Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Badriyya Tijjani Kalarawi, Usman Minjibir da Ahmad Tijjani Bawage

  1. An samu wani mutum da laifin kashe ɗiyarsa da wuƙa

    A samu wani mutun da laifin kisan kai bayan ya yi iƙirarin cewa ƴarsa ta mutu a wani 'haɗari mai ban mamaki" yayin da ta wasa da wuƙa.

    Scarlett Vickers, ƴar shekara 14, ta mutu ne a gidansu da ke Darlington a watan Yuli bayan ta samu rauni mai zurfin inci 4 a ƙirjinta.

    Simon Vickers ya yi iƙirarin cewa ya haddasa mummunan rauni a lokacin da suke 'wasa da wuƙa', amma wani masanin ilimin ƙwayoyin cuta ya shaidawa kotun Teesside Crown cewa “a zahiri ba zai yiwu ba” wuƙar da aka jefa kamar yadda wanda ake tuhuma ya yi ikirari ta yi sanadiyar mutuwar matashiyar ba.

    Alƙalin kotun ya ki amincewa da bayanin mutumin mai shekara 50.

    Za dai a yanke masa hukunci a watan Fabrairu.

    Kotu dai ta ji cewar Scarlett ta mutu ne a gidansu da ke titin Geneva bayan an caka mata wuka a ranar 5 ga Yuli. Iyayenta ne kaɗai sauran mutanen da suka kasance a wurin da lamarin ya auku.

  2. An kama dan kwallon Belgium Nainggolan bisa zargin safarar hodar iblis

    An kama ɗan wasan ƙwallon ƙafa ɗan ƙasar Belgium Radja Nainggolan a wani ɓangare na bincike kan safarar hodar iblis.

    Ɗan wasan mai shekaru 36, yana ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ƴansandan Belgium ne suka kama a safiyar ranar Litinin, bayan wasu samame daban daban da aka kai a faɗin ƙasar.

    "Binciken ya shafi bayanan da ake zargin an shigo da hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa Turai, ta tashar ruwa ta Antwerp, da kuma sake rarraba shi a Belgium," in ji ofishin mai gabatar da ƙara na Brussels a cikin wata sanarwa.

    Babu wani ƙarin bayani da aka bayar ga jama'a.

    Kamen dai na zuwa ne kwanaki shida kacal bayan da Nainggolan ya dawo daga ritaya ya kuma koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lokeren a rukunin na biyu na gasar Belgium.

    Ya zura ƙwallo a wasansa na farko, inda ya bai wa ƙungiyarsa maki a wasan da suka tashi 1-1 gida da K. Lierse.

    Ɗan wasan tsakiyan ya shafe yawancin rayuwarsa a Italiya, inda ya taka leda a Roma da Inter Milan. Tsakanin 2009 da 2018, ya buga wasanni 30 a tawagar ƙasar Belgium.

  3. Ƴan tawaye da sojoji na ci gaba da gwabza faɗa a Jamhuriyar Kongo

    Ana ci gaba da gwabza Ƙazamin faƊa a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yayin da Ƴan tawaye da sojoji ke musayar wuta.

    "Abin da muke ji kawai [shi ne] harbe-harbe a kewayen birnin," wani mazaunin Goma, wanda ke maƘale a gidansa tun Ƙarshen mako, ya shaida wa BBC.

    Mazauna yankin sun yaɗa bidiyo na ƴan tawayen M23 da ke sintiri a manyan titunan birnin Goma bayan farmakin da suka yi a ranar Lahadin da ta gabata kan sojojin Kongo wanda ya sanya dubban mutane suka tsere zuwa garuruwan da ke makwabtaka da birnin.

    Ƴan tawayen sun ce su ne ke iko da birnin amma hukumomin Kongo sun musanta hakan. Wata ɗan jarida a garin Goma Prosper ta shaida wa BBC cewa an yi artabu tsakanin sojoji da ƴan tawaye a sassan birnin. "Muna cikin matuƙar damuwa," in ji shi.

    Ƙungiyar M23 ta karɓe iko da gidan rediyon RTNC reshen Goma, kamar yadda gidan rediyon Okapi da Majalisar Dinkin Duniya ke ɗaukar nauyinsa ta ruwaito.

    Wata mazauniyar Goma mai suna Lucie ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa tana ɓoye a ƙarƙashin gadonta saboda ta firgita. "Muna iya jin harbe-harbe a wajen gidajenmu, ba za mu iya fita ba."

    Wannan lamari dai na zuwa ne sa'o'i bayan da ministan harkokin wajen DR Congo ya zargi makwabciyarta Rwanda da kaddamar da yaƙi ta hanyar tura dakarunta zuwa kan iyaka domin tallafawa ƙungiyar M23.

