An gano maganin hana coronavirus yaduwa

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye game da abubuwan da suke faruwa a duniya - wanda coronavirus ta mamaye.

    Ku ci gaba da karanta labarai da kallon hotuna da bidiyo a babban shafinmu.

  2. Trump ya yi wa Google shigar sauri kan shafin Coronavirus da yake kirkira

    Google

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama Shugaba Trump ya bai wa Google mamaki da sanarwar da ya bayar ranar Juma'a cewa injiniyoyi 1,700 ne ke aiki kan shafin da kamfanin zai samar da zai rika bayyana wanda za a yi wa gwajin coronavirus da kuma wurin da za a yi.

    "Za a kammala shi cikin sauri ...sun dukufa sosai suna ci gaba da aikinsa," Trump ya fada.

    Google ya tabbatar da cewa wani kamfani mai alaka da shi mai suna Verily Life Sciences, yana aiki kan shafin amma "yana matakin farko" tukunna.

    Kamfanin fasahar ya kara da cewa yayin da yake sa ran gwada shi a San Francisco Bay Area nan gaba kadan - kamar mako mai zuwa - zai dauki lokaci kafin ya iya karade kasar baki daya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Wanda yake jin alamun cutar zai shiga shafin ne ya bayyana abin da yake ji, inda nan take za a fada masa matakin da ya kamata ya dauka, ya kamu da cutar ko kuma a'a.

  3. An gano maganin hana coronavirus yaduwa

    coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rukunin masana kimiyya sun ce sun samu wani magani da zai iya taimakawa wurin ganowa da kuma hana kwayar cutar coronavirus yaduwa a tsakanin jama'a.

    Zuwa yanzu ba a gwada kwayar ba a kan 'yan Adam - abin da zai daukki watanni.

    Masu binciken na cibiyar Erasmus Medical Centre da kuma jami'ar Utrecht University, sun bayyana binciken da cewa garkuwa ne ga kwayar cutar Sars2, wato coronavirus (Covid-19) da ke yada annobar da ake fama da ita.

    Masanan dama can suna aiki kan Sars1 a lokacin da coronavirus ta barke, sun ce sun gano cewa kwayoyin garkuwar na iya dakile cutar da kuma hana ta yaduwa.

  4. Shugaban Fifa ya kalubalanci manyan 'yan kwallo

    Shgaban Hukumar Kwallon Kafa ta Fifa, Gianni Infantino ya bi sahun takwaransa na Hukumar Lafiya ta Duniya wato Dr Tedros wurin wayar da kai kan cutar Coronavirus.

    Infantino ya kalubalanci taurarin kwallon kafa irinsu Drogba na Ivory Coast da Kaka na Brazil da Alex Morgan 'yar kwallon Amurka da su fito su kwatanta abin da ya yi domin yada kiran kawo karshen cutar.

    A wannan bidiyon da Fifa ta wallafa a shafinta na Twitter, ana iya ganin Infantino yana nuna yadda za a rika wanke hannu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Mutum 155 sun sake kamuwa a Netherlands

    Wadnda suka kamu da Coronavirus a kasar Netherlands sun karu da 155, inda suka kai 959.

    Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce mutum biyu ne suka mutu tun da cutar ta barke.

  6. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus: Wadanda suka mutu a Birtaniya sun kai 21

    Adadin mutanen da Coronavirus ta kashe a Birtaniya ya kusan ninkawa a cikin sa'a 24, inda ya karu daga 11 zuwa 21.

    Hukumar Lafiyar kasar ta National Health Service ce ta bayyana hakan.

  7. Dalilin da ya sa Nahiyar Turai ta zama cibiyar Coronavirus

    Tedros Adhanom Ghebreyesus

    Asalin hoton, @DrTedros

    Fiye da mutum 132, 000 ne suka kamu da annobar cutar Coronavirus a kasashe 120.

    Wadanda suka mutu kuma sun kai kusan 5,000 - lamarin da Dr Tedros na hukumar WHO ya kira shi da "tarihi maras kyau".

    "Nahiyar Turai yanzu ta zama cibiyar annobar, inda mutane ke kamuwa da mutuwa fiye da sauran sassan duniya da China," in ji shi.

    "Ana ta samun masu cutar a kowace rana fiye da yadda ake samu a China a lokacin da cutar na kan ganiyarta."

  8. Mutum 1,500 sun kamu da Coronavirus a Spain a rana guda

    Spaniya

    Asalin hoton, Reuters

    Masu kamuwa da annobar Coronavirus a Spaniya sun karu da 1,500 a rana daya, inda adadinsu ya kai kai 5,700, a cewar hukumomin kasar.

    Spaniya ce ta biyu da cutar ta dabaibaye a Turai bayan Italiya, wadda take da mutum 15,000 da suka kamu.

    Labarin ya zo ne yayin da gwamnatin kasar ke shirin ayyana dokar-ta-baci a karo na biyu a tarihin kasar na baya-bayan nan.

    A ranar Juma'a ne Hukumar Lafiya ta WHO ta ce Nahiyar Turai ta zama "cibiyar" annobar coronavirus.

  9. Labarai da dumi-dumi, Coronavirus ta sake kashe mutum 97 a Iran

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutum 611 kenan suka mutu baki daya a kasar

    Wadanda Coronavirus ta kashe a Iran sun karu da 97, abin da ya kai yawansu zuwa 611 gaba daya a kasar, a cewar rahoton gidan talabijin na kasar.

    Hukumomi sun ce mutum 12,729 ne suka kamu.

    A ranar Laraba ne wasu hotunan tauraron dan Adam suka nuna yadda Iran ke gyara wani kabari da aka binne mutane da yawa a cikinsa.

  10. Me zai faru idan aka ce an gama wasannin Premier League haka saboda Coronavirus?

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Me zai faru idan aka ce an gama wasannin Premier League haka saboda Coronavirus?

    'Yan Arsenal da Man United da Tottenham ya kasuwarku za ta kasance ne?

  11. Me zai faru idan aka ce an gama wasannin La Liga haka saboda Coronavirus?

    La Liga

    Asalin hoton, Getty Images

    Halin da coronavirus ta saka wasannin ya yi kamari fa jama'a.

    Yanzu da tsautsayi zai sa a ce an gama wasanni a La Liga, me zai faru?

  12. Turkiyya ma ta dakatar shiga da fita zuwa Turai

    Turkish Airlines

    Asalin hoton, Getty Images

    Turkiiya ta ce za ta dakatar da jirage daga fita da shiga kasashen Turai ciki har da Jamus da Faransa har zuwa 17 ga watan Afrilu, Reuters ya rawaito.

    Dakatarwar za ta fara ne a yau Asabar.

    Sauran kasashen da abin ya shafa su ne: Spaniya , Norway, Denmark, Austria, Sweden, Belgium, Netherlands. Tuni dama da ta dakatar da shiga da fita zuwa Italiya.

    Zuwa yanzu mutum biyar ne suka kamu da cutar a Turkiyya.

    A gefe guda kuma, Yankin Northern Cyprus da ke cin gashin kansa, ya haramta wa duk wanda ba dan yankin ba shiga kasar har zuwa 1 ga watan Afrilu.

    Yankin ya bayar da rahoton kamuwa na farko a ranar Talata na wani dan Jamus mai yawon bude ido. Tun bayan nan mutum biyar ne suka kamu.

  13. Saudiyya za ta hana jirage sauka a kasar

    Harami

    Asalin hoton, Getty Images

    Daga gobe Lahadi Saudiyya za ta haramta wa dukkanin jirage sauka a kasarta na tsawon mako biyu.

    Haramcin zai shafi kowa da kowa sai dai fa "al'amura na musamman", a cewar kamfanin dillancin labaran Saudiyyar na SPA.

    Akwai rahotn mutum 86 da suka kamu da coronavirus a kasar amma babu wanda ya mutu ya zuwa yanzu.

    Sai dai akwai fargaba a yankin saboda kasar Iran, inda annobar ta kashe sama da mutum 500 kuma rahotannin da ba na gwamnati ba na cewa sun fi haka yawa.

  14. Coronavirus ta bulla kasashen Namibia da Rwanda

    Wasu ma'aurata 'yan kasar Spaniya da suka a kasar Namibia ranar Laraba, an gano suna dauke da coronavirus, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Gwamnatin Namibia ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da bukukuwan 'yancin kai a cikin watan nan na Maris.

    Reuters ya ce kasar Rwanda ma ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da cutar a kasarta.

  15. Trump ya ce a koma ga Allah kan Coronavirus

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A jiya Juma'a Trump ya saka dokar-ta-baci kan annobar cutar ta Covid-19

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar addu'o'i a kasa baki daya domin neman sauki daga annobar cutar coronavirus.

    Shugaban ya roki Amurkawa da su dukufa wurin addu'o'i a duk inda suke.

    "A duk inda kuke, na karfafi gwiwarku da ku mika lamuranku ga Allah da addu'o'i. Cikin sauki sai ku ga mun tsira tare," Trump ya bayyana a shafinsa na Twitter.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Ya kara da cewa: "Cikin girmamawa, na ayyana Lahadi 15 ga watan Maris a matsayin Ranar Addu'o'i ta Kasa. Kasarmu, a tarihi, ta sha mika lamuranta ga Allah domin neman sauki a lokuta irin wannan."

