KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Lahadi 03/05/2026

Wannan shafi ne da ke muku Labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Lahadi 03/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Peter Obi ya tabbatar da ficewa daga jam'iyyar ADC

    Obi

    Asalin hoton, Peter Obi/X

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023, kuma jigo a jam'iyyar ADC ta masu haɗaka, Peter Obi ya tabbatar ficewa daga jam'iyyar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Peter Obi ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar.

    Mista Obi ya ce rigimar da ya yi ƙoƙarin guje wa a tsohuwar jam'iyyarsa ta LP, ta sake kunno kai a cikin sabuwar jam'iyyar da ya shiga ta ADC.

    Ya kuma bayyana cewa ya ɗauki matakin ne ba don wani shugaba ko jigo a cikin ADC ya ɓata masa rai ba.

    ''Ban ɗauki matakin saboda shugaban jam'iyyar, David Mark ko Atiku ko wani jigo a jam'iyyar ya yi min wani abu ba'', in ji shi.

    Jam'iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci, wanda yanzu haka ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda Nafi'u Bala ya shigar da ƙarar tsagin David Mark da cewa ba halastattun shugabanni ba ne.

    A makon mai ƙarewa ne Koton Kolin ƙasar ta ce ɓangarorin biyu su koma babbar kotun tarayyar domin ci gaba da shari'ar.

    Tun a cikin makon ne kuma ake ta raɗe-raɗin cewa Peter Obi da Kwankwaso za su fice daga jam'iyyar ADC zuwa NDC, kodayake kawo yanzu ba su tabbatar da hakan ba.

    Shi ma kwankwason a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce yana tuntuɓar abokan siyasarsa domin ɗaukar mataki kan makomarsa a siyasance.

  2. Dole Amurka ta zaɓa tsakanin ci gaba da yaƙin 'da ba zai yiwuwa ba' ko yarjejeniya maras kyau - IGRC

    Sashen tattara bayanan sirri na rundunar juyin juya halin Iran ya ce Amurka na cikin tsaka mai wuya na zaɓin ci gaba da yaƙi, wanda ta bayyana da ''abin da ba zai yiwuwa ba'' ko kuma ta amince da yarjejeniya maras kyau'' da Iran.

    Cikin wata sanarwa da sashen ya fitar ya ce ''lokacin Amurka na ɗaukar mataƙi na ci gaba da ƙurewa''.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa wa'adin da Iran ta bayar kan dakatar da rufe tasoshin ruwanta da kuma matsayin Rasha da China da Turai kan Amurka, da ma wasiƙar Trump ga majalisa da kuma amincewa da sharuɗaɗan Iran duka ba abin da za su haifar.

    ''Don haka dole ne Trump ya zaɓa tsakanin ''ci gaba da kai hare-hare, wanda kuma hakan ba abu ne da zai yiwuwa ba, ko kuma ta amince da yarjejeniyar maras kyau da Iran'', in ji sanarwar.

  3. ADC ta fara sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100

    ADC

    Asalin hoton, ADC

    Jam'iyyar hamayya ta ADC ta fara sayar da fom ɗin takara muƙamai daban-daban gabain babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ta ce jam'iyyar ta saka kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100.

    Sanarwar ta kuma ce jam'iyyar ta fitar da jadawalin zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar, inda za a yi na shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Mayu.

    Jam'iyyar ta kuma saka kuɗin fom ɗin takarar gwamna kan naira miliyan 50, yayin da na sanata ke naira miliyan 20, sai na ɗan majalisar tarayya a kan naira miliyan 10 da ɗan majalisar jiha naira miliyan uku.

    Sanarwar ta kuma bayyana rangwamen kashi 50 cikin ɗari ga matasa, da ragin kashi 25 ga mata da masu buƙata ta musamman.

  4. Iran ta ce a shirye take ga tattaunawa ko komawa yaƙi

    Tutar Iran da Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban jami'in sojin Iran, Mohammad Jafar Asadi, ya ce akwai ''yiwuwar'' sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, sakamakon yadda Trump ya soki buƙatun da Iran ta gabatar don tattaunawar zaman lafiya a baya-bayan nan.

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ambato Asadi, wanda mamba ne rundunar sojin Iran ta 'Khatam al-Anbiya command center' na cewa ''Akwai yiwuwar ɓarkewar sabon yaƙi tsakanin Iran da Amurka, kuma alamomi da dama sun tabbatar da cewa Amurka ba ta shirya wa amincewa da kowane irin alƙawari ko yarjejeniya ba''.

    A wani abu mai kama da wannan, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi ya ce Iran a shirye take ga tattaunawar zaman lafiya ko kuma komawa yaƙin.