    Ƙasar Rwanda ba ta musanta goyon bayan ƙungiyar M23 ba, sai dai tana zargin mahukuntan Kongo da goyon bayan mayakan sa kai a yunƙurin hambarar da gwamnati a Kigali.

  4. Manhajar DeepSeek ta China ta haifar da ruɗani a kasuwannin Amurka

    Hannun jarin manyan kamfanonin fasahar ƙere-ƙere na Amurka sun rikito bayan da aka samu saurin bunƙasar wani kamfani na ƙirƙirarriyar basira mai rahusa da wani kamfanin China ya ƙera.

    'DeepSeek app', wanda aka ƙaddamar a makon da ya gabata, ya wuce abokan hamayyarsa ciki har da OpenAI ta ChatGPT don zama manhaja mafi sauƙin saukewa kyauta a Amurka.

    Manyan kamfanonin fasahar Amurka da suka haɗa da Nvidia da Microsoft da Meta duk sun ga faduwar farashin hannun jarin su ranar Litinin.

    A wani ɓangaren kuma, DeepSeek ya ce a ranar Litinin za ta takaita yin rajista na wani ɗan lokaci saboda "manyan munanan hare-hare" a kan manhajar sa.

    Rahotanni na nuna cewa, an ƙirƙiri DeepSeek chatbot ne da wani kaso na farashin abokan hamayyarsa, inda sanya alamar tambaya game da makomar mamayear da Amurka ta yi wa ƙirƙirarriyar basirar AI da kuma girman jarin da kamfanonin Amurka ke shirin sanyawa a ɓangaren fasahar.

    A makon da ya gabata, kamfanin OpenAI ya shiga cikin rukunin wasu kamfanoni waɗanda suka yi alƙawarin saka hannun jari na dala biliyan 500 (£ 400bn) don gina abubuwan inganta fasahar AI a cikin Amurka.

    A ɗaya daga cikin sanarwarsa ta farko tun bayan komawarsa karagar mulki, Shugaba Donald Trump, ya bayyana yunƙurin a matsayin "aikin inganta fasahar AI mafi girma a tarihi" wanda zai taimaka wajen tabbatar da Amurka a matsayin jagorar fasahar a duniya.

  5. An yanke ruwa da lantarki a Goma, in ji hukumar agaji

    Hukumar ba da agaji na cocin Katolika a Ingila da Wales, Cafod, ta kwatanta lamarin da ke faruw a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo a matsayin "mai muni".

    "Ma'aikatan mu da ke can sun faɗa mana cewa an katse ruwa da lantarki kuma farashin kayan abinci na ci gaba da tashi. Sun ce birnin an rufe birnin baki-ɗaya saboda faɗa da ake gwabzawa," in ji sanarwar hukumar.

    Cafod ta ƙara da cewa ana buƙatar jin-kai cikin gaggawa a Goma.

    "Jami'an mu na taimako da abin da suke da shi kuma za mu ƙara yawan agaji da muke bayar wa nan take. Muna kira ga duka ɓangarori da su tabbatar da cewa an ba da hanyar cigaba da kai agaji Goma," in ji ta.

  6. Hukumar Hisbah ta kuɓutar da ƴan mata da aka yi yunƙurin safararsu

    Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kuɓutar da wasu ‘yan mata 15 waɗanda aka yi yunƙurin safararsu zuwa ƙasashen waje.

    Hukumar ta ce an gano yaran ne waɗanda dukkansu ƴan mata ne a tashar mota a cikin birnin Kano.

    Rahotanni na cewa masu safarar mutane na amfani da nacewar da ƴan ƙasar ke yi na sai sun fita ƙasashen waje neman rayuwa mai daɗi suna saka su a ƙangin bauna ta zamani.

    Hukumar ta HISBA ta ce ta samu wannan nasarar ce yayin wani samame da jami’anta suka kai wata tashar mota.

    Hukumar ta ce yaran masu ƙananan shekaru an kuɓutar da su ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin yin safararsu zuwa Legas.

    Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne kwamandan Hisba na Kano ya kuma shaidawa BBC cewa "Mun samu rahoto na wani kamfani da ya yi yunƙurin fitar da mata zuwa ƙasar Saudia, mun kuma miƙa shugabannin kamfanin da muka kama a hannun jami'an hukumar yaƙi da safarar mutane domin gudanar da bincike."

    BBC ta yi ƙoƙarin jin ƙarin bayani daga hukumar ta NAPTIP ofishin jihar Kano, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.

    Safarar mutane musamman ƴan mata wata babbar matsala ce da aka jima ana yi a Najeriya.

