Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 03/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 03/01/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ake dawowa domin kawo muku wasu sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Amurka za ta jagoranci Venezuela har zuwa lokacin kafa gwamnati - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta ja ragamar gwamnatin Venezuela har zuwa lokacin da al'amura za su daidaita tare da miƙa mulki ga gwamnatin da za a kafa.

    Da safiyar yau Asabar ne Trump ya sanar da kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro da mai ɗakinsa a wani ''mummunan'' hari da Amurka ta kai ƙasar.

    Kawo yanzu dai bayanai na cewa Mista Maduro na New York inda zai fuskanci shari'a kan zargen-zargen safarar miyagun ƙwayoyi.

  3. A shirye ɓangaren adawa yake don karɓe ragamar Venezuela - Jagorar adawa

    Jagorar adawar Venezuela, wadda ta taɓa lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, Maria Corina Machado ta ce lokacin samun ƴancin ƙasarta ya yi.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na sada zumunta Ms Machado ta ce a shirye ɓangaren adawa yake ya karɓi ragamar jagorancin ƙasar.

    Ta ƙara da cewa lokaci ya yi da za a maido da doka da oda a ƙasar tare da sakin fursunonin siyasa.

    Ms Machado ta ci gaba da cewa tun da farko ƴan Venezuela sun zaɓi Edmundo Gonzalez a matsayin halastaccen shugabansu a za ben ƙasar da ya gabata, don haka yanzu lokaci ya yi da zai karɓi ragamar ƙasar.

  4. Fubara ne jagoran APC a Rivers - Yilwatda

    Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Nentawe Yilwatda, ya ce gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ne jagoran jam'iyyar a jihar.

    Yilwatda ya bayyana haka ne ranar Juma'a ta cikin wani shirin siyasa na gidan Talbijin na Channels a Najeriya.

    Shugaban na APC ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ne ya tanadi cewa gwamnonin da jam'iyyar ke mulki a jihohinsu ne jagororin jam'iyyar a matakan jihohi.

    “Don haka a kowace jiha, da jam'iyyarmu ke mulki gwamnonin ne za su ja ragamar jam'iyyar,'' in ji shi.

    To sai dai Yilwatda ya buƙaci gwamnonin su yi aiki tare da duka masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihohinsu.

    A watan da ya gabata ne dai Gwamna Fubara ya koma APC bayan ficewarsa daga PDP.

  5. Maduro da matarsa na kan hanyar zuwa New York - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa na kan hanyarsu ta zuwa New York bayan dakarun Amurka sun kama su a wani hari da suka ƙaddamar.

    Mista Trump ya ce an tuhumi mutanen biyu a wata kotun gunduma a New York, yayain da a yanzu za a wuce da su zuwa babban birnin jihar ta hanyar jirgi mai saukar ungulu da na ruwa.

    "Sun kashe mutane da dama da Amurkawa da yawa, da mutanen ƙasarsu,'' in ji Trump

    A yau ne dakarun Amurka suka kama Maduro da matarsa a wani hari da ta ƙaddamar a ƙasar.

  6. Amurka za ta 'shiga dumu-dumu' cikin harkokin man Venezuela - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya faɗa wa shugaban Venezuela cewa ya miƙa wuya mako guda kafin harin da Amurka ta kai yau tare da kama shi.

    Yayin zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Shugaba Trump ya ce daga yanzu Amurka za ta ''shiga dumu-dumu'' cikin harkokin man Venezuela.

    Ya ƙara da cewa mako guda da ya wuce ya yi magana da Maduro, inda ya shaida masa cewa ''ya kamata ka haƙura ka mika wuya''.

  7. Kama Maduro ya nuna Trump ka iya yin duk abin da ya ce zai yi - JD Vance

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce kamun da jami'an Amurka suka yi wa shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa ya nuna cewa Trump zai iya aiwatar da duk abin da ya ce.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Vance ya ce ''ruwa ya ƙare wa ɗan kada, dole ne yanzu a dakatar da safarar miyagun ƙwayoyi, sannan a maido da man Amurka da aka sace''.

    "Duk abin da Trump ya ce zai yi to lallai zai iya, Maduro zai tabbatar da hakan''.

    JD Vance ya kuma jinjina wa dakarun Amurka kan jajircewar da ya ce sun yi wajen ƙaddamar da harin.

  8. MDD ta yi kira ga Isra’ila ta janye dakatarwar da ta yi wa ƙungiyoyin agaji

    Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya yi kira ga Isra’ila ta janye dakatarwar da ta yi wa ƙungiyoyin bayar da agaji a a Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Mai Magana da yawun babban sakataren ya ce yunkurin Isra’ilar zai ƙara tsananta matsalolin jinkai da Falasdinawa ke ciki.

    Ƙungiyoyin agaji 37 Isra’ila ta dakatar da aiki a Gaza, ciki har da ƙungiyar Doctors Without Borders da Norwegian Refugee Council da ƙungiyar International Rescue Committee.

    Isra’ila ta ce ta dakatar da su ne saboda sun ƙi bayar da haɗi kai kan buƙatar da ta yi cewa su gabatar da bayanan ma’aikatansu, wanda ta ce ya zama dole saboda kare abin da ta kira aiki tare da ƴanta’adda.

  9. Kwankwaso ya barranta kansa daga komawa APC tare da Abba

    Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Injiniya Rabiu Kwankwaso ya barranta kansa daga kiraye-kirayen komawa APC.

    Kwankwaso ya bayyana hakan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya ranar Juma'a.

    Cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, ta ce Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar NNPP kuma ya yi watsi da duk wani labarin sauya sheƙa inda ya ce da kansa zai sanar da matakin gaba.

