Lewis-Skelly ya amince da tsawaita zamansa a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan bayan Ingila, Myles Lewis-Skelly ya amince da tsawaita zamansa a Arsenal.
Matashin mai shekara 18 ya amince da tsawaita zamansa a Gunners na zuwa nan da wasu shekaru masu zuwa.
Tsawaita kwantiragin na zuwa ne bayan ɗan wasan ya haska a kakar wasa da ta gabata, bayan da ya buga wasa 39 a duka karawa.
Ya fara taka wa Arsenal wasa ne a karawar da ƙungiyar ta yi da Manchester City a watan Satumba, daga nan an riƙa amfani da shi a a matsayin ɗanwasan baya daga hagu.
Ƙoƙarin Lewis-Skelly ya sa ya samu shiga tawagar Ingila a karon farko a watan Maris, bayan da a baya ta taɓa bugawa tawagogin ƴanƙasa da shekara 16 da 19.
Ya samu asarar zura ƙwallo a wasan da Ingila ta doke Albania da ci 2-0, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya zura ƙwallo a wasansa na farko a Ingila.
Ƙoƙarin ɗan wasan ya sanya shiga jerin ƴantakarar gwarzon matashin ɗan wasan Premier na 2025, inda yake takarar tare da Morgan Rogers da Liam Delap da Dean Huijsen da Milos Kerkez da kuma Ethan Nwaneri.

















