KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 04/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Cape Verde ta ƙi amincewa da jirgin alfarma bisa tsoron cutar HantaVirus

    jirgin ruwan yawon buɗe ido

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Hukumomin lafiya a Cape Verde sun ƙi amincewa su bai wa wani jiirgin ruwan alfarma mai ɗauke da wasu mutane da ake zargi na ɗauke da cutar HantaVirus mai haɗari tsayawa a wata tashar jiragen ruwan ƙasar, inda suka ce wajibi ne su kare ƴan ƙasar.

    Masu kula da jirgin na ta neman izini domin fitar da wasu fasinjoji biyu da basu da lafiya.

    Jirgin na fama da matsalar rashin lafiya mai tsananin gaske, bayan tasowa daga Argentina zuwa Cape verde.

    Fasinjoji uku sun mutu, sai dai mutum guda da zuwa yanzu aka tabbatar yana ɗauke da cutar wani bature ne wanda a yanzu ke asibiti a Afirka ta Kudu.

  2. Farashin mai ya tashi bayan iƙirarin Iran na kai hari kan jirgin ruwan Amurka

    gidan mai

    Farashin mai a kasuwannin makamashi na duniya ya tashi bayan rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Iran sun ce ta harba jirage marasa matuƙa biyu kan wani jirgin ruwan yaƙi na Amurka a yayin da yake ƙoƙarin shiga Mashigar Hormuz.

    Ɗanyan mai nau'in Brent ya ƙaru da dala huɗu kan kowane ganga cikin mituna bayan ɓullar rahotannin, inda ya kai dala 114 duk ganga.

    Sai dai ya ragu kaɗan bayan da Amurka ta musanta cewa an kai harin.

    A daren jiya ne Donald Trump ya sanar da shirin yi wa jiragen ruwan da suka maƙale a Mashigar rakiya, inda ya ce ya yi hakan ne domin taimakawa alumma.

    Idan ƙoƙarin rakiyar jiragen ruwa ya kai ga ɓarkewar wani rikicin, hakan zai sake rage fatan da ake dashi na ci gaba da jigilar mai da iskar gas, kuma mai yiwuwa ya sa farashin mai ya sake tashi.

  3. NDLEA ta kama dattijai da ake zargi da safarar wiwi

    Hannun tsoho

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wani mutum ɗan shekara tamanin da uku (83), da wani mai shakara saba'in da takwas (78) ɗauke da miyagun ƙwayoyi a jihohin Abia da Ekiti.

    A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, NDLEA ta ce ta kama dattijo na farko ne ne a ranar 28 ga watan Afrilun 2026 a yayin wani samame da jami'anta suka kai yankin Samek da ke Aba a jihar Abia, bayan samun bayanan sirri cewa ana safarar ƙwayoyi a yankin.

    An kuma kama shi da giram 700 na wani nau'in wiwi da aka ƙunshe a cikin ledoji.

    Mutumin mai shekara 83 ya shaida wa masu gudanar da bincike cewa a baya shi ƙwararren mai haɗa takalma ne, kafin daga bisani ya rikiɗe ya koma sayar da ƙwayoyi.

    A wani aikin na daban kuma, jami'an hukumar a jihar Ekiti sun kama wani dattijo a ranar 30 ga watan Afrilu a gidansa da ke yankin Ilupeju-Ekiti bisa zargin shi da safarar ƙwayoyi, kuma an kama shi da ƙwayoyin da yawansu ya kai nauyin giram 350.

  4. Amurka ta musanta iƙirarin Iran na kai hari kan jirgin ruwan sojojinta

    Babbar cibiyar tafiyar da harkokin tsaro ta Amurka (Centcom) ta musanta rahotannin cewa Iran ta kai hari kan ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta da makamai masu linzami biyu.

    A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na X, Cibiyar tsaron ta ce '' babu jirgin sojojin ruwan Amurka da aka kai wa hari'' inda ta kuma ce '' Rundunar sojin Amurka na goyon bayan shirin Shugaba Trump na rakiyar jiragen da suka maƙale a Mashigar mai suna 'Project Freedom' kuma tana cigaba da toshe tashoshin jiragen ruwan Iran.''

    Tun da farko sojojin Iran sun yi iƙirarin cewa sun hana wani jirgin sojin ruwa Amuurka shiga Mashigar Hormuz bayan sun kai masa hari.

  5. Mun kai hari kan jirgin ruwan sojojin Amurka - Iran

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa sojojin Iran sun harba makamai masu linzami kan wani jirgin ruwan yaƙin Amurka domin hana shi shiga Mashigar Hormuz.

    Har yanzu dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da iƙirarin, hakazalika Amurka ma ba ta ce komai ba.

    Rahotannin harin na zuwa ne bayan da Iraniyawa suka ce za su kai hari kan dakarun Amurka idan har suka aiwatar da shirin Shugaba Trump na yi wa jiragen ruwan kasuwanci waɗanda suka maƙale rakiya ta Mashigar.

