Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/08/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/08/2024

Taƙaitattu

  • Shugaban kwastan ya nuna damuwa kan kutsen jami'ansa a kasuwanni
  • Kamala Harris na yaƙin zaɓe a jiha mai muhimmanci a Amurka
  • Hukumomin jihar Kogi sun buƙaci a yi addu'ar samun ruwan sama
  • Tinubu ya rage yawan tawagar Najeriya a babban taron MDD
  • 'An ceto kwamishinan jihar Anambra da matarsa da aka sace'
  • Jami'an NDLEA sun kama mutumin da ya haɗiyi tarin ƙullin koken
  • Sakataren Wajen Amurka ya sake zuwa Isra'ila, kan yarjejeniyar Gaza
  • Ko YouTube zai iya mayar da Kannywood kan ganiyarta?
  • Na fi Kamala Harris kyan gani a ido - Trump
  • Me ya sa hukumomin zaɓen jihohi ke 'tsawwala kuɗin' fom?
  • Matashiya mai shekara 37 ta kafa gwamnati aThailand
  • PDP ta lashe zaɓen duka ƙananan hukumomin jihar Bauchi

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu yi sallama da ku, a yau, Lahadi, 18 ga watan Agusta, 2024.

    Sai kuma gobe Litinin, 19 ga watan na Agusta, 2024 idan Allah Ya kai mu, da hali za mu sake dawowa.

    Kafin sannan, ni Muhammad Annur Muhammad, nake cewa mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - '' Ba a nuna wa mai ido a tsakar ka sama.''

  2. Kamala Harris na yaƙin neman zaɓe a jiha mai muhimmanci ta Amurka

    Kamala Harris

    Asalin hoton, AFP

    'Yar takarar shugabancin Amurka, ta jam'iyyar Democrat, kuma mataimaliyar shugaban kasar, Kamala Harris na yakin neman zabe a jihar Pennsylvania yau, Lahadi kafin ta nufi Chicago, inda jam'iyyar za ta tabbatar da ita a matsayin 'yar takarar, yayin babban taron jam'iyyar a wannan makon.

    Pennsylvania na daga cikin jihohin Amurka mafiya muhimmanci ga duk wani dan takara, domin jihohi da ba su da alkibila - kowane dan takara zai iya yin nasara a can.

    Ita da abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican, Donald Trump suna ziyarce-ziyarce a Pennsylvania da manyan jihohin arewacin Amurka.

    'Yan jam'iyyar Republican sun bukaci Mista Trump ya ƙara jajircewa a yakin neman zaben nasa to amma yana ci gaba da caccakar Ms Harris.

  3. Shugaban kwastan na Najeriya ya nuna damuwa kan kutsen da jami'ansa ke yi a kasuwanni

    Shugaban kwastan da gwamnan jihar Ogun

    Asalin hoton, NCS/FACEBOOK

    Shugaban hukumar kwastan ta Najeriya, Mr. Adewale Adeniyi, ya nuna bacin ransa a kan duk wani kutse da jami'an hukumar ke yi a kasuwanni, inda ya nuna takaicinsa kan hakan tare da alkawarin magance matsalar.

    Babban Kwanturolan na kwastan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da jawabi kan wannan korafi da Gwamnan jhar Ogun, Dapo Abiodun, ya gabatar masa.

    A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Lekan Adeniran, ya fitar a yau Lahadi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Gwamnan ya yi rokon ne a lokacin da shugaban hukumar kwastan din, ya ziyarce shi a ofis.

    Tun da farko Gwamnan ya roki jami'an hukumar hana fasa-kwaurin da su rika nuna halin ya kamata a kan 'yan kasuwa kan yadda suke shiga kasuwanni suna fasa shaguna da wuraren ajiyar kaya a fadin jihar.

    'Yan kasuwa a jihar, da ke kudu maso gabashin Najeriya na zargin jami'an kwastan da fasa musu shaguna da manyan gidajen ajiyar kayayyakinsu da sunan neman kayan da aka yi satar shiga da su kasar.

