Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 03/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 03/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan muke rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye daga sashen Hausa na BBC.

    Da fata kun ji daɗin kasance tare a mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Trump ya janye yunƙurin dakatar da ciyar da miliyoyin Amurkawa abinci kyauta

    Gwamnatin Trump ta shaida wa manyan kotuna biyu a kasar cewa za ta ware wasu kudade daga wani asusun ajiya na ko-ta-kwana, domin samar da wani bangare na kudin da ake bukata domin samar da tallafin abinci ga miliyoyin Amurkawa.

    Tun a baya ta yi shirin daina biyan kudaden, a cewarta saboda karancin kudi sakamakon dakatar da ayyukan gwamnati.

    Amma a yanzu ta ce za ta yi amfani da wasu kudaden da aka ajiye domin biyan fiye da rabin dala biliyan takwas din da ake bukata duk wata.

    Matakin na nufin a wannan watan, iyalai masu karamin karfi za su sami wani kaso ne kawai na tallafin da ake ba su.

  3. Yunwa na ƙaruwa a Sudan saboda yaƙin sojojin ƙasar da dakarun RSF

    Yunwa ta bazu a karin wasu yankuna biyu na Sudan, ciki har da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur wanda mayakan RSF su ka kwace ikon sa a makon da ya gabata.

    Daya yankin da kungiyar da ke bibiyar lamurran da suka shafi yunwa a duniya wadda ke da goyon bayan Majalisar Dinkin duniya ta ambata shi ne Kadugli da ke Kudancin Kordofan.

    Kungiyar Integrated Food Security Phase Classification ta ce biranen biyu na fama da koma baya a tsarin tafiyar da rayuwa, da yunwa, da matsanancin rashin abinci mai gina jiki da mace mace.

    Wakilin BBC ya ce kungiyar ta kuma yi gargadin cewa akwai wasu yankuna ashirin a Sudan de ke gab da fadawa yunwa.

  4. Ribadu da manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun gana kan barazanar Trump

    Bayanai suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump.

    Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaƙi maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu iƙirarin jihadi.

    A sanarwar, ya ce, "na ba sashen yaƙinmu umarni su fara shirin ɗaukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda ƴanta'addan nan suke kai hari kan kiristoci," in ji shi, sannan ya ƙara da kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi gaggawar ɗaukar matakin magance matsalar.

    Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, inda shugaban ƙasar Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa cewa babu wata barazana da kiristocin ƙasar suke fuskanta.

  5. Rundunar ƴansandan Legas na neman Sowore ruwa a jallo

    Rundunar ƴansandan jihar Legas ta ayyana neman tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ruwa a jallo bisa zarginsa ta tayar da zaune tsaye a jihar.

    Tun da farko, Kwamishinan ƴansandan jihar Olorundare Jimoh, ya gargaɗi Sowore kan yunƙurin shirya zanga-zanga saboda rushe-rushen da aka yi a yankin Oworonshoki a Legas.

    Sai dai duk da gargaɗin, Sowore ya umarci jama'arsa da su gudanar da zanga-zangar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Sai dai ƴansanda sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar, wadda ba a ga shi Sowore ɗin ba.

    Da yake jawabi bayan tarwatsa masu zanga-zangar ne kwamishinan ƴansandan ya ce, "Sowore ya karya doka, ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala, musamman baƙi. Ba za mu bari ana abin da aka gadama ba, kuma duk inda yake (Sowore) sai mun kama shi. Ya ƙi zuwa zanga-zangar ne saboda yana jin tsoro"

  6. A riƙa hukunta masu damfarar mutane ta intanet - Kotun Indiya

    Kotun kolin India ta ce wajibi ne a dauki matakai masu tsauri domin dakile karuwar ayyukan masu karyar cewa su jami'an tsaro ne domin damfarar mutane ta intanet.

    Wani alkali ya ce wajibi ne a kawo karshen damfarar, wadda ake kira kame ta intanet. Masu damfarar na shiga irin ta ƴansanda ko masu karbar haraji, su kira mutane ta bidiyo, musamman ƴan fansho da mata, sai su ce sun aikata wani laifi.

    Daga nan sai su bukace su su biya kudade ko su yi barazanar kama su. Alkaluma sun nuna cewa masu damfarar sun damfari mutane har na kusan dala miliyan dari uku cikin shekarun baya-bayan nan.

  7. Barazanar Trump kan Najeriya abin damuwa ne ga dukkan ƴanƙasa - Obi

    Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour Peter ya ce barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan tura sojojin ƙasarsa su yaƙi ta'addanci, da ma sanya ƙasar a cikin waɗanda yake sa ido a kansu abin damuwa ne da ɗaga hankali ga dukkan ƴanƙasar.

    Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar dole abin da faruwa ya ja masa hankali.

    "Babu shakka Najeriya na fama da matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma asarar dukiya. Ƙungiyar Amnesty ta ruwaito cewa aƙalla mutum 10,000 aka kashe a Najeriya daga watan Mayun 2023, kuma kamar yadda na sha nanatawa, kashe-kashe a Najeriya abin takaici ne, kuma abin Allah-wadai da ya zama dole a tashi haiƙan wajen magancewa."

    Obi ya ce za a iya magance matsalar ta hanyar samun shugabanci na nagari, "duk da cewa ba a wannan gwamnatin matsalar ta fara ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin takaɓus daga ɓangaren wannan mulkin na gwamnatin APC wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta."

    Ya ce Najeriya da Amurka suna da tarihin alaƙa da juna mai kyau, "kuma bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu. Wannan sabuwar dambarwar na buƙatar haɗakar diflomasiyya da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar."

  8. Sojoji sun kashe ƴanbindiga 19 a Kano

    Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar daƙile ƴanbindiga daga yunƙurin da suka yi na kai hari a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano.

    Sojojin na aikin soji na musamman na MESA da ke ƙarƙashin birged na uku da ke Kano ne suka yi jagoranci aikin bayan bayanan sirri da suka ce sun samu kan yunƙurin ƴanbindigar na kai harin.

    A wata sanarwa da kakakin sashen, Babatunde Zubairu ya fitar, ya ce, "mun samu bayanan sirri ne cewa an ga ƴanbindiga a ƙauyen Unguwan Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse a ƙaramar hukumar Shanono da misalin ƙarfe biyar na yamma a ranar 1 ga watan Nuwamba."

    Ya ce wannan ne ya sa aka tura sojoji yankin domin fuskantar maharan, "inda suka samu nasarar tarwatsa su bayan musayar wuta da aka yi na tsawon lokaci."

    "Haka kuma sojojin da aka tura ƙauyen Tsaure sun gamu da ƴanbindiga, inda nan suka yi musayar wuta, har suka kora su, sannan suka ƙwato babura da makamai."

    Sanarwar ta ce sojoji sun kashe ƴanbindiga 19 a gumurzun, "amma an kashe mana sojoji guda biyu," in ji shi.

    Kwamandan sashen Birgediya Janar Ahmed Tukur ya buƙaci mutanen yankin su ci gaba da gudanar da harkokinsu, sannan ya yi kira gare su da su riƙa sa ido kan abubuwan da ke wakana tare da kai musu bayani da gaggawa.

    Ya kuma yi alƙawarin haɗa hannu da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar Kano baki ɗaya.

  9. Daga ƙasashen waje aka kitsa rikicin bayan zaɓe a Tanzania - Samia

    Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta daura alhakin rikicin zaben da aka samu a kasar kan wasu da ba ƴan kasar ba.

    A jawabinta na farko bayan kama aiki a karo na biyu, ta sha alwashin cewa gwamnati za ta kare kasar ta dukkanin hanyoyin da su ka dace.

    Majalisar dinkin duniya ta ce jami'an tsaro sun hallaka akalla mutum 10, sai dai ƴan adawa sun ce adadin ya zarce hakan.

    Shugaba Samia, wadda ta lashe zaben da kusan kashi 98 na kuri'un da aka kada, ta dage cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, duk da sukar da masu sanya ido da ƴan adawa ke yi.

    Wakilin BBC ya ce jam'iyyar adawa ta Chadema wadda aka haramta wa jagoranta tsayawa takara ta yi watsi da sakamakon zaben.

  10. Mutanen da suka rasu a zaftarewar ƙasar Kenya sun haura 40

    Zaftarewar kasa sakamakon kwanakin da aka shafe ana mamakon ruwa a Kenya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da arba'in.

    Wakiliyar BBC ta ce a cewar ma'aikatar Ilimi, mutum 11 daga cikin wadanda suka mutu yara ne ƴan makaranta a yankunan da ke cike da tsaunuka da ke kan iyakar kasar da Uganda.

    Masu aikin ceto daga kasashen biyu na ci gaba da neman gwamman mutanen da su ka bace.

    Hukumomi na gargadin za a ci gaba da samun zaftarewar kasar, kuma an nemi wandanda ke yankunan su fice zuwa wuraren da ke kan tudu.

