'Yan Najeriya na tofa albarkacin bakunansu kan yadda dan majalisar wakilan kasar Alhassan Ado ya gabatar da matansa a zaman majalisar na jiya Laraba.
Bidiyon ya nuna Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjayen majalisar yana tinkaho a gaban majalisar cewa shi ''tsayayye ne a majalisar da ma a gidansa.''
Dan majalisar ya
dawo zauren ne bayan samun nasara a zaben ranar Asabar da ta gabata. A baya
kotun sauraren kararrakin zabe ta soke nasararsa a zaben watan Maris na
shekarar 2019.
Da yake jawabi
dan majalisar ya bukaci matan nasa su mike.
''Mai girma shugaban majalisa ina sanar da cewa a yau ina tare da matana guda hudu masu alfarma. Halima na iya mikewa, Umma ma haka,'' inji shi yayin da takwarorinsa ke ta sowa.
Ya kara da cewa ''Mai girma shugaban majalisa matan nan nawa su hudu sun haifa mani 'ya'ya 27, kuma ina fatan samun kari.''
“Wani dalili kuma shi ne domin in sanar da kai cewa kamar yadda 'yan majalisa ke ce mani mai fada a ji, karfin fada a ji ba ba a majalisa ba ne kadai .... har a gida... domin ina kula ne da mace hudu,'' inji Doguwa.
Kalaman nasa sun jawo mahawa a tsakanin masu goyon bayan hakan wasu kuma na kushewa.