Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ziyarar Buhari a Kano: Ba kuka, ba guda?

Ku bi wannan shafin domin samun labarai da sharhi game da ziyarar aikin da Shugaba Muhammadu Buhari yake a jihar Kano

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan, Yusuf Yakasai and Nasidi Adamu Yahya

  1. A nan muka kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye na ziyarar Shugaba Buhari a Kano.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na bbchausa.com don karanta karin wasu labarai.

  2. Shugaba Buhari ya bar asibitin Giginyu

    Tawagar Shugaba Buhari ta bar asibitin Giginyu bayan kaddajmar da wani asibiti da gwamnatin Kano ta gina.

    Nan gaba kuma zai kaddamar da wani asibitin a titin Gidan Zoo.

    Wakilinmu da ke can, Muhammad Abdu Tudunwada, ya ce tuni titin ya dinke da jama'a masu dakon karasowar shugaban.

  3. Buhari ya nemi gwamnoni su yi koyi da Ganduje

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi sauran gwamnoni su yi koyi da gwamnan jihar Kano wurin gudanar da ayyukan ci gaban jihohinsu.

    A wani takaitaccen jawabi da ya yi a wurin kaddamar da asibiti a ungunwar Giginyu da ke tsakiyar birnin, Shugaba Buhari ya ce irin wadannan ayyuka suna kawo sauyi sosai a rayuwar al'uma.

    A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya yaba wa shugaban kasar bisa ziyarar da yake yi a jihar.

  4. Kalli ficewar ayarin Motocin Buhari..

    Kalli ficewar ayarin motocin Buhari daga gidan gwamnatin Kano.

  5. Buhari zai gana da malaman addini

    Wani na hannun damar Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa shugaban zai gana da malaman addini a Kano domin yi musu godiya kan addu'o'in da suka rinka yi masa a lokacin da ba shi da lafiya.

    Ba ya ga malaman addini, shugaban zai kuma gana da manyan 'yan kasuwa da sauran shugabannin al'umma a ziyarar kwana biyun da zai yi.

    Shugaban dai ya shafe watanni yana jinya a kasar Ingila, abin da ya sa aka dinga shakku kan ko zai iya cigaba da mulkin kasar.

    Jihar Kano na daya daga cikin wuraren da aka rinka shirya addu'o'i na musamman domin nema wa shugaban lafiya.

  6. Buhari: An gafartawa fursunoni 500

  7. 'Ba ma murna da zuwan Buhari'

    Wasu mazauna birnin Kano sun shaida wa BBC cewa ba sa murna ko kadan da ziyarar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke yi a jihar.

    Sun shaida wa wakilinmu Ibrahim Isa cewa ba su ga wani abin arziki da shugaban ya yi wa jihar ba a sama da shekara biyun da ya shafe yana mulki.

    Sai dai magoya bayan shugaban sun ce inganta tsaro da habaka aikin noma na daga cikin ayyukan da ya yi kawo yanzu.

    Jihar Kano ce ta fi kowacce jiha bai wa shugaban kuri'a a zaben da ya gabata.

  8. Buhari 'ya ci taliyar karshe', Wasu daga cikin ra'ayoyinku

    Jama'a na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan ziyarar aiki ta kwana biyu da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi a jihar Kano.

    Ga wasu daga ciki da muka tsakuro daga shafinmu na BBC Hausa Facebook:

    Muhammad Ishaq: Wallahi shi kansa Buhari ya san cewa jama'a sun chanja masa, ka ga wai shi ne ya zo Kano ba kowa sai wadanda aka ba kudi.

    Muazzam Bello Malamee: Lallai Buhari ya ci taliyar karshe, sai karya a radio wai an yi cikar kwari... Yunwa duk ta cika wa mutane ciki. Wa zai fita tararsa?

    Sadeeq Nabageh: Kanawa kar ku ba mu kunya, ku fito don Allah, gobe a ba da mamaki, a cika a batse, a nuna tumbin giwar.