    Gwamna Abiodun, ya ce duk da cewa ba za a rasa wasu daidaikun mutane da ke satar shiga da kaya ba, amma ya ce yawancin al'ummar jihar mutane ne masu bin doka.

  4. Sakataren Wajen Amurka ya sake zuwa Isra'ila, kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Anthony Blinken

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya isa Isra'ila don ganin an cimma nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    Ana sa rai zai gana da Firaiminista Benjamin Netanyahu da sauran shugabannin Isra'ila a gobe Litinin, kafin ya wuce Masar jibi, Talata.

    A lokacin wani taro da ya yi da majalisar zartaswa, Mista Netanyahu ya ce Isra'ila ba za ta yi sassauci a batun ba, yayin tattaunawar tsagaita wautar.

    Hamas ba ta halarci taron kwanaki biyu da ya gudana a Qatar ba a makon da ya gabata bayan ta zargi Isra'ila da yin ƙari cikin sharuddan da aka amince da su a baya.

    Jami'an lafiya a Gaza sun sanar da mutuwar aƙalla mutum 16 da suka hada da wasu yara 6 tare da mahaifiyarsu sakamakon sabbin hare-haren Isra'ila.

  5. Hukumomin jihar Kogi sun buƙaci a yi addu'ar samun ruwan sama

    Gona

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Kogi da kungiyar manoma ta Najeriya sun yi kira da a yi addu'o'in samun ruwan sama, sakamakon mummunan kamfar ruwan da ake yi a gonaki da kuma karancin abinci a jihar.

    Kwamishinan aikin gona Mr Timothy Ojomah da shugaban kungiyar manoma, AFAN, na jihar, Salihu Adobayi, su ne suka yi kiran a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, a Lokoja.

    Suka ce tsawon sama da wata daya yanzu babu rwuwan sama, kula illar rashinsa za ta shafi tallafin da gwamnati ta bai wa manoma don bunkasa samar da abinci a jihar.

    Shugaban kungiyar manoman ya ce kafin a shiga wannan yanayin na rashin ruwan, yanayin damunar ya karfafa wa manoma gwiwa a jihar.

    ''Abin takaici yanzu abin da muke fuskanta a fadin jihar shi ne rashin ruwa. Rashin ya shafi dukkanin abubuwan da aka shuka, musamman ma shinkafa fa masara..'' in ji shugaban.

  6. 'An ceto kwamishinan jihar Anambra da matarsa da aka sace ranar Juma'a'

    Chukwuma Charles Soludo

    Asalin hoton, Facebook/Charles Chukwuma Soludo

    Hukumomin jihar Anambra, sun tabbatar da sakin kwamishinan harkokin matasa na jihar, Patrick Aghamba, da matarsa, da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Abuja, ranar Juma'a.

    Jaridar Daily Trust, wadda ta ruwaito labarin ta ce, ta bayar da labarin cewa, an ce ma'auratan na kan hanyarsu ne ta zuwa Abuja domin halartar bikin auren, Ifeatu Adaora, 'yar gwamnan jihar ta Anambra, Chukwuma Charles Soludo, lokacin da aka kama su.

    A lokacin harin an kashe daya daga cikin masu taimaka wa kwamishinan, Kpajie Offia, kamar yadda bayanai suka nuna.

    A wata sanarwa da babban sakataren harkokin yada labarai na gwamnan, Christian Aburime, ya fitar a yau, Lahadi, ya ce bayan sa'a 24 da kwamishinan da matarsa suka yi a hannun barayin, an samu nasarar fito da su.

  7. Jami'an NDLEA sun kama mutumin da ya haɗiyi tarin ƙullin koken domin fita waje

    Jami'an NDLEA

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an hukumar yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, sun kama wani fasinja a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja bayan da aka gano yana da alamun koken a cikinsa.

    A wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar yau Lahadi, ya ce mutumin, Paul Okwuy Mbadugha, mai shekar 54, wanda dan kasuwa ne da zai tafi Vietnam, ya shiga hannun hukumar ne a ranar Litinin 12 ga watan Agustan nan na 2024, yayin da yake shirin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Vietnam, bayan yada zango a Doha.

    Sanarwar ta kara da cewa: ''Bayan kwana hudu da aka sanya shi yana bahaya, Mbadugha ya kasayar da kullin koken 88 da nauyinsu ya kai kilgram 1.171.

    Hukumar ta ce a bahasin da mutumin ya bayar ya ce, shi dan kasuwa ne a Lagos kuma wani abokinsa ne a Isolo, ya ba shi kullin ya hadiye domin kaiwa Vietnam a kan kudi dala 2,000.

    Haka kuma hukumar ta NDLEA ta ce jami'ant sun kama wani babban kulli na na ganyen wiwi da nauyinsa ya kai kilogram 800, da aka boye a kwalayen taliyar yara, da nufin kaiwa kasar Kongo.

    Hukumar ta ce bayn da aka bi diddigin inda kayan ya fito an kama wani mutum mai suna Nnamani Sunday Sunny a kasuwar Alaba International market, a yankin karamar hukumar Ojo, a Lagos.

  8. Netanyahu ya zargi Hamas da yin 'biris' da tattaunawar tsagaita wuta

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya zargi Hamas da yin 'biris' da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da sakin Isra'ilawan da ake garkuwa da su.

    Yayin da yake jawabi a taron majalisar ministocinsa ranar Lahadi, Mista Netanyahu ya ce Hamas ba ta tura wakilai tattaunawar da aka yi a birnin Doha cikin makon da ya gabata ba.

    Ya ƙara da cewa za a ƙara matsin lamba kan ƙungiyar da kuma sabon shugabanta, na tsagin siyasa, Yahya Sinwar.

    Hamas ta ƙi halartar tattaunawar bayan da ta zargi Isra'ila da ƙara sabbin sharuɗa kan waɗanda ta fara gabatarwa.

    Nan gaba a yau ne ake sa rana sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken zai isa Isra'ila a wata ziyara da yake yi yankin Gabas ta Tsakiya a yunƙurin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma tabbatar da sakin Isra'ilawan da ake garkuwa da su a Gaza.

    Ana kallon yarjejeniyar a matsayin yunƙurin kare yankin daga faɗawa cikin rikici bayan kisan tsogon shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran cikin watan da ya gabata

  9. Shugaban riƙon Bangladesh ya alƙawarta tallafa wa Musulman Rohingya

    'Yan ƙabilar Rohingya

    Asalin hoton, Getty Images

    A jawabin tsare-tsaren mulkinsa na farko, sabon shugaban riƙo na Bangladesh, Muhammad Yunus, ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa 'yan gudun hirar Rohingya, wadanda Musulmi ne masu yawan gaske a ƙasar.

    Yayin da yake jawabi ga jami'an diflomasiyya ga wakilan Majalisar Dinkin Duniya a birnin Dhaka, Mista Yunus ya ce Bangladesh na buƙatar ci gaba da aiwatar da ƙudurin ƙasashen duniya na ayyukan jinƙai, don mayar da 'yan ƙabilar Rohingya zuwa Myanmar cikin mutunci da girmamawa tare da kare haƙƙoƙinsu

    'Yan ƙabilar ta Rohingya - waɗanda marasa rinjaye na a ƙasar Myanmar - sun fice daga ƙasar a shekarar 2017, don tsere wa azabtarwar sojojin gwamnatin ƙasar, wani batu da Majalisar Dinkin Duniya ke binciken aikata kisan ƙare dangi a kansa.

    A farkon wannan wata ne aka naɗa Mista Yunus a matsayin sabon shugaban riƙo na Bangladesh bayan zanga-zangar da ta karaɗe ƙasar ta tilasta kifewar gwamnatin ƙasar

  10. Sudan na son aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Jedda

    ..

    Asalin hoton, ...

