Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Lahadi 12/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Lahadi 12/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. "Majalisar Ɗinkin Duniya a shirye take ta yi aiki da Zamfara"

    Mataimakiyar sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Amina Mohammed ta ce yanzzu akwai tituna a Zamfara dan haka hukumomin duniya za su iya aiki da gwamnatin jihar.

    Ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ta kai a ƙaramar hukumar Maru inda daga nan kuma aka yi tattaunawa da ta musamman.

    "A yau Zamfara na da hanyoyi. Kuma nan gaba sai tafi zama wurin da za a shiga ko ina saboda titunan da ake ci gama da ginawa," in ji ta.

    Tace samar da ababan more rayuwa za su ƙara haɓɓaka tattalin arziƙin jihar, tana mai cewa, "yayin da aka kammala ayyukan baki ɗaya, za su farfaɗo da lasuwanci da kuma kasuwannin da ke maƙwabtaka, shi ne fatanmu, sannan za a samu ƙarin zaman lafiya."

    Hajiya Amina ta ce ayyukan da ke tafiya a yanzu sun ƙarawa MDD kwarin gwiwa kan Zamfara.

    Ta kuma jaddada buƙatar sauya tunani kan jihar zuwa na zaman lafiya.

  2. Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

    Manchester City ta ƙara rage yawan makin da ke tsakaninta da Arsenal bayan nasarar da ta samu a wasan da ta fafata da Chelsea.

    Manchester City ta yi nasara kan Chelsea da ci 0-3 a filin wasa na Stamford Bridge.

    Yanzu Manchester City tana da maki 64 a matsayi na biyu, bayan Arsenal da ke ta ɗaya da maki 70.

    City na da wasa guda kwantai da Crystal Palace, wanda aka ɗaga yin shi saboda dalilai a baya, idan City ta ci wasan zai zama saura maki 3 kacal tsakaninta da Arsenal.

    A yanzu haka kuma a makon gobe ne Arsenal ɗin za ta fafata da City a filin wasa na Etihad da ke Manchester.

    Ko da Manchester City ta ci wasan zai zama akwai banbancin kwallo tsakaninta da Arsenal, wanda watakila hakan ya baiwa Gunners damar ci gaba da zama a matsayi na daya a gasar.

    Wasa shida ne ya rage wa Arsenal kuma ta ba da tazarar maki shida, yayin da City wasa bakwai ne ya rage mata.

    Wannan ne kusan karo na uku da Arsenal ke dadewa a saman teburi amma daf da ƙarshen kaka ta fuskanci koma baya.

  3. Za mu toshe mashigar Hormuz - Trump

    Shugaba Trump ya ce sojin ruwan Amurka za su toshe mashigin Hormuz, bayan tashi daga tattaunawa ba tare da cimma wata matsaya ba.

    Cikin wata sanarwa Trump ya ce Amurka za ta kama duk jirgin da ya biya Iran kudi wucewa ta mashigar ruwan da Iran ta rufe.

    Ya kara da cewa sauran ƙasashe za su taimaka wajen sanya shinge ga mashigar.

    Ya bayyana yadda rashin amincewar Iran ta dakatar da shirin makamin nukiliya ya haifar cikas a tattaunawar.

  4. Tottenham har yanzu ba ta sake zani ba

    Tafiyar Tottenham a gasar Premier bana na ci gaba da fuskantar koma baya, biyo bayan kashin da ta sha a hannun Sunderland da ci ɗaya mai ban haushi.

    Da wannan sakamakon Tottenham ta ƙara tabbata a matsayi na 17 a teburin gasar Premier, da maki 30.

    Tun a ranar Juma'a da West Ham ta lallasa Wolverhampton Wanderers Tottenham ta koma matsayin, amma da rashin nasarar da ta yi a yau zamanta a wajen a yanzu ya ƙara tabbata.

    Tun farkon wannan kakar ƙungiyar ta arewacin London ke fama da koma bayan rashin ƙoƙari, wani abu da ya kai su ga sauya masu horaswa a ƙalla guda uku.

  5. Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?

    Tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke, sai maganar mashigar Hormuz ta fara jan hankali, inda mutane suke ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

    Sa'o'i bayan gaza cimma matsaya a tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Pakistan, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta tare "duka jiragen da suka yi yunƙurin wucewa ta Hormuz ko barin mashigar ba".

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da Iran ta ce za ta ci gaba da karɓar haraji ga duk jirgin ruwan da zai bi ta mashigar.

    Cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce ''ganawar da wakilan Amurka da na Iran suka yi a Pakistan ta tafi daidai tun da fari, inda aka amince da sharuɗa masu yawa, amma da aka zo kan batun nukiliyar Iran komai ya rushe, wanda kuma shi ne muhimmi''.

    Kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas na duniya ne ke bi ta mashigar.

