Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata muhawarar gwamnan jihar Kano

Yadda ake gudanar da muhawara tsakanin 'yan takara biyar da ke neman kujerar gwamnan jihar Kano.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahya and Mustapha Musa Kaita

  1. A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na musamman da muka gabatar muku a kan muhawarar da 'yan takarar gwamnan Kano. Sai ku kasance da mu a makon gobe domin sauraren muhawarar da za mu kawo muku ta 'yan takarar gwamnan jihar Sokoto. Ni ne Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita ke fatan ku huta lafiya.

  2. Masu bukata ta musamman a wurin muhawara

    Ba a bar masu bukata ta musamman a baya ba wajen wannan muhawara.

  3. Ma'aikatan BBC a wurin muhawara

    Hotunan wasu daga cikin ma'aikatan BBC da suka halarci wurin muhawarar 'yan takarar gwamnan jihar Kano.

  4. Mahalarta muhawara

    Hotunan wasu daga cikin dimbin mahalarta muhawarar da BBC Hausa ta shirya ga 'yan takarar gwamnan Kano.

  5. 'Kwankwaso ba zai sa na yi abin da ba daidai ba'

    Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tabbatar tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso ba zai sa ya yi abin da ba daidai ba.

    Da aka tambaye shi, shin idan Kwankwaso ya bukaci ya yi abin da ya saba da manufofin ci gaban Kano zai bijire masa, sai ya ce ce ba bijirewa zai yi ba, zai yi kokarin ganar da shi gaskiya ne ta hanyar bayani.

    "Na san halin Kwankwaso tamkar yadda na san yunwar cikina; ina da tabbaci ba zai sa na yi abin da ya sha bamban da ci gaban Kano ba."

  6. Zan kawo tsarin iyali - Mustapha Getso

    Mustapha Getso na jam'iyyar NPM ya ce zai kawo tsarin iyali idan ya zama gwamna a yunkurinsa na magance matsalar almajiranci. Ya ce zai wayar da kan iyaye su daina haihuwar 'ya'ya rakwacam suna tura su bara.yana mai shan alwashin bunkasa kananan sana'o'i irinsu kafinta da walda da gini.

  7. Har yanzu Ganduje bai iso wurin muhawara ba

    Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ke kan karagar mulki ya rasa damar kare manufofin gwamnatisa kan matsalolin da sauran 'yan takara suka ce za su magance a Kano domin har yanzu bai karaso wurin muhawar ba ana daf da kammalawa. Ku dubi wannan mumbarin nasa babu kowa a kai.

  8. Masu bukata ta musamman sun halarci muhawara

    Wasu daga cikin masu bukata ta musamman kenan da suka hallarci wannan muhawara ta 'yan takarar gwamnar jihar Kano.

  9. Hotunan wasu mahalarta muhawara

  10. Ma'aikatan BBC da ke kawo muku bayanai kai tsaye

    Ma'aikatan BBC Hausa a bakin aiki inda suke gabatar muku da labarai da rahotanni kai tsaye game da muhawarar da ake tafkawa tsakanin 'yan takarar gwamnan jihar Kano. Ma'aikatan su ne: Nasidi Adamu Yahaya da Mustapha Kaita da Abdulbaki Jari da kuma Umar Mika'ilu.

  11. Ra'ayoyinku daga Facebook

    Abdurahman Bala: "Duk da ban san dalilin rashin zuwan Abdullahi Umar Gaduje ba. Ya cacanci zagaye na biyu ganin yanda duk ayyukan da Kwankwaso da Mallam Ibrahim Shekarau ya yi dukkan ayyukan da suka bari".

    Aminu Dankaduna Amanawa: "Tambaya ta ta ga dan takarar jam'iyyar PDP, ko yaushe ana maganar ayukkan yi, ayukkan yi, ga wadanda sukayi karatu kenan, ga wadan da basuyi karatu ba fa, miye makomar su".

    Suleiman Muhammad Musa: "Ganduje yana tsoran a tambaye shi maganar dollar shi ya sa ya ki zuwa".

  12. Jagorancin muhawara

    Abokin aikinmu, Ibrahim Isa ne yake jagorantar muhawarar da 'yan takarar gwamnan jihar Kano ke tafkawa.

  13. Bidiyon 'yan takara suna hawa mumbari

  14. Har yanzu Ganduje bai zo wurin muhawara ba

    Har yanzu dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje bai zo wurin muhawarar da BBC ke gudanarwa ba. Bai kuma bayar da dalilinsa na rashin isowa ba. Idan kuka duba hoton da ke kasa za ku ga mumbarinsa babu kowa a wurin.

  15. Zan inganta rayuwar mata, Maimuna

    'Yar takarar gwamnan Kano a jam'iyyar UPP, Maimuna Muhammad, ta ce za ta bayar da muhimmanci wurin inganta rayuwar mata da matasa. Za ta sauya rayuwarsu. Ta ce ta fito takara ne saboda su. Za ta takaita yawan dalibai a ajin firamare zuwa dalibi 30 sannan ta yi gine-gine. Ta kara da cewa za ta bude cibiyoyin koyon sana'o'i ba wai ba da jarin N5k ko N10k ba, saboda ya yi kadan.

  16. Zan magance matsalar daba - Takai, Zan magance dabanci

    Salihu Sagir Takai, dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PRP, ya ce zai magance dabanci da inganta ilimi cikin kwana 100 zai gyara makarantun firamare da sakandare. Zai yi amfani da kudin kananan hukumomi wajen inganta ilimi a mataki na farko. Zai bayar da horo ga malamai da samar da kayan karatu.

  17. Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar NPM, Mustapha Getso ya ce ya kamata tsofaffi daga cikin masu yin takara su je su huta su bai wa matasa kamarsa dama, yana mai shan alwashin tabbatar da ganin 'ya'yansa da iyalinsa na zuwa asibiti da makarantun gwamnati. Ya kuma ce ba zai fitar dan kowa karatu waje ba, saboda shi zai yi kokarin inganta makarantun gida.

  18. Kun ji abin da Abba Kabir Yusuf ya ce zai yi wa jama'ar Kano?

    'Yan takara sun fara gabatar da kansu. Abba Kabir Yusuf na PDP ya ce cikin kwana 100 zai habbaka harkar ilimi. Zai ciyar da dalibai da ba su littafai da inganta rayuwar malamai. Cikin kwana 100 zai farfado darajar malamai da inganta harakar noma da kuma ayyuka. Abba Kabir ya ce zai kuma dubi makomar ilmin daliban da suka kammala sakandare ta hanyar daukar nauyinsu zuwa jami'o'i a ciki da wajen Kano.

  19. Kun ga 'yan takarar da suka isa wurin muhawarar?

  20. Gwamna Ganduje na APC da Maimuna ta UPP ba su iso ba

    'Yan takara uku cikin biyar sun isao zauren da za a tafka muhawara, sai dai Gwamna Ganduje na APC da Maimuna ta UPP har yanzu ba su iso ba.