    Gwamnatin ƙasar Sudan ta ce za ta tura wakilai zuwa Masar domin tattaunawa kan aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Jedda na ƙasar Saudiyya, wadda za ta bayar da damar tsagaita wutar yaƙin basasar ƙasar.

    Kawo yanzu dai ba a saka ranar tattauanwar ba.

    Shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ƙi shiga tattaunawar da Amurka da shirya a birnin Geneva, yana mai cewa a maimakon hakan gara a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Jedda cikin watan Mayu.

    Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF ta ƙunshi bayar da damar shigar da kayan agaji, da mayar da hankali kan tattaunawa da za ta bayar da damar tsagaita wuta na godon lokaci, da kuma shirya tattaunawar da za ta kawo ƙarshen tashin hankalin da ake fuskanta a ƙasar.

  11. Jami'an MDD uku sun ji rauni a wani hari da aka kai kudancin Lebanon

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya uku a kudancin Lebanon sun samu ƙananan raunuka a wata fashewa da ta auku a kusa da motarsu.

    Rahotonni sun ce duka mutanen uku sun koma sansanoninsu bayan harin.

    Cikin wata sanarwa da jami'an UNIFIL - da ke sintiri tsakanin kan iyakokin Lebanon da Isra'ila - sun ce suna cikin motar da ke ɗauke da tambarin Majalisar Dinkin Duniya.

    Majalisar ta ce tana bincike kan lamarin, sannan ta yi kira da babbar murya kan duka ɓangarorin da ke faɗa da juna su daina cutar da jami'an wanzar da zaman lafiya ko fararen hula.

    A baya-bayan nan Isra'ila da Hezbolla sun tsananta hare-hare kan juna, tun bayan harin Isra'ila da ya kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Hezbollah a birnin Beirut cikin watan da ya gabata.

  12. SERAP ta buƙaci majalisun dokokin Najeriya su bayyana kuɗin gudanarwarsu

    Shugabannin majalisun dokoki

    Asalin hoton, Social Media Handle

    Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban majalisar dattawan Najeriya,Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon. Tajudeen Abbas su bayyana ''haƙiƙanin kuɗin gudanarwar'' da ake bai wa mambobin majalisun biyu a kowane wata

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci shugabannin majalisun biyu su bayyana mata cikakkun bayanan kuɗin da majalisun biyu ke kashewa a matsayin kuɗin gudanarwa.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan ƙasar ke ci gaba da tafka muhawara kan yawan kuɗin gudanarwa da ake bai wa 'yan majalisar dokokin ƙasar a kowane wata.

    A makon da ya gabata ne tsohon shugaban ƙasar, Olusegun Obasanjo ya zargi 'yan majalisar da yanka wa kansu albashi da alawus -alawus a ƙasar.

    Lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan ƙasar, inda har wasu 'yan majalisar dokokin ƙasar suka bayyana abin da ake biyansu.

    Ko a makon da ya kamata ma, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila daga jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa ana biyansa naira miliyan 21 a kowane wata a matsayin kuɗin gudanarwar ofishinsa.

    Yayin da ya ce yana karɓar albashin da bai kai naira miliyan guda ba a kowane wata.

    Ƙungiyar ta Serap ta kuma yi kira ga jagororin majalisar dokokin ƙasar su dakatar da yanka wa kansu albashi da alawu-alawus da sunan kuɗin gudanarwar, kamar yadda aka yi zargi.

    Haka kuma ƙungiyar ta kira da a daina sanya wa 'yan majalisar kuɗin gudanarwar da ake zargi cikin asusun ajiyarsu na banki, kai tsaye, bayan da ta yi zargin cewa suna amfani da kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

    Tana mai cewa rashin sanya kuɗin a asusun 'yan majalisun zai bai wa hukumomin yaƙi da cin hanci damar gudanar da bincike idan buƙatar hakan ta taso.

  13. Rundunar 'yansanda Najeriya ta tura ƙwararrun jami'ai don kuɓutar da ɗaliban da ka sace a Benue

    ,,

    Asalin hoton, Nigeria Police/X

    Babban sifeton 'yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin tura ƙarin ƙwararrun jami'an rundunar zuwa jihar Benue don taimakawa wajen kuɓutar da ɗaliban jami'ar da 'yan bingida suka sace a jihar.