  5. Ba za mu yi sulhu da ƴanbindiga a Arewa Maso Yamma ba - Gwamnan Sokoto

    Gwamnan sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ba za su yi sulhu da ƴanbindigar da ke addabar yankin ba.

    Yayin da yake jawabi a wurin bikin ƙaddamar da wani titi da gwamnan Katsina ya gina, Ahmad Aliyu ya ce gwamnonin yankin na yin aiki tare domin kawo ƙarshen matsalar.

    Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai ya shafe shekaru yana fuskantar hare-haren ƴanfashin daji, masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya sa ake tsananta kiraye-kirayen kawo ƙarshen matsalar, ciki har da masu kiran amfani da hanyar sulhu.

    Sai dai gwamnan na Sokoto ya ce ba za su yi tattaunawar sulhu da ƴanbindigar ba.

    “Ba za mu yi sulhu da kowane mai laifi ba, ba za mu amince da duk wata buƙatarsu ba, har sai sun amince za su ajiye makamansu ba tare da kowane irin sharaɗi ba,'' kamar yadda ya jaddada.

    Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatocin jihohin yankin na aiki da jami'an tsaro don kawo ƙarshen matsalar.

    Ya kuma yi kira ga mutane su riƙa bai wa gwamnati da jami'an tsaro haɗin kai wajen fallasa masu kwarmata wa ƴanbingar bayanan sirri, yana mai cewa babu wani harin, yanbindiga da zai gudana ba tare da hadin bakin ƴan garin ba.

  6. Wani ƙaton jirgin dakon mai da zai je Indiya ya wuce ta mashigar Hormuz

    Jirgin dakon mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar kula da fiton kaya da Indiya ta ce wani katafaren jirgin dakon mai ɗauke da fetur da nauyinsa ya kai metric ton 46,313, ya ƙetare mashigar Hormuz a ranar Asabar.

    A cikin wata sanarwa, da ma'aikatar ta fitar ta ce jirgin ɗauke da ma'aikata 20, ana sa ran zai isa tashar jiragen ruwa ta Visakhapatnam a gabashin ƙasar ranar 13 ga watan Mayun da muke ciki.

    Har yanzu dai mashigar ta Hormuz ta kasance a rufe yayin tattaunawar ƙawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran ke cikin halin rashin tabbas.

  7. Maniyyatan Najeriya 50,000 ne za su sauke farali a 2026 - NAHCON

    maniyyata

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON ta ce maniyyatan ƙasar kimanin 50,000 ne za su sake farali a wannan shekara ta 2026.

    Mataimakiyar darakta a sashen yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ce ta bayyana haka a hirarta da BBC.

    A yau ne dai ake fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.

    Fatima Sanda Usara ta ce tuni hukumarsu ta kammala dukkan shirye-shirye da suka kamata don gudanar da jigilar maniyyatan cikin nasara.

    A baya dai ana yawan samun jinkiri a aikin jigilar alhazan Najeriyar a duk shekara, wanda hakan kan sa wasu alhazan su gaza samun damar sauke faralin, sai dai Fatima, ta ce tuni suka ɗauki mataki kan lamarin.

  8. Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum bakwai a Lebanon

    Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan mayaƙan Hezbollah a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar dakatar da wuta.

    Sojojin Isra'ila na ci gaba da rusa gine-gine a kudancin Lebanon, ciki har da wani Cocin Katolika da ke wani ƙauyen kan iyaka.

    Dakarun na Isra'ila sun ce Hezbollah na amfani da ginin domin harba makaman roka zuwa Isra'ila, zargin da Cocin Katolika a Lebanon ya yi watsi da shi.

  9. Amurka ta karɓi daftarin buƙatun Iran 14

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da karɓar daftarin buƙatun Iran domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin ɓangarorin biyu.

    Buƙatu 14 ne ke ƙunshe a daftarin na Iran, ciki har da buɗe tasoshin jiragen ruwanta da Amurka ta datse, da biyanta diyyar abubuwan da aka lalata mata a tsawon yaƙin da kuma sakin kadarorinta da aka riƙe

    Mista Trump ya ce yana nazarin sharuɗɗan da Iran ɗin ta gindaya cikin buƙatun nata, amma ya ce ba lallai ya amince da su ba.

    Kafin yanzu shugaban na Amurka ya ce gwamnatin Iran ta matsu a cimma yarjejeniya, kuma a cewarsa gwamnatin ƙasar ta ragu.

    Yanzu dai Iran ɗin ta ce tana jiran martanin Amurka.

  10. Barkanmu da hutun ƙarshen mako

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza Ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci