Labarin wasanni daga 18 zuwa 24 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 18 zuwa 24 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Wardley zai dambata da Parker a karshen mako

    An tsara damben boksin tsakanin dan Burtaniya, Fabio Wardley da tsohon zakaran kambun duniya, Josep Parker.

    Da zarar mai shekara 30 daga Ipswich ya yi nasara a wasan, kenan shi ne zai kalubalanci zakaran kambun duniya Oleksandr Usyk a kambun WBO.

    Shin ko Wardley na bukatar yin bugun kwaf daya karo na 19 jimilla, kafin ya kai bante.

  2. Djokovic ba zai buga gasar kwallon tennis ta Paris Masters ba

    Djokovic

    Asalin hoton, Reuters

    Novak Djokovic ya sanar ba zai buga gasar kwallon tennis ta Paris Masters ba da za a fara a farkon mako gobe, sai dai bai fadi dalilinsa ba.

    Sai dai anga Djokovic na dingisawa da ta kai ya hakura da wasan da yake buga wa da Taylor Fritz a Six Kings Salam a makon jiya a Saudiyya.

    Haka kuma mai Grand Slam 24 baya cikin kuzari a karawar da ya yi rashin nasara a hannun Valentin Vacherot a daf da karshe Shanghai Masters ranar 11 ga watan nan.

    Da yake daf ake da karkare kakar tennis ta bana, ana sa ran Djokovic zai shiga ATP 250 da za a yi Girka a watan gobe da wasannin da za a yi a birnin Turin na Italiya.

  3. An samu karin masu kallon MLS da bibiyar gasar a talabijin da kafar sada zumunta

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Gasar kwallon kafa ta Amurka da ake kira Major League Soccer ta sanar cewar ta samu kari masu kallon wasannin ido da ido da masu kallo a talabijin da masu bibiya ta kafar sada zumunta da tarin yawa.

    An samu karin kaso 29 cikin 100 a duk mako da suke zuwa sitadiya, kuma karon farko da a samu karin tarin mabiya MLS a tarihi.

    MLS ta ce matsakaicin wasanni ana samun ƴan kallo sama da miliyan uku a duk sati har da ta kafar sada zumunta.

  4. Saudiya za ta gabatar da gasar tennis ta ATP 1000

    atp

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudi Arabia za ta karbi bakuncin sabuwar gasar kwallon tennis ta ATP 1000 a farko farkon 2028.

    ATP Tour ce ta sanar da haka a dazun nan tare da hadin gwiwar masu zuba hannun jari daga Saudiyya.

    Za a fafata tsakanin yan wasa 56 a jadawalin da za a fara a cikin watan Fabrairu a lokacin da ATP za ta gudanar da kananan wasanni a Doha da Qatar da Dubai da hadaddiyar daulal larabawa.

  5. Messi ya tsawaita ƙwantiraginsa da Inter Miami zuwa karshen kakar 2028

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Inter Miami, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Alhamis.

    Mai shekara 38, ƙyaftin din tawagar Argentina da ta lashe kofin duniya a 2022, zai ci gaba da murza leda a Inter Miami zuwa karshen kakar 2028.

    Messi ya koma buga babbar gasar tamaula ta Amurka a 2023, wanda ya lashe Champions League huɗu da La Liga 10 lokacin da ya buga wa Barcelona wasanni.

    Ana sa ran Messi zai buga wa Argentina gasar cin kofin duniya, domin kare kofin dake hannunta a fafatawar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.

    Wannan tsawaita ƙwantiragi da Messi ya yi, ci gaba ne ga ɗaya daga mamallakan Inter Miami, David Beckham, kuma tun farko ɗan kasar Argentinar ya koma Inter Miami daga Paris St Germain a 2023.

    Wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or takwas zai ci gaba da zama a ƙungiyar har lokacin da za ta koma sabon filin wasanta a Freedom Park a 2026.

  6. Liverpool ta je Jamus ta huce haushi a kan Frankfurt

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta je ta sharara ƙwallo 5-1 a gidan Eintracht Frankfurt a wasa na uku a cikin rukuni a Champions League ranar Talata.

    Liverpool ta ci ƙwallayen ta hannun Hugo Ekitike da Virgil Van Dijk da Ibrahim Konate da Cody Gakpo da kuma Dominik Szoboslai.

