Jerin sunayen mutum 25 da suka rasu a hatsarin jirgin soji a jihar Ondo
Rundunar sojin saman Najeriya ta saki sunayen mutum 25 da ta ce su ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu da ya faru ranar Litinin a jihar Ondo.
Hukumomi sun ce jirgin yana kan wani aiki ne na yau da kullun daga Benin zuwa Legas lokacin da ya faɗi kusa da sansanin sojojin ruwa a safiyar Litinin.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa jirgin ya faɗi kusa da wani kurmi kuma an gano tufafi da takalma a wurin. Ana iya ganin hayaki yana tashi daga yankin.
Rahotanni a baya sun nuna cewa mutum 32 ne suka rasu.
Rundunar ƙarƙashin babban hafsanta, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ta bayyana sunan mutum 25, a shafinta na X a ranar Talata da suka hada da matuƙan jirgin biyar da fasinjoji 20. Rundunar ta ce ba a samu wani wanda ya tsira da ransa ba.
Matuƙa da ma'aikatan jirgi
- Squadron Leader MI Aburime
- Squadron Leader AP Man-Ugwueje
- Flight Lieutenant IS Bako
- Warrant Officer Abubakar A (Mai gyaran jirgi)
- Corporal Uguru HC (Mai gyaran jirgi)
Fasinjoji
- Flight Lieutenant TL Lazarus
- Flight Lieutenant M Akinloye
- Flying Officer IM Adeshina
- Master Warrant Officer Onwuka F
- Master Warrant Officer Matini BA
- Warrant Officer Nuhu FS
- Flight Sergeant James RB
- Flight Sergeant Mohammed AI
- Sergeant Ani AE
- Sergeant Izibenikien SI
- Sergeant Alafuka C
- Sergeant Mbadugha AN
- Lance Corporal Ugwuba FC
- Lance Corporal Eledan GE
- Mrs Ezeh Nneka
- Godstmine Tarabina
- Joy Micheal
- Sunday Micheal
- Ukeme David
- Gideon Omotola