Shugabannin Turai sun nuna goyon bayansu ga Ukraine
Shugabannin ƙasashen Turai sun yi ta wallafa saƙonnin goyon bayansu ga Mista Zelensky bayan cacar-bakinsa da Mista Trump.
Shugaba Macron na Faransa - wanda ya gana da Mista Trump a farkon makon nan - ya ce a bayyane take Rasha ce ta tsokani Ukraine kuma yana da kyau a mutunta mutanen da suka riƙa faɗa don kare kansu.
Shi ma shugaban Poland, Donald Tusk, ya gaya wa Ukraine cewa 'Muna tare da ku.'
A Amurka, 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dokokin ƙasar sun zargi Mista Trump da mataimakinsa JD Vance da yi wa shugaban Rasha Vladimir Putin aiki.
Wakilin BBC a ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ya ce wannan ya zama taɓarbarewar dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine da masu mara mata baya a Turai, kuma da wuya a sake gina su a nan kusa.






