    Ita kuwa ƙungiyar Jamus ta zare ɗaya ta hannun Rasmus Kristensen.

    Liverpool ta yi namijin kokarin a wasan, wadda ta yi rashin nasara huɗu a jere a dukkan fafatawa, kafin ta je Jamus.

    Cikin rashin nasarar da ta yi ya haɗa da a hannun Crystal Palace da Galatasaray da Chelsea da kuma Manchester United.

    Liverpool, wadda take ta huɗu a teburin Premier League za ta je Brentford ranar Asabar 25 ga watan Oktoba daga nan ta karɓi bakuncin Crystal Palace a Carabao Cup ranar Laraba 29 ga watan Oktoba a Anfield.

    Ita kuwa Frankfurt za ta karɓi bakuncin St Pauli a Bundesliga ranar Asabar 25 ga watan Oktoba, sannan ta kece raini da Borussia Dortmund a German Cup ranar Talata 28 ga watan Oktoba.

  7. Tonali ya tsawaita ƙwantiraginsa da Newcastle zuwa 2030 lokacin da aka dakatar da shi

    Tonali

    Asalin hoton, Getty Images

    Sandro Tonali ya tsawaita ƙwantiragin ci gaba da taka leda a Newcastle United zuwa karshen kakar 2030 lokacin da aka dakatar da shi kan laifin karya dokar yin caca.

    Ɗan kasar Italiya ya koma Newcastle kan yarjejeniyar kakar biyar kan fam miliyan 55 daga AC Milan a Yulin 2023.

    Sai dai an dakatar da shi wata 10 a cikin watan Oktoba, bayan da hukumar ƙwallon kafar Italiya ta same shi da laifin karya dokar yin caca.

    Haka kuma cikin ƙunshin yarjejeniyar da ya ƙulla, Newcastle za ta iya kara masa wata 12 da zarar ya ci gaba da sa ƙwazo.

  8. Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na tunanin zawarcin dan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (i Paper)

    Manchester United na neman dan wasan Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22. (Mirror)

    A shirye dan wasan gaba na Brazil Endrick yake ya bar Real Madrid a watan Janairu, kuma wakilan dan wasan mai shekaru 19 na aiki kan yiwuwar tafiyarsa aro. (ESPN)

    Dan wasan tsakiya na Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, yana shirin tattaunawa kan sabon kwantaragi da Aston Villa. (Sky Sports)

    Har ila yau Villa a shirye take ta ba dan wasan tsakiyar Scotland John McGinn mai shekaru 31 sabon kwantaragi. (Fabrizio Romano)

  9. An soke wasan La Liga da aka tsara tsakanin Villareal da Barcelona a Amurka

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan Barcelona sun yi murna da aka soke wasan da aka tsara da ƙungiyarsu za ta buga da Villareal a birnin Miamin Amurka.

    Tun farko an tsara yin karawar a filin Hard Rock ranar 20 ga watan Disamba, karon farko da za a buga La Liga a wajen Sifaniya, kuma ɗaya daga babbar gasar nahiyar Turai da aka tsara yi a wajen kasar.

    Magoya bayan Barcelona sun ce ya kamata a ci gaba da buga wasannin lik a cikin gida, kuma duk abinda za a yi ake duban dubban magoya bayan cikin gida.

    Tuni dai hukumar ƙwallon kafa ta Turai ta amince da tsarin da ake jiran Fifa ta sahale.

    Tun daga makon jiya ƴan wasan dake buga gasar suka yi ta zanga-zanga, inda suke ƙin taka leda na dakika 15 a lokacin gasar La Liga - koda yake ba a nuna zanga-zangar da ƴan wasan suka yi ba a talabijin da sakon rashin amincewa da magoya baya suka rubuta a ƙyalle ba.

  10. Chelsea za ta fuskanci Ajax duk da cewa ƴan wasanta da yawa na jinya, Champions League

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea na fama da yan wasan da ke jinya a shirin da take na karbar bakuncin Ajax a Champions League a yau Laraba.

    Watakila Enzo Fernandez ya buga karawar bayan jinyar mako, Benoit Badiashile shi ne na baya bayan da ya ji rauni na shida a Chelsea dake jinya.

    Haka kuma kungiyar Chelsea na fama da rashin da'a, wadda aka bai wa yan wasanta hudu jan kati a wasa shida baya.

