Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 28/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe shafin na labaran yau da kullum. Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Shugaban Kenya ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan batun Ingilishi

    Shugaban Kenya, William Ruto ya janye kalamansa da ya yi a makon da ya gabata, waɗanda suka bayyana kamar yana yi wa Turancin Ingilishin ‘yan Najeriya ke yi ba’a.

    An tafka zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, tun bayan da ya bayyana a wani taron ƴan Kenyar mazauna Italiya cewa, Ingilishin da ‘yan Najeriya ke yi yana da wahalar fahimta, har ma ana iya buƙatar mai fassara.

    Da yake magana a birnin Nairobi, Mista Ruto ya ce an sauya kalamansa ne daga abin da yake nufi, kuma dukkanin ‘yan Afirka suna yin Ingilishi mai kyau.

    Ya kuma tunatar da mahalarta wani taron ma’adinai cewa, ɗaya daga cikin ‘ya’yansa mata na auren wani ɗan Najeriya, kuma yana fatan ba za a samu wata matsala daga iyayen mijin sakamakon kalaman nasa ba.

  3. Elon Musk da Sam Altman za su bayyana a gaban kotu kan AI

    Fitattun attajiran nan biyu a fannin fasahar zamani, wato Elon Musk da kuma wanda ya kirkiro ƙirƙirarriyar basirar AI ta ChatGPT, Sam Altman, za su bayyana a wata kotun tarayya ta jihar California, a wata shari’a da ake ganin za ta iya tsara makomar fasahar ƙinrarrarriyar basirar.

    Mista Musk na tuhumar shugaban kamfanin OpenAI da zargin damfararsa kan wasu miliyoyin daloli, tare da saba alkawarin da aka yi kan ci gaba da tafiyar da kamfanin a matsayin wata ƙungiya mai zaman kanta.

    Sai dai Mista Altman ya musanta zarge-zargen. A baya dai Mutanen biyun da suka kafa kamfanin na OpenAI sun kasance abokai, inda daga bisani suka koma manyan abokan hamayya a ‘yan shekarun nan.

  4. MSF ta zargi Isra'ila da datse hanyoyin ruwan Falasɗinawa

    Ƙungiyar agaji ta MSF ta zargi hukumomin Isra’ila da datse hanyoyin ruwa a matsayin makami ga Falasɗinawa.

    Rahoton ya ce Isra’ila ta lalata kusan kashi 90 cikin 100 na cibiyoyin ruwa da tsaftar gine-gine a Zirin Gaza.

    Ya ƙara da cewa rashin samun ruwa ya jawo ƙaruwar cututtuka da suka shafi numfashi, da fata, da na hanji. Sai dai Isra’ila ta ce zarge-zargen na MSF ba su da tushe bare makama.

  5. 'Shugaban Mali ya gana da wakilan Rasha'

    Gwamnatin sojin Mali ta ce shugaban ƙasar ya gana da wakilan Rasha, kwanaki kaɗan bayan hare-haren ƴanbindiga da ƴan aware, waɗanda suka fatattaki sojojin Mali da na Rasha tare da kashe ministan tsaron ƙasar.

    Ba a ga Janar Assimi Goita ba tun bayan hare-haren, amma dai gwamnatin ƙasar ta wallafa wasu hotuna na wakilan Rasha suna ganawa da wani mutum sanye da kakin sojoji mai ɗauke da sunansa.

    Sai dai ba a ga fuskar mutumin ba domin ya rufe fuskar.

    Rasha dai ta nanata cewa an samu kwanciyar hankali kuma komai ya lafa a Mali.

  6. Rasha ta zargi Ukraine da tayar da tarzoma a kasuwar makamashin duniya

    Fadar Kremlin ta zargi Ukraine da tayar da tarzoma a kasuwannin makamashi na duniya, bayan sabbin hare-haren jirage marasa matuki sun haddasa wata mummunar gobara a wata matatar mai ta Rasha.

