Muna maraba da duk haɗin gwiwa da zai kawo ƙarshen matsalar tsaro - Gwamnatin Sokoto

Asalin hoton, Ahmed Aliyu
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da harin da aka kai a wasu sassan ƙananan hukumomin jihar, wanda Amurka ta ce ta kai kan mayaƙan IS.
Gwamnatin ta ce an kai harin ne a jiya Alhamis, inda ta ce an yi haɗin gwiwa ne tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya wajen ƙaddamar da harin, wanda ta ce ba a rasa rai ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar, ya ce, "Ba za iya tantance haƙiƙanin sakamakon harin ba a cikin ƙanƙanin lokaci, saboda har yanzu muna jiran cikakken rahoton aikin na musamman," in ji sanarwar.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa babu fararen hula da harin na garin Jabo ya kashe ko ya jikkata.
"Gwamnatin Sokoto na maraba da duk wani aikin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da wata ƙasa ko wasu masu ruwa da tsakiya domin magance matalolin tsaro da sauran laifuka a jihar."
Sanarwar ta ƙara da cewa a shekara biyu da suka gabata, gwamntin jihar ta yi ƙoƙarinta wajen magance matsalar ta hanyar ba jami'an tsaro duk goyon bayan da suke buƙata domin su gudanar da aikinsu da kyau."
A ƙarshe gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su ci gaba da ba gwamnatin tarayya da ta jiha hadin kai ta hanyar fitar da bayanan sirri ga jami'an tsaro, "domin hakan ne zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Sannan mu ci gaba da addu'ar neman agajin Allah wajen magance matsalar."

