    Wasa na uku da za su yi a Champions League kenan tun bayan 2019/20 - a can Netherlands Chelsea ta je ta ci 1-0, amma a wasa na biyu a Ingila sai suka tashi 4-4 a babbar gasar zakarun Turai.

  11. Ko Bayern Munich za ta doke Club Brugge a Champions League?

    Kompany

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai horar da Bayern Munich, Vincent Komfany zai ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar 2029, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare tun farko a 2027.

    Tsohon kociyan Burnley ya lashe kofin Bundesliga a kakarsa ta farko, tun bayan da ya maye gurbin Thomas Tuchel a Mayun 2024.

    Fafatawa ta uku da za su yi a Champions League kenan tsakanin Bayern Munich da Club Brugge tun bayan 2005/06.

    Bayern ce ta ci 1-0 a wasan farko da aka je Belgium sai suka tashi kunnen doki 1-1.

  12. Ko Liverpool za ta doke Frankfurt a gasar zakarun Turai, Champions League

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Liverpool da Arne Slot ke jan ragama ta sha dan karen atisayen tunkarar Eintracht Frankfurt a Champions League da za su kara a Jamus ranar Laraba.

    Frankfurt tana ta 16 a teburin Champions League a wasa biyu da maki uku, iri ɗaya da na Liverpool ta 17, wadda ta yi kasa zuwa mataki na huɗu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Liverpool na fatan komawa kan ganiya, bayan da aka doke ta wasa hudu a jere a bana a dukkan fafatawa daga ciki har da wanda Manchester United ta je Anfield ta ci 2-1 ranar Lahadi.

    Frankfurt da Liverpool za su fuskanci juna karo na biyu tun bayan 1972/73 a Uefa Cup, inda Liverpool ta ci 2-0 a Anfield, sai suka tashi ba ci 0-0 a Jamus a wasa na biyu.

  13. Me kaka son sani kan wasan Real Madrid da Juventus a Champions League

    Mbappe

    Asalin hoton, ge

    Real Madrid za ta karbi bakuncin Juventus ranar Laraba a wasa na uku a Champions League, kuma ƙungiyar Sifaniya za ta fuskanci Juventus wadda ba ta kan ganiya a kakar nan.

    Kungiyar Italiya ba ta ci wasa ba cikin wata daya kuma tana ta bakwai a teburin Serie A da maki 12 da tazarar hudu tsakani da AC Milan mai jan ragama.

    Karo na 22 da za a yi tata burza tsakanin kungiyoyin, inda Real Madrid ta yi nasara 11, Juventus ta ci tara da canjaras biyu.

    Wasan karshe da suka fuskanci juna shine a Fifa Club World Cup a Amurka a bana cikin watan Yuli, inda Real Madrid ta yi nasara 1-0.

    Ƴan wasan Real Madrid:

    Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.Masu tsare baya: Militão, Asencio, Á. Carreras, Fran García da kuma Mendy.masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler da kuma Thiago.Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Endrick, Mbappé, Rodrygo, Gonzalo, Brahim da kuma Mastantuono.

    Tuni golan Real Madrid, Thibaut Courtois ya caccaki shugaban La Liga, Javier Tebas kan amincewa a buga wasan La Liga tsakanin Villareal da Barcelona a birnin Miamin Amurka cikin watan Disamba - ya ce za a raba hankali a gasar.

    Wasan La Liga na farko da za a yi a wajen Sifaniya, kuma hukumar kwallon kafar Turai ta sahale da hakan ƴan wasan Real Madrid da wasu masu buga gasar na zanga zanga kan lamarin kuma Coutois ne ke jagoranci.

  14. Wasa tara da za a buga a Champions League ranar Laraba

    Champions League

    Asalin hoton, ge

    Yau Laraba za a ci gaba da wasannin cin kofin zakarun Turai da za a yi tata burza tara

    • Atalanta da Slavia Prague
    • Athletic Bilbao da Qarabag
    • Bayern Munich da Club Brugge
    • Chelsea da Ajax
    • Eintracht Frankfurt da Liverpool
    • Galatasaray da Bodo/Glimt
    • Monaco da Tottenham
    • Sporting da Marseille
    • Real Madrid da Juventus
  15. Anthony

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun bayyana cewa Tottenham na son yin tayin kusan Yuro miliyan 60 (£52m) domin sayen dan wasan gaban Al-Ahli da Ingila Ivan Toney, mai shekara 29. (Fichajes)

    West Ham na zawarcin akalla 'yan wasa uku, dan wasan gaba, da dan wasan tsakiya da kuma mai tsaron baya a watan Janairu. (Sky Sports)

    Har yanzu Barcelona na bin bashin fam miliyan 138 na kudin saye da sayarwa, ciki har da fam miliyan 36.5 da take bin Leeds United kan dan wasan Brazil Raphinha, mai shekara 28, da fam miliyan 12 da take bin Manchester City kan dan wasan gaban Spain Ferran Torres, mai shekara 25. (talkSPORT)

    Kocin Manchester United Ruben Amorim yana sha'awar sayen dan wasan gaban Barcelona da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37 a bazara mai zuwa. (Star)

  16. Hakimi da Salah suna sahun gaba a ƴan takarar gwarzon Afirka na 2025

    Caf

    Asalin hoton, Getty Images

    Achraf Hakimi da Mohamed Salah suna kan gaba a jerin ƴan takara 10 dake fatan lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon kafar Afirka na 2025.

    Hakimi mai tsaron bayan tawagar Morocco ya bayar da gudunmuwar da Paris St Germain ta lashe kofi uku a Faransa da Champions League a kakar da ta wuce, shi kuwa Salah ya ɗauki Premier League tare da Liverpool.

    Ɗan wasan dake taka leda a Everton, Iliman Ndiaye da na Tottenham, Pape Matar Sarr, waɗanda suka taka rawar da kasashensu suka samu damar samun tikitin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026, suna cikin ƴan takara tare da mai taka leda a Galatasaray ɗan Najeriya, Victor Osimhen, gwarzon a 2023.

    Sauran dake takara sun haɗa da ɗan kasar Kamaru, Andre-Frank Zambo Anguissa da na Jamhuriyar Congo, Fiston Mayele da na Gabon, Denis Bouanga da na Guinea, Serhou Guirassy da ɗan ƙwallon tawagar Moroccan, Oussama Lamlioui.

    Wanda ya lashe ƙyautar a bara, Ademola Lookman baya cikin ƴan takara a bana.

    Masu yin zaɓen sun ƙunshi ƙwararru da hukumar ƙwallon kafar Afirka ta zaɓa tare da ƙyaftin da kociyan tawaga mambobin Caf da za a fayyace ƙwazon ƴan wasa da suka yi tsakanin watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban 2025.

    Sai dai har yanzu hukumar ƙwallon kafar Afirka ba ta fayyace ranar da za a gudanar da bikin ba.

    Masu takarar ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2025:

    Gwarzon ɗan kwallon Afirka: Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli & Cameroon), Denis Bouanga (Los Angeles FC & Gabon), Serhou Guirassy (Borussia Dortmund & Guinea), Achraf Hakimi (Paris St-Germain & Morocco), Oussama Lamlioui (Renaissance Berkane), Fiston Mayele (Pyramids & DR Congo), Iliman Ndiaye (Everton & Senegal), Victor Osimhen (Galatasaray & Nigeria), Mohamed Salah (Liverpool & Egypt), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur & Senegal).

    Mai tsaron raga da ba kamarsa: Yassine Bounou (Al Hilal & Morocco), Aymen Dahmen (CS Sfaxien & Tunisia), Marc Diouf (TP Mazembe & Senegal), Edouard Mendy (Al-Ahli & Senegal), Munir Mohamedi (RS Berkane & Morocco), Stanley Nwabali (Chippa Utd & Nigeria), Andre Onana (Trabzonspor & Cameroon), Ahmed El Shenawy (Pyramids & Egypt), Vozinha (Chaves & Cape Verde), Ronwen Williams (Mamelodi Sundowns & South Africa).

    Kociyan da ya fi taka rawar gani: Bubista (Cape Verde), Moine Chaabani (Renaissance Berkane), Hossam Hassan (Egypt), Krunoslav Jurcic (Pyramids), Mohamed Ouahbi (Morocco U20), Romuald Rakotondrabe (Madagascar), Walid Regragui (Morocco), Tarik Sektioui (Morocco U23), Pape Thiaw (Senegal), Sami Trabelsi (Tunisia).

    Tawagar da ta fi yin ƙwazo: Algeria, Cape Verde, Egypt, Ghana, Ivory Coast, Morocco, Morocco U20, Senegal, South Africa, Tunisia.

  17. Arsenal ta ragargaji Atletico Madrid a Champions League, Arsenal 4-0 Atletico Madrid

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta sharara 4-0 a ragar Atletico Madrid a wasa na uku a rukuni a Champions League ranar Talata a Emirates.

    Tun farko sun yi minti 45 ba ci, bayan da suka je hutu ne suka koma zagaye na biyu ne Gunners ta ɗura ƙwallayen ta hannun Gabriel da Gabriel Martinelli da Viktor Gyökeres, wanda ya ci biyu a fafatawar.

    Ƙwallon farko da Gyokeres ya ci wa Arsenal a Champions League, kuma na farko tun cikin watan Satumba, bayan da ya ci Nottingham Forest, mai uku jimilla a Gunners kafin karawa da Atletico.

    Arsenal, wadda ta haɗa maki tara a wasa uku za ta karɓi bakuncin Crystal Palace ranar Lahadi a Premier League daga nan ta karɓi bakuncin Brighton a League Cup ranar 29 ga watan Oktoba.

    Ita kuwa Atletico Madrid za ta je gidan Real Betis ranar Litinin daga nan ta karɓi bakuncin Sevilla ranar 1 ga watan Nuwamba a La Liga.

  18. Arsenal za ta kece raini da Atletico a Emirates a gasar zakarun Turai, Champions League

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal za ta karɓi bakuncin Atletico Madrid a wasa na uku-uku a rukuni da za su kara a Emirates ranar Talata.

    Karawar Arsenal da Atletico Madrid za a kai ruwa rana, bayan da Gunners ta yi dare-dare a kan teburin Premier League.

    Ita kuwa kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta fara kakar nan da rashin kokari da cin wasa ɗaya daga shida har da wanda ta sha kashi a hannun Liverpool a Anfield a gasar zakarun Turai.

    Sai dai a yanzu haka kungiyar Sifaniya ta yi nasara hudu daga wasa biyar baya har da caskara Real Madrid abokiyar hamayya 5-2 a La Liga da doke Eintracht Frankfurt 5-1 a Champions League – sa dai rabon da Arsenal ta yi rashin nasar tun cikin watan Agusta a hannun Liverpool a Premier League.

    Wannan shine wasa na uku da za su yi a Champions League tun bayan 2017/18, inda aka tashi kunnen doki 1-1 a Emirates, sannan Atletico ta yi nasara 1-0 a Sifaniya.

  19. Manchester City ta ziyarci Villareal a Sifaniya, Champions League

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a kece raini tsakanin Villareal da Manchester City ranar Talata a Sifaniya.

    Manchester City ba ta ji dadi ba da fara kakar bana, bayan rashin nasara biyu a jere a cikin watan Agusta,

    sai dai kawo yanzu ta yi karawa takwas ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa tana kuma ta biyu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Tuni kociyan Villareal, Marcelino ya ce ko kadan wasan ba zai yi musu sauki ba, amma za su sa kwazo har sai an tashi.

    Ita dai Villareal tana ta uku a kan teburin La Liga - wasa na na uku da za a kece raini tsakanin kungiyoyin biyu bayan 2011/12 , inda City ta yi nasara gida da waje da da cin 2-1 a Etihad da dura 3-0 a Sifanifaniya.

  20. Newcastle United za ta kara da Benfica a gasar zakarun Turai, Champions League

    Mourinho

    Asalin hoton, Getty Images

    Jose Mourinho zai je gidan Newcastle United tare da Benfica a gasar ta zakarun Turai ranar Talata.

    Ɗan kasar Portugal mai fatan ɗaukar kofi na 26 jimilla, bayan lashe Premier League uku da League Cups hudu a FA Cup da Europa League lokacin da ya horar a Chelsea da kuma Manchester United, ya san ciki da wajen wasannin ƙungiyoyin Ingila.

    Karo na uku da za su yi wasa a tsakaninsu tun bayan 2012/13 a Europa League, inda Benfica ta yi nasara 3-1 a Portugal da kunnen doki 1-1 a St James Park.