Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 08/06/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu a nan za mu y sallama da ku a daidai wannan lokaci.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Sojojin Somaliya da mayaƙan al-Shabab sun gwabza a arewacin Mogadishu

    Gwamnatin Somaliya da 'yan tawayen Al-Shaban na iƙirarin samun narasa a fafatawar da ɓangarorin biyu suka yi a El-Dheer.

    A wani hari da suka ƙaddamar kan sansanonin juna a garin El-Dheer da ke arewa maso gabashin birnin Mogadishu.

    Gwamnatin Somaliya ta ce kafin mayaƙan al-Shabab ɗin su ƙaddamar da harin, sojojinta su samu bayanan sirri, lamarin da ya sa suka janye dakarunsu daga sansaninsu da ke garin, tare da shirya musu kwanton ɓauna.

    Rundunar sojin ƙasar ta ce kwanton ɓaunar da dakarunta suka yi wa mayaƙan al-Shabab ɗin ya yi sanadin kashe mayaƙan fiye da 40, inda ta ce dakarunta biyar ne suka mutu.

    A nata ɓangare ƙungiyar Al-Shabab ta ce ta kashe gomman sojoji a wani samame da ta kai sansanin sojin ƙasar, inda ta wallafa hotunan mayaƙanta a cikin sansanin.

    Shekara biyu da suka gabata ne gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da hare-hare domin sake ƙwace iko da yankunan dake tsakiya da kudancin Somaliya da ke hannun mayaƙan.

    Bayan samun nasara a karon farko, mayaƙan Al-Shabab sun sake haɗa ƙarfi tare da ƙwace wasu yankunan.

    Rikicin na baya-bayan nan alama ce da ke nuna taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, a daidai lokacin da dubban masu aikin wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar Haɗin kan Afirka ke shirin fita daga ƙasar a ƙarshen shekarar da muke ciki.

  3. Southgate ya ce Ingila tana da sauran aiki a Euro 2024

    Kociyan tawagar Ingila, Gareth Southagate ya ce tawagarsa tana jan aiki a gabanta, bayan da ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Iceland a Wembley ranar Juma'a.

    Shi ne wasa na karshe da ta buga daga nan za ta je Jamus, domin buga wasannin cin kofin nahiyar Turai Euro 2024 da za a fara ranar 14 ga watan Yuni.

    Ingila, wadda take ta ukun rukuni za ta fara wasan farko da Serbia.

  4. Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi

    Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi a faɗin jihar a wani mataki na farfaɗo da ɓangaren ilimin jihar.

    Yayin da yake jawabi a wani taro da gwamnatin jihar ta shiyya, gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya ce matakin ya zama wajibi domin magance matsalolin da ɓangaren ilimin jihar ke fuskanta.

    Gwamnan ya kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimin jihar su fito su haɗa ƙarfi domin magance matsalolin da suka yi wa ɓangaren ilimin jihar katutu.

    ''Ina Kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma, su haɗa kai, wajen farfaɗo da fannin ilimi, domin ci gaban al’ummarmu'''.

    ''Samun ilimi mai inganci shi ne babban makami mafi inganci na yaƙi da talauci da miyagun laifuka cikin al'ummarmu''.

    Gwamna ya ce manufar ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi shi ne samar da gagarumin sauyi kan yadda fannin ilimin jihar ya taɓarɓare.

    Abba Kabir ya ce matakin zai bai wa gwamnati damar yin shiri domin aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa da mai da hankali wajen lalubo dabarun da za su sake gina ɓangaren ilimin jihar.

    ''Matakin zai taimaka wajen ceto makarantunmu da suka durƙushe, mataki ne mai tsauri na tabbatar da cewa kowane yaro a jihar Kano ya samu ilimi mai inganci, wanda shi ne babban hakkinsu'', in ji gwamnan.

    Gwamnan ya kuma ce wannan mataki zai taimaka wajen kawar da duk yaran da ba su zuwa makaranta daga titunan jihar domin mayar da shu makarantu.

    ''Domin cimma wannan, da farko, dole mu samar da azuzuwa domin yara kimanin 989,234, da ba sa zuwa makaranta a cikin Jiharmu, Za mu gina azuzuwa 28,264 nan da shekaru 3 masu zuwa a fadin jihar''.

    ''Ma’aikatar ilimi da SUBEB za su sa ido kan yadda za a gudanar da ayyukan''.

    ''Domin daƙile matsalar rashin malamai, musamman a makarantu 400 da ke shiyyar Kano ta Kudu, inda ake samun malamai ɗaya a kowace makaranta, mun bayar da umarnin bai wa malaman BESDA 5632 takardun ɗaukar aiki na dindindin da za su fara daga yau'', in Abba Kabir.

    ''Haka kuma, mu bayar da dama wajen ɗaukar ƙarin malaman makaranta 10,000'',

    Gwamnan ya ce ya bai wa SUBEB damar tsara yadda za ta gudanar aikin horas da malaman makarantar a faɗin jihar.

    Abba Kabir Yusuf ya ce malaman makaranta za su ci gaba da samun horo lokaci zuwa lokaci don cimma burin da gwamnatin ta sanya a gaba.

  5. Bayanai kan cutar Kyandar Biri

  6. Idan gwamnoni suka rage cin hanci za su iya biyan fiye da N60,000 - NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta ce gwamnonin jihohin ƙasar za su iya biyan foye da naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, idan suka rage cin hanci da rashawa da kuɗin da suka kashewa wajen gudanar da mulki a jihohinsu.

    Aranar Juma'a ne dai ƙungiyar gwmanonin ta fitar da wata sanarwar da a ciki take cewa gwamnonin jihohin ƙasar 36 ba za su iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata ba.

    To sai dai a cikin martanin da ta mayar ƙungiyar ta NLC, ta yi Allah wadai da sanarwar gwamnonin.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NLC, Benson Upah,ya fitar ya ce idan gwamnaonin suka mayar da hankali babu abin da zai hana su biyan mafi ƙarancin albashin.

    ''Koda nawa ne mafi ƙarancin albashi ba ma naira 60,000 ba, in suka rage kuɗin da suke kashewa wajen gudanar da gwamnati, sannan suka rage cin hanci da rashawa to za su iya biya domin tabbatar da walwalar ma'aikata'', in ji sanarwar.

    A ranar Juma'a ne bayan wata ganawa da wakilan gwamnati ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya ta biya naira 250,000 a matsayin maf ƙarancin albashi.

  7. Goron Sallah: Gwamnan Katsina ya amince da bai wa ma'aikatan jihar N15,000

    Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya amince da bai wa ma'aikatar jihar goron sallah a naira 15,000.

    Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X, ya ce sakamakon yanayin matsin rayuwa da ake ciki, ya amince da bayar da naira 45,000 ga ma'aikatan jihar da na ƙananan hukumomi.

    ''Sai dai naira 30,000 daga cikin kuɗin zai kasance bashi ne gwamnati ta ba su, wanda kuma za su biya cikin wata uku masu zuwa, inda za a riƙa cire naira 10,000 a cikin albashinsu a kowane wata daga Yuli zuwa Satumba'', in ji sanarwar.

    Gwamna Dikko Radda ya ce ya yi hakan ne domin bai wa ma'aikatan jihar da ya kira ''haziƙan ma'aikata'' su samu damar gudanar da shagulgulan bukukuwan babbar sallah cikin walwala, duba da halin matsin rayuwa da ake ciki.

  8. Mai kyautar littattafai da jana'izar tsohon shugaban Ivory Coast

  9. Muna ƙoƙarin saisaita raɗaɗin matsin rayuwa da ake ciki - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sake jaddada cewa yana sane da halin matsin rayuwa da 'yan ƙasar ke fama da shi.

    Yayin da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da aikin titin Guzape Lot II, a Abuja babban birnin ƙasar ranar Asabar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin sauƙaƙa wa 'yan ƙasar halin matsin rayuwar da suke fuskanta.

