Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.

    Sai kuma gobe, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya, idan mai duka ya amince.

    Mu kwana lafiya.

  2. Dole ne Isra'ial da dakatar da barazanar mamaya - MDD

    Baban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres babu dalilin da zai sa Isra'ila ta ci gaba da ''faɗaɗa matsugunan Yahudawa'' a Gaɓar Yama da Kogin Jordan.

    Yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Amurka, Mista Guteres ya ce dole ne a dakatar da abin da ya kira ''barazanar mamaya da ke ''ƙara rura rikicin ƴan kama wuri zauna''.

    Babban jami'in na Majalisar Dinkin duniya ya ce hanya guda da za a samu masalahar rikicin ita ce amincewa da kafa ƙasashe biyu masu cin gashin kai da za su yi hulɗa da ƙasashen duniya

    Amincewa da ƙasar Falasdinu ''abu ne da ya kamata, ba wai goya baya ba ne'', yana mai ce ƙin amincewa da ƙasar Falasdinu zai riƙa bunƙasa ayyukan masu tsattsauran ra'ayi.

  3. Labarai da dumi-dumi, Faransa ta amince ta kafa ƙasar Falasɗinu a hukumance

    Shugaban Faransa na jawabi a taron MDD

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasdinu a hukumance.

    Yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Mista Macron ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da sakin sauran Isra'ilawa 48 da Hamas ke garkuwa da su.

    Ya ce lokaci kaɗan ne ya rage wa duniya ta iya wanzar da zaman lafiya, don haka ya ce vai kamata a jira ba.

    Mista Macron ya yi Allah-wadai da harin na ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai wa Isra'ila.

    Shugaban na Faransa ya ce yana son ganin an samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kai da ke zama makwabtan juna.

    ''Babu wata hujja na ci gaba da yaƙin da yi", in ji Macron, yana mai ƙarawa da cewa "ya kamata a kawo ƙarshen komai''.

  4. Waɗanne ƙasashe ne suka amince da ƙasar Falasɗinu?

    Ƙasashen Birtaniya da Australia da Kanada da kuma Portugal sun amince da kafa ƙasar Falasdinu a hukumance a ranar Lahadi.

    Ana sa ran wasu da dama za su amince a taron ƙolin Majalisar dinkin Duniya da ake yi a a birnin New York na Amurka.

    A ranar Juma'a, mai bai wa shugaban Faransa shawara ya lissafo sabbin ƙasashen da suka amince da matakin da suka haɗa da:

    • France
    • Belgium
    • Luxembourg
    • Andorra
    • San Marino
    • Malta

    Foye da kashi uku cikin hudu na ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 suka amince da kafa ƙasar Falasɗinu.

    Ƙasashen da ba su amince da matakin ba sun haɗa da Amurka da isra'ila da Italiya da Jamus

  5. Amurka ta yi barazanar hana ƴan Najeriya masu laifin cin hanci biza

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta yi gargaɗiin daina bayar da biza ga manyan mutane a Najeriya da aka samu da laifukan cin hanci da rashawa a ƙasar.

    Cikin wani saƙo da ofishin jakadancin ƙasar ya wallafa a shafinsa na X, ya ce idan ana batun yaƙi da cin hanci da rashawa ba a taƙaita shi an wasu mutane daban.

    ''Abu ne na ba sani, ba sabo. Ko manyan mutane aka samu da laifin cin hanci da rashawa, za mu iya hana su bizar Amurka''.

    A baya dai gwamnatin Amurka ta haramta wa wasu yansiyasar Najeriya biza da ta zarga da yin karen-tsaye ga zae da kuma zagon-ƙasa ga dimokuradiyya.

    Amurka na ganin hana wa jami'an gwamnati izinin shiga Amurka wata babbar hanya ce ta tabbatar da gaskiya da adalci da rikon amanar al'umma tare da mutunta dokokin kasashen da Amurka ke amintaka da su.

    Matakin Amurkan na hana biza ga jami'an Najeriya da aka samu da rashawa ya ja hankalin yan Najeriya, inda wasu da dama ke cewa mataki ne mai kyau ga ƙoƙarin duniya na yaƙi da rashawa.