    Kwamared Hafizu Sanka muƙaddashin kodinatan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'Adam ta duniya ofishin jihar Kano, ya ce safarar mutane na ƙaruwa.

    "Daga bayanan da muka samu, waɗanda ake safararsu suna shan baƙar wahala, har ma wasu suna tuntuɓarmu don a mayar da su Najeriya."

  7. KACRAN ta buƙaci hukumar raya yankin arewa maso gabas ta inganta harkar kiwon dabbobi

    Ƙungiyar Fulani makiyaya a Najeriya ta Kulen Allah (KACRAN) ta yi kira ga hukumar raya yankin arewa maso gabas da ta ci gaba da yin tsare-tsaren da take yi na ganin an inganta harkar kiwon dabbobi da kuma daɓɓaka cigaban yankin na arewa maso gabas.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar wanda ya samu sa hannun shugabanta, Khalil Moh’d Bello, KACRAN ta yaba wa hukumar ta NEDC bisa ƙoƙari wajen ganin an samu zaman lafiya da sake ginda al'ummomi da kuma taimakawa makiyaya, inda ya kwatanta hukumar a matsayin abin koyi.

    "Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta kawo cigaba sosai, ciki har da ƙoƙarinta na ganin shugabancin da za a shigar da kowa-da-kowa," in ji sanarwar ƙungiyar.

    Har ila yau, KACRAN ta yaba wa haɗin gwiwar da hukumar ke yi da ƙananan hukumomi da kuma jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya, wanda ta ce yana da matukar muhimmanci domin ɗorewar ci gaba a yankin.

    "Muna kuma yaba wa NEDC kan rawa da take takawa wajen kai agaji a bala'o'i da ake samu, musamman ma iftila'in ambaliya a Maiduguri da kuma ƙoƙarinta wajen sake gyara makarantu da asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji," in ji ƙungiyar.

  8. Sama da mutum 200,000 suka shiga arewacin Gaza cikin sa'o'i biyu, in ji jami'ai

    Sama da mutum 200,000 waɗanda aka ɗaiɗaita ne suka koma arewacin Gaza a kafa cikin sa'o'i biyu bayan buɗe mashigar yankin, a cewar wani jami'in tsaro a Gaza yayin magana da kamfanin dillancin labarai na AFP.

    An buɗe shingayen binciken motoci da misalin karfe 9 na safe agogon yankin, inda bayan sa'o'i biyu kuma aka sake buɗe wa masu shiga ta kafa hanya - sai dai, wakiliyar BBC Rushdi Abualouf ta ruwaito cewa an samu jinkiri wajen buɗe wa motoci hanya.

    AFP ya kuma ce gwamnati a Gaza ta ɗauki mutum sama da 5,500 domin taimaka wa wajen mayar da waɗanda aka ɗaiɗaita zuwa gida.

    Gwamnati ta kiyasta cewa mutane a birnin Gaza da kuma arewaci na buƙatar tantuna 135,000 da kuma masu kula da su yayin da suke komawa gidajensu da aka lalata.

  9. Shugabannin DR Congo da Rwanda za su gana kan rikicin M23

    Shugaba William Ruto na Kenya, ya ce shugabannin kasashen Rwanda da Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo za su gana domin tattaunawa kan kazamin yakin da ya barke tsakanin sojojin Congo da na 'yan tawayen M23.

    Ruto na magana ne bayan lamura sun kara yamutsewa a kasar, inda mazauna Goma ke ba da rahotannin jin karar harbe-harbe.

    Paul Kagame da Félix Tshisekedi sun amince su halarci taron gaggawar da za a gudanar a ranar Laraba mai zuwa kan rikicin.

    Gwamnatin Congo ta jima ta na zargin Rwanda da taimakawa 'yan tawayen na M23, zargin da Kigali ta musanta.

  10. Labarai da dumi-dumi, Takwas daga cikin 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su sun rasu

    Rahotannin da ke fitowa daga Isra'ila kan halin da wadanda Hamas ke garkuwa da su ke ciki, da ake sa ran sakinsu a mako mai zuwa na cewa wasu daga ciki sun rasu.

    Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila David Mencer, ya ce cikin farar hula 33 da suka rage a hannun Hamas, 25 ne kadai su ke raye. Hakan na nufin 8 daga cikin Isra'ilawan da ke hannun Hamas sun rasu.

    Ya kara da cewa a yanzu za a sako 18 daga cikinsu a makonni masu zuwa, kuma tuni an sanar da iyalan mutanen kan halin da ake ciki.

  11. Fashewar nakiya ta janyo mutuwar mutum guda a Neja

    Wata dattijuwa ta rasa ranta bayan fashewar nakiya a kauyen Sabon Fegi na karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja.

    Fashewar ta kuma janyo lalacewar gidaje 12.

    Shugaban karamar hukumar ta Mashegu, Umar Jibril ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce akwai waɗanda suka samu munanan raunuka.

    "Mutum shida da suka jikka na can suna karɓar kulawa a babban asibiti da ke Kainji," in ji Umar.

    Ya ƙara da cewa suna ci gaba da bincike kan abin da ya faru, kuma tuni aka aika sojoji zuwa yankin.

  12. Komawar Falasɗinawa Gaza babbar nasara ce - Hamas

    Hamas ta ce komawar Falasɗinawa zuwa arewacin Gaza babbar nasara ce ga masu yunkurin ɗaiɗaita ƴan yankin.

    "Komawar waɗanda aka ɗaiɗaita babbar nasara ce ga al'ummar mu da kuma ya nuna kasawa ko shan kaye ga masu shirin ɗaiɗaita da kuma mamaye yankin," in ji ƙungiyar yayin da aka buɗe mashigar komawa a yau.

    Takwarar Hamas, Islamic Jihad, ta kira hakan da "martani ga dukkan waɗanda suka yi shirin ɗaiɗaita al'ummar mu".

    A ranar Lahadi da daddare a Isra'ila, Firaminista Netenyahu ya ce buɗe mashigar na zuwa ne bayan da Hamas ta sauka daga matsayinta kan sakin Arbel Yehud wadda ta kasance cikin ƴan ƙasar da aka yi garkuwa da su.

    "Hamas ta yi amai ta lashe kuma za ta cigaba da sakin ƙarin waɗanda ta yi garkuwa da su a Alhamis ɗin nan, 30 ga watan Janairu," kamar ofishin Netanyahu ya bayyana a shafin X.

  13. Mawaƙi 2Face ya tabbatar da cewa sun rabu da matarsa Annie

    Duniyar mawaƙa da masoya wakoki har da ƴan ba ruwanmu ce ta girgiza lokacin da fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya sanar da batun rabuwa da matarsa jarumar fina-finai, Annie Idibia.

    Ranar Lahadi 26 ga Janairun 2025, fitaccen mawaƙin ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa shi da matar shi da suka yi zaman auren shekara 10 ba sa tare, suna jiran lokacin da saki zai tabbata tsakaninsu.

    "Abin da zan faɗa kaɗan ne, amma ainihin bayanin mai tsawo ne. Mun jima ba ma tare da Annie Macaulay, a yanzu mun shigar da buƙatar saki."

    2Baba ya yi alkawarin fitar da sanarwa ba da jimawa ba, domin ya bayyana abin da ya faru daga ɓangaren shi da har ya kai ga batun saki tsakaninsa da Annie.

    Tun da fari, 2Baba ya musanta batun rabuwa da matarsa bayan ɓullar labarin.

    Amma daga baya ya yi amai ya lashe, inda ya tabbatar da hakan.

  14. Dubban mutane sun tsere daga birnin Goma yayin da faɗa ya kazance

    Dubban mutane sun tsere daga birnin Goma na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo yayin da faɗa ke cigaba da kazancewa.

    Garuruwa da dama da ke wajen birnin, sun zama kufai babu kowa, wanda kuma ke ɗauke da mutum 300,000 da aka ɗaiɗaita, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

    An toshe hanyoyi da dama da za su kai Goma, yayin da aka durkusar da filin jirgin saman birnin da kuma dakatar da aikin jin-kai da kuma kwashe mutane, in ji MDD.

    Lamarin na cigaba da tsananta a daidai lokacin da aka dakatar da aikin agaji da kuma toshe hanyoyin fita daga birnin.

    Tun shiga 2025, an tilasta wa mutum sama da 400,000 tserewa gidajensu a arewaci da kuma kudancin Kivu, kusa da iyaƙa da Rwanda, a cewar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

  15. Hotunan komawar Falasɗinawa zuwa arewacin Gaza

  16. Tinubu ya buƙaci hukumar FRSC ta kare haɗurran tankokin mai

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar kare hadurra ta kasar FRSC, da hukumomin da ke kula da dokokin kan hanya su dauki matakan kariya kan hadurra da fashewar tankokin mai a kasar, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

    Ana yawan samun hadurran fashewar tankar mai a sassa daban-daban na Najeriya lamarin da ke haddasa mutuwar gwamman mutane da jikkatar wasu da dama baya ga salwantar dukiya.

    Ko a ranar Lahadin karshen mako, wata tankar mai ta fashe a yankin Ugwu Onyeama da ke titin birnin Onitsha na Enugu, inda hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 18 da jikkatar wasu da dama.

    Ana danganta yawan hatsarin motoci a Najeriya kan tukin ganganci da gudu fiye da kima da direbobi ke yi, da rashin kywun tituna.

  17. Colombia za ta kwashe 'yan kasarta daga Amurka

    Amurka ta janye kudurinta na lafta haraji kan kayan da Colombia ke shigar wa kasar, bayan Bagota ta amince ba tare da wani sharadi ba, na tasa keyar 'yan ciranin kasar zuwa gida.

    Tun da fari shugaba Donald Trump ya bada umarnin sanya harajin kashi 25 cikin 100 na kayan Colombia, bayan shugaba Gustavo Pedro ya ki amincewa jiragen sojin Amurka biyu dauke da 'yan cirani sauka a kasar a ranar Lahadi.

    Shugaba Petro, ya ce zai amince 'yan kasar su koma gida cikin mutunci a jirgin farar hula, ba jirgin sojin Amurka kamar wadanda suka aikata muggan laifuka.

    A yanzu fadar White House ta ce Colombia, ta amince a maida 'yan ciranin a jirgin sojin kasar ba tare da bata lokaci ba, za kuma a yi la'akkari da mutunta 'yan kasar ya yin wanna aiki.

  18. 'Yan tawayen M23 sun karbe ikon birnin Goma na DR Congo

    'Yan tawaye a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sun ce sun karbe iko da birnin Goma da ke gabashin kasar, amma gwamnati ba ta tabbatar da ikirarin ba.

    Mazauna Goma sun wallafa hotuna da bidiyon yadda mayakan M23 ke sinitiri a titunan birnin, bayan dannawar da suka yi Goma tare da cin galaba kan sojojin Congo.

    Dubun-dubatar farar hula ne suka tsere daga birnin Goma a jiya Lahadi, zuwa garuruwa makofta.

    An dauki sa'o'i ana musayar wuta tsakanin sojojin Congo da 'yan tawayen, rahotanni sun bayyana cewa titunan birnin mai hada-hadar jama'a sun yi tsit babu motsin kowa.

    Wannan na zuwa ne, bayan ministan harkokin wajen Congo, ya zargi Rwanda da kaddamar da yaki a kasarsa ta hanyar tura sojoji iyakar kasar domin taimakawa 'yan tawayen M23, zargin da Rwanda ta musanta.

  19. Kwankwaso ya caccaki 'yansandan Kano kan barazanar kai hari

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga rundunar ƴansandan Najeriya su dinga amfani da ƙwarewa, da kaucewa bayanan da ka iya tada hankali yayin gudanar da ayyukansu, musamman a jihar.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, hakan na zuwa ne bayan damuwar da aka nuna kan sanarwar 'yan sandan jihar Kano na yiwuwar za a kai harin ta'addanci a jajibaren bikin Mauludin da mabiya ɗarikar Tijjaniyya suke gudanarwa a duk shekara, da aka shirya yi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.

    Kwankwaso ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ƙara da taya mabiya ɗarikar Tijjaniyya da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Sarki Sanusi Lamido Sanusi II, kan nasarar yin taron Maulidin lami lafiya.

    A makon da ya wuce ne dai, rundunar 'yansandan jihar Kano ta fitar da sanarwar gargaɗi kan barazanar kai harin ta'addanci a jihar, da buƙatar a dakatar da bikin Maulidin da yake tara ɗaruruwan mutane daga sassan jihar da jihohi makofta.

  20. An gano gashin tsuntsu a cikin injin jirgin da ya yi hatsari a Koriya ta Kudu

    Masu bincike, sun gano shaidar gashin tsuntsu a jirgin saman da ya yi hatsari a Koriya ta Kudu a watan Disambar 2024, inda mutane 179 suka mutu.

    An gano gashin da kuma alamun jini a cikin injinan jirgin saman mallakin kamfanin Jeju. Gashin ya yi kama da wani tsuntsu mai yanayi da agwagwar ruwa kamar yadda masu binciken su ka bayyana da kuma aka wallafa rahoton a ranar Litinin.

    Binciken da ake yi kan musabbabin hatsarin jirgin mafi muni da Koriya ta Kudu ta fuskanta a dan tsakanin nan, zai maida hankali kan rawar da tsuntsun ya taka ta hanyar shigewa cikin injin Jirgin a lokacin da ya fadi.

    Za dai an cire injin jirgin samfurin Boeing 737-800, da kankaren da ke kan titin jirgin domin sake gano karin bayani kan hatsarin jirgin saman.