    Wakilin BBC ya ce wannan ne karo na uku da Ukraine ke kai hare-haren jiragen marasa matuki kan cibiyar da ke tashar jiragen ruwa ta Tuwaps, a wannan watan.

    Hare-haren sun yi mummunar illa ga muhalli, inda ake ganin hayaki mai kauri da baƙi yana tashi daga wurin. Ukraine ta ce tana kai hare-haren ne kan cibiyoyin makamashi, saboda suna tallafa wa ci gaba da mamayar da Rasha ke yi.

    Kafofin watsa labaran gwamnatin Rasha sun ce Shugaba Vladimir Putin ya umarci ministan kula da agajin gaggawa da ya ziyarci wajen, domin sanya ido.

  7. An saki ɗan jarida da aka tsare a Belarus saboda sukar gwamnati

    An sako dan jaridar nan da aka tsare a Belarus saboda rahotanninsa kan gwamnati, a matsayin wani bangare na musayar fursunoni da Poland.

    Andrzej Poczobut wanda ya kasance mai sukar gwamnatin da ake zargi da kama-karya ta Alexander Lukashenko, an yanke masa hukuncin daurin shekara 8 a shekarar 2023, bisa zargin tayar da rikicin kabilanci da kuma barazana ga tsaron Belarus.

    Ya kasance ɗaya daga cikin wadanda suka lashe kyautar karramawa ta Sakharov a bara, wadda majalisar Turai ke bayarwa ga masu kare hakkin bil’adama da ‘yancin dan Adam.

    Kafafen watsa labarai na gwamnatin Belarus, sun ce Belarus ɗin da Poland sun yi musayar fursunoni biyar-biyar.

  8. Zelensky ya ce Isra'ila na amfani da hatsin da Rasha ta ƙwace musu

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi tsokaci kan yadda Isra'ila ke karɓar abin da Kyiv ta bayyana a matsayin hatsin da aka sato daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Ya ce a karo na biyu wani jirgin ruwa yana shirin sauke irin wannan hatsi a tashar jiragen ruwa ta Isra'ila, yana mai cewa babu yadda za a yi Isra'ila ta ce ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Zelensky ke goyon bayan Amurka da Isra'ila a yaƙin da suke yi da ƙasar Iran.

  9. Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta fice daga ƙungiyar OPEC

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce za ta fice daga ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur a duniya OPEC, bayan fiye da shekaru 60.

    UAE ta ce ta matakin na cikin muradun tattalin arziƙinta na tsawon lokaci da kuma sauyin da ake samu a ɓangarenta na makamashi.

    Ana dai ganin matakin zai kawo tsaiko ga ayyukan ƙungiyar, inda wani mai sharhi kan harkokin makamashi ya ce ''wannan na nuna alamun soma rugujewar Opec''

    Ministan Makamashi na ƙasar, wadda ke yankin Gulf, ya ce ƙasar za ta fi walawa idan ya kasance babu wasu ƙa'idoji na ƙungiyar a kanta.

    Ƙasashe biyar, da suka haɗa da Iran da Iraqi da Kuwait da Saudiyya da kuma Venezuela ne suka kafa ƙungiyar Opec a shekarar 1960, kuma manufarta ita ce tsara yadda za a riƙa sarrafa man fetur da kuma samar da riba ga mambobinta.

    Haɗaɗɗiyar ɗaular larabawa ta shiga ƙungiyar a 1967, kuma ficewarta zai bar ƙungiyar da mambobi 11.

  10. Gwamnatin Nijar ta ƙaddamar da sabon katin shaidar zaman ɗan ƙasa

    A jamhuriyar Nijar gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da sabon katin shaidar zama ɗan ƙasa, da nufin ƙarfafa tsaro da zamanantar da tsarin tantancewa.

    An fara ƙaddamar da shirin ne a birnin Yamai a ofishin ƴan sanda na Yantala.

    Shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙasashen yankin Sahel ke yi na daidaita bayanan sirri da tafiye-tafiye tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar.

