona 25 a faɗin Najeriya.

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar ce ta bayyana hakan a wani saƙon Twitter, wanda ta ce hakan ya biyo bayan kafa cibiyar ne a Cibiyar Gwamnatin Tarayya da ke Yolan Jihar Adamawa.

    Kazalika ta ce aka kan ginin irin waɗannan cibiyoyi a jihohin Katsina da Ƙwara da Anambra da Gombe.

    NCDC ta ce an yi wa mutum 30,657 gwajin cutar ya zuwa ranar Juma'a.

    Ya zuwa daren Alhamis, Najeriya na da mutum 5,162 da suka harbu da cutar korona da kuma 167 da suka rasa rayukansu, sai kuma 1,180 da suka warke daga cutar.

  14. Ƙarin mutum 186 sun mutu a Ingila

    Wasu mutum 186 sun mutu bayan jinyar da suka sha ta cutar korona a Ingila, kuma hakan ya sa jumillar adadin waɗanda suka mutu a asibitocin ƙasar zuwa 24,345, a cewar hukumar NHS.

    A Scotland kuwa, jumillar majinyata 2,053 ne suka mutu bayan kamuwa da cutar, ƙarin mutum 46 kenan daga 2,007 na alƙaluman ranar Alhamis, kamar yadda Babban Minista Nicola Sturgeon ya bayyana.

    Hukumar Lafiya ta yankin Wales ta ce an samu ƙarin mutuwar mutum tara, inda 1,173 suka mutu jumilla.

  15. Wani gwajin riga-kafin korona ya yi nasara a kan birai

    Wata allurar riga-kafin cutar korona ta nuna alamun bayar da kariya daga cutar da aka gwada a kan wasu birai jinsin rhesus macaques guda shida.

    A gwajin da aka yi a Amurka da ya haɗa da wasu masana daga hukumar National Institutes of Health (NIH) da kuma Jami'ar Oxford, an bai wa biran raga-kafin kafin a shafa musu cutar SARS-CoV-2.

    Daga baya binciken ya gano biran suna dauke ne da kaɗan daga cikin ƙwayoyin cutar a huhu da kuma numfashinsu idan aka kwatanta da biran da ba a ba su riga-kafin ba.

    Jinsin birai na rhesus macaques na da siffar garkuwar jiki iri ɗaya da ɗan Adam kuma yanzu haka ana gwada ta a kan mutane.

  16. 'Yan ƙungiyar ISWAP 11 sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya

    Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Abuja ta ce mayaƙan ƙungiyar ISWAP - ƙungiyar da ke mara wa IS baya a yammacin Afirka - guda 11 new suka miƙa wuya gare ta ranar Litinin a Jihar Adamawa.

    Rundunar ta ce wannan "alamu ne na nasarar da take samu kan ƙujngiyoyin Boko Haram da ISWAP", sannan ta ce akwai wasu alamun da nuna cewa wasu ma za su biyo baya.

    "A ranar 11 ga watan Mayun 2020, mayaƙan ƙungiyar ISWAP 11 sun miƙa wuya ga rundunar Operation Lafiya Dole a Jihar Adamawa. Ana ci gaba da ɗaukar bayanansu domin ɗaukar mataki na gaba," in ji rundunar a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.

    Rundunar ta ce an jibge mata 33 da ƙananan yara 39 a ƙofar shiga garin Ngala da ke Jihar Borno ranar Lahadi 10 ga watan Mayu, "abin da ke nuna cewa wasu da dama daga cikin mayaƙan ƙungiyar za su biyo baya," a cewarta.

    Ta ƙara da cewa mutanen suna hannunta domin ɗaukar mataki na gaba.

  17. Wasu na amfani da dokar zaman gida don yin zambar soyayya

    Mazambata ta kafar intanet na amfani da halin da mutane ke ciki na dokar kulle domin zambatarsu dubban kuɗaɗe da nufin yin soyayya da su.

    Binciken da aka yi a wani yanki ya nuna cewa ana raba waɗanda aka yaudara ta hanyar zambar soyayya da kuɗi kusan fan 47,000 - kusan naira miliyan 22.

    Wata bazawara mai shekara 62 ta ce ta yi asarar dubban fan a kan wani mutum da ya ce mata Ba'amurke ne da ke zaune a kasar waje, kafin daga baya ta gano cewa wasu gungun mazambata ne ke yi mata yawo da hankali.

    Mutanen sun nuna mata cewa sun daɗe suna ƙaunarta daga nesa tun kafin korona, amma annobar ta sa sun ƙara tatsar kuɗi daga hannunta.

    Wata ta bayyana yadda "zuciyarta ta rinjayi ƙwaƙwalwarta" a lokacin da take tura wa wani mutum da ta yi zaton masoyinta ne na ƙwarai kuɗi.

    Mutane da dama a faɗin duniya sun yawaita amfani da intanet tun bayan da gwamnatoci suka fara kafa dokar kulle domin daƙile yaɗuwar annobar korona a watan Fabarairu.

  18. WHO za ta soma koyar da darusa da Hausa kan korona

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce za ta soma koyar da darusa kan cutar korona cikin harshen Hausa, da Swahili da kuma Amharic.

    Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.

    A cewarsa, za a soma koyar da darasin, mai taken 'Intro to #COVID19' a turance, wato 'Gabatarwa kan cutar korona' a shafin intanet.

  19. Korona ta jefa Jamus cikin taɓarɓarewar tattalin arziki

    Jamus, wadda ta fi kowacce ƙasa girman tattalin arziki a Nahiyar Turai, ta faɗa cikin taɓarɓarewar tattalin arziki yayin da tasirin annobar korona ke ci gaba da bayyana.

    Tattalin arzikinta ya faɗi da kashi 2.2 cikin 100 a wata huɗun farko na shekarar nan biyo bayan faɗuwar farko da ya yi a wata huɗu kafin haka sakamakon rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China.

    Alƙaluma daga ma'aikatar ƙididdiga sun bayyana acewa wannan ne koma-baya mafi girma cikin fiye da shekara 10, sannan suka yi gargaɗin cewa abin zai iya munana idan tasirin dokar kulle ya gama bayyana.

    Faɗuwar tattalin arzikin na Jamus bai yi tsauri kamar na sauran manyan ƙasashe ba irin su Faransa, wadda ta bayar da rahoton faɗuwar kashi 5.8 cikin 100 a iirn wannan lokaci.

  20. 'Hare-hare kan asibitoci ka iya daƙile yaƙi da korona a Libya'

    Kungiyar International Rescue Committee (IRC) - mai ƙoƙarin kiyaye zaman lafiya - ta yi gargaɗin cewa akwai yiyuwar Libya ta gaza a yaƙi da cutar korona sakamakon hare-haren da ake kai wa asibitoci a ƙasar.

    An kai wa Asibitin Tripoli Central Hospital hari ranar Alhamis, yayin da aka jikkata fararen hula 14 a wani harin a unguwannin da ke birnin Turabulus ko kuma Tripoli.

    Asibitin na binrin Tripooli na cikin manyan asibitoci a ƙasar baki ɗaya - kuma yana da mahimmancin gaske a yaƙin da ƙasar ke yi da korona.

    "Hare-hare a Libya suna ƙara ƙamari. Duk da cewa babu wanda ya jikkata a yau, Asibitin Tripoli na da ma'aikata 5,000 da kuma gado 950, saboda haka rayuwar dubban mutane na cikin haɗari," a cewar shugaban IRC na Libya, Tom Garofalo.

    Libya ta kasance cikin rikici tun daga tunzurin shekarar 2011, wanda ya yi sanadiyyar tumɓuke Shugaba Muammar Gaddafi daga karagar mulki.