    Wasu na ganin sako ne mai ƙarfi ga yan Najeriya musamman masu hulda da amurka, wajen ganin sun tabbatar da kaucewa aikata rashawa, inda suke ganin cin hanci da rashawa na ɗaya daga cikin matsalolin da suka hana Najeriya samun ci gaban da za ta iya gogayya da wasu takwarorinta na ƙasashen waje.

    Sai dai ofishin jakadancin na Amurka bai bayyana lokacin da zai fara ɗaukar matakin ba.

    A Najeriya an jima ana zargin wasu ƴansiyasar ƙasar da wawuse dukiyar kasa lokacin da suke riƙe da manyan muƙamai, su kuma gudu zuwa manyan ƙasashen Turai da Amurka, domin sayen manyan kadarori.

  6. Tattalin arzikin Najeriya ya haɓaka a rubu'i na biyu na 2025 - NBS

    hannu na ƙirga kudi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙara da kashi 4.23 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.

    Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48 idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantuwar tattalin arzikin ƙasar.

    Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wana ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024.

    Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana'antu da, da fan fetur da kuma fannin ma'adinai.

    NBS ta ce a rubu'i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna ƙarin kashi 19.23 cikin 100.

  7. An ɗage shari'ar tsohon Mataimakin Shugaban Sudan ta Kudu Mashar

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    An ɗage shari’ar tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu Riek Mashar, bayan da aka samu rikici akan hurumin kotun da ke sauraron karar.

    Lauyoyinsa sun ce shari’ar ta saba wa kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018, inda suka ce ba zai iya fuskantar shari’a ba a yayin da yake kan mukami sai da amincewar majalisar dokokin ƙasar.

    Sai dai masu gabatar da ƙara sun yi watsi da ikirarin, suna mai cewa kotun na da hurumin sauraron karar.

    Magoya bayan Riek Mashar, sun zargi shugaba Salva Kiir, da yunkurin shafe tarihinsa a siyasa ta ko wanne hali.

    Mr Mashar na fuskantar tuhumar aikata kisa da cin amanar kasa da kuma laifukan yaƙi.

  8. Masar ta yi afuwa ga ɗan gwagwarmayar ƙasar Abdel-Fattah

    Masar

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi afuwa ga fitaccen ɗan rajin siyasar nan Alaa Abdel-Fattah, wanda ya kasance ɗan ƙasar Masar da kuma Birtaniya.

    Mr El-Fattah ya dade yana tsare tun daga shekarar 2019 bisa tuhume-tuhumar yada labarai na ƙarya.

    Tun kafin kifar da gwamnatin tsohon shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011, wanda ya taka muhimmiyar rawa a ciki, an sha kulle shi a gidan yari sau da dama, da kuma bayan kifar da gwamnatin.

    A lokacin da ake tsare da shi ya sha yin yajin cin abinci. Mahaifiyarsa, Laila So'if wadda ita ma ƴan Birtaniya ce, ta yi dogon yajin cin abinci a Birtaniya domin neman a saki ɗanta.

  9. Mata sun buƙaci a ware musu kujeru a majalisun Najeriya

    Mata

    Kungiyoyin mata daga jihohi 36 da ke Najeriya sun taru a babban birnin kasar Abuja domin gudanar da taron jin ra’ayoyin al'umma da kuma mika kudurin dokar neman a kebe wa mata kujeru a majalisun kasar.

    Kungiyoyin na bukatar a ware wa mata kujera 37 a majalisar wakilai, da kujera 37 a majalisar dattawa, a matakin jihohi suna su a ware kujera 108, wato kujeru uku daga kowacce jiha.

    Kakakin majalisar wakilan Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya halarci taron, ya jinjina wa kungiyoyin mata da matasa da masu bukata ta musamman, inda ya ce yin hakan zai kara karfafa samar da daidaito a kasar, da tabbara da ana tafiya da kowa.

    Hajiya Fatima Zakari Ita ce mataimakiyar kungiyar league of women voters, ga kuma karin bayanin da ta ce suna fafatukar ce domin ganin ana damawa da mata a siyasa da mulki, sannan ta yi fata za su samu nasara.

    Kudirin dokar dai na bukatar amincewar kashi biyu cikin uku na yan majalisun kasar, hakazalika qnq bukatar amincewa da dokar a kashi biyu cikin uku na majalisun jihohi wato jihohi akalla 24 cikin 36.