    Iran ɗin ta ce wajibi ne a haɗa kai da ita kafin wani jirgi ya wuce lafiya.

    Rundunar sojin Amurka ta ce za ta aike da jiragen ruwan yaƙi da kuma jiragen sama, domin su bai wa jirage shawarar hanyoyin da za su bi su wuce, kuma su samar da garkuwa ga duk wani hari da Iran za ta kai.

    Ɗaruruwan jiragen ruwan kasuwanci, da aƙalla ma'aikata dubu ashirin ne suka maƙale a yankin tun bayan soma yaƙin Amurka da Iran watanni biyu da suka gabata.

  6. Shugabannin ƙasashen Nahiyar Turai na ganawa a Armenia domin tattauna tsaronsu

    shugabannin ƙasahsn Turai

    Asalin hoton, AFP Via Getty Images

    Bayanan hoto, Fira Ministan Armenia Nikol Pashinyan (tsakiya) da shugabannin ƙungiyar Tarayyar Turai

    Shugabannin ƙasashen Turai da suka haɗu a Armenia sun jaddada buƙatar haɗin gwiwa a fannin tsaro, a matsayin martani ga rikicin da ake samu a faɗin duniya da kuma tsamin dangantaka tsakaninsu da Washington.

    Shugaban Ukraine Volodymir Zelensky ya shaidawa taron cewa akwai buƙatar Nahiyar Turai ta samar da duk abin da take buƙata domin kare kanta daga duk wata barazana.

    Da yake jawabi a Yerevan a taron ƙungiyar masu ruwa da tsaki na siyasar ƙasashen Turai, ya ce Ukraine a shirye ta ke ta taimaka wajen bunƙasa abubuwan da ake buƙata wajen samar da tsaro a Nahiyar.

    Tun da farko Shugaba Macron na Faransa ya ce wajibi ne Nahiyar ta daina dogara da kowa, ta hanyar samar da tsaronta.

    Canada ta shiga taron ƙungiyar masu ruwa da tsakin - wata ƙungiya da aka kafa bayan mamayar Rasha a Ukarine.

  7. Mutum 5,000 sun tsere daga gidajensu a Philippines bayan aman wuta da wani dutse ya yi

    dutse mai aman suta

    Asalin hoton, Marco Restivo / Barcroft Media

    Dubban mutane a Philippines sun tsere daga gidajensu sakamakon aman wuta da wani dutse ya yi a kasar.

    Dutsen Mayon da ke yankin Bicol ya yi aman ne ranar Asabar din da ta gabata, inda ya fitar da toka da ta turnuƙe sararin samaniya.

    Sama da mutane dubu biyar da ke zaune a kasan dutsen yanzu haka suna matsugunan gaggawa na wucin gadi, yayin da hukumomi ke kokarin bude hanyoyin da toka ta mamaye.

    Kasar Philippines na daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar bala'i a duniya, inda ake yawan samun duwatsu masu aman wuta da girgizar kasa da ambaliya da kuma zabtarewar kasa.

  8. Ana gudanar da azumi a yau a Nijar domin neman nasara a yaƙi da ƴan bindiga

    mace na addu'a da charbi a hannu

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar, a yau Litinin ne gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta ware domin gudanar da azumi a faɗin ƙasar.

    Zaman majalisar ministoci na ƙarshen mako ne ya umurci al'ummar ƙasar da su gudanar da azumin na yau tare da addu'o'in Allah ya ba ƙasashen AES nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

    Yanayin tsaro a yankin Sahel na ci gaba taɓarɓarewa yayin da masu iƙirarin jihadi ke ƙara matsa lamba kan sojojin ƙasashen.

    Ƙasashen uku da suka haɗa da Nijar da Mali da Burkina Faso na ƙara fuskantar matsala wajen aiwatar da iko a kan dukkanin yankunansu, har ma ya kai wasu yankuna sun faɗa hannun ƴan bindigar.

    Lamarin ya sake ta'azzara ne bayan harin haɗin gwiwar da masu iƙirarin jihadi suka kai a Mali a ƙarshen watan da ya gabata.

    A jamhuriyar NIjar, bayan matakan sojin da gwamnatin mulkin soji ta ce tana ɗauka a yayin zaman majalisar a ƙarshen mako, ta kuma buƙaci ƴan ƙasar da su duƙufa yin addu'oi domin nasara a kan abokan gaba

    Wasu ƴan ƙasar dai sun bayyana ra'ayoyinsu inda suka ce suna fatan azumin ya zama karɓaɓɓe, inda wasu suka ce dama sukan yi azumin, kuma idan hakan bai saɓawa addini ba za su yi.

  9. Amurka za ta miƙa wa Iran ma'aikatan jirgin ruwanta da ta kama a watan da ya gabata

    jirgin ruwan sojin Amurka yayin da ya kai hari kan wani jirgin ruwan Iran

    Asalin hoton, Centcom

    Gwamnatin Pakistan ta ce Amurka ta miƙa mata ma'aikata 22 dake cikin jirgin ruwan Iran da ta kama a watan da ya gabata, kuma nan gaba a yau za ta miƙa su ga hukumomi a Iran.

    Dakarun Amurka sun ƙwace jirgin na Touska a watan da ya gabata, bayan sun kai hari kan ɗakin da injinsa yake.

    Iran ta bayyana kama jirgin a matsayin 'fashin teku', yayin da Shugaba Trump kuma ya ce 'jirgin yayi ƙoƙarin tsallake shingen da sojojin ruwan Amurka suka sanya ne'.

    Pakistan ta ce mayar da ma'aikatan jirgin wani mataki ne na Amurka na samar da ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da ake na samar da sasanci tsakaninsu.

    Ta kuma ce za a kai jirgin ruwa kan tekun yankin Pakistan, kuma za a mayar wa masu shi da zarar an kammalla gyara shi.

  10. Najeriya za ta kwaso ƴan ƙasarta da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu

    masu zanga zanga a Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA/Shutterstock

    Najeriya ta soma shirin dawo da ƴan ƙasarta da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu, a yayin da ake samun ƙaruwar fargaba cewa za a iya samun ƙaruwar kai hari kan baƙi.

    Ministar harkokin wajen ƙasar Bianca Odumegwu-Ojukwu ta ce zuwa yanzu mutum 130 sun yi rijista cikin shirin, inda ta ce ana hasashen adadin zai ƙaru.

    A cikin sanarwar da ta fitar, ta bayyana irin damuwar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi kan hare haren da ake kai wa a ƙasar, kuma ya yi Allah wadai da tashin hankali da kuma zanga zangar ƙin jinin baƙi da kuma kalaman nuna ƙiyayya da masu zanga zangar ke yi.

    Ministar ta kuma ce an kashe ƴan Najeriya biyu a hare hare daban daban wanda jami'an tsaro suka yi, inda ta jaddada cewa ƙasarta na neman adalci.

    Shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa ya yi Allahwadai da hare haren, sai dai kuma ya gargaɗi ƴan ƙasashen wajen da ke ƙasar da su mutunta dokokin ƙasar.

  11. Wata babbar mota ta auka cikin jama'a a filin wasan motoci a Colombia

    babbar mota

    Asalin hoton, Popaya Pauta Via Facebook

    Mutane 3 sun mutu, yayin da wasu fiye da talatin suka samu raunuka lokacin da wata babbar mota ta auka cikin jama'a a wani filin wasan motoci a ƙasar Colombia.

    Lamarin ya faru ne a Popayán da ke yankin kudancin jihar Cauca.

    Ƴan sanda sun shaida wa kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa birkin motar ne ya samu matsala.

    Wakilin BBC ya ce wani bidiyo mai tayar da hankali da ƴan kallo suka naɗa ya nuna yadda motar ta tsallaka shingen da ya kyallace ƴan kallo daga filin wasan ta kuma auka cikin mutane.

    Gwamnan jihar Cauca, Octavio Guzmán, ya jajantawa waɗanda abin ya shafa, ya kuma ce an umarci asibitocin yankin da su kula da waɗanda suka ji rauni.

  12. Za mu kai hari kan dakarun Amurka idan suka bi ta Mashigar Hormuz - Iran

    jiragen ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, an ɗauki hoton daga gaɓar Oman a ranar 1 ga watan Mayu

    Rundunar sojin Iran ta ce za ta kai hari kan dakarun Amurka idan har suka shiga Mashigar Hormuz - bayan da shugaba Trump ya ce Rundunar sojin Amurka za ta fara raka jiragen ruwan ƴan kasuwa da za su wuce ta Mashigar Hormuz, a yau litinin

    Sanarwar ta ce shirin, wanda Mista Trump ya yi wa laƙabi da Project Freedom, zai kunshi dakarun sojin Amurka dubu goma sha biyar, da jiragen ruwan yaƙi masu lalata makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaƙi sama da ɗari.

    Wakilin BBC ya ce shugaban ya ce Amurka za ta raka waɗannan jiragen ruwan su fice daga yankin, kuma za zu ci gaba da gudanar da kasuwancinsu ba tare da wata matsala ba.

    Tun da farko dai, Wani babban jami'in Iran Ebrahim Azizihas ya yi gargadin cewa za a ɗauki duk wani yunƙurin Amurka na yin katsalandan a harkokin mashigar ruwan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

  13. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da shiga sabon mako.

    A yau ma, kamar yadda muka saba, za mu kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a sassan duniya, kama daga yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

    Muna fatan za ku kasance tare da mu.