Yadda Iran ke sake gina wuraren da yaƙi ya lalata

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tehran
    • Marubuci, علی رمضانیان
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, روزنامه‌نگار
  • Lokacin karatu: Minti 5

Hotunan yadda yaƙi ya lalata Iran ya bayyana abubuwa biyu. Da farko akwai ƙididdigar mummunar asarar da yaƙin ya haifar da kuma buƙatar wa'adin sake gini tsakanin shekaru 2 da biyar, yayin da a wani ɓangaren kuma gwamnati ta sanar da fara bayar da agaji da ya ƙunshi kuɗin gina muhallai da yadda za a raba diyya.

Ƙididdigar farko da gwamnatin Iran ta yi ta bayyana yadda asarar da ta yi ta kai ta kimanin dala biliyan 270. Yayin da rahotanni suka ce farar hula sun rasa gidajen da yawansu ya kai 138,000, kuma sake gininsu zai laƙume Toman tiriliyan 40.

Akwai kuma wasu rahotanni da suka bayyana yadda aka lalata kusan ababen hawa da yawansu ya kusan 19,000 a faɗin ƙasar, biyan diyyarsu zai karya ƙarfin kamfanonin inshora.

Abdolmohar Mohammadkhani, kakakin yankunan tsakiyar birni ya ce an samu haɗurra 649 a birnin a ƙarshen Farvardin 1405, cikin rukunin wasu gidaje 46,000, 1,460 na bukƙatar a rushe su sannan a sake ginin su. Akwai rahotannin da suka ce sama da motoci 9,000 da kusan babura 600 aka lalata a yayin yaƙin.

Hukumar a Tehran ta sanar da cewar za ta ɗauki nauyin sake gina muhallai. Amma wani mai Magana da yawun gwamnati ya ce gwamnati ba ta da kuɗin da kai tsaye za ta ɗauki nauyin sake gine-ginen gidaje don haka sun nemi mafita.

Ƙwarewa wajen sake gine-gine bayan yaƙi

Iran na da kwarewa wajen sake ginin yankunan da yaƙi ya lalata. Bayan kwashe shekaru 8 ana fafata yaƙin Iran da Iraki, Iran ta yi asarar kusan dala tiriliyon 1.

''An kafa hedikwatar sake ginin yankunan da yaƙi ya lalata'' sai dai maimakon ta biya ƴan kasa kuɗi kai tsaye sai gwamnatin ta zaɓi tsarin bayar da bashin kayan gini. A wancan lokacin mutanen da aka lalata gidajensu a Khuzestan da Kermanshad da kuma Kurdistan sun karɓi bashi daga gwamnati don sayen ƙarfe da siminti.

Iran ta na da ƙwarewa a sake ginin wasu yankunan Kudancin Lebanon da aka lalata a yaƙin Isra'ila da Hezbolla a shekara ta 2006. Ta hanyar kafa hedikwatar sake gini a Lebanon, Iran ce ta ɗauki nauyin kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sake ginin dubban gidaje da makarantu da masallatai da gadoji.

Ba kamar yadda Iran ta sake ginin biranen ta ba, ta hanyar bayar da bashi daga bankuna. Wadɗannan ayyuka an gudanar da su ta hanyar fidda wasu kuɗaɗe na musamman don mayar da mabiya ɗarikar shi'a muhallansu a Lebanon.

.

Asalin hoton, Majid Asgaripour/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS

Bayanan hoto, Wuraren da yaƙi ya lalata.

Yadda ƴan ƙasa suka bayyana rashin jin daɗi game da yadda za a sake ginin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnati da kananan hukumomi sun ce zasu fara sake gine-gine a yankunan da aka lalata, musamman bayan tsagaita wutar makonni biyu ya fara aiki ranar 9 ga watan Afrilu. Sun ce da farko za a fara gyara ƙofofi da tagogin gidajen da suka fuskanci ƙaramar lalacewa, amma yayin da adadin gidajen da suka lalace ya ƙaru sai suka mayar da hankali wajen baiwa al'umma bashi.

Kakakin Hukumar Majalisar Injiniyoyi ya sanar da cewar a matsayinsu na wani sashe a Hukumar Kula da Birane zasu raba bashin sama da Toman miliyan 300 a ƙauyuka sannan akwai Toman miliyan 700 da za a yi amfani da su wajen sauyawa waɗanda suka rasa muhallansu matsuguni na wucin gadi ya ƙara da cewa za a raba wani ɓangare na waɗannan kuɗaɗe kyauta sannan za a bayar da ragowar kuɗaɗen a matsayin bashi don mutane su gyara gidajensu a yankunan da yaƙi ya lalata.

A Tehran da Karaj, ƙananan hukumomi ne zasu kula da sake ginin, rahotanni sun bayyana yadda suka tuntubi yan kwangila tuni.

Sai dai al'ummar kasar sun bayyana ra'ayinsu da ya bambanta da na mahukunta. Mutanen da gidajensu suka lalace sun bayyana cewar a farkon yaƙi ana saurin dɗaukar matakan gyara gidajen da suka lalace inda tawagar wasu magina ke gaggawar zuwa yankunan da ba a yiwa ɓarna sosai ba.

Amma yayin da rikicin ya yi tsanani kuma aka samu ƙarin gidajen da suka lalace sai aikin ya daina sauri, an daina kulawa da gidaje koda sun bayar da takardun bukatar a duba yanayin da suke ciki. A wasu lokutan ana cewa magidanta su koma su sake ginin gidajensu da kansu dagabaya daga baya sai su kaiwa hukuma shaidar kuɗaɗen da suka kashe don a mayar musu a hukumance.

Akwai iyalan da suke zaune a otal otal bayan gidajensu sun lalace sakamakon yaƙi. A ƙarshen yaƙi an biya wasu magidanta wani kashi na kuɗin ginin gida don su samu damar kama gidan haya.

Rahotanni sun bayyana irin ƙalubalen da masu gidajen haya ke fuskanta, hukumomin Tehran na biyan diyyar lalacewar gidajen ne kawai amma ba sa bayar da taimako don sayen kayan gini ko injina da wata dukiya da aka yi asara sakamakon yaƙin.

Wani mai shago a yankin Chardangeh da ke Karaj ya shaidawa BBC cewar ''Ya miƙa takardar buƙatarsa Hukumar Gidaje amma an ce da shi akwai mabuƙata da dama don haka ya dakata.'' ya jaddada yadda irin lalacewar da wurin aikinsa ya yi ya haifarwa mutane da dama rashin aikin yi.

Wani mazaunin birnin Tehran wanda jirgin sama ya rusawa gidansa ya shaidawa BBC cewar sojoji sun kwashe ɓaraguzai amma ba su gyara masa gidansa ba kuma sun bar wani babban rami da ya hana mutane zama a gidan.

Cikin birane ma al'umma basu gamsu da yadda ake raba diyyar gidajen da aka lalata a yaƙin ba.

Wani mazaunin Isfahan ya shaidawa BBC cewar gidansa ya lalace a lokacin yaƙin kuma ya kai ƙorafinsa gidan gwamna amma bai samu taimako ba.

Diyyar ababen hawa

.

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Ƙididdiga ta bayyana yadda aka lalata sama da motoci 9,000 yayin da kusan babura 600 suka lalace lokacin yaƙin.

Wani masanin inshora a Iran da bai bayyana sunan sa ba ya bayyanawa BBC cewar kusan ababen hawa 19,000 aka lalata a faɗin ƙasar adadin kuɗin diyyar su zai kai tomans tiriliyon 15.

Alhakin biyan wannan diyya na kan Kamfanin Ishorar na Iran kuma tuni ya fara biyan sama da Tomans miliyan 30 a matsayin diyya.

Hanyar da ake bi wajen karɓar diyyar ababen hawa ta dogara da irin inshorar da abin hawa ya mallaka. Masu motoci a Tehran da farko zasu shigar da buƙatar su ofishin ƙaramar hukuma wanda zai miƙawa kamfanin Inshora.

kodayake wasu ganau sun ce da BBC kamfanonin Inshora masu zaman kan su, sun ƙi ɗaukar matakin fara biyan diyya, akwai rahotannin da suka bayyana yadda wasu kamfanonin Inshora suka karye.

Wata majiya daga Kamfanin Inshora na ƙasa ta bayyanawa BBC yadda kamfanonin Inshora masu zaman kansu da dama suke fama da rashin kuɗi. Majiyar ta ƙara da cewa kamfanin Inshora na Iran wanda ke da alhakin biyan diyya na fama da rashin kuɗi.