    Kwankwaso ya kuma yi kira ga mabiyansa su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai a wannan lokaci.

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf zai koma APC.

    Nan da ƴan kwanaki masu zuwa ne ake sa ran gwamnan na jihar Kano zai koma jam'iyyar APC.

  10. Za mu jibge duka dakarunmu don kare ƙasarmu - Venezuela

    Ministan tsaron Venezuela, Vladimir Padrino López ya ce ƙasar za ta gaggauta jibge duka dakarun tsaronta don kare iyakokinta.

    Yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan harin Amurka da kama shugaban ƙasar, Mista López ya yi kira ga dakarun tsaron ƙasar su fuskanci abin da ya kira mummunan hari da ƙasar ta taɓa fuskanta.

    Ya ƙara da cewa Venezuela na biyayya ne ga ''umarnin Shugaba Maduro'', don haka za a jibge duka dakarun ƙasar, don kare martabarsa.

  11. Labarai da dumi-dumi, 'Sojojin Amurka na rundunar Delta ne suka kama Maduro'

    Jami'an Amurka sun shaida wa kafar yaɗa labaran CBS - wadda abokiyar ƙawancen BBC ce - cewa jami'an sojin Amurka na rundunar Delta ne suka kama shugaban ƙasar Venezuela Nicolás Maduro.

    Rundunar Delta ce babbar rundunar sojin Amurka mai yaƙi da ta'addanci.

  12. Gwamnatin Neja ta amince da sake buɗe makarantun jihar

    Gwamnatin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta amince da sake buɗe makarantun furamare da na sakandiren jihar.

    Cikin wata sanarwa da kwamishiniyar ma’aikatar ilimin furamare da sakandiren jihar, Hajiya Hadiza Mohammed ta fitar ta ce an ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi a jihar.

    Sanarwar ta ce za a sake bude makarantun jihar ranar 12 ga watan Janairun da muke cikin domin ci gaba da harkokin koyo da koyarwa.

    Sai dai sanarwar ta fayyace cewa makarantun da suke wurare masu tsaro ne kawai za a buɗe domin ci gaba da karatu.

    Matakin na zuwa ne bayan da jihar Kebbi mai makwabtaka da sanar da sake bude makarantu a ranar 5 ga watan Janairun.

    Cikin watan Nuwamba ne dai jihohin suka sanar da rufe makarantun jihohin sakamakon hare-haren da ƴanbindiga suka kai wa wasu makarantun jihohin hare-hare tare da sace ɗalibai.

  13. Bidiyon yadda aka kai hari Venezuela

    A yau ne Amurka ta ƙaddamarv da abin da ta kira ''manyan hare-hare'' kan Venezuela tare da kama shugaban ƙasar da matarsa tare da ficewa da su daga ƙasar.

    A wannan bidiyon an ga yadda jirage masu saukar ungulu ke ta shawagi a sararin samaniyar ƙasar yayin ake jin ƙarar abubuwan fashewa a tsakiyar babban birnin ƙasar.

  14. Mataimakiyar shugaban Venezuela ta buƙaci a tabbatar da shugaban yana raye

    Mataimakiyar shugaban ƙasar Venezuela, Delcy Rodríguez ta buƙaci tabbacin yana raye daga jami'an Amurka.

    Yayin da take jawabi jim kaɗan bayan harin Amurka, Ms Rodríguez ta ce kawo yanzu gwamnatin Venezuela ba ta san inda shugaban ƙasar da matarsa Cilia Flores suke ba.

    ''Muna so a gaggauta tabbatar mata da cewa dukansu suna nan da ransu'', kamar yadda ta yi ƙarin haske.

  15. Labarai da dumi-dumi, Amurka ta kai hari a Venezuela tare da 'kama' shugaban ƙasar

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa ta ƙaddamar da wani ''mummunan hari kan Venezuela" tare da "kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro" da matarsa.

    Cikin wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka ya ce a lokacin harin an kama Shugaba Maduro da matarsa tare da ficewa da su daga ƙasar.

    Mista Trump ya ce an ƙaddamar da harin ne tare da haɗin gwiwar jami'an Amurka.

    Dama dai Amurka ta jima tana barazanar kai hari Venezuela sakamakon tsamin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.

  16. ‘Muna takaicin yadda gwamnonin PDP ke fita daga jam’iyyarmu’

    Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi allah wadai da matakin da gwamnan jihar Plateau ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar tare da komawa APC mai Mulki.

    PDP ta ce duk da cewa jam’iyyar na cikin wani hali, amma bai kai a ce gwamnoninta suna ficewa zuwa wata jam’iyyar ba.

    Kakakin jam’iyyar ta ƙasa, Hajiya Farida Umar ta shaida wa BBC cewa matakin gwamnan Plateau ya ba su mamaki da takaici.

    ‘’Ita fa jihar Plateau mun karɓeta ne daga hannun APC, don haka wannan ba zai hana mu fitar da wani ɗan takara a zaɓe mai zuwa ba kuma mu yi nasara’’, in ji ta.

    A ranar Juma’a ne dai gwamnan ya sanar da komawa APC bayan ficewarsa daga PDP.

    Matakin na zuwa ne wata guda bayan wasu gwamnonin PDP sun fice daga cikinta.

    Bayan babban zaɓen ƙasar na 2023 dai, jam’iyyar na da gwamnoni 12, to said ai ya zuwa yanzu gwamnoni huɗu kawai suka rage wa jam’iyyar.

  17. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, ta fuskar labarai.

    Kada ku manta za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.