    Mallakar Katin shaidar dai zai zama tilas ga yan ƙasa masu shekaru 15 zuwa sama.

  11. Ghana ta kawo ƙarshen tattaunawar tallafin kiwon lafiya da Amurka bayan gaza cimma matsaya

    Rahotanni daga Ghana na cewa gwamnati ta kawo ƙarshen tattaunawa da Amurka kan tallafin kiwon lafiya.

    A cewar wakilin BBC, hukumomin Ghana sun ce Washington na son samun bayanan lafiyar ‘yan kasar, wata buƙata da Ghanan ta yi watsi da ita.

    Ba a samu wani cikakken bayani ba daga bangaren Ghana ko Amurka kan rahotannin.

    Rahotanni sun kuma ce irin wannan matsalar ce ta daƙile tattaunawar Amurka da Zimbabwe da kuma Kenya.

    Gwamnatin Donald Trump ta rusa hukumar bayar da tallafin Amurka a farkon wannan shekara, daga bisani Washington ta sanar da wani sabon tsari da ke buƙatar ƙasashe masu tasowa su ƙara ɗaukar nauyin kula da lafiyarsu da kansu.

  12. Tinubu ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027

    Shugaban Najeriya mai ci a yanzu Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sha'awarsa ta sake yin takarar shugabancin ƙasar a babban zaɓen 2027, bayan da ya sayi fom ɗin shiga takara a yau Talata.

    Ɗan majalisa mai wakiltar Ikeja a majalisar Tarayya, kuma wanda ke jagorantar ƙungiyoyi da ke goyon bayan Tinubu, James Faleke ne ya sayi fom ɗin a madadinsa a Abuja, kan naira miliyan 100.

    Sakataren tsare-tsare na jamiyyar APC, Suleiman Argungu ne ya miƙa fom ɗin bayan da aka ƙaddamar da soma sayar da fom ɗin neman yin takara ga dukkanin masu son tsayawa takara.

  13. Rasha ta zargi Ukraine da hargitsa kasuwar mai ta duniya bayan ta kai hari kan matatar ta

    Fadar Kremlin ta zargi Ukraine da ƙoƙarin hargitsa kasuwar ɗanyen mai ta duniya, bayan sabbin hare haren jirage marasa matuƙa ya janyo gobara a wata matatar man Rasha.

    Ukraine ta kai hari kan matatar da ke tashar jiragen ruwa ta Tuapse sau da dama a wannan watan.

    Hare haren sun gurɓata yanayi, inda baƙin hayaƙin da ke fitowa daga matatar ya turnuƙe sararain samaniya.

    Ukraine ta ce tana kai hari kan cibiyoyin samar da makamashi ne saboda suna samarwa Rasha kuɗin da take amfani da shi wajen ci gaba da mamayar da take mata.

    Kafafen yaɗa labarai na Rasha sun ce Shugaba Putin ya bayar da umurnin cewa ya yi gaggawar isa Tuapse domin sanya ido kan ƙoƙarin da ake yi na shawo kan gobarar.

  14. Kamfanin jirgin sama ya dakatar da aiki a Mali sakamakon hare haren ƙarshen mako

    Wani kamfanin jirgin sama na Mali ya dakatar a sufurin jiragen sama daga birane biyu a arewaci da tsakiyar ƙasar, bayan ƴan bindiga sun kashe ministan tsaron ƙasar a ƙarshen mako tare da ƙwace ikon wurare da dama.

    Rahotanni daga babban birnin ƙasar Bamako, da ke kudu maso yammaci, na nuna cewa alumma na cikin natsuwa amma har yanzu akwai yanayi na fargaba.

    Zuwa yanzu ba a ji ɗuriyar shugaban mulkin sojin Mali Janar Assimi Goita ba, wanda ya ƙwace iko shekaru shida da suka gabata, tun bayan da ƴan tawaye masu iƙirarin jihadi masu ƙawance da ƴan tawayen Tuareg suka ƙaddamar da hari ranar Asabar, wanda ya kai ga fattatakar sojojin ƙasar da sojojin hayar Rasha.