    Abdulrasheed Gabas Cin Adarawa: Muna yi wa Shugaba Buhari barka da zuwa Birnin Kano. Shugaba Buhari muna maka fatan alheri Allah ya sa a yi taro lafiya a kare lafiya.

  9. An tsaurara matakan tsaro

    Bayanai daga birnin Kano da kewaye sun ce an tsaurara matakan tsaro domin ziyarar da Shugaba Buhari ke yi a jihar.

    Dubban jama'a ne dai suka fito domin yi wa shugaban marhabin zuwa jihar, wacce ita ce ta fi kowacce bashi kuri'u a zaben shekara ta 2015.

    Sai dai jama'a da dama sun dawo daga rakiyar gwamnatinsa suna masu cewa ya kasa aiwatar da alkawuran da ya dauka.

    Wasu Kanawa a shafukan sada zumunta sun yi zargin cewa an tsaurara matakan tsaron ne domin ana hasashen cewa wasu masu adawa za su nuna rashin jin dadinsu kan ziyarar tasa.

  10. Shugaba Buhari ya isa gidan yarin Kurmawa

    Shugaba Buhari ya ziyarci gidan yarin Kurmawa domin gane wa idonsa yadda ake zama a gidajen yarin Najeriya, in ji mai taimaka masa kan kafofin sa da zumunta, Bashir Ahmad.

  11. Ra'ayi:

    Aliyu Dahiru Aliyu ya ce "gaskiya dai ya cika abin kunya a ce wai mai gaskiya zai zo Kano amma duk an bi an tsorata don ka da a yi masa ihu! Yanzu a ce yadda ake son Mai gaskiya a Kano amma duk ya tsorata saboda shi ya san bai yi abin kirki a garin ba. Sarkin Kano da gwamnatin Kano da hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro duk sun hadu suna fadakarwa a kan zuwan mai gaskiya don ka da a yi masa bore! To idan mai gaskiya na tsoron shigowa Kano to ina ga sauran jihohi?!

    Shi ma Sheriff Almuhajir mai yawan bayyana ra'ayinsa a shafin Facebook ya rubuta cewa: Da Buhari wani garin zai je ba Kano ba, da yanzu sun ishi mutane da korafin an yi mutuwa a Numan bai je ba. An yi walkiya.

  12. 'Na gamsu da tarbar da Kanawa suka yi min'

    Shugaba Muhamamdu Buhari ya ce ya gamsu da tarbar da al'ummar Kano suka yi masa a lokacin da ya isa birnin domin fara ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar.

    "Duk da cewa ban yi tsammanin wani abu kasa da haka ba, amma na yi matukar mamakin yadda Kanawa suka tarbe ni a safiyar nan," kamar yadda wani jami'insa ya rawaito shi yana cewa a lokacin da ya ziyarci fadar sarkin Kanon.

  13. Magoya bayan Buhari sun yi fitowar dango

  14. Mutane na dakon Shugaba Buhari..

    Mutane na dakon Shugaba Buhari a titin gidan zoo inda zai bude asibitin yara.

  15. Kalli yadda Buhari ya sauka

    Kalli yadda Buhari ya sauka

  16. Kalli jerin gwanon motocin Buhari

    Wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa yadda mutane suka tarbi jerin gwanon motocin Buhari.

  17. Daga wajen fadar sarkin Kano

    Magoya bayan Shuga Muhammadu Buhari daga wajen fadar sarkin Kano suna jira yayin da jami'an tsaro ke aikinsu.

  18. Ya isa fadar Sarkin Kano

    Shugaba Muhammadu Buhari ya isa fadar sarkin kano domin kai ziyarar ban girma.

  19. Magoya bayan APC

  20. Magoya bayan jam'iyyar shugaban

    Magoya bayan jam'iyyar sun yi anko.