    Majlisar wakilai ta sha alwashi cewa za ta kammala duba kammala kudurin cikin lokaci.

    Bayan majalisun sun amince, wajibi ne majalisun dokoki suma su amince karkashin sashi na 9 na kudin tsarin mulki.

  10. Tarayyar Turai ta tsawaita wa'adin takunkumi kan masu rura wutar yaƙin Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Avaaz via Getty Images

    Ƙungiyar tarayyar turai ta tsawaita wa’adin takunkumin da ta kakaba wa manyan masu ruwa da tsaki a yakin basasar Sudan da shekara guda.

    Takunkumin wanda yanzu zai ƙare a watan Oktobar shekarar 2026, ya shafi mutum 10 da kuma kamfanoni 8 da ke da nasaba da sojojin Sudan da dakarun RSF.

    Ya kuma shafi kamfanonin da ake zargin suna ba da makamai da motocci da kuma ƙarin wasu kayan yaƙi ga bangarorin 2, wadanda ake tuhuma da kawo cikas ga zaman lafiya da kuma sauyin siyasa.

    Takunkumin ya haɗa da haramta wa mutanen shiga dukkanin ƙasashen Tarayyar Turai da kuma kulle dukkannin asusu da kadarorinsu.

    Sai dai gwamnatin sojin ta Sudan da ke Khartoum ta yi watsi da matakin, tana mai cewa ya sabawa ƙa'ida, kuma babu adalci acikin sa.

  11. Fursunoni 68 sun ci jarabawar NECO a Kano

    ...

    Asalin hoton, CSC Musbahu Lawan K Nassarawa

    Fursunoni 68 a Jihar Kano ne suka ci jarabawar kammala sakandaire ta NECO ta shekarar 2025, a cewar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen jihar.

    A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, fursunonin sun ce wannan nasarar ta kasance abin farin ciki gare su inda suka bayyana cewa hakan zai zama wata babbar dama wajen sauya rayuwarsu gaba ɗaya.

    Hukumar ta bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon tallafin gwamnatin Kano, wadda ta ɗauki nauyin ci gaban ilimin fursunonin.

    "Wannan shiri ya yi daidai da dokar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya ta 2019, wadda ke mai da hankali kan gyara da sake tarbiyyar fursunoni ta hanyar ilimi da horo na sana’o’i." in ji sanarwar.

    Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara jaddada aniyyarta ta samar da damammakin ilimi ga fursunoni domin ƙarfafa su su zama abin koyi nagari a cikin al’umma.

    Wannan mataki na cikin shirin muradun shugaba Tinubu na 'Renewed Hope', wanda hukumomin ƙasar suka ce yana ƙunshe da inganta rayuwar duk ‘yan Najeriya cikin har da fursunoni.

    ...

    Asalin hoton, CSC Musbahu Lawan K Nassarawa

  12. Tinubu bai da shirin tsawaita mulki bayan 2031 – Fadar shugaban ƙasa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ba shi da wani shiri na ci gaba da riƙe muƙamin shugaban ƙasar bayan Mayun 28, 2031, idan har aka sake zaɓensa a shekarar 2027.

    Mai bai wa shugaba Tinubu shawara, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a matsayin martani ga kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

    A yayin wata ziyarar jaje daga tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a ƙarshen mako, El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da karkata zuwa mulkin kama karya, inda ya kwatanta Shugaban da Paul Biya na Kamaru, wanda ya shafe yana mulki tun daga 1982 har yanzu.

    Sai dai Onanuga a mayar da martani ya bayyana cewa wannan magana ta El-Rufai ba ta da wani tushe bare makama.

    Onanuga ya ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu ɗan dimokuraɗiyya ne, kuma ba shi da wani shirin zama shugaban ƙasa har abada. Zai sauka daga mulki ne a ranar 28 ga watan Mayu, 2031 idan ya ci zaɓen 2027."

  13. Rikicin zaɓe ya ɓarke yayin jiran sakamakon zaɓe a Malawi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ƴan Malawi ke jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudunar, rikicin siyasa ya ɓarka kan zargin tafka maguɗi.

