Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Tsohon ministan Isra'ila ya zargi Netanyahu da kisan gilla a Gaza

    Tsohon ministan tsaron Isra'ila, Moshe Ya’alon, ya ce gwamnatin Benjamin Netanyahu ta kama hanyar aiwatar da kisan gilla a arewacin Gaza.

    Ya ce hakan zai iya kawo rugujewar ƙasar.

    Kalaman nasa da suka zo da ba zata sun janyo suka daga ministocin gwamnatin Mr Netanyahu, waɗanda suka nemi ya janye kalaman nasa.

    Mr Ya’alon dai ya yi fice wajen sukar firaiministan Isra'ila.

    Isra'ila wadda ta umarci dubban Falasɗinawa su koma arewacin Gaza, ta kuma riƙa yin luguden wuta ta sama a yankin, ta musanta zargin da ake mata na kisan gilla.

    Rahotannin da ke fitowa daga yankin sun ce wani sabon harin Isra'ila ya kashe mutane da dama tare kuma da jikkata wasu.

    Isra'ila dai ta ce za ta yi bincike a kan lamarin.

  2. Ƴan adawar Namibia sun sha alwashin ƙin amincewa da sakamakon zaɓe

    Panduleni Itula

    Asalin hoton, AFP

    Ɗan takarar shugaban Ƙasa na jam'iyyar adawa a Namibiya ya ce ba zai amince da sakamakon zaɓe be, saboda tsawaita lokacin gudanar da zaɓen da aka yi.

    Panduleni Itula ya ce an saɓa tanadin doka a matakin da aka ɗauka.

    Yana magana ne a ranar ƙarshe ta kaɗa ƙuri'a a zaɓen da ya kamata a kammala shi a cikin kwana ɗaya.

    An riƙa samun tangarɗar na'ura a wajen kaɗa ƙuri'a, lamarin da ya janyo dogayen layin zasu zaɓe.

    Ƴan adawa dai sun yi ƙorafin cewa ana muzgunawa masu zaɓe.

    Mr Itula ya na ƙoƙarin ƙwace mulki ne a hannun gwamnati mai ci, wadda ke kan mulkin ƙasar tun daga 1990.

  3. Hotunan yadda ƴan tawayen Syria suka kutsa cikin Aleppo

    Yanzu haka birnin Aleppo yana cikin dokar hana zirga-zirga da ƴan tawaye suka ƙaƙaba.

    Ga wasu daga cikin hotunan yadda birnin ke ciki a safiyar yau Asabar.

    SYRIA

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ƴan tawaye a Arewa maso yammacin Idlib da sanyin safiyar Asabar.
    SYRIA

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ƴan tawaye na murna a Idlib
    SYRIA

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutane na taruwa a wajen tarihi na Aleppo
    SYRIA

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ana ƙona tutar Syria yayin da ƴan tawaye ke ci gaba da mamaya a Aleppo
  4. Ministocin harkokin wajen Iran da Rasha sun tattauna kan Syria

    IRAN/RASHA

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministocin harkokin wajen Iran da Rasha sun tattauna ta waya a yau Asabar, inda suka bayyana goyon bayan su ga Syria a yaƙin da take yi da ƴan tawayen da suka ƙwace birnin Aleppo.

    A wani saƙo da ya wallafa a Telegram, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce sun tattauna a kan buƙatar haɗa kai tsakanin Iran da Rasha da kuma Turkiyya wajen fuskantar lamarin.

    Ya ce hakan zai taimaka wajen aiwatar da abin da ya kira "kawar da hatsarin da ke tafe"

    Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ƙasashen sun tattauna yadda za su tsara hanyar kai ɗauki Syria.

  5. Rasha ta gayyaci Koriya ta Arewa zuwa faretin ranar nasara a watan Mayu

    Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta gayyaci dakarun Koriya ta Arewa domin shiga faretin ranar nasara da za ta yi cikin watan Mayun baɗi, a dandalin Red Square da ke birnin Moscow

    Bikin wanda ake yi kowacce shekara, a baɗi zai yi daidai da cika shekara 80 da samun nasara a kan dakaru Nazi na Jamus.

    Kawo yanzu babu tabbacin ko Koriya ta Arewan za ta amsa wannan gayyata.

    Ministan tsaron Rasha, Andrei Belousov, ya gana da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a Pyongyang, a wani mataki na ƙara ƙulla alaƙa da juna.

    Koriya ta Arewa tana taimakawa Rasha da dakaru da kuma makamai a yaƙin da take da Ukraine.