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  16. Barka da warhaka

    Yau fa labaran ba za su wuce na kalatacciyar cutar Covid-19 ba wato Coronavirus, wadda ta kashe mutum sama da 5,000 sannan wasu sama da 132,000 suka kamu.

    Kasashe kusan 120 ne cutar ta addaba a fadin duniya.

    Me zai hana ku biyo mu domin ji da ganin abin da ke faruwa, yayin da cutar ke neman durkusar da duniya?

    Kuna tare da Umar Mikail a wannan hantsi.

  17. Mu kwana lafiya

    Sai da safenku jama'a.

    Umar Mikail ke cewa a sha barci lafiya - da munshari.

  18. Trump ba ya dauke da coronavirus

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba ya nuna wasu alamun kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ganawa da ya yi da wani hadimin shugaban kasar Brazil.

    "Ba mu da alamar (kwayar cutar) ko kadan," ya fada yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a fadar White House.

    Trump ya zauna kusa da shugaban Brazil Jair Bolsonaro a lokacin da suka ci abincin dare. Wasu rahotanni sun ce Bolsonaro ya kamu da cutar amma shugaban ya musanta a yau Juma'a.

  19. Kasashen Turai da suka garkame wa duniya kofa kan coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sa'o'i bayan Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana Nahiyar Turai a matsayin "cibiyar coronavirus", ga kasashen da suka garkame kofofinsu ga duniya:

    • Ukraine: Ta hana 'yan kasar waje shiga na tsawon mako biyu (ban da jami'an difilomasiyya)
    • Denmark: Ta hana dukkanin 'yan kasar waje ba tare da cikakken katin shaida ba - kamar shaidar zama a kasar ko kuma ziyarar iyali ta gaggawa.
    • Poland: Daga ranar Lahadi za a hana duk 'yan kasar waje shiga.
    • Czech Republic:Ta hana 'yan kasar waje shiga, sai wadanda ke da shaidar zama a kasar. Ta hana 'yan kasarta fita.
    • Slovakia: Ta hana 'yan kasar waje shiga ban da 'yan kasar Poland da kuma masu shaidar zama a kasar
    • Austria: Ta rufe iyakoki uku na kasa tsakaninta da Italiya sai dai fa wadanda ke da shaidar asibiti da aka ba shi cikin kwana hudu. 'Yan Austria ma za su iya shiga.
    • Hungary: Ta garkame iyakokinta da kasashen Austria, Slovenia.
    • Slovenia: Ta rufe iyakokinta shida tsakaninta da Italiya. An dakatar da zirga-zirgar motocin bas da jirgin kasa. 'Yan kasar waje za su shiga ne kawai idan suna da shaidar likita da aka bayar cikin kwana uku.
    • Serbia: Ta rufe iyakarta da kasashen Romania, Bulgaria, North Macedonia, Montenegro, Bosnia da Croatia.
    • Romania: Ta rufe iyakarta da kasashen Hungary, Ukraine, Bulgaria da Moldova.
    • Albania: Ta rufe iyakokinta da kasashen Montenegro, Kosovo da North Macedonia
  20. Labarai da dumi-dumi, Donald Trump ya saka dokar-ta-baci kan coronavirus

    Trump

    Asalin hoton, White House

    Shugaba Donald Trump ya saka dokar-ta-baci a Amurka kan annobar coronavirus.

    Ya bayyana haka ne a jawabin da yake yi yanzu haka ga kasa baki daya.

    Hakan zai ba shi damar taba kudin ko-ta-kwana da suka kai dala biliyan 40 da aka ware domin yaki da cutar.

    Trump ya ce Amurka ta yi nasara sosai idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.

    Shugaban ya kuma haramta wa 'yan kasashen waje shiga Amurka wadanda suka je Nahiyar Turai a cikin mako biyu da suka gabata.

    Sannan ya ce su ma Amurkawa da ke dawowa daga tafiye-tafiye za a killace su na tsawon mako biyu.

    Shugaban ya gode wa kamfanin Google bisa shafin da yake yunkurin samarwa da zai taimaka wurin yaki da cutar, inda injiniyoyi 1,700 ke aiki a kansa yanzu haka.

    Shafin Google na coronavirus

    Asalin hoton, White House

    Bayanan hoto, Yadda shafin zai kasance

    Wanda yake jin alamun cutar zai shiga shafin ne ya bayyana abin da yake ji, inda nan take za a fada masa matakin da ya kamata ya dauka, ya kamu da cutar ko kuma a'a.