Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 9 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Sarki Charles III ya nuna damuwa zargin da aka yi wa ƙaninsa Andrew

    Sarkin Birtaniya Charles III ya nuna matuƙar damuwa kan zarge-zargen da ake yi wa kaninsa, Andrew Mouthbatten Winsotr wanda ke da alaƘar da muamallarsa da marigayi Jefrre Epstein wanda aka samu da laifin lalata.

    Wannan na zuwa ne yayin yansanda ke nazari kan wani ƙorafi da wata ƙungiyar da ke adawa da masauratar ƙasar ta yi kan zargin cewa yarima Andrew ya samar da wasu bayanan sirri ga Mista Esptin a lokacin da yake riƙe da muƙamin wakilin Birtaniya kan harkokin cinikayya.

    An tuntubi Mista Mountbatten Windor kan zarge zarge amma ya zuwa yanzu be ce komai ba mid

  2. 'An fara samun barazanar ƙarewar mai a Cuba'

    Kamfanin jirgin sama na Canada ya dakatar da jigilar fasinjoji zuwa Cuba saboda fargabar rashin man jirgi a ƙasar.

    Gwamnatin Trump ta hana kai mai Cuba ta hanyar barazanar ƙaƙaba haraji ga duk ƙasar da ta shigar da mai Cuba.

    Kamfanin jirgin sama na Air canada ya ce zai tura jirage domin kwaso ƴan ƙasar da suka maƙale a can.

  3. Ana neman mutum 50 bayan kifewar kwale-kwalensu a tekun Libya

    Ƴan ci-rani

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana neman mutum 50 ciki har da jarirai biyu, bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tekun Libya.

    Hukumar kula da ƙaura ta duniya ta ce mata biyu 'yan Najeriya ne kaɗai hukumomin Libya suka yi nasarar ceto wa lokacin da kwale-kwalen ya kife a ranar 6 ga watan Fabrairu.

    Haɗarin ya faru ne sa'o'i shida bayan tashin sa daga Al-Zawiya, ɗauke da 'yan ciranin ƙasashen Afirka daban-daban.

    Hukumar ta ƙara da cewa kusan mutum 500 ne aka ba da rahoton sun mutu ko ɓata a tekun na Libya a shekarar nan.

    Yawancin ƴan ci-ranin dai na son tsallakawa Turai domin samun ingantacciyar rayuwa bayan guje wa tashe-tashen hankula da yaƙe-yaƙe da talauci daga ƙasashensu.

  4. Harin Isra'ila ya hallaka mutum uku a Lebanon, in ji jami'ai

    Lebanon

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai a Isra'ila sun ce aƙalla mutum uku aka kashe ciki har da wani yaro a hari ta sama da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon.

    Kafar yaɗa labaran Lebanon ta ruwaito cewa harin ya faɗa kan wata mota a garin Yanouh.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan waɗanda suka kira 'yan ta'adda na ƙungiyar Hezbollah.

    Duk da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi, har yanzu Isra'ila na kai hare-hare kusan kowacce rana kan duk waɗanda ke da alaƙa da kungiyar Hezbullah.

    A ɓangare guda, hukumomin Lebanon sun ce a yanzu lamarin ya fi kama da yaƙin ɓangaren Isra'ila.

  5. Za mu kawar da barazanar ƴanbindiga a Najeriya - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta magance barazanar da ƴanbindiga da ƴan fashin daji ke yi wa ƙasar.

    Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartaswa ta kasa da ke gudana a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce za mu ƙara ƙoƙari domin lalubo hanyoyin ƙarfafa jami'an tsaronmu domin kawar da ayyukan ta'adanci da na ƴan fashin daji.

    “Wannan ce matsalar da ke hana mu barci, amma na tabbatar muku cewa ina da ƙwarin gwiwa za mu yi nasara a kan su, mu kawar da ayyukansu, wannan baƙon al'amari ne, ba al'adarmu ba ce,'' in ji shi.

    Haka kuma Shugaba Tinubu ya yaba wa wasu gwamnonin ƙasar, musamman na jihohin Borno da Katsina da Kaduna kan ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen kare ƴanci da tsaron ƙasar.