    Shin ina ce mashigar Hormuz kuma ya sa take da muhimmanci a wannan yaƙin?

  6. ADC ta saka ranar 12 ga watan Mayu don rantsar da sabbin shugabanninta

    Jam'iyyar ADC ta haɗakar ƴan hamayya a Najeriya ta saka ranar 12 ga watan Mayu mai kamawa a matsayin ranar da za ta rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabanninta a faɗin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar tsagin David Mark, Bolaji Abdullahi, jam'iyyar ta taya murna ga mambobinta da suka gudanar da tarukansu na jihohi domin zaɓen shugabanninta na rassan jihohin, wanda ta ce an gudanar cikin kwanciyar hankali.

    ''Wannan ya nuna muradin jam'iyyar na yin abubuwanta cikin kwanciyar hankali da lumana tare da bin tsarin dimokraɗiyya da martaba doka'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta kuma buƙaci sabbin shugabannin jihohi da aka zaɓa su yi aiki da uwar jam'iyyar ƙarƙashin shugabancin David Mark, domin ƙarfafa jam'iyyar a faɗin Najeriya.

    Tun da farko shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Joash Amupitan ya gargaɗi jam'iyyar kada ta gudanar da tarukan zaɓukan shugabannin nata, yana mai cewa hakan ya saɓa da hukuncin kotun da ya ce ta rushe shugabancin jam'iyyar.

  7. Ba za mu bari duk jirgin da ya biya Iran haraji ya wuce ta Hormuz ba - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta tare "duka jiragen da suka yi yunƙurin wucewa ta Hormuz ko barin mashigar ba".

    Cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Trump ya ce ''ganawar da wakilan Amurka da na Iran suka yi a Pakistan ta tafi daidai tun da fari, inda aka amince da sharuɗa masu yawa, amma da aka zo kan batun nukiliyar Iran komai ya rushe, wanda kuma shi ne muhimmi''.

    Shugaba Trump ya ci gaba da cewa tattaunawar ta kai matakin amincewa da wucewa ta mashigar Hormuz ''amma Iran ta ƙi amincewa da hakan, inda ta ce wai akwai nakiyoyin da ta dasa a wasu wuraren, da babu wanda ya san su sai ita kaɗai.''

    Shugaban na Amurka ya ce ya umarci rundunar sojin ruwan Amurka ta hana duk wani jirgin ruwa da ya biya haraji ga Iran wucewa ta wurin.

    Sannan ya ce sojojin ruwan na Amurka za su fara lalata nakiyoyin da Iran ta dasa a cikin ruwan mashigar.

    "Duk jirgin da ya biya haraji ga Iran ba za mu bari ya wuce lami lafiya ta mashigar ba, kuma duk ɗan Iran ɗin da ya kai mana hari ko kan wani jirgin ruwan zaman lafiya, zai fuskanci fushinmu'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa "nan ba da jimawa ba za mu fara rufe mashigar".

  8. Iran ta ce fiye da mutum 3,300 aka kashe a ƙasar a lokacin yaƙin

    Iran ta ce fiye da mutum 3,300 ne aka kashe tun bayan fara yaƙin ƙasar da Amurka da kuma Isra'ila.

    Alƙaluma daga sashen lafiya na ma'aikatar shari'ar ƙasar - wanda ke ƙarƙashin kulawar fannin shari'ar ƙasar - ya ce kawo yanzu an gano gawarwaki 3,375.

    Sashen ya ƙara da cewa daga cikin wannan adadi, 2,875 maza ne, yayin da gawarwaki 496 suka kasance na mata.

    Lardunan Tehran da Hormozgan da Isfahan ne kan gaba a yawan waɗanda suka mutu.

    Alƙaluman sun nuna cewa ɗaruruwan yara aka kashe, ciki har da jarirai bakwai ƴan ƙasa da shekara ɗaya da 255 masu shekara ɗaya zuwa 12 da kuma 121 masu shekara 13 zuwa 18.

    Rahoton ya ce cikin waɗanda aka kashe har da ƴan ƙasashen Afghanistan da Siriya da Turkiyya da Pakistan da China da Iraƙi da kuma Lebonon.

  9. Ministan cikin gida na Isra'ila ya shiga Masallacin Ƙudus

    Ministan harkokin tsaron cikin gida na Isra'ila, Itamar Ben Gvir ya shiga masallacin Al Aqsa da ke Birnin Ƙudus, domin nema wa masu bautar Addinin Yahudanci babbar dama.

    Al Aqsa - wanda Yahudawa ke ɗauka a matsayin tsarkakken wuri - ya kasance ɗaya daga cikin wurare mafiya tsarki da muhimmanci a faɗin Gabas ta Tsakiya.

