Ana fargabar kashe ƴan banga 70 a harin kwanton ɓauna a Filato
APC ta fara sayar da fom na zaɓukan cike giɓin ƴan majalisu
Ba ruwan Najeriya da gwajin makamin nukiliya - Shettima
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
To jama'a masu bin wannan shafi na BBC Hausa na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau Talata 8 ga watan Yuli, 2025.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah Ya kai mu.
Mu kwan lafiya
Yawan Falasɗinawan da ake kashewa a Gaza ya ƙaru sosai - Red Cross
Ƙungiyar agaji ta duniya ta Red Cross ta ce an samu ƙaruwa sosai ta mutanen da ke jin rauni da kuma waɗanda ke rasuwa a wuraren da ake rarraba kayan agaji a Gaza.
Red Cross ta ce marassa lafiya sun yi wa asibitocin Gaza da tuni aka lalata su yawa tun bayan da ƙungiyar nan mai raba kayan agaji wadda Isra'ila da Amurka ke gudanarwa ta karɓi ikon raba kayan a ƙarshen watan Mayu.
Yawan marassa lafiyan suna fama da raunin bindiga ne.
Ƙungiyar ta Red Cross ta ce a cikin sama da wata ɗaya, ta yi wa marassa lafiya magani a cibiyarta ɗaya tilo da ta rage a kudancin Gaza fiye da yawan waɗanda ta yi wa magani a gaba ɗayan shekarar da ta wuce.
Kotu a Pakistan ta umarci YouTube ya rufe wasu shafuka kan zargin yaɗa labaran ƙarya
Asalin hoton, OTHERS
Wata kotu a Pakistan ta umarci hukumomin shafin sada zumunta da muhawara na YouTube da ya toshe ko kuma ya cire wasu shafuka 27 bayan da gwamnati ta zarge su da saɓa dokar yaɗa labaran ƙarya - dokar da ake ce-ce-ku-ce a kanta.
Jami'an gwamnatin ƙasar ta Pakistan suna zargin shafukan da laifin yaɗa labaran ƙin jinin gwamnati da wasu abubuwa na ɓata suna.
Da yawa daga cikin shafuka na fitattun 'yanjaridar Pakistan da masu sharhi da masu raji waɗanda ke sukar gwamnati ne.
Wasu daga cikin shafukan kuma na da alaƙa da jam'iyyar tsohon firaministan ƙasar ne Imran Khan, da aka ɗaure.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam sun ce gwamnati za ta iya amfani da dokar yaƙi da aikata laifuka ta intanet ta haramta hamayya.
Mutanen da aka kashe a zanga-zangar Kenya sun ƙaru zuwa 31
Hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam ta gwamnatin Kenya ta ce mutanen da aka tabbatar sun mutu a zanga-zangar gama-gari ta jiya Litinin yanzu sun ƙaru zuwa talatin da ɗaya.
Ta ce an kama sama da mutum 500 bayan da wasu da dama suka ɓace.
Wakiliyar BBC ta ce rundunar 'yan sandan Kenyan ta ce ta ƙaddamar da bincike a kan lamarin.
Majalisar ɗinkin duniyar ta yi Allah-wadarai da yadda jami'an 'yansanda suka yi amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima da kuma harsashi a kan masu zanga-zagar.
Vladimir Putin ya zama mai bakin ganga - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara ƙaimi a sukar da yake yi wa shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya zargi Putin ɗin da yin baki biyu.
Lokacin da ya yi magana a fadar gwamnatin Amurka ta White House, Trump ya ce shugaban na Rasha na yin alƙawurran da a ƙarshe ba ya cikawa.
A ranar Litinin, Trump ya ce Amurka za ta tura wa Ukraine ƙarin makamai, lamarin da ya sha bamban da matakinsa na makon da ya gabata na dakatar da tura wasu makamai zuwa Ukraine.
Sai dai Trump ya ce akasarin makaman da Amurka za ta bai wa Ukraine na kare kai ne.
A ranar Juma'ar da ta gabata Ukraine ta ce Rasha ta ƙaddamar da harin sama mafi girma kan biranen ƙasar tun bayan fara yaƙin.
Harin ya faru ne jim kaɗan bayan wayar da aka yi tsakanin Trump da shugaba Vladimir Putin.
