Man City ta tabbatar da ɗaukar Reijnders kan fam miliyan 46.5

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labarai na wasanni a faɗin duniya daga 9 zuwa 15 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

  • Real Madrid ta fara da canjaras a Club World Cup
  • Barcelona ta ɗauki golan Espanyol Joan Garcia
  • An fitar da jadawalin sabuwar kakar Premier League
  • An sake buɗe kasuwar saye da musayar 'yanwasa
  • Real Madrid ta sayi matashi Mastantuono daga Argentina
  • Italiya ta naɗa Gattuso sabon kocinta
  • Sabbin dokokin da Fifa ta ɓullo da su a gasar Club World Cup
  • Inter Miami ta Messi ta fara Club World Cup da canjaras
  • Abin da ya kamata ku sani kan Fifa Club Wold Cup 2025

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Liverpool ta amince da ɗaukar Wirtz kan fam miliyan 116

    Florian Wirtz

    Asalin hoton, Getty Images

    Zakarun Gasar Premier, Liverpool sun amince su ɗauki ɗan wasan Jamus, Florian Wirtz kan fam miliyan 116 daga Bayer Leverkusen.

    Da fari kudin ya ƙunshi fam miliyan 100 na sayen ɗan wasan, sai kuma ƙarin fam miliyan 16 idan ƙungiyar na samu cimma wasu nasarori.

    Idan har Liverpool ta biya duka, kuɗin ɗan wasan zai kasance mafi tsada aka saya a tarihi a Birtaniya.

    Yanzu haka ɗan wasan da ya fi tsada a kuɗin sayensa na farko shi ne Enzo Fernandez, ɗan Argentina da Chelsea ta saya daga Benfica a 2023.

    Daga nan sai Moises Caicedo shi ma da Chelsea ta saya daga Brighton kan fam miliyan 100 da farko, wanda ake ganin kuɗinsa zai iya ƙaruwa zuwa fam miliyan 115.

    Cinikin zai kasance mafi tsada da Liverpool ta saya a tarihi.

    A yanzu Darwin Nunez da ta saye daga Benfica kan fam miliyan 64 daga baya ya kai fam miliyan 85 ne ɗan wasa mafi tsada da ƙungiyar ta saya, sai kuma Virgil van Dijk da ta saya daga Southampton 2018.

  2. De Bruyne ya koma Napoli

    De Bruyne

    Asalin hoton, EPA

    Kevin de Bruyne ya kammala komawa Napoli bayan ɗan ƙasar Belgium ɗin ya bar Manchester City a ƙarshen kakar wasa ta Premier League.

    De Bruyne zai yi aiki da tsohon kocin Chelsea da Tottenham ne Antonio Conte bayan cim ma nasarori a City.

    Ya ƙi amincewa da tayin da ƙungiyar Chicago Fire mai buga gasar Major League Soccer ta Amurka ta yi masa, abin da zai ba shi damar buga gasar Champions League a kaka mai zuwa.

    Napoli ta sanar da ɗaukar mai shekara 33 ɗin ne a shafukan sada zumunta da wani hotonsa na boge zaune a kan kujera.

  3. Man United ta kammala ɗaukar Cunha daga Wolves

    Mathues Cunha

    Asalin hoton, BBC Sport

    Ɗanwasan gaba na Brazil Matheus Cunha ya ce "burinsa" ne ya cika bayan kammala komawa Manchester United kan fan miliyan 62.5 daga Wolves.

    A farkon watan nan ne United ta amince da biyan farashin da ke ƙunshe cikin yarjejeniyarsa da Wolves, kuma ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar tare da zaɓin tsawaita ta da shekara ɗaya.

    "Abu ne mai wuya na iya faɗar abin da nake ji bayan zama ɗanwasan Man United," a cewarsa.

    "Tun ina yaro lokacin da nake kallon wasannin Premier League a talabijin, Man United ne kulob ɗina kuma na dinga burin saka jan rigar."

