Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta yi watsi da karar APC a Sokoto

Muna kawo muku bayanai dangane da zaman kotun musamman mai sauraron korafe-korafen zaben a jihohin Kano da Sokoto wadanda za su yanke hukunci kan wanda ya lashe zaben jihohin.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Rayyan

  1. Karshe!

    Nan muka kawo karshen kawo mako bayanai kai tsaye daga kotuna na musamman da ke zaman sauraron korafe-korafen zabe a jihohin Kano da Sokoto. Mun gode.

  2. An yi watsi da karar Ahmad Aliyu na APC a Sokoto

    Kotun sauraron kararrakin zabe wadda ta yi zama a Abuja ta yi watsi da karar da Ahmad Aliyu na APC ya shigar a gabanta, inda ya kalubalanci nasarar da Gwamna Aminu Tambuwal na PDP ya samu a jihar Sokoto a zaben gwamnan 2019.

    Kotun ta ce jam'iyyar APC da dan takararta sun kasa gabatar da kwararan hujjoji da za su nuna an saba wa ka'idojin zabe da kuma dokar zabe ta 2010.

  3. Buhari ya taya Ganduje murna

    Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Plateau Simon Lalong murnar nasarar da suka samu a kotun sauraron kararrakin zabe.

  4. Buhari ya tafi Afirka ta Kudu da Ganduje da Lalong

    Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya kama hanyar tafiya Afirka ta Kudu tare da wasu Gwamnonin jihohin Kano da Plateau Abdullahi Ganduje da kuma Simon Lalong a ranar Laraba.

  5. Kotu ta tabbatar da Simon Lalong a Plateau

    Kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Plateau ta tabbatar wa Simon Bako Lalong a matsayin zababben gwamnan jihar Plateau.

  6. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    Har yanzu ana dakon hukuncin kotu kan zaben Sokoto

  7. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    Kotu mai sauraron karar gwamnan jihar Sokoto ta koma zama bayan wani hutun dan wani lokaci.

  8. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    Kotu mai sauraron karar gwamnan jihar Sokoto ta tafi hutun dan wani lokaci kafin ta koma zaman nata. Sai ku kasance da mu

  9. Zaben Kano, Ganduje/Abba Kabir

    Mai shari'a Halima Shamaki ta nemi jama'ar Kano da su kwantar da hankalinsu, inda ta bukaci wadanda hukunci bai musu dadi ba da su garzaya zuwa kotun daukaka kara.

  10. Zaben Kano, Ganduje/Abba Kabir

    Mai shari'a Halima Shamaki ta kori karar da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya shigar gabanta yana kalubalantar Gwamna Ganduje.

  11. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    Kotunn sauraron karar gwamnan Sokoto na ci gaba da zama a birnin Abuja, inda dan takarar jam'iyyar APC, Ahmed Aliyu yake kalubalantar gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal.

  12. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Mai shari'a Halima Shamaki na magana kan irin muhummanci da ya kamata masu korafi su bayar ga rubuta shaida daga mutumin da bai iya rubuta da karatu ba. Mai shari'ar ta kuma janyo wasu sharu'u na baya a matsayin dogaronta na yin wurgi da wasu shaidu.

  13. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Mai shari'a Shamaki na bayani kan abubuwan da ya kamata mai korafi ya yi da irin yadda ya kamata ya gabatar da korafe-korafensa. Ta kuma yi bayani kan hanyoyin da hukumar zabe ya kamata ta bi wajen soke zabe.

  14. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Jama'ar da ba su samu damar shiga kotun ba na wajen kotu suna jiran tsammani.

  15. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Mai shari'a Halima Shamaki na karanto abubuwan da shaidun masu kara da wadanda ake kara suka bayar a gaban kotu dangane da yadda aka gudanar da zaben gwamna a karo na biyu a mazabar Gama ward da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar ta Kano.

  16. Zaben Sokoto, Tambuwal/Ahmed Aliyu

    Ana ci gaba da zama, inda ake karanta hukuncin da kotu ta yanke game da karar da dan takaran gwamna na APC a jihar Sokoto ya shigar yana kalubalantar zaben da aka yi wa gwamna Aminu Tambuwal na jam'iyyar PDP. Amma har yanzu ba a karanta hukuncin karshe ba.

  17. Zaben Kano, Ganduje/Tambuwal

    Mai shari'a Halima Shamaki na ci gaba da karanto irin abubuwan da shaidun masu kara da wadanda ake kara suka gabatar.

  18. Zaben Kano, Ganduje/Abba Gida-Gida

    Mai shari'a Halima Shamaki na ci gaba da karanto hukunci a zaman kotun da ke gudana yanzu haka a birnin Kano. Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook wato https://www.facebook.com/BBCnewsHausa/ domin kallon yadda zaman ke gudana.

  19. Zaben Kano, Ganduje/Abba Kabir

    Tuni kotu ta fara zamanta a Kano, inda kuma yanzu haka aka fara karanto hukunci.

  20. Zaben Sokoto, Tambuwal/ Ahmed Aliyu

    Kotun shari'ar zaben jihar Sokoto ta fara zama a unguwar Wuse da ke birnin Abuja. An dai mayar da zaman sauraron karar zuwa Abuja saboda yanayin da jihar take ciki.