  6. Fararen hula na tururuwar ficewa daga Aleppo bayan 'yan tawaye sun kwace ikon birnin

    Yadda fararen hula ke ficewa daga birnin Aleppo

    Asalin hoton, Getty Images

    Dogayen layukan motoci sun cika manyan titunan birnin Aleppo, a ƙoƙarin fararen hula na ficewa daga birnin - wanda 'yan tawaye da masu iƙirarin jihadi suka ƙwace iko da birnin na biyu mafi girma a Syria.

    Waɗanda ke mara wa gwamnatin ƙasar baya sun fusata da shugaba Bashar al-Assad, suna ganin tserewar dakarun gwamnati daga yankin a matsayin cin amanarsu.

    'Yan tawayen ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar HTS ta masu iƙirarin jihadi, na sake tattara mayaƙanta a yankin.

    Jiragen yaƙin Rasha na ta kai hare-haren boma-bomai a yankunan.

    Masu lura da jiragen yaƙin sun ce mutum 16 ne suka mutu yayin da dama suka jikkata yayin da suka kai hari kan ababen hawan fararen hula.

    Wasu masu lura da al'amura na ganin cewa Turkiyya ce ke da hannu wajen kai hare-haren na kwanaki huɗu da aka yi a yankin, a wani yunƙuri na matsa wa Mista Assad lamba.

    Mahimman masu taimaka masa Iran da Hizbullah, sun raunana sakamakon hare-haren Isra'ila

  7. Dikko Radda ya amince da naira 70,000 mafi ƙanƙantar albashi a Katsina

    Dr. Dikko Umaru Radda

    Asalin hoton, Dr. Dikko Umaru Radda/Facebook

    Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma'aikata jihar.

    Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce amincewar ta ƙunshi sake fasalin albashin ma'aikatan jihar ciki har da na ƙananan hukumomi da malaman makaranta.

    Dikko Radda ya ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Disamba mai kamawa.

    ''Ina miƙa godiya da jinjina ga ma'aikatan jihar Katsina bisa haƙuri da jajircewa da suka nuna, kuma ina kira a gare da ku ƙara jajircewa wajen aiki bisa gaskiya da riƙon amana...'', in ji gwamnan na Katsina.

    A ranar Juma'a ne ƙungiyar NLC ta yi barazanar fara yajin aiki a wasu jihohin ƙasar ranar Litinin, ciki har da Katsina, saboda rashin amincewa da sabon tsarin albashin a jihohin.

  8. Saudiyya na dab da samun damar karɓar baƙuncin gasar cin Kofin Duniya na 2034

    Kofin Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Da alama za a tabbatar wa ƙasar Saudiyya damar karɓar baƙuncin gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta 2034, bayan FIFA ta amince da ƙoƙarinta wajen kare hakkin ɗan'adam a wani sabon rahoton tantance matsayinta kan kare haƙƙin bil-adama.

    Hukumar ƙwallon ƙafa da Duniya FIFA ta bai wa ƙasar maki 4.198 cikin maki biyar - maki mafi yawa da aka bai wa ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya a baya.

    Duk da fargabar da ake da ita kan tarihin taƙe haƙƙin ɗan'adam a ƙasar, rahoton ya ce babu wata fargaba game da 'yancin ɗan'adam a ƙasar.

    Rahoton ya kuma ce gasar ka iya zama wani mataki na kawo sauye-sauye a fannin taƙe haƙƙin binl-adama a ƙasar.

    Saudiyya ta kasance ƙasa ɗaya tilo da ke neman damar karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta 2034 bayan janyewar Australia a shekarar da ta gabata.

    A wata mai zuwa ne ake sa ran FIFA za ta amince wa ƙasar karɓar baƙuncin gasar.

  9. Isra'ila ta ce jiragenta sun kai hari kan wani sansanin sojin a kusa da Syria

    Sojojin Isra'ila sun ce jiragenta sun kai hari kan abin da suka kira wani sansanin soji a kusa da kan iyakar Syria, wanda ta ce ƙungiyar Hezbollah na amfani da shi wajen safarar makamai zuwa Lebanon.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ayyukan sananin sun saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a makon nan.

    Masu lura da al'amura na ganin yadda Isra'ila ke ci gaba da ruguza ƙungiyar Hezbullah - wata katanga da ke kare gwamnatin Assad a Siriya - a matsayin wani abu da ya janyo nasarar 'yan tawaye a arewacin Siriya.