  6. 'Tuƙin gaganci ne ya janyo mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar Jigawa'

    ...

    Hukumar kiyaye haɗurra ta Road Safety ta yi karin bayani kan wani mummunan haɗarin mota da ya faru a Jihar Kano, a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama.

    Haɗarin ya auku ne jiya sakamakon adunguren wata babbar mota a kan hanyar zuwa Gujungu ta Jihar Jigawa.

    Lamarin ya rutsa da mutane da dama, inda wasu suka rasu wasu kuma suka jikkata.

    Da farko, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 30. Sai dai Hukumar Road Safety ta ce bayan binciken da ta gudanar, adadin mutanen da suka mutu ya tsaya ne a bakwai.

    Jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kai na hukumar Road Safety reshen Jihar Kano, CRC Abdullahi Labaran, ya shaida wa BBC cewa "bayanan da suka tattara zuwa yanzu sun nuna cewa gudun wuce kima da tukin ganganci ne suka haddasa hatsarin."

    Ya ƙara da cewa "saboda yawan mutanen da suka jikkata, an raba su zuwa asibitoci huɗu domin samun kulawar gaggawa."

    Rahotanni na nuna cewa ana yawan samun haɗurran mota a manyan titunan Najeriya wanda ake danganta hakan da rashin kyawun tituna da tuƙin ganganci, da kuma gudun da ya wuce kima da masu ababen hawa ke yi.

    Masana dai na ganin cewa wajibi ne hukumomi su ƙarfafa tsare-tsaren da za su inganta yadda ake tuka ababen hawa a ƙasar da ke da yawan al’umma da miliyoyin ababen hawa. Haka kuma, suna jaddada buƙatar gina hanyoyi masu kyau da tsari a sassan ƙasar, kafin a iya samun raguwar haɗurran mota.

  7. Iran ta kama manyan jagororin masu ra’ayin kawo sauyi bayan zanga-zangar ƙin jininta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Iran na cewa cikin 'yan kwanakin nan, an kama yawancin 'yan kungiyar masu ra'ayin kawo sauyi, a wa ni mataki da ake ganin gwamnati na maida martani kan masu zanga-zangar ƙin jininta da aka yi a watan da ya gabata.

    A yau Litinin an kama mai magana da yawun ƙungiyar Javad Emam, da jagoran su Azar Manzouri da wasu mutum biyu inda ake tsare da su a wani wuri da ba a bayyana ba.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jami'an Amurka da na Iran sun hau teburin tattaunawa domin cimma matsaya kan shirin makamin nukiliyar Iran.

  8. Dole ne a cire shugaban INEC - Sheikh Jingir

    Sheikh Jingir

    Asalin hoton, SHEIKH SANI YAHAYA JINGIR FANS/FB

    Shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana kasancewar Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya matsayin kasada.

    Yayin da yake jawabi a ƙarshen bitar kwana uku da ƙungiyar Izala ta shirya a a birnin Jos, Sheikh Jingir ya ce Musulman Najeriya ba su amince da naɗin Amupitan a atsayin shugaban INEC ba, kamar yadda Jardiar Daily Trust ta ruwaito.

    Amupitan na fsuaknatr suka tsakanin Musulman ƙasar kan wata takarda da ya rubuta shekarun baya kan ƙorafin kisan ƙare dangin da ake yi wa Kiristocin ƙasar.

    Sheikh Jingir ya ce shugaban INEC ya taɓa zargin Musulmai da kisan ƙare dangi a kan Kiristoci a fili, don haka bai kamata a ba shi muƙamin da ya shafi muhimman ayyuka kamar na INEC ba.

    “Me yasa mutumin da ya zagi Sheikh Usman Danfodio da Musulmai a kuma naɗa shi shugaban INEC?” in ji Sheikh Jingir.

    Sheikh Jingir ya yi mamakin shiru da ‘yan Majalisar Dokoki suka yi kan wannan al’amari, inda ya yi kira su tabbatar an yi adalci wajen naɗin shugaba mai gaskiya ga hukumar.

    A baya-bayan nan ma Majalisar Ƙoli kan harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ta yi kiran cire shugaban na INEC saboda wannan zargi.