    Wata gidauniyar Addinin Musulunci a Jordan ce ke kula da masallacin na tsaron gomman shekaru, bisa sharaɗin bai wa Yahudawa damar ziyartarsa amma ba za su yi ibada a ciki ba.

    A lokacin ziyartar, Mista Ben Gvir ya ce ya ji ''kamar wanda ya mallaki masallacin'' na wurin.

    Wasu na ganin duk wani yunƙuri na ƙalubalantar matsayar da ake kai yanzu game da masallacin daga ɓangaren Isra'ila zai iya haifar da tashin hankali.

  10. An naɗa mace ta farko kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Jamus

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Union Berlin a Jamus ta naɗa Marie-Louise Eta a matsayin kocinta - karon farko da aka naɗa mace matsayin mai horas da wata babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta maza a ɗaya daga cikin manyan gasannin Turai biyar.

    Za ta ja ragamar ƙungiyar har zuwa ƙarshen kaka, bayan sallamar Steffen Baumgart a ranar Asabar.

    Sau biyu kawai Union Berlin ta yi nasara a wasa 14 da ta buga a gasar Bundesliga a bana.

    Eta - wadda ta lashe Gasar Zakarun Turai da ƙungiyar Turbine Potsdam ta mata - ta kasance mataimakiyar kocin Union Berlin tsawon shekara biyu da suka gabata.

  11. Birtaniya ta buƙaci Amurka da Iran su sake shirya 'zaman sulhun'

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Iran da Amurka su ''ƙara lalubo wata hanyar zaman sulhu'' bayan gaza cimma komai a zaman farko da suka yi a Pakistan.

    Fadar Downing Street ta ce a wata tattaunawa da firaministan ya yi da Sultan na Oman, Starmer ya ce ci gaba da tsagaita wutar na da ''mihimmanci'' kuma yana da kyau ''duka ɓangarorin biyu su kauce wa sake tayar da yaƙin''.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da sakataren lafiyar Birtaniya, Wes Streeting ya shaida wa BBC cewa abin ''taikaici'' ne yadda aka tashi a zaman na Pakistan ba tare da cimma matsaya ba.

    Mista Streeting ya kare matakin Birtaniya na rashin shiga yaƙin.

  12. Mu ke da iko da Mashigar Hormuz kuma dole a biya haraji - Iran

    Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Haji Babaei ya ce mashigar Hormuz ta kasance wurin da Tehran ba ta wasa da shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Mehrs mai alaƙa da dakarun juyin juya halin ƙasar ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa Iran ce ke da cikakken iko da mashigar, kuma dole jirage su biya haraji kafin wucewa.

    A ɗaya gefen kuma Shugaba Trump ya dage cewa za a buɗe mashigar ''nan ba da jimawa ba'', kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance bai ambaci mashigar ta Hormuz ba a jawabin da ya yi wa manema bayan tattaunawar da suka ɗauki sa'o'i suna yi da wakilan Iran a Pakistan.

    Muhimmiyar hanyar ruwan, wadda kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wurin - na daga cikin sharuɗɗan tattaunawar.

    Muhimmin sharaɗin da aka saka a tattaunawar shi ne wucewa ta mashigar lami lafiya.

    Tun da farko rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ta ce jiragen sojinta biyu sun wuce ta mashigar a aranar Asabar, kodayake Iran ta musanta iƙirarin.

    Rundunar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗin kai hari kan duk jirgin sojin da ya yi yunƙurin wucewa ta mashigar.

  13. Amurka ta kasa gamsar da wakilan Iran a tattaunawar Pakistan - Ghalibaf

    Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf - da ya jagoranci tawagar wakilan ƙasar a tattaunawar da aka yi a Pakistan - ya ce yanzu lokaci ya yi da Amurka za ta fahimci cewa ''za ta iya sayen imaninmu ko kuma a'a''.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Ghalibaf ya jaddada maganar da ya yi kafin zaman, cewa Iran za ta je tattaunawar ne da ''zuciya ɗaya'', amma saboda abubuwan da suka faru a lokacin yaƙe-yaƙen ƙasar biyu da suka gabata, yanzu ''ba za ta yarda da abokan faɗanta ba''.

    Ya ce tawagar wakilan Iran ''ta nuna muradin cimma matsaya, amma ɗaya ɓangaren ya kasa gamsar da wakilan Iran a wannan tattaunawar''.

    Ghalibaf ya ci gaba da cewa: "Ba za mu yi wani abu da zai rusa nasarar da muka samu ta tsawo kwana 40 na kare ƙasarmu ba.''

    Ya ƙara da cewa sai da tattaunawar ta yi ''ƙarfi'', sannan ya gode wa Pakistan kan ƙoƙarinta na shirya zaman.

  14. Me ya sa Amurka da Iran suka kasa cimma matsaya?

    Wakilan Amurka da na Iran sun tashin baram-baran ba tare da cimma matsaya ba a tataunawar da suka a Pakistan da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke gwambazawa.

    Tun da farko an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar wucin gadi ta mako biyu bisa taimakon Pakistan, inda ƙasashen biyu suka amince da zama domin lalubo hanyoyin da za su kawo ƙarshen yaƙin.

    Ɓangarorin biyu sun gaatar da sharaɗɗan da suke ganin sai an amince da su kafin kawo ƙarshen yaƙin.

    Amurka, wadda ke samun goyon bayan Isra'ila a yaƙin ta gabatar da sharuɗɗa 15, yayin da Iran ta gabatar da 10.

    To sai dai ɓangarorin biyu ba su samu matsaya ba, lamarin da ya sa tattaunawa ta watse ba tare da wata matsaya ba.

    Kafofin watsa labaran Iran ɗin sun rawaito cewa buƙatun da Amurka ta gabatar da suka kira marasa kan gado ne suka hana samun ci gaba.

    Sun ce Amurka ta nemi Iran ta yi watsi da hatta haƙƙinta na samar da shirin nukiliya na farar hula don samar da magunguna da kuma wutar lantarki, wani abu Iran ɗin ta ce ya yi kama da yin saranda ko miƙa wuya.

    Wani abu da ya sake haifar da saɓanin shi ne batun matsayin mashigar Hormuz, da kuma batun tsagaita wuta a Lebanon.

  15. Trump ya halarci wasan kokawa a Miami

    A daidai lokacin da ake tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran a Pakistan, Shugaba Trump ya halarci bikin kokawa a Miami tare da wasu daga cikin iyalansa da jami'an gwamnatinsa, ciki har da sakataren harkokin wajen ƙasar, Marco Rubio.

    Mataimakinsa, JD Vance - wanda ke jagorantar tawagar wakilan Amurka a Pakistan ya ce ya yi ta yin magana da Trump ''akai-akai'' ta waya a lokacin tattaunawar ta Pakistan.

    "Ban san sau nawa muka yi magana da shi ta waya ba, ko sau shida ne, ko sau 12 ne a cikin sa'a 21'', in ji Vance.

    Ya ƙara da cewa: ''Mun riƙa tuntuɓar jina a tawagar tamu, saboda mun je tattaunawar ce da zuciya ɗaya.''

  16. Iran ta yi gargaɗin kai hari kan duk jirgin sojin da ya yi yunƙurin shiga Hormuz

    Dakarun juyin juya halin Iran sun yi gargaɗin kai hari ga duk wani jirgin ruwa na soja da ya yi yunƙurin bi ta mashigin Hormuz.

    Kalaman sun zo ne bayan rundunar sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya ta ce jiragen ruwan sojin Amurka biyu sun wuce ta mashigar, a karon farko tun bayan soma yaƙin.

    Sai dai Tehran ta musanta wannan iƙirari, tana mai cewa ita ce ke iko da mashigar ruwan.

    Tun da fari, Washington ta ce dakarunta sun fara cire nakiyoyi daga mashigar, ikirarin da Tehran ta sake musantawa.

    Wani jami’in sojan Amurka ya ce ƙoƙarin na mayar da hankali ne kan samar da hanya mai tsaro ga jiragen kasuwanci.

  17. Wakilan Iran sun kama hanyar barin Islamabad

    Tawagar wakilan Iran a tattaunawa da Amurka da aka yi a Pakistan ta kama hanyar komawa gida bayan gaza cimma yarjejeniya.

    Kamfanin dillancin labaran Iran Mehr ya ruwaito cewa wakilan ƙasar - ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad-Bagher Ghalibaf - ta fice daga Pakistan da misalin ƙarfe 9:00 na safe agogon Pakistan.

    Ficewar tasu na zuwa ne jim kaɗan bayan tafiyar wakilan Amurka, bayan da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ta gaza.

  18. Wakilan Amurka na kan hanyar gida bayan gaza cimma matsaya a Pakistan

    Tawagar wakilan Amurka, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance, na kan hanyarsa ta komawa Amurka bayan wata doguwar tattaunawa a birnin Islamabad na Pakistan da wakilan Iran ta gaza cimma yarjejeniya don kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Mista Vance ya bayyana tattaunawar a matsayin mai muhimmanci, amma ya ce ɓangaren Iran bai amince da abin da ya kira tayin ƙarshe na Amurka ba.

    Tawagarsa ta gaza shawo kan Iran, ta amince cewa ba za ta samar da makamin nukiliya, ko wasu kayayyaki da za su taimaka mata wajen ƙera makamin ba, wani batu da Iraniyawan suka sha musantawa.

    Kafofin watsa labaran Iran ɗin sun rawaito cewa buƙatun da Amurka ta gabatar da suka kira marasa kan gado ne suka hana samun ci gaba.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.