  10. An gano gawa 27 yayin da ake neman fiye da mutum 100 bayan kifewar kwale-kwale a jihar Kogi

    kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Najeriya sun ce har yanzu ba a ga fiye da mutum 100 ba, bayan kifewar wani kwale-kwale ɗauke da sama da mutum 200 a jihar Kogi.

    Har yanzu masu ninƙaya da ƙwararrun shiga ruwa na ci gaba da aikin ceto domin lalubo mutane da gawarwakin waɗanda suka mutu.

    Cikin wata sanarwa da ofishin gwamnan jihar Kogi ya fitar, ya tabbatar da ceto aƙalla mutum 24, waɗanda yanzu haka ke karɓar magani a asibitoci.

    Jami'an bayar da agajin gaggawa sun ce kawo yazu an lalubo gawarwaki 27 a daidai inda lamarin ya faru.

    Kwale-kwalen - wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Katcha da ke ci mako-mako a jihar Neja - ɗauke da fasinjoji waɗanda galibi 'yan kasuwa ne da manoma ya nutse a yankin Dambo-Ebuchi na Kogin Neja

    Kawo yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba. Akwai alamun da ke nuna cewa da dama daga cikin fasinjojin ba sa sanye da rigunan kariya lokacin faruwar hatsarin.

    Hatsarin shi ne irinsa na uku da aka samu a Najeriya cikin wata biyu. A watan da ya gabata wani ƙaton kwale-kwale ɗauke da fasinjoji kusa 300 ya kife a tsakiyar Kogin Neja inda kusan mutum 200 suka rasa rayukansu.

    Ko a makon da ya gabata wasu mutum biyar sun mutu bayan da wasu jiragen ruwa biyu suka yi hatsari a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

  11. Ƙasar Guinea na shirin yin dokokin taƙaita wa yara shiga shafukan sada zumunta

    yaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a ƙasar Guinea na neman yin wata doka da za ta bai wa hukumomi damar kula da shafukan sada zumunta domin kare ƙananan yara daga ganin abubuwa masu cutarwa a shafukan.

    Firaministan ƙasar, Amadou Oury-Bah ya bai wa ma'aikatar kula da kamfanonin sadarwa da ma'aikatar sadarwar ƙasar umarnin lalubo ƙudirin dokokin domin taƙaita wa yara abubuwan da za su riƙa gani a shafukan.

    Ya ce matakin zai taimaka wa iyayen yara wajen kula da abubuwan da yaran nasu za su riƙa gani a shafukan na sada zumunta.

    Mista Oury-Bah ya ce sabuwar dokar za ta taƙaita wa yaran ganin abubuwan da ya kira 'marasa dacewa' da ake wallafawa a shafukan.

    Wannan doka idan ta tabbata za ta kasance mafi tsauri da aka ƙaƙaba wa shafukan sada zumunta a Afirka.

    To sai dai masu suka na ganin matakin wani shirin gwamnati ne ta taƙaika wa al'ummar samun bayanai a ƙasar da ke da tarihin cusgunawa wa kafafen yaɗa labarai, ƙarƙashin mulkin sojoji.

  12. Mun yi wa ƙudirin haraji karatu na biyu don kwamiti ya samu damar bibiyarsa - Sanata Barau

    Satana Barau

    Asalin hoton, Barau I Jibril/Facebook

    Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I Jibril ya ce Majalisar Dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin haraji karatu na biyu ne domin a samu damar miƙa shi ga kwamitin kuɗi domin bibiyarsa da faɗaɗa nazari a kansa.

    Cikin wata hira da BBC Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa ya ce majalisar ta bayar da shawarar miƙa wa kwamitin kuɗi ya duba tare da shirya jin ra'ayin jama'a, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai an yi wa ƙudirin karatu na biyu.

    ''E an ji an yi jawabai, kuma mu a nan majalisa za mu iya tambayarsu, amma 'yan Najeriya ba za su samu damar yin tambaya game da ƙudirin ba har sai an kira jin ra'ayin jama'a''.

    Sanata Barau ya ce dokar haraji ba za ta tabbata ba dole sai da masu ilimin haraji, ''kan haka ne yanzu aka tura domin su je su duba, su feɗe komai sannan su yi mana bayanin abin da ya ƙunsa''.

    Ƙudirin harajin - da majalisar dattawan ta yi wa karatu na biyu a makon nan - ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman tsakanin wasu 'yan arewacin ƙasar, da ke zargin cewar ƙudirin zai cutar da yankin.

    To amma mataimakin shugaban majalisar ya ce karatu na biyu ba shi ke nuna cewa majalisar ta amince da ƙudurin ba, ''ai a nan ne ma aikin yake farawa''.