    Duk da gwamnatin Tinubu ta musanta zargin kisan kiristoci a ƙasar, har yanzu ba ta mayar da martani kan kiran cire Amupitan daga muƙamin ba.

  9. 'Za mu hukunta masu saɓa wa dokokin tuƙi a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan'

    Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa FRSC reshan Legas ta gargaɗi direbobi, ciki har da masu tuƙa motocin tsaro da nagwamnati da kada su yi tuƙi a hanyar da ba ta dace ba ko bi ta hannu ɗaya kan babbar hanyar Legas–Ibadan, tare da jaddada cewa duk wanda ya saɓa wa dokokin tuƙi zai fuskanci hukunci yayin da ake ci gaba da gyaran gadar Kara.

    Kwamandan hukumar, Kehinde Hamzat, ya bayar da wannan gargaɗi ne a ranar Litinin yayin da yake hira manema labarai a wajen taron cinkoso na ababen hawa a wannan hanya.

    Ya ce, “Ba daidai bane kuma za mu dinga ɗaukar bayanan duk wanda ya saɓa wa dokokin tuƙi kuma mu kai ƙara ga hukumomin ya suka dace.”

    Hamzat ya ƙara da cewa hukuncin da hukumomin su ke bayarwa sau da yawa ya fi wanda FRSC ke bayarwa tsanani.

    Wannan gargaɗi na zuwa ne a lokacin da cunkoson ababen hawa ya ƙaru saboda gyare-gyaren da ake yi a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

    A makon da ya gabata, FRSC ta sanar cewa gyaran zai ɗauki akalla watanni biyu.

  10. An kama gungun masu aikata laifukan batsa da yara a Senegal

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Hukumomin Senegal sun kama mutum 14 da ake zargin suna cikin wata ƙungiyar masu aikata laifuka ta duniya da ake zargin tana aikata laifukan batsa da yara, wacce ake ganin tana da alaƙa da Faransa.

    A cewar wata sanarwar ‘yan sanda, waɗanda aka kama dukkansu ‘yan ƙasar Senegal ne.

    Ƙungiyar ta kasance tana aiki tun shekarar 2017.

    An zarge su da “batsa da yara da sayar da yara da fyade kan yara ƙasa da shekara 15 da lalata yara ta jima’i, da kuma nufin yaɗa cutar HIV/Aids.”

    Ana zargin suna tilasta wa yara maza yin jima’i ba tare da kariya ba da maza da dama da galibinsu ke ɗauke da cutar HIV, sannan su ɗauki bidiyo.

    An ce huɗu daga cikin waɗanda ake tuhuma suna aiki “ne bisa umarnin wani ɗan Faransa da aka kama a ƙasar a watan Afrilun 2025.”

    An gurfanar da mutum 14 da aka kama a gaban alƙali a ranar Jumma’a, bayan an gudanar da bincike a unguwanni da dama a Dakar da birnin Kaolack, kilomita 200 kudu-maso-gabas daga babban birnin.

    Sanarwar ‘yan sandan ta ce an gudanar da gagarumar ssamame tare da haɗin kan hukumomin Faransa da

  11. IPOB ta janye dokar zaman gida duk ranar Litinin a gabashin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar da janye dokar zaman gida da ake gudanarwa duk ranar Litinin a duk fadin gabashin Najeriya, farawa daga Litinin, 9 ga Fabrairun 2026.

    A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun IPOB, Emma Powerful ya fitar, Kanu ya bayar da wannan umarni ne domin ɗalibai su koma makaranta kuma ‘yan kasuwa da sauran hukumomi a yankin Igbo su gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ko tsangwama ba.

    Sanarwar ta ce duk wanda bai yarda da wannan saƙo ba zai iya zuwa gidan yarin da Nnamdi Kanu yake tsare a jihar Sokoto domin jin hakan daga bakin sa.

    Sanarwar ta bayyana cewa duk mutum ko ƙungiyar da ke kiran a ci gaba da dokar zaman gida, suna karya umarnin Kanu, kuma za a ɗauke su a matsayin maƙiyan ci gaban gabashin Najeriya.