  4. Sane na gab da komawa Galatasaray daga Bayern Munich

    Leroy Sane

    Asalin hoton, Galatasaray

    Ɗanwasan gaba na Bayern Munich Leroy Sane na gab da kammala komawa kulob ɗin Galatasaray ta Turikiyya.

    Ɗanwasan mai shekara 29 ya isa birnin Istanbul a yau Alhamis kafin ƙarasa abin da ya rage na zama ɗanwasan zakarun na Super Lig.

    Rahotonni sun ce tuni Sane ya amince da kwantaragin shekara uku.

    Galatasaray ta wallafa hotunansa a shafukan sada zumunta sanye da ƙyallen kulob ɗin a filin jirgi, tana cewa sun "fara maganar ɗaukar" ɗan ƙasar Jamus ɗin.

    Magoya bayan ƙungiyar fiye da miliyan ɗaya ne suka kama tashar ƙungiyar ta dandalin YouTube domin bin sawun jirgin da ke ɗauke da Sane zuwa garinsu na Istanbul.

    Sane ya koma Bayern kan yarjejeniyar shekara biyar daga Manchester City a 2020, sai dai kwantaraginsa na gab da ƙarewa a ƙarshen watan nan.

  5. Yadda za a fafata a gasar Kofin Duniya ta Fifa Club World Cup

    Fifa Club World Cup

    Asalin hoton, EPA

    A karon farko hukumar ƙwallon kafa ta duniya Fifa za ta gabatar da gasar kofin duniya ta ƙungiyoyin tamaula 32 da aka zaɓo daga nahiya shida, wadda za a gudanar a Amurka a wani sabon tsari da ya bambanta da na baya.

    Nahiyoyin sun haɗa da Asia da Afirka da Arewa da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean da Kudancin Amurka da Oceania da kuma Turai.

    An tsara fara wasannin da Amurka za ta karɓi baƙunci daga 14 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin 2025 a filaye 12 a faɗin ƙasar.

    Karon farko da aka sauya fasalin gasar da ƙungiya 32 za ta yi tataburza, har da guda huɗun da suka lashe Fifa Club World Cup a baya.

    Manchester City ce mai riƙe da kofin, wadda ta ɗauka a karon farko da ta buga gasar a 2023 lokacin tsohon fasali.

    Tun cikin watan Maris din 2019 aka sanar da sabunta tsarin yadda za ake buga Fifa Club World Cup, kuma China aka tsara za ta fara shirya wasannin a 2021 daga baya aka soke shirin, saboda ɓullar cutar Korona.

    Daga nan Fifa ta amince aka ƙara yawan ƙungiyoyin da za su buga gasar daga nahiyoyi shida a Fabrairun 2023, kuma wata hudu tsakani aka sanar da Amurka a matakin mai masauƙin baƙi a gasar 2025.

  6. Mafarkina ne ya zama gaskiya - Alexander-Arnold

    Alexander-Arnold

    Asalin hoton, @realmadriden

    Da yake magana yayin gabatar da shi a harshen Sifaniyanci, Trent Alexander-Arnold ya ce "mafarkina ne ya zama gaskiya" na komawa Real Madrid.

    "Ba kodayaushe mutum ke samun damar taka wa kulob kamar Real Madrid leda ba," a cewarsa.

    Mafarkina ne ya zama gaskiya. Ina matuƙar farin cikin kasancewata a nan. Na ƙagu na nuna wa 'yan Real ƙwarewata kuma na yi bakin ƙoƙarina saboda wannan bajon."

  7. Ina sane da ɗawainiyar taka wa Real Madrid leda - Alexander-Arnold

    Alexander-Arnold

    Asalin hoton, Reuters

    Alexander-Arnold ya ce yana sane da ɗawainiyar da ke tattare da taka wa Real Madrid leda.

    "Ina sane da cewa taka wa Real Madrid leda na tattare da ɗawainiya mai yawa, kuma a shirye nake na yi duk abin da zan iya don daɗaɗa wa masoya Madrid [Madridistas]," in ji shi jim kaɗan bayan gabatar da shi.

    "Na ƙagu na nuna ƙwarewata, na lashe kofuna, na zama zakara, na girma, kuma na ji daɗin murza leda a kodayaushe tare da 'yanwasa mafiya ƙwarewa a duniya.

    "Na gode, Hala Madrid!"

  8. Real Madrid na gabatar da Alexander-Arnold

    Real Madrid

    Asalin hoton, @realmadriden

    A yau Alhamis Real Madrid ke bikin gabatar da sabon ɗanwasanta Trent Alexander-Arnold da ta ɗauka daga Liverpool a kyauta.

    Tuni shugaban kulob ɗin Florentino Perez ya gabatar wa Arnold da riga mai lamba 12, abin da ke nufin da ita zai dinga taka leda.

    'Yanwasa irinsu Marcelo da Eduardo Camavinga ne suka saka jasin a baya kafin shi.

    Sunan da za a rubuta masa a jasin shi ne 'Trent' maimakon 'Alexander-Arnold' da yake rubutawa a Liverpool.

  9. Maraba

    Barka da sake haɗuwa a shafin labarin wasanni na BBC Hausa.

    Kamar kullum, yau ma za mu ɗora da labaran abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni tare da ni Umar Mikail.

  10. Liverpool na gab da ɗaukar Wirtz daga Leverkusen

    Wirtz

    Asalin hoton, EPA

    Liverpool ta zafafa yunƙurin sayen ɗanwasan tsakiyar Bayer Leverkusen Florian Wirtz, inda ƙungiyoyinke tattauna yadda cinikin zai kasance.

    Ana sa ran farashin ɗanwasan zai kai fanmiliyan 114.

    Liverpool ta miƙa tayi na uku kan ɗanƙwallon Jamus ɗin a makon da ya gabata. Idan cinikin ya faɗa, zai zama mafi tsada da ta kashe fiye da fan miliyan 75 da ta kashe wajen sayen kyaftin ɗinta Virgil van Dijk a 2018.

    Leverkusen ta yi wa ɗanwasan mai shekara 22 farashi kan kusan fan miliyan 126, wanda ya fara buga mata wasa tun yana shekara 17 kuma ya ci mata ƙwallaye 57 cikin wasa 197.

  11. Magoya bayan Amurka sun yi wa koci Pochettino ihu bayan ɗura musu ƙwallo huɗu har gida

    Mauricio Pochettino

    Asalin hoton, Reuters

    Switzerland ta ɗura wa tawagar Amurka ƙwallo huɗu cikin minti 36 har gida waɗanda suka jawo magoya baya suka yi wa mai horarwa Mauricio Pochettino ihu bayan wasan na daren Talata.

    Sakamakon na nufin an doke Amurka sau huɗu a jere a karon farko tun daga shekarar 2007.

    Ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya ta 2026 tare da haɗin gwiwar Mexico da Canada, ta sha kashi a hannun Panama da da Canada da Turkiyya kafin shiga gasar Gold Cup a watan nan.

    Dan Ndoye na Switzerland ne ya buɗe ragar Amurka bayan minti na 13 da fara wasa, kafin Michel Aebischer ya ƙara ta biyu minti 10 bayan haka.

    Breel Embolo da Johan Manzambi ne suka ci sauran biyun kafin a tafi hutun rabin lokaci, abin da ya sa Switzerland ta ci wasa uku kenan a jere.

    Magoya baya sun yi wa 'yanwasan nasu ihu ne bayan ƙwallo ta huɗu ta shiga.

    Yanzu Pochettino ya yi rashin nasara biyar da cin wasa biyar cikin wasa 10 a matsayin kocin Amurka, yayin da ya rage shekara ɗaya cif kafin fara gasar ta Kofin Duniya.

  12. Brazil ta samu gurbin gasar Kofin Duniya ta 