  13. Shigar Ukraine Nato ne kawai zai kawo ƙarshen yaƙinmu da Rasha - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce idan har ana son dakatar da yaƙin ƙasar, to dole ne a bai wa sauran yankunan ƙasar da ke ƙarƙashin ikonsa damar shiga ƙungiyar tsaro ta Nato.

    A wata doguwar hira da kafar yaɗa labarai ta Sky News, an tambayi shugaban na Ukraine ko zai amince da zama mamba a Nato, da yankunan da ke karƙashin ikonsa kawai?

    Sai ya ce zai amince ne kawai bisa sharaɗin Nato za ta amince da duka yankunan ƙasar da duniya ta sani a matsayin Ukraine.

    Ya ƙara da cewa idan Ukraine ta samu shiga daga nan sai ta fara ƙoƙarin ƙwato sauran yankunanta da ke hannun Rasha ta 'hanyar diplomasiyya''.

    To sai dai har yanzu ƙungiyar ta Nato ba ta yi wa Ukraine tayin hakan ba.

  14. Tinubu ya yaba da sake zaɓar Ngozi shugabar WTO

    Dakta Ngozi Okonjo-Iweala

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Bayanan hoto, A shekarar 2021 aka fara zaɓar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar WTO

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya - shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, (WTO) Dakta Ngozi Okonjo-Iweala - murnar sake zaɓarta a muƙamin a wa'adin mulki na biyu.

    A ranar Juma'a ne aka sake zaɓar Dakta Ngozi a matsayin shugabar WTO a wa'adin mulki na biyu.

    Cikin wata sanarwar da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce ya yi farin ciki da yadda ƙasashe mambobin WTO suka amince wa Ms Okonjo-Iweala ta zarce a karo na biyu na shugabancin WTO.

    ''Hakan ya nuna irin ƙwarin gwiwa da amincewa da duniya ta yi da jagorancinta, tare da cike da fatan ƙarfafa da bunƙasa kasuwancin duniya'', in ji Tinubu.

    A shekarar 2021 ne tsohuwar ministar ta Najeriya - wanda kuma fitacciyar masaniyar tattalin arziki da kuɗaɗe ce - ta kafa ta tarihin zama 'yar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta taɓa jarogantar ƙungiyar WTO mai mambobin ƙasashe 164 a faɗin duniya.

    Wa'adin mulkinta na farko a matsayin shugabar WTO ta bakwai zai ƙare ranar 31 ga watan Agustan 2025, yayin da wa'adinta na biyu zai ƙare a shekarar 2029.

  15. Trump ya gana da firaministan Canada a Amurka kan baranazar ƙarin haraji

    Donald Trump

    Asalin hoton, Pool

    Firaministan Canada Justin Trudeau, ya ci lifayar abincin dare tare da zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump a Florida, kwanaki kaɗan bayan Trump ya furta zai sanya wa kayan da ƙasar ke shiga da su Amurka haraji.

    Da yake jawabi kan batun, Mista Trudeau ya ce dole a ɗauki barazanar da muhimmanci.

    Jami'ai a Canada sun ce wataƙila ƙasar ta maida martani ta hanyar ƙara haraji ga kayan Amurka, matuƙar Mista Trump ya aikata abin da ya furta, kamar yadda ita ma Mexico ta ce za ta yi.

    Mista Trump dai ya zargi ƙasasshen biyu makwabatn Amurka da rashin ɗaukar matakin daƙile amfani da ƙasashen kan kwararar 'yan cirani zuwa ƙasarsa.

  16. 'Yan tawaye da masu iƙirarin jihadi sun karɓe iko da birnin Aleppo a Syria

    'yan tawaye

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan tawaye da masu iƙirarin jihadi a Syria sun karɓe iko da kusan rabin birnin birni na biyu mafi girma a kasar wato Aleppo.

    Ƙungiyar da ke sa ido kan yaƙin na Syria mai mazauni a Birtaniya, ta ce dakarun shugaba Bashar al-Assad sun janye daga yankin ba tare da turjiya ba.

    Wannan lamari ya kawo gagarumin sauyin iko a Syria, tare da fito da raunin gwamnatin ƙasar a fili.

    Bidiyon da aka yaɗa a kafar intanet, ya nuna yadda 'yan tawayen ke ɗaga tutarsu a muhimmin wurin tarihi da ke birnin Aleppo.

    A ɓangare guda kuma, dakarun sojin babbar aminiyar gwamnatin Bashar al-Assad, wato Rasha na luguden wuta a wasu sassan da 'yan tawayen suke.

  17. Asslamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdaullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.