Kotun duniya ta ICC ta bayar da sammacin kama wasu shugabannin Taliban a Afganistan
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bayar da sammacin kama wasu manyan shugabannin Taliban a Afganistan, inda take zarginsu da laifin take hakkin ɗan'Adam kan hukunci da suka yankewa wasu mata da ƙananan yara.
Alkalan sun ce akwai hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da zargin shugaban ƙungiyar Taliban, Hibbatullah Akhundzada da babban alƙalin gwamnati Abdul-Hakim Haqqani sun aikata laifin da ake tuhumarsu.
A sanarwar da kungiyar Taliban ta fitar, ta bayyana sammacin na kotun ICC a matsayin mara amfani.
Tun bayan da Taliban ta karɓe iko da gwamnatin Afghanistan a watan Agustan 2021, ta haramta wa 'yan mata zuwa makarantun Sakadandare da jami'a.
Mahara sun kashe mutum uku a jirgin ruwan dako na Girka a tekun Maliya
Mutum uku daga cikin ma'aiakatan jirgin ruwan Girka sun mutu a wani hari da aka kai musu a gaɓar kogin Yemen.
Sojojin Tarayya Turai da ke aikin samar da tsaro a tekun, sun ce aƙalla mutum biyu daga cikin mutanen cikin jirgin sun ji rauni, ciki har da wani ɗan Rasha da ya rasa ƙafa.
An kai wa Jirgin dakon mai suna Eternity C hari ne a jiya Litinin.
Maharan sun yi wa jirgin na Girka ƙawanya da ƙananan jiragen ruwa masu gudu tare da kai ma sa hari.
Ofishin jadakacin Amurka a Yemen ya ce 'Yan tawayen Houthi na Yemen ne suka kai harin, wadɗanda suka zafafa kai hare-hare tun bayan fara yaki tsakanin Isra'ila da Hamas.
Hare-haren da suka ce na goyon bayan Falasɗinawa ne.
Sarkin da ke koyar da yara a makaranta
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
A jihar Osun ta kudu maso yammacin Najeriya wani sarki na yin abin da ba a saba gani ba, inda yake koyarwa a wata makarantar yara marasa galihu.
Yayin da ake yi wa sarakuna kallon masu kare al'ada, yin ayyuka irin na sauran al'umma kamar koyarwa a makaranta, ana ganin tamkar bai dace da su ba.
Sai dai Sarki Adedokun Abolarin ya ce yana son sauya yadda ake tafiyar da mulki ta hanyar inganta rayuwar al'umma ta hanyar ba yara ilimi.
Amnesty ta buƙaci a binciki kashe-kashen Filato da Benue
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare haƙkin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta gudanar da binciken ainihin abin da ya haddasa kashe-kashen da aka samu a jihohin Filato da Binawau da ke tsakiyar ƙasar.
Kiran na zuwa ne bayan wasu ƴanbindiga sun kashe aƙalla ƴan banga 50 a wani harin ƙwanton ɓauna.
An yi wa ƴan bangar jana'izar bai ɗaya a garin Kukawa, yayin da ake fargabar samun ƙarin wasu gawarwaki.
Amnesty ta ce an lalata duka garuruwan a lokacin da aka ƙaddamar da hare-haren, tare da kashe ƙananan yar.
Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi gwamnatin Shugaba Tinubu ta gudanar da binciken musabbabin rikicin.
Hotunan ziyarar shugaban Faransa a Birtaniya
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya isa Birtaniya a ziyarar da ya kai ƙasar karon farko da wani shugaban Faransa ya kai Birtaniya cikin shekara 17.
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Macron ya samu tarba daga Sarki Charles lll, da mai ɗakinsa Sarauniya Camilla.
Asalin hoton, Getty Images
An dai shirya wa shugaban na Faransa tare da mai ɗakinsa, liyafar girmamawa.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yarima William da mai ɗakinsa
Ƴan sanda sun kama mutum uku kan zargi kisan wasu ƴan gida ɗaya kan zargin maita
Ƴansanda a arewacin India sun kama mutum uku bisa hannu a kisan wasu mutum biyar ƴan gida ɗaya bisa zargin mayu ne.