    A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka sace ɗaliban jami'ar Maiduguri da ta Jos, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Enugu domin halartar wani taron shekara-shekara.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yansandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce Egbetokun ya bayar da umarnin tura ƙwararrun jami'an da kayan aiki, ciki har da jirage marasa matuƙa da masu saukar ungulu da motocin sulke domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.

    Mista Egbetokun ya kuma yi kira ga mazauna yankin su bayar da bayanan da za su taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban.

    Ya kuma jajanta wa iyalan ɗaliban tare da alƙawarta kuɓutar da su.

    ''Rundunar 'yansanda na tare da iyalai da 'yan'uwan ɗaliban a wannan lokaci na baƙin ciki da damuwa, kuma rundunarmu za ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da waɗannan ɗaliabi'', in ji sanarwar.

  14. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Garin da aka fi haihuwar tagwaye

    A cikin shirin namu na wannan makon - wanda Haruna Shehu Tangaza da Aisha Sheriff Baffa suka jagoranta - akwai tarin labarai masu ƙayatarwa da nishaɗantarwa, ciki har da labarin wani gari da aka fi haihuwar tagwaye da matar da ta sace fuka-fukan kaji.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  15. PDP ta lashe zaɓen duka ƙananan hukumomin jihar Bauchi

    Gwamnan Bauchi

    Asalin hoton, Bala Mohammed/X

    Bayanan hoto, Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed a lokacin ƙaddamar da 'yan takarar PDP

    Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Bauchi, ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar 20 da aka gudanar ranar Asabar 17 ga watan Agusta.

    Shugaban hukumar zaɓen jihar, Ahmed Makama, ne ya bayyana sakamakon a daren da ya gabata a birnin Bauchi.

    To sai dai majiyar BBC da ke jihar ta tabbatar da cewa jam'iyyar APC mai hamayya a jihar ta yi watsi da sakamakon zaɓen tana mai bayyana shi a matsayin ''fashi kan 'yancin masu zaɓe da cutar da tsarin dimokraɗiyya''.

    Yayin wani taron manema labarai da jam'iyyar ta kira sakatariyarta da ke jihar, APCn ta zargi jam'iyyar PDP da jirkita sakamakon zaɓen.

    A watan da ya gabata ma dai, jam'iyyar PDP da ke mulkin jihar Adamawa ta lashe duka zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomin jihar 21.

    Masu rajin kare dimokraɗiyya a Najeriya kan soki yadda tsarin zaɓukan ƙananan hukumomi ke gudana a ƙasar, inda galibi jam'iyyar da ke mulkin jiha kan lashe zaɓe a duka ƙananan hukumomin da ke jihar.

    Wani abu da suka ce yana barazana ga 'yan cin gashin ƙananan hukumomin da Kotun Ƙolin ƙasar ta tabbatar a watan da ya gabata.

  16. Matashiya mai shekara 37 ta kafa gwamnati aThailand

    Paetongtarn Shinawatra

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ms Shinawatra, ta zama matashiya mafi ƙanƙantar shekaru da ta kafa gwamnati a Thailand

    Sabuwar firaiministan Thailand, mai shekara 37 ta kafa gwamnati a Thailand.

    Paetongtarn Shinawatra, ta samu goyon bayan sarki a wajen wani taro a birnin Bankok.

    Hakan ne ya sa ta zama matashiya mafi ƙanƙantar shekaru da ta kafa gwamnati a tarihin ƙasar.

    Ms Shinawatra ta ce za ta ɗauki matakan shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi da matsalar ta'ammalin da miyagun ƙwayoyi, tare da haɓaka ɓangaren lafiyar ƙasar.

    Naɗin nata na zuwa ne a daidai lokacin da aka saki mahaifinta wato tsohon firaiministan ƙasar, Thaksin Shinawatra daga gidan yari, inda yake zaman hukuncin da aka yanke masa kan laifin saɓa ƙa'ida a lokacin da yake kan mulki.

  17. Na fi Kamala Harris kyan gani a ido - Trump

    'Yan takarar Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya ce ya fi babbar abokiyar karawarsa zaɓen ƙasar da ke tafe, Kamala Harris kyan gani a ido.

    Yayin da yake jawabi a taron yaƙin neman zaɓensa a jihar Pennyslvania, mista Trump ya riƙa nuna hoton Harris da ke bayan wata mujalla yana cewa, ko a ido ya fi ta kyan gani.

    Ya ce ''kodayake kyakkyawar mace ce, amma na fi ta kyan gani a ido''.

    A wani yunƙuri na sukar 'yar takarar jam'iyyar Democrats ɗin, Mista Trump ya zargi Ms harris da haddasa mummunan hauhawar farashi a Amurka.

    Haka kuma ya bayyana ta a matsayin mai ra'ayin gurguzu, wadda kuma ya ce ba ta da ''cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa''

    Masu ba da shawara a yaƙin neman zaɓen Trump sun buƙaci ya mayar da hankali wajen bayyana manufofinsa musamman hanyoyin da zai kawo ƙarshen hauhawar farashi da batun baƙin haure a ƙasar.

  18. 'Yansanda Indiya sun hana babban taro a kusa da asibitin Kolkata

    'Yansandan Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a birnin Kolkata na Indiya sun haramta duk wata zanga-zanga da kuma babban taro a kusa da asibitin da aka kashe likita bayan an yi mata fyade a makon da ya gabata.

    Lamarin dai ya janyo zanga-zanga da yawanci mata suka jagoranta domin nuna fushinsu kan cin zarafin.

    M a'aikatan lafiyar ƙasar sun shiga yajin aikin gama gari kan batun.

    Hukumomin yankin da lamarin ya faru sun sanar da wasu matakai da za su samar da kariya ga ma'aikatan lafiya mata.

  19. Tinubu ya rage yawan tawagar Najeriya a babban taron MDD

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shuagabn ƙasa

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanar da rage yawan tawagar wakilan ƙasar da za su halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, da za a gudanar a birnin New York na Amurka cikin watan Satumba mai zuwa.

    Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan ranar Asabar, lokacin wani taron bita da fadar shugaban ƙasar ta shirya wa shugabannin hukumomin gwamnati da ke ƙarƙashin kulawar fadar, kamar yadda kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya bayyana cikin sanarwa da ya fitar.

    Gbajabiamila ya ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa a lokacin tafiye-tafiyen jami’an gwamnatin.

    Da yake ƙarin haske kan ƙudurin, ya ce fadar shugaban ƙasar da hukumomin da ke ƙarƙashin kulawarta, na gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka da ƙa’ida, da kuma bin umarnin shugaban ƙasar, Gbajabiamila ya ce shugaban ya ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da ingantaccen tsari wajen gudanar da gwamnatinsa

    ”Na tattauna da shugaban ƙasa kan wannan, kuma ya sanar da ni cewa za mu ga haka cikin makonni masu zuwa lokacin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York’’.

    Mista Gbajabiamila ya ƙara da cewa a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a ƙasar, an yi maganar rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa, don haka ya ce yanzu kowa na jiran ganin yawan tawagar da Najeriya za ta je da ita taron na Majalisar Dinkin Duniya.

    ”A baya mun sani cewa, wasu na amfani da taron wajen tafiya harkokinsu na ƙashin kai, don haka ne shugaban ƙasa ya bayar da umarnin cewa, a wannan karon duk wanda ba shi da abin yi a taron, to kada ya kuskura ya shigar tawagarmu zuwa Amurka, wannan shi ne umarnin Shugaban ƙasa’’, in shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar.

  20. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan ske kasancewa da ku a wanna rana ta Lahadi.

    Ku biyo mu a wannan shafi domin sanar da ku halin da wasu sassan duniya ke ciki, kamar kullum kada ku amnta da shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawa.