Muna shirya makaman ƴaki ko da Iran za ta yi mana tutsu - Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka na ci gaba da zuba wa jiragen yaƙinta kayan yaƙi domin sake komawa fagen yaƙi da zarar tattaunawar da ake yi da Iran ta wargaje.
Da yake magana a wata tattaunawa ta waya ga gidan jaridar New York Post a ranar Juma'a, Trump ya ce "za mu ga abin da zai faru a sa'o'i 24 masu zuwa".
"Muna zuba wa jiragenmu na yaƙi makaman da ba taɓa ganin irinsu ba fiye da irin wadanda muke amfani da su wajen lalata abubuwa."
"Idan ba a cimma komai ba to za mu yi amfani da su kuma za mu yi amfani da su da gaske."
Trump ya sake bayyana Iraniyawa da mutanen da "ba su da tabbas kan faɗin gaskiya".
Ana dab da fara tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da Iran ranar Asabar a Pakistan.