    Jam’iyyar adawa ta United Democratic Front, ta bi sahun jam’iyyar gwamnati wajen shigar da ƙorafe-ƙorafe ga hukumar zabe, tana neman a bayyana dukkan takardun ƙididdiga da aka sa hannu a kansu.

    An kama ma’aikatan zaɓe takwas a ƙarshen mako, bisa zargin yin maguɗi.

    Kididdigar hukuma ta nuna jihohi tara cikin 36 da aka sanar a daren Asabar cewa tsohon shugaban ƙasa Peter Mutharika ne ke jagorantar, yayin da mai ci Lazarus Chakwera ke a matsayi na biyu.

    A shekarar 2019, kotun koli ta ƙasar ta soke nasarar tsohon shugaban ƙasar Mutharika, inda ta bayyana cewa an samu maguɗi sosa.

  14. Hisbah ta daƙile yunƙurin safarar wasu mata daga Kano zuwa ƙasashen waje

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce jami'anta sun yi nasarar daƙile wani shirin safarar mata huɗu daga Kano zuwa wasu kasashe domin neman kuɗi inda ta ce ta dauki matakin gaggawa domin hana aukuwar lamarin.

    Hukumar ta bayyana cewa an yaudari matan ne da cewa za su samu takardun izinin tafiya da biza a Ghana, sannan daga nan za su tafi Saudiyya domin samun ayyukan yi.

    Hukumar ta kuma ce ta tabbatar da cewa, an tsare lafiyarsu, domin karesu daga faɗawa cikin haɗarin cin zarafi ko bautar da su.

  15. Gwamnatin Kano ta yi gargaɗi kan zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da cututtuka ta jihar Kano KNCDC ta fitar da sanarwar gargadi ga ƴan jihar dangane da rahoton da hukumar kula da cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta bayar kan wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar zazzaɓi mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini a Abuja.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukan sada zumuntarta.

    KNCDC ta ce wannan gargaɗi na daga cikin shirin kare lafiyar al’umma, duba da yadda Kano ke da yawan jama’a da kuma hulɗar kasuwanci da tafiye-tafiye zuwa sauran sassan ƙasar.

    Sanarwar ta tabbatar da cewa binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar ba su da cutar Ebola.

    Duk da haka, ana ci gaba da gwaje-gwaje domin gano ko cututtuka irin su zazzaɓin Lassa ko zazzaɓin Dengue ne suka haddasa alamomin da aka gani.

    "Cutar zazzaɓin mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini wato 'Viral Hemorrhagic Fevers' na daga cikin manyan cututtuka masu haɗari, kuma suna iya bayyana da alamun zazzabi ko amai ko gudawa da kuma zubar jini daga jiki." in ji KNCDC.

    "Waɗannan cututtuka na iya yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane ko kuma daga mutum zuwa mutum ta hanyar jini ko zufa." hukumar ta ƙra da cewa.

    KNCDC ta kuma shawarci jama'ar Kano da "Su kiyaye tsafta ta hanyar wanke hannu akai-akai da sabulu ko abubuwan tsaftace hannu da kauce wa hulɗa da mutanen da ke da zazzabi ko zubar jini ba tare da sanin ko mene ne ba, da kuma gujewa hulɗa da namun daji saboda gujewa kamuwa da cutar.

    Haka kuma, ta yi kira da a tabbatar an dafa nama da kyau kafin a ci, sannan a garzaya asibiti idan aka fuskanci alamomin cutar.

  16. Shettima ya sauka birnin New York domin taron MDD

    ...

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

    Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya sauka a birnin New York ta Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga Satumba zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.

    Shettima, wanda ke wakiltar Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabin Najeriya tare da shiga tattaunawar manyan jami’an MDD da kuma halartar wasu muhimman taruka a gefe.

    A cewar ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, Najeriya na jagorantar ƙoƙarin samar da yarjejeniyar haraji ta duniya.

    Wannan ne karo na biyu a jere da Shettima ke jagorantar tawagar Najeriya zuwa taron - bayan ya yi hakan a watan Satumban 2024.

  17. Shugaban Afirka ta Kudu zai halarci taron MDD kan rikicin Isra’ila da Falasɗinawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, zai shiga taron manyan jami’ai da za a gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya a New York yau, domin tattaunawa kan tsarin samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar, SABC ya ruwaito.

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da Yariman Saudiyya, Mohammed Bin Salman ne za su jagoranci taron domin “haddasa goyon bayan ƙasashen duniya mafi yawa da faɗi ga tsarin samar da ƙasa biyu.

    Ƙasashe da dama na Yammacin Turai, ciki har da Birtaniya dai sun amince da kafa ƙasar Falasɗinu a hukumance jiya, kafin sanarwar da za a fitar a zaman taron MDD a New York yau.

    Afirka ta Kudu ta daɗe tana mara baya ga kafa ƙasar Falasɗinu, inda ta kai Isra’ila gaban Kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa (ICJ) bara, bisa zargin aikata kisan ƙare dangi a Gaza.

    Ofishin shugaban ƙasar ya bayyana cewa Ramaphosa zai yi jawabi a MDD gobe, inda zai jaddada buƙatar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa domin samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, da kuma ƙarfafa kare haƙƙin ɗan adam ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.

  18. An fara ƙirga ƙuri’u bayan zaɓen raba gardama a Guinea

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da ƙirga ƙuri’u a Guinea bayan zaɓen raba gardama kan sauya ƙundin tsarin mulkin ƙasar wanda ka iya bai wa shugaban sojoji janar Mamady Doumboya damar tsawaita zamansa a mulki ta hanyar tsayawa takarar shugabancin ƙasar.

    Doumboya ya yi alƙawarin cewa ba zai tsaya takara ba lokacin da ƙasar ta koma hannun farar hula bayan juyin mulkin da ya kawo shi kan ƙaragar mulki a shekarar 2021.

    Sai dai masu suka na ganin wannan mataki sabon yunƙuri ne na tabbatar da karfinsa da kuma halasta mulkinsa.

    Har yanzu Doumboya bai tabbatar da ko zai tsaya takara ba a zaben da ake sa ran gudanarwa daga baya a bana.

  19. Rikici ya ƙara ƙamari a El-Fasher ta Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Faɗa ya ci gaba a garin El-Fasher da ke Darfur ta Sudan, inda Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi a karshen mako kan taɓarɓarewar yanayi a yankin.

    Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 7,500 da aka riga aka tsugunar a sansani sun tsere makon da ya gabata bayan da dakarun RSF suka mamaye wurin.

    Firaministan Sudan da sojoji suka naɗa, Kamil Idris, ya ce zai ɗaga batun halin da ake ciki a El Fasher a wannan mako a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

  20. Obasanjo ya musanta neman wa’adi na uku lokacin mulkinsa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya karyata zargin cewa ya taɓa neman wa’adi na uku a lokacin mulkinsa.

    Ya bayyana hakan ne a taron tattaunawar dimokraɗiyya da aka shirya a Accra, Ghana ta gidauniyar Goodluck Jonathan.

    Obasanjo ya ce babu wani ɗan Najeriya, raye ko mamaci, da zai iya gaskata cewa ya taɓa roƙon goyon bayansa don samun wa’adi na uku.

    Ya ce: “Ni ba wawa ba ne, idan na son wa’adi na uku, zan san yadda zan yi. Kuma babu wanda zai ce na taɓa kiran sa na ce ina son nayi wa’adi na uku.”

    Ya kuma ƙara da cewa samun yafiya ga bashin da Najeriya ta ciyo a lokacin nasa mulki ya fi wahala fiye da neman wa’adi na uku, amma ya cimma hakan.

    Ya gargadi shugabanni da ke yin dogon zama kan mulki, yana mai cewa tunanin cewa babu wani da zai iya maye gurbinsu babban zunubi ne ga Allah.

    Obasanjo ya jaddada cewa shugabanci ya kamata ya kasance hidima ce, ba matsayin da za a riƙe da dole ba.

    A nasa jawabin, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce shugaban da ya gaza ya kamata a cire shi ta hanyar ingantaccen zaɓe.

    Ya yi gargadin cewa maguɗin zaɓe na daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a nahiyar Afrika, yana mai cewa idan ba a sake tunani da gyara tsarin ba, dimokuraɗiyyar na iya durƙushewa.

    Jonathan ya ce ’yan Afrika na buƙatar dimokuraɗiyya da ke tabbatar da ’yancinsu da sahihin zaɓe da tsaro da ilimi da aiki da lafiya da mutunci.