  15. Chadi ta kori ƴan gudun hijirar Najeriya - AFP

    An kori ɗaruruwan ƴan Najeriya da ke zama a Chadi domin neman mafaka daga hare haren masu iƙirarin jihadi zuwa Najeriya a makon da ya gabata, kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP.

    Hakan na zuwa ne a yayin da masu sharhi ke gargaɗin cewa an samu ƙaruwar hare hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta gabata.

    Wasu ƴan Najeriya biyu da aka kama a Chadin sun shaidawa AFP cewa ƴan ƙasarsu ɗari shida aka tsare bayan an kama su, kuma aka yi watsi da su a birnin Kousseri, wanda ke kusa da iyakar babban birnin ƙasar N'Djamena.

    Ƴan sandan Chadi sun tabbatar cewa an kori mutanen, amma basu bayar da adadi ba.

    Sun ce sun ƙaddamar da wani shiri da suka saba yi kan ƴan gudun hijira da suka shigo ta ɓarauniyar hanya, ba tare da la'akari da ƙasar su ba.

    '' A ranar Juma'a jami'an tsaro suka dira a gidanjenmu, suka ce duk ƴan gudun hijira daga Najeriya ƴan Boko Haram ne, kuma su fice daga ƙasar su. Kuma suka ɗauki bayanan hannunmu'' kamar yadda Kyari Musa ya shaidawa AFP.

    A cewar sa sun kuma yi gargaɗin cewa duk wada ya dawo kuma aka kama shi zai je gidan yari na shekara 20.

    Ƴan Najeriyan sun kuma ce a ranar Asabar ne jami'an Kwastam na Chadi suka kai su garin Gamboru da ke kan iyakar ƙasar da Najeriya.

    Najeriya dai ta shafe kusan shekara 17 tana fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka yi ta bazuwa zuwa ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi.

  16. Amurka na nazari kan tayin Iran na kawo ƙarshen yaƙi

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce tana duba wani 'rubutaccen saƙo' daga Iran, wadda Pakistan ta gabatar mata.

    Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi tayin buɗe Mashigar Hormuz domin kawo ƙarshen yaƙin gabaɗaya, sai dai za a jinkirta yarjejeniya kan ayyukanta na nukiliya.

    Wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun bayyana cewa Shugaban Trump bai ji daɗin shirin Iran ɗin ba.

    Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce shirin da Iran ta gabatar 'ya fi yadda yake tunani' , sai dai ya jaddada cewa wajibi ne a tabbatar cewa Iran ba ta taɓa samun makamin nukiliya ba.

    Iran ɗin ta ce buƙatun Amurka na son rai waɗanda suka wuce gona da iri ne ke hana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi.

  17. Ƴansandan jihar Kaduna sun kama gomman masu garkuwa da mutane a watan Afrilu

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama mutum talatin da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, da masu safarar makamai 4, tare da tarwatsa gungun masu satar motoci cikin a watan Afrilun 2026.

    A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ƴan sandan jihar Rabiu Muhammad ya fitar, ya ce sun sami waɗannan da ma wasu nasarori ne sakamakon yin aiki da bayanan sirri, da aiki bisa tsari da kuma ƙara yawan jami'ai da ke sintiri a faɗin jihar.

    Ya kuma ce sun ƙwato makamai biyar da harsasai, da kuma motoci huɗu da aka sace cikin watan.

    A cewar sa, sun gundanar da wani aiki a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda jami'an tsaron suka yi bata kashi da wasu da ake zargi ƴan bindiga ne, waɗanda suka tsere tare da raunuka kuma suka bar makamansu na AK47 da harsasai.

    Rundunar ta kuma tarwatsa gungun masu satar motoci, inda ta kama wasu da take zargi da satar a Kaduna da Kano da Katsina.

    Haka zalika ya ce ƴan sandan sun ceto wani yaro ɗan shekara bakwai wanda aka sace a ƙaramar hukumar Kubau kuma aka nemi biyan Naira miliyan 40 kuɗin fansa.

    Kwamishinan ƴan sandan ya kuma bayar da tabbacin cewa rundunarsa za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka a jihar Kaduna, inda ya ce a yanzu haka ana ƙoƙari wajen kamo ƴan bindigar da suka tsere da kuma tarwatsa gungun masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

  18. Wani babban jirgin ruwa mai alaƙa da Rasha ya bi ta Mashigar Hormuz

    Wani babban jirgin ruwa da ke da alaƙa da ɗaya daga cikin makusantan shugaban Rasha Vladimir Putin ya wuce ta Mashigar Hormuz, duk da rufe muhimmiyar mashigar da aka yi.

    Jirgin Nord Luxury mai tsawon mita 142, da ke da alaƙa da hamshaƙin mai kuɗin nan da aka sanya wa takunkumai Alexey Mordashov, ya yi tafiya ne zuwa Muscat da ke Oman daga Dubai a ƙarshen mako, kuma ya kasance ɗaya daga cikin jiragen ruwa waɗanda ba na gwamnati ba ko kasuwanci da ya bi ta mashigar a cikin ƴan watannin nan.

    Iran ta yi wata ganawa mai muhimmanci da Rasha a cikin makon nan, a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakaninta da Amurka kan sake buɗe Mashigar Hormuz.

    A ƙiyashi kashi ɗaya cikin biyar da ɗanyan mai da iskar gas da ake amfani da shi a duniya ne ke wucewa ta Mashigar.

  19. Ukraine na zargin Isra'ila da sayen ''hatsin sata'' daga yankunanta da Rasha ta mamaye

    Ukraine ta gayyaci jakadan Isra'ila a ƙasar, bayan da Kyiv ta zargi Isra'ilar da sayen abin da ta kira hatsin sata daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce irin wannan sayayya na kawo cikas ga alaƙa mai kyau da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Ya ce jirgin ruwan dakon kaya na biyu ya isa Haifa, bayan na farkon ya kai hatsi yakin.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Sa'ar ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.

    Sai dai kuma ya yi gargaɗin cewa zargi ba shaida bane, inda ya ja hankalinsu kan gudanar da hulɗar diflomasiyya ta intanet ko kafafen yaɗa labarai.

  20. Dukkan jagororin Iran masu tsattsauran ra'ayi ne - Rubio

    A wata hira da ya yi da kafar talibijin ta Fox News, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi ƙarin bayani game da halin da ake ciki a Iran, da kuma tsaikon da Amurka ke samu wajen cimma yarjejeniya da gwamnatin ƙasar.

    A tattauwnawar ta sa, Rubio ya bayyana jagororin Iran da cewa ‘’ Dukkaninsu masu tsatsauran ra’ayi ne, Amma akwai masu tsatsauran ra’ayin da sun san cewa dole za su tafiyar da alamuran kasa kuma dole su tabbatar tattalin arzikin kasar na tafiya yadda ya kamata. Sai dai addini ne abin da suka fi mayar da hankali kai''.

    Sai dai a cewarsa ‘abin takaici, ana iya cewa masu tsatsauran ra’ayi waɗanda ba sa ma duniya fatan alkhairi ne ke rike da wuyar kasar’’.

    Rubio ya kuma ce masu tsautsauran ra’ayin addinin ba wai kawai dakarun juyin juya halin Iran bane, har ma da shugaban Iran ɗin da majalisar sa.

    Ya kuma kara da cewa mutane kamar Fira ministan kasar da Shugaban ƙasar da Shugaban majalisa duk masu tsatsauran ra’ayi ne, amma kuma sun san cewa dole ne ƙasar ta samu tattalin arziki mai inganci, kuma dole ne yan ƙasar su ci abinci.