Wani babban jami'i a jihar Bihar ya ce an yi wa mutanen dukan tsiya da sanduna kafin daga bisani a banka musu wuta.
Dama dai maigidan sannan nen boka ne a yankin.
Kawo yanzu ba a tabbatar da abin da ya jawo suka kai wa mutanen hari ba, amma bisa dukkan alamu wata rashin jituwa ce ta haifar da matsalar.
Akwai wani mutum na huɗu da ake zargi da hannu a kisan wanda a yanzu haka ya yi layar zana.
Gwamnatin Najeriya ta ƙayyade shekarun shiga jami'a
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami'o'in ƙasar.
Ministan ilimin ƙasar, Tunji Alausa ne ya bayyana haka ranar Talata a lokacin taron tsara fitar da guraben karatu na 2025 a ƙasar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Za a shigar da ƙa'idar cika shekara 16 a cikin manhajar hukumar JAMB da ke tantance ƙa'idojin bayar da gurbin karatu.
Haka kuma Ministan ya ce za a yi la'akari da ɗaliban da za su cika shekara 16 ranar 31 ga watan Agustan 2025.
A Najeriya ana samun yawan ƙorafi kan bai wa ƙananan yara guraben karatu a jami'o'in ƙasar, wani abu da masana ke cewa zai shafi fahimtarsu da kuma yadda za su iya jure wa wahalhalun karatun jami'a.
JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami'o'i
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami'o'in ƙasar.
Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar da babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.
Haka kuma hukumar ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin sabun gurbi kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100.
An dai samu gagarumar faɗuwa a jarawabar JAMB da aka rubuta a wannan shekara.
Ƴansandan Kenya na amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi ƴansandan Kenya da amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima kan masu zanga-zangar jiya Litinin.
Rahotonni sun ce aƙalla mutum 11 ne ƴansanda suka mutu sakamakon harbin ƴansanda.
Ƴansanda sun yi amfani da harsasai da hayaƙi mai sa hawaye da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati da suka taru a manyan biranen ƙasar, ciki har da Nairobi.
Ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kaɗu da kashe kashen da aka samu da kuma ɓarnata dukiya.
A nata ɓangare rundunar ƴansandan ƙasar ta ce fiye da jami'anta 50 aka raunata a lokacin zanga-zangar.
A watan da ya gabata ma mutum 19 aka kashe a lokacin zanga-zanga kawo ƙarshen muzgunawar ƴansanda.
ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara
Asalin hoton, University of Abuja
Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin aikin da ta ƙudiri aniyar farawa a yau saboda rashin biyan mambobinta albashin watan Yuni.
Tun da farko ƙungiyar ta yi barazanar daina shiga azuzuwan ɗalibai saboda rashin biyansu albashin watan Yunin da ya gabata.
Ƙungiyar ta bayar da wa'adin cewa idan har ba a biya albashin watan a jiya Litinin ba, to za ta dakatar da shiga azuzuwan ɗalibai.
Jaridar Leadership a ƙasar ta ambato, shugaban ƙungiyar reshen Abuja, Dakta Sylvanus Ugoh na cewa an janye matakin ne saboda tuni gwamnati ta fara biyansu albashi.
“Mambobinmu sun fara samun albashinsu na watan Yuni tun a jiya kafin 12:00 na dare, wanda kuma shi ne wa'adin da muka bayar'', in ji shi.
Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati - Radda
Asalin hoton, Dikko Radda/X
Bayanan hoto, Gwamnan Katsina, Dikko Radda
Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi watsi da sabuwar haɗakar ƴan hammayar ƙasar, waɗanda ya bayyana da masu haushin rashin gwamnati a hannunsu.
Yayin da yake jawabi a gidan talbijin na Channels ta cikin shirin Sunrise Daily, Gwamnan ya ce shirin haɗakar ADC ba wani abu ne face tsantsar yaudara.
“Ya kamata mu faɗa wa kanmu gaskiya, lokacin yaudarar mutanen Najeriya fa ya ƙare'', in ji shi.
A makon da ya gabata ne gamayyar wasu ƴan hamayya daga jam'iyyu daban-daban suka haɗe kai ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ADC da nufin ƙalubalantar gwamnatin APC a 2027.
Ƴan hamayyar sun zargi gwamnatin APC da lalata Najeriya da kuma yunƙurin mayar da ƙasar mai bin tafarkin jam'iyya guda.
To sai dai Gwamnan na Katsina ya ƙalubalanci masu haɗakar da cewa me suka yi wa Najeriya a lokacin da suke riƙe da madafun iko.
“Wane ne a cikinsu ba ya cikin gwamnatin da ta gabata? Waye a cikinsu bai taɓa shiga gwamnati ba? Muna sane da irin abubuwan da kowanensu ya yi,” in ji Gwamnan na Katsina.
“Mun san irin abubuwan da suka yi lokacin da suke gwamnati, sai yanzu za su zo suna ɓaɓatu saboda ba sa cikin gwamnati.” a cewar Gwamna Radda.
An amince da maganin cizon sauro na jarirai
Asalin hoton, Getty Images
An amince da amfani da Maganin zazzaɓin cizon sauro na farko da ya dace da jarirai da ƙananan yara kuma ana sa ran ƙaddamar da amfani da shi a nahiyar Afirka nan ba da jimawa ba.
Ya zuwa yanzu mugungunan da ake amfani da su ba a yi su don jarirai ba kuma yana jefa su cikin hadari saboda hantarsu ba ta gama bunƙasa ba.
Yara ƴan Afirka ƴan kasa da shekara biyar ne ke da kaso mai yawa cikin mutum 600,000 da zazzaɓin cizon sauro ke kashewa a kowace shekara.
Bayanan hoto, Ziyarar ce ta farko da wani shugaban Faransa zai kai Birtaniya cikin shekara 17
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai kai ziyarar aiki Biritaniya a yau Talata a wani mataki na yunƙurin kyautata alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.
Wannan ce ziyara ta farko da wani shugaban Faransa zai kai Birtaniya cikin shekara 17.
A baya dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami bayan da Birtaniya ta ƙudiri aniyar ficewa daga ƙungiyar EU.
Za a karrama Mista Macron da wata liyafa a fadar Windsor inda Sarki Charles lll zai jaddada buƙatar ganin Burtaniya da Faransa su yi aiki tare don fuskantar abin da ya kira barazana mai cike da sarkakiya.
Daga bisani a ziyarar, shugaban na Faransa zai gana da firaministan Birtaniya, Keir Starmer, inda ake sa ran za su tattauna hanyoyin daƙile kwararar baƙin haure cikin ƙananan jiragen ruwa daga Faransa zuwa Birtaniya.
An kashe sojojin Isra'ila biyar a arewacin Gaza
Asalin hoton, IDF
Rundunar sojin Isra'ila ta ce a kashe dakarunta biyar tare da raunata wasu biyu a lokacin wani faɗa a arewacin Zirin Gaza.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce dakarun ƙasar sun gamu da ajalinsu ne sakama kon wani bom da aka dasa a gefen titi a yankin Beit Hanoun.
Kakakin Hamas ya ce mayaƙan ƙungiyar sun yi wa sojojin Isra'ila ''illa'' a yankin mai cike da sarƙaƙiya.
A watan da ya gabata ma an kashe sojojin Isra'ila bakwai a kudancin Gaza, a wani lamari mafi muni ga rundunar sojin Isra'ila tun bayan fara yaƙi da Hamas.
Ba ruwan Najeriya da gwajin makamin nukiliya - Shettima
Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za ta ci gaba da aiki da haramcin gwajin makaman nukiliya.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da tawagar hukumar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ƙarƙashin jagorancin sakataren zartarwarta, Dr Robert Floyd, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce Najeriya kamar sauran ƙasashen Afirka da dama na fama da tarin matsaloli na zamantakewa da tattalin arziƙi da suka haɗa da fatara da talauci da sauyin yanayi.
Ya ce yanzu babban abin da ke gaban Afirka shi ne ta ga ta shawo kan matsalolin da ke barazana ga wanzuwarta - na fatara da kuma tasirin sauyin yanayi, amma ba batun mallakar makaman nukiliya ba.
A nasa ɓangaren jagoran tawagar hukumar, Dr Robert Floyd, ya yaba da ƙoƙarin Najeriya wajen cimma muradun hukumarsa.
Sannan kuma ya yaba da shugabancin Najeriya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen bayar da gudummawar rage gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya, kamar yadda ya ce.