‘Yan Sanda sun tabbatar da mutuwar mutum takwas sakamakon harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Wadanda lamarin ya rutsa da su, jami’an tsaron sa-kai ne da ke aikin sintiri a kauyen ‘Yandoto.
Bayanai na cewa wannan yanki yana fama da matsalar ‘yan bindiga wadanda suke aukawa mutane, inda ko makonni biyu ma da suka gabata sai da aka kashe mutane da dama.
Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun rasa rayukansu ne lokacin da suka yi yunkurin kai dauki, kasancewar an shaida musu cewa yan bindiga za su kai hari garin.
Wani mazaunin Yandoto ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis tsakanin karfe goma zuwa goma sha daya na dare.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar wannan hari.
Duk da irin kokari da hukumomi ke cewa suna yi na kakkabe matsalar tsaro a jihar Zamfara, ga alama har yanzu da sauran rina a kaba, saboda ko makonni biyu da suka gabata sai da 'yan bindigar suka aukawa mutanen garin na Yandoto lokacin da suke sallar asuba, inda suka kashe mutane da dama ciki har da limamin masallacin sannan suka kuma yi garkuwa da ƙarin wasu mutane.
Bayanai na cewa mutanen garin na Yandoto suna yawan kai wa hukumomi koken cewa a kai musu karin jami’an tsaro, saboda sun yi iyaka da wani yanki na jihar Katsina, inda ‘yan bindiga ke tsallakawa suna kai musu farmaki, saboda sulhun da suka yi a wancan bagaren.