    Haka kuma, sanarwar ta nuna cewa babu wani gwamna da ke da hurumin barazanar rufe ko lalata kasuwanci, tare da cewa za su mayar da martani ga gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra ko duk wani gwamna da ya yi irin wannan barazana.

    A gefe guda kuma, bidiyon da aka saki na dakarun ƙungiyar Ipob waɗanda ake zargin su ne ke tilasta aiwatar da dokar zaman gida, sun bayyana cewa an soke dokar a sauran sassan Najeriya.

  12. Shugabannin duniya sun taya Sanae Takaichi murnar nasara a zaɓen Japan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen duniya na ta aikawa da saƙon taya murna ga firaiministar Japan, Sanae Takaichi bayan nasarar data samu a babban zaɓen ƙasar da aka gudanar.

    Jam'iyyarta ta Liberal Democratic, ta samu nasara da kashi biyu bisa uku na kujerun 'yan majalisar wakilan ƙasar.

    Yanzu suke da gagarumin rinjaye a majalisar dokokin ƙasar hakan ne kuma zai ba wa ƙasar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya ta fuskar dimokraɗiyya.

    Shugaba Trump ya ce matakin Takaichi na kira da a gudanar da zaɓen share fage babbar dabara ce.

    Shi kuwa takwaranta na Indiya Narendra Modi ya yi maraba da sakamakon, Inda ya ce zai bai wa Takaichi damar ƙara faɗaɗa muradunta a ƙasar.

  13. Ana zanga-zanga kan gyaran dokar zaɓe a Najeriya

    ...

    An fara zanga-zanga a Abuja, babban birnin tarayya kan gyaran dokar zaɓe a Najeriya yayin da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago ke zargin Majalisar Tarayya da tauye dimokuraɗiyya ta hanyar ƙin amincewa da ƙudirin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na'ura.

    Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da ‘yan majalisa suka ƙi amincewa da wani sashe na gyaran Dokar Zaɓe da zai tilasta tura sakamakon zaɓe daga rumfunan kaɗa ƙuri’a ta na'urar da jama’a za su iya gani.

    Masu sukar matakin sun ce hakan na rage gaskiya da sahihanci a zaɓuka, tare da dawo da fargabar maguɗin zaɓe.

    Ƙungiyoyi da dama sun bayyana shawarar a matsayin cin amanar amincewar jama’a.

    Masu zanga-zangar sun fara taruwa a kusa da harabar Majalisar Tarayya a Abuja, yayin da ake fargabar cewa gangamin na iya yaɗuwa zuwa wasu jihohin ƙasar.

    Ƙungiyoyin farar hula da masu goyon bayan jam’iyyun adawa na cewa wajabta tura sakamakon zaɓe ta lantarki muhimmin mataki ne wajen kare ƙuri’ar jama’a a ƙasar da ake yawan samun ce-ce-ku-ce kan zaɓe.

    ...

    Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta gargaɗi cewa ƙin saka tanadin tura sakamakon zaɓe ta na'ura a doka na iya janyo zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da ƙara rashin amincewar jama’a da tsarin zaɓe.

    A halin da ake ciki, Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da kiran zaman gaggawa a ranar Talata, 10 ga Fabrairu, a lokacin da take fuskantar matsin lamba daga jama’a da kuma suka kan yadda ake gudanar da gyaran Dokar Zaɓe.

    ...
  14. An yanke wa ɗan adawar Hong Kong hukuncin shekaru 20 a gidan yari

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An yankewa wani mai rajin kare mulkin Dimokradiyya a Hong Kong, Jimmy Lai, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 20.

    Wannan ne dai hukunci mai tsauri da aka taba yankewa wani a yankin a ƙarƙashin dokar data shafi ɓangaren tsaro wadda China ta ce ta zama dole saboda zaman lafiyar yankin.

    An samu Lai wanda ke da shekaru 78 da haihuwa kuma ɗan ƙasar Birtaniya da laifin haɗa baki da ƙasashen waje.

    Iyalansa sun ce hukuncin ya yi tsauri, yayin da Taiwan kuma ta ce an hana mata 'yancin hukunta masu riƙe da muƙmai.

  15. Tinubu ya karɓi baƙuncin shugaban dakarun Amurka na Afrika

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin shugaban rundunar sojin Amurka a Afirka AFRICOM, Janar Dagvin Anderson, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Lahadi, 8 ga Fabrairu 2026.

    Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara tattaunawa kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro a yankin.

    A taron, Janar Anderson ya zo ne tare da tawagar AFRICOM da ta haɗa da Muƙaddashin Jakadan Amurka a Najeriya, Keith Heffern, Babban Mai Ba da Shawara kan Harkokin Waje na AFRICOM, Ambasada Peter Vrooman da ƙarin mutum ɗaya.

    Shugaba Tinubu ya karɓi tawagar tare da manyan jami’an gwamnatinsa da suka haɗa da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu da sauransu inda aka tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da musayar bayanan sirri.

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Ziyarar ta AFRICOM na nuni da ƙudirin ɓangarorin biyu na ci gaba da aiki tare domin inganta tsaro da daidaita ayyukan horo, da kuma tallafa wa ƙoƙarin Najeriya na dawo da zaman lafiya a sassan da ke fama da rikici.

    Gwamnatin Najeriya ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da ƙasashen abokai wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

    ...

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

  16. Fafaroma Leo ya nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Leo XIV ya nuna damuwa kan jerin hare-haren da ake ci gaba da kai wa a sassan Najeriya, inda ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka tare da buƙatar hukumomi su ɗauki ƙwararan matakai domin kare rayuwakan al’umma.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Fafaroman ya ce ya samu labarin hare-haren da ke “cike da baƙin ciki da damuwa,” yana mai cewa an kai hare-haren ne kan al’ummomi daban-daban lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa.

    “Na samu labarin hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomi a Najeriya wanda ya haifar da mummunar asarar rayuka, wannan labarin na da matuƙar baƙin ciki da damuwa. Ina miƙa addu’ata da ta'aziyya ga dukkan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankali da ta’addanci,” in ji Fafaroman.

    Ya ƙara da cewa yana fatan “hukumomin da abin ya shafa za su ci gaba da aiki da cikakkiyar jajircewa domin tabbatar da tsaro da kare rayuwar kowane ɗan kasa.”

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar munanan hare-hare a wasu sassan Najeriya, inda jihar Kwara ta fi fuskantar mummunan haron ƴanbindiga.

    A tsakanin ranakun 3 zuwa 4 ga Fabrairun 2026, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ƙauyukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, abin da mazauna yankin suka bayyana a matsayin kisan kiyashi.

    Rahotanni sun nuna cewa mutum 162 ne suka mutu, sai dai jami’an yankin da waɗanda suka tsira daga harin na cewa adadin wadanda aka kashe ya haura 200, yayin da ake ci gaba da gano gawarwaki a dazukan da ke kewaye da yankin.

    Amma kuma, ‘yan sanda da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, sun tabbatar da mutuwar musulmai 75.

    Biyo bayan harin, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin tura ƙarin sojoji zuwa yankin.

  17. Bukatunmu kan gyaran dokar zaɓen Najeriya - El-Rufai

    ...

    Gyara ga dokar zabe na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya, inda yan'adawa suka ce tilas ne majalisar dattawan ƙasar ta amince da amfani da na'ura wajen aika sakamakon zabe nan take ta intanet.

    Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC, ya ce suna son a amince da dokar zaɓen da Majalisar Wakilai ta amince.

    Amincewa da gyaran dokar zaɓen da majalisar dattawan Najeriya ta yi ne ya haifar da cecekuce a Najeriya musamman kan cire sashen da ke wajabta tura sakamakon zaɓe nan take ta na'ura.

    Yan'adawa da ƙungiyoyin farar huka sun soki majalisar dattawan Najeriya da ƙin amincewa da gyaran sashen da zai tilasta aika sakamakon zaɓe ta na'ura.

    "Tura sakamako ta na'ura dole ne a dawo da shi, kuma dole ne a ce hukumar zaɓe ta yi aiki da shi."

    "Kuma lokacin da aka bayar na zaɓe a duba a rage shi domin ya yi yawa kuma yana wahalar da jam'iyyu da ƴantakara," in ji Malam Nasir El-Rufai.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.