  11. Gwamnan Osun ya buƙaci tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka

    Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya yi kiran sabunta tattaunawar diplomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka, yayin da ake samun ƙaruwar nuna yatsa tsakanin ƙasashen biyu.

    Cikin wata sanarwa da kakain gwamnan, Olawale Rasheed ya fita,, Gwamnan Adeleke ya buƙaci a tattauna kan barazanar da Shugaban Amurka ya yi a baya-bayan nan kan kai wa Najeriya hari.

    Trump ya yi barazanar kai wa Najeriya hare-hare sakamakon abin da ya kira yawan kisan kiristoci a ƙasar.

    Gwamnan ya yi kira a samar da wata hanyar lalama domin samo bakin zaren tsakanin ƙasashen biyu.

    “Ina kira ga fadar shugaban Amurka ta tallafa wa Najeriya wajen aiwatar da sabbin dabarun tsaro na zamani'', in ji shi.

  12. Gwamnan Kano ya umarci ƙananan hukumomi su riƙa shirya tarukan tsaro

    ‎Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su riƙa shirya tarukan tsaro domin ƙarfafa tsaro tsakanin garuruwan jihar.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwmanan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamnan Abba Kabir ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayarsu a tsakanin al'umman garuruwa da jami'an tsaro.

    Matakin na zuwa ne yayin da ake sa ƙara samun rahotonnin hare-haren ƴanbindiga a ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da jihar Katsina, mai fama da matsalar tsaro.

    Gwamnan ya ayyana ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa da Tudun Wada da Doguwa da kuma Gwarzo a matsayin ƙananan hukumomin da ke buƙatar kulawar tsaro ta musamman, saboda barazanar tsaro da ake sa mu a yankunan.

  13. Kotun Isra'ila ta bayar da umarnin tsare wata babbar lauyar sojin ƙasar

    Wata kotu a Isra'ila ta bayar da umarnuin tsare wata babbar lauyar sojojin ƙasar - da ta ,dauki alhakin fitar da wani bidiyo da aka yi zargin ya nuna yadda sojojin Isra'ila suka yi ta cin wani Bafalasdine ta hanyar lalata.

    A makon da ya gabata ne Manjo Janar Yoifat Tomer-Yerushalmi ta yi murabus a matsayin babbar lauyan sojojin Isra'ila.

    Ta ce ita da abokan aikinta sun riƙa fuskantar barazana saboda sun tsaya a kan tsarin doka.

    An shiga damuwa a kan walwalarta bayan da aka bayar da rahotonnin ɓacewarta a ranar Lahadi, kafin a gano a kuma kamata.

  14. Kotun Ƙolin Indiya ta ɗauki matakan daƙile ƙaruwar ayyukan masu damfarar intanet

    Kotun ƙolin India ta ce wajibi ne a ɗauki matakai masu tsauri domin daƙile ƙaruwar ayyukan masu ƙaryar cewa su jami'an tsaro ne domin damfarar mutane ta intanet.

    Wani alƙali ya ce wajibi ne a kawo ƙarshen damfarar, wadda ake kira kame ta intanet.

    Masu damfarar na shiga irin ta ƴansanda ko masu karɓar haraji, su kira mutane ta bidiyo, musamman yan fansho da mata, sai su ce sun aikata wani laifi.

    Daga nan sai su buƙaci su biya kuɗaɗe ko su yi barazanar kama su.

    Alƙaluma sun nuna cewa masu damfarar sun damfari mutane kusan dala miliyan 300 cikin shekarun baya-bayan nan.

  15. Sakataren tsaron Amurka ya ziyarci iyakar Koriya

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya isa kan iyakar Koriya ta Arewa da ta Kudu, a wani ɓangare na ziyarar da yake yi a Seoul.

    Wannan ne ziyara ta farko da jagoran ma'aikatar tsaro ta Pentagon ke yi a Amurka cikin shekara takwas.

    Mista Hegseth ya je wurin ne tare da takwaransa na Koriya ta Kudu, wanda ya ce za su tattauna shirin tsaron da suka yi wa Koriya ta Arewa.

    Gwamnatin Amurka na duba yiwuwar ƙarfafa tsaro a yankin, bayan da Donald Trump ya ziyarci ƙasar a makon da ya gabata.

  16. Likitoci masu neman ƙwarewa na yajin aiki a Najeriya

    Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa Najeriya (NARD) sun fara yajin aiki na dindindin daga ranar Asabar, lamarin da ya tsayar da ayyuka da dama a cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

    Shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman, ya tabbatar da fara yajin aikin a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar.

    Wannan yajin aiki na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 30 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka yi a baya.

    Dakta Suleiman ya ce yajin aikin ya zama dole ne bayan gwamantin ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da ake da ita duk da tarurruka da roƙe-roƙe da gargaɗi da ƙungiyar ta yi.

    "Buƙatunmu ba wai na son kai ne ko siyasa ba, muna neman yanayi mai kyau da zai bai wa likitoci damar yin aiki cikin aminci da kulawa da inganci ga marasa lafiya ba tare da hatsarin lafiyar su ba," in ji shi.

    Daga cikin manyan ƙorafe-ƙorafen NARD sun haɗa da albashin da ba a biyasu ba da rashin kyawawan yanayin aiki da ƙarancin ma’aikata, nauyin aiki mai yawa, da kuma rashin kayan aiki na asibiti, waɗanda ya ce sun lalata tsarin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.

  17. An girke tarin jami'an tsaro a sakatariyar jam'iyyar PDP

    An girke jami'an tsaro a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja, yayin da mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    Kwamitin gudanarwar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu, ne ya sanar da naɗin Mohammed bayan dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagun.

    Rikicin babban jam'iyyar hamayyar Najeriyar ya ta'azzara bayan da a ƙarshen mako, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Iliya Damagum da wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar suka sanar da dakatar da babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu da wasu ƴan kwamitin

    Lamarin da ya sa ɓangaren Anyanwu ya mayar da martani ta hanyar dakatar da Damagum da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar da wasu mutum huɗu.

  18. Ba lallai mu kai wa Venezuela hari ba - Trump

    Shugaba Trump na Amurka ya ce ba lallai ƙasarsa ta aiwatar da aniyarta na yin yaƙi da ƙasar Venezuela ba, amma ya ce kwanakin da suka rage wa Shugaba Nicolar Maduro ƙayyadaddu ne.

    Da aka tambaye shi ko Amurka za ta yaki Venezueal, sai Shugaba Trump ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS cewa ''ina tababa game da haka, Bana tunani za mu yaƙe su, amma suna yi mana abubuwan da ba su kamata ba.''

    Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da Amurka ke ci gaba da kai hare-hare ta sama kan waɗanda ake zargi da safarar ƙwayoyi a jiragen ruwa a yankin Karibiyan.

    Gwamnatin Trump ta ce tana kai hare-haren ne domin daƙile kwararar ƙwayoyi zuwa cikin Amurka.

    Kafar yaɗa labarai ta CBS , abokiyar BBC ta bayar da rahoton cewa aƙalla mutum 64 ne aka kashe sakamakon hare-haren Amurka a yankin gabashin Pacific.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta yi barazanar kai hari Najeriya, saboda zargin yi wa ''kiristoci kisan kiyashi'' a ƙasar.

  19. Za mu iya kai wa Najeriya hari ta sama ko ta ƙasa - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren da kasarsa za ta iya kai wa Najeriya za su haɗa da ta ƙasa da ta sama.

    Yayin da manema labarai ke yi masa tambayoyi kan yadda hare-haren za su iya kasancewa ta sama ko ta ƙasa?, sai ya ce ''komai zai iya faruwa, abuibuwa da dama za su faru - ina nufin abubuwa masu yawa,'' kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    “Suna kashe kiristoci, kuma suna kashe su da yawa, ba za mu bari hakan ya ci gaba da faruwa ba,'' in ji shi.

    A ranar Asabar ne Mista Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, cewa ya buƙaci ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta duba yiwuwar shirya kai hari Najeriya, kwana guda bayan ya yi gargaɗin cewa kiristoci na fuskantar kisan kiyashi a Najeriya.

    Sai dai a martanin da ya mayar gwamnatin Najeriya ta ce Amurka da Najeriya na cikin ƙawancen duniya mai yaƙi da ta'addanci, kuma idan shugabbnin ƙasashen biyu suka gana za a samu masalaha mai kyau.

  20. An rantsar da Samia Saluhu Hassan a wa'adin mulkin Tanzaniya na biyu

    An rantsar da Shugaba Samia Suluhu Hassan a wa'adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya.

    Cikin wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin tsaurara matakan tsario a Dodoma, babban birnin ƙasar an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bar mutane da dama sun halarta ba.

    Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar zuwa wurin, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar, sakamakon rikicn zaɓe da aka samu a ƴankwanakin nan.

    Shugaba Samia ta lashe zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi 98 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Sai dai ƴan hamayya sun yi watsi da sakamakon a matsayin magudi.