    “Wannan lokaci ne mawuyaci a ƙasarmu,Har yanzu muna ƙoƙarin saisaita tsarin tattalin arzikin ƙasar, domin kawo sauƙi da ingantuwar tattalin arzikin ƙasarmu,'' in ji Shugaba Tinubu.

    Shugaban ƙasar ya ce kammala aikin titin alama ce ta abin da za a iya yi, ta hanyar abin da ya kira ''kyakkyawan tsari da haɗin kai da kuma aiki tare''.

    Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ministan Abuja, Nyesom Wike, kan ƙoƙari da jajircewar da ya nuna wajen ayyukan waɗanda ke cikin alƙawuran da gwamnatin tarayya ta yi wa mazauna birnin Abuja.

    ''Haƙiƙa na yaba maka kan wannan jajircewa da ƙoƙarin da kake yi wajen kammala ayyuka'', in Shugaban

  10. An kashe gomman mutane a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

    An kashe fararen hula 35 a wasu hare-haren da aka kai yankin arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, mai fama da rikici.

    Shekarun da aka shafe ana gwabza faɗa tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai saboda albarkatun ƙasa da ke yankin, lamarin da ya tilastawa mutane da dama yin ƙaura.

    Gwamnatin Konga bata bayyana ko su waye ke da alhakin kisar ta wannan makon ba, amma majiyoyi sun alaƙanta lamarin da ƙungiyar ADF mai tsattsauran ra'ayin addini.

    Maharan sun afkawa ƙauyukan da ke gefen birnin Beni, inda kuma mafi yawan jama'a suka yi ƙaura.

    Rahotanni sun ce ɓarnar ta fi yawa a ƙauyen Mamove, inda aka ƙona gidaje da ababen hawa, da kuma sace wasu da dama.

    Tun a 1990 aka ƙaddamar da ƙungiyar ADF, kuma ta ɗauki makamai domin yaƙi da shugaban ƙasar da ya daɗe kan karagar mulki, Yoweri Museveni, saboda zargin yana nuna wariya ga musulmai.

  11. Firaiministar Denmark ta tsallake rijiya da baya

    Firaiministar Denmark, Mette Frederiksen ta ji ciwo a wuya bayan wani mutum ya kai mata hari tana cikin tafiya a ƙasa, a tsakiyar birnin Copenhagen.

    Wani mutum ne ya nushi ƴar siyasar a daidai lokacin da take tattaki a birnin.

    Tuni aka kama mutumin da ya kai mata harin kuma zai bayyana a gaban kotun Frederiksberg domin amsa tuhumar da ake masa.

    Wannan hari na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan an harbi Firaiministan Slovakia Robert Fico, yayin da yake gaishe da magoya bayan sa.

    Shugabar tarayyar Turay, Ursula von der Leyen ta bayyana harin a matsayin mummunan aiki da ya saɓa duk wata hanyar kirki da nahiyar Turai ta amince da ita.

  12. Al Shabab ta yi garkuwa da malaman Sufaye 20 a Somalia

    Rahotonni da ke fitowa daga Somaliya na cewa mayaƙan ƙungiyar Al-Shabab sun yi garkuwa da malaman ɗariƙar sufaye kusan 20.

    Mayaƙan masu alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda sun jima suna hamayya da ɗariƙar sufaye a ƙasar.

    Malaman sun fito ne daga sassa daban-daban na ƙasar domin halartar taron addini na shekara-shekara da suke shirin gudanarwa a garin Lanta-Buto da ke yammacin Mogadishu, babban birnin ƙasar.

    Shafin intanet mai kusanci da ƙungiyar ya ce wasu malaman sun tsere a lokacin da ƙungiyar ta kai wa malaman hari.

    Kafin ɓarkewar yaƙin basasar Somaliya a shekarar 1991, ɗariƙar sufanci ce ke da manyan malamai a ƙasar.

    To amma tun bayan yaƙin suke zargin jagorin yaƙin da muzguna musu, sai a yanzu kuma ƙungiyar Al-Shabab.

    Ƙungiyar mai alaƙa da al Qaeda na da saɓanin ra'ayin fatawa tsakaninta da ɗariƙar sufaye, inda ake zargin ta ruguza wuraren ibadar sufayen masu yawa.

    A nasu ɓangaren su ma sufayen sun kama tasu ƙungiyar masu ɗauke da makaman, domin kare wuraren ibadarsu, sannan kuma suke taimaka wa sojojin gwamnati wajen yaƙar al-Shabab.

  13. Sojin Isra'ila sun ce sun ceto mutum 4 cikin waɗanda da Hamas ta yi garkuwa da su

    Dakarun Isra'ila sun ce sun ceto ceto mutum huɗu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin wani samame da suka kai Nuseirat a tsakiyar Gaza.

    Mutanen sun hada da Noa Argamani da Almog Meir Jan da Andrey Kozlov da kuma Shlomi Ziv.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce mutanen suna cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoban bara, kuma ta tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

    Rahotanni sun ce Firaiminista Benjamin Netanyahu ya zanta ta waya da ɗaya daga cikin mutanen da aka ceto mai suna Noa Argamani.

    Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kashe mutane aƙalla 50, ciki harda da ƙananan yara a lokacin samamen.

  14. Dole a samar da inshora ga masu haƙar ma'adanai - Gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta tilastawa kamfanonin haƙar ma'adanai yin inshora ga ma'aikatan su, domin bayar kariya gare su idan wani haɗari ya faru.

    Ministan ma'adanan ƙasar, Dele Alake, ya daga yanzu gwamnati ba za ta sake amincewa da lasisin duk wani kamfanin haƙar ma’adanai da bai nuna ƙwaƙwarar shaidar cika ƙa'idojin gudanar da aiki ba.

    Ministan ya na magana ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje a jihar Neja, inda ƙasa ta rufta da masu haƙar ma'adanai a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro.

    Ya ce gwamnati za ta tabbatar da bin duk hanyar da ta dace domin kare afkuwar irin wannan matsala a nan gaba, dmin haka ta faraɓullo da irin wannan mataki.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon zaftarewar kasar da ta auku a wani wurin hakar ma’adinai, a ranar Litinin.

    Hukumomin jihar sun ce ana ci gaba da aikin ceton mutanen da ƙasar ta rufta da su, duk da cewa ana samun koma baya a aikin saboda ruwan sama da kuma ƙalubalen tsaro a yankin.

  15. MDD ta sha alwashin ceto jami'anta 11 daga mayaƙan Houthi

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gaggauta sakin ma'aikatanta 11 da mayaƙan Houthi ke tsare da su a Yemen.

    Ma'aikatan sun ɓace ne a bakin aikin su a sassan ƙasar, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai alamar an tsara ɗauke su ne a lokuta daban-daban.

    Kakain Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric za su yi duk abin da ya dace domin ceto ma;aikatan cikin gaggawa.

    Mayaƙan Houthi sun daɗe suna kai hare-hare a kan kamfanoni da cibiyoyin soji, lamarin da ya janyo mayar da martani daga Amurka da ƙawayen ta.

    Majiya daga gwamnatin Yemen ta ce akwai ma'aikatan ƙungiyoyin ƙasar waje da dama a hannun mayaƙan na Houthi.

    Mayaƙan ne ke da ƙarfin iko da babban birnin ƙasar, Sana'a, da kuma mafi yawan Arewa maso yammaci, inda suke gudanar da gwamnati ta daban.

    Ita kuma gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita tana gudanar da mulki ne a Kudanci.

  16. Mun cimma matsaya a kan sabon albashin ma'aikata – Gwamna Uzodimma

    Gwamnan jihar Imo State, Hope Uzodimma, ya ce kwamitin tsara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kusa cimma matsaya a kan sabon albashin.

    A ƙarshen taron kwamitin, gwamna Uzodimma, ya ce bayan shafe sa'oi 12 ana tattaunawa tsakanin mabobin kwamitin, an cimma matsaya kan shawarar da ta dace su bai wa gwamnati.

    Gidan talabijin ɗin Channels ya ruwaito gwamna Uzodimma, ya na cewa: “Mun yi tattauwa mai daɗin gaske kuma ana iya cewa mun cimma matsaya a matakinmu na ƙaramin kwamitim, don haka idan muka je ga babban kwamiti komai zai tafi lafiya.”

    Ya yi bayanin cewa kwamitin ya tuntuɓi duk waɗanda ya kamata, kuma sakamakon rahoton sa zai zamo abin da ake sa ran yin amfani da shi wajen cimma matsaya a babban kwamitin da zai yi aiki na gaba a kan sabon albashin.

    Gamayyar kungiyoyin ƙwadago a Najeriya dai ta ƙi amincewa da tayin naira 60,000 da gwamnati ta yi mata a matsayin mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya sa ta fara yajin aikin gama gari daga ranar Litinin.

    Sai dai gamayayar ta dakatar da yajin aikin a ranar Talata bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ƙara wa a kan tayin ta na farko, kuma hakan ya buɗe sabuwar hanyar tattaunawa a kan batun.

  17. Brazil za ta amso ƴan ƙasarta da suka gudu Aregentina

    Ƴan sandan Brazil sun ce a mako mai zuwa za su aike da buƙatar Argentina ta taso ƙeyar wadanda ake zargi da hannu a far wa gine-ginen gwamnati a birnin Brazilia

    An yi ƙiyasin akwai aƙalla mutum 65 cikin wadanda suka kai harin, kuma magoya bayan tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro ne.

    Sun kuma tsere Argentina bayan hukumomi sun ƙaddamar da bincike.

    Lamarin ya tayar da tarzomar a ranar 8 ga watan Junairun bara, kusan mako guda da shugaba Luice Inacio Lula de Silva ya yi nasara a zaben shugaban kasar.

    Sai dai babu tabbacin ko gwamnatin Argentina za ta miƙa mutanen, saboda shugaba Javier Milei, aminin Mr Bolsonaro ne, kuma ya na sukar shugaba de Silver.

  18. MDD ta sanya Isra'ila cikin masu keta haƙƙin yara

    Saɓani ya ƙaru tsakanin Isra'ila da Majalisar Dinkin Duniya, bayan sanya sojin ƙasar da na Hamas cikin waɗanda suka tafka laifi da ƙetare iya a kan yara ƙanana.

    Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya ne ya tsegunta rahoton gabannin a gabatar da shi a gaban kwamitin tsaro na Majalisar a mako mai zuwa.

    Mai magana da yawun babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarrik ya ce sun kaɗu da abin da jami'in Isra'ilar ya aikata ba kuma za a lamunci hakan ba.

    Ya ce wajibi ne a fitar bidiyon duk abin da ke faruwa a Gaza tsakanin Isra'ila da Falasdinawa domin ɗaukar matakan da suka dace.

  19. Amurka ta zargi Rasha da China da kawar da hankali kan makamin Nukiliya

    Wani babban jami'in Amurka ya ce ƙasasshen Rasha da China da Koriya ta Arewa na kara kawar da hankali kan ƙera makaman nukiliya da suke yi cikin sauri.

    Pranay Vaddi ya ce sam ba su damu da takaita ƙera makamai ba, domin haka ya ce kamata Amurka ta ƙara adadin makaman da ta ke fitarwa nan da shekaru masu zuwa.

    Mr Vaddi ya ƙara da cewa kasashen uku na da kyakkyawar alaƙa tsakaninsu kan hakan.

    A halin da ake ciki Amurka na bin tsarin takaita samar da makamin nukiliya 1500, kamar yadda Rasha ta rattaɓa hannu kan hakan a shekarar 2020.

    Sai dai daga bisani Moscow ta fice daga wannan yarjejeniya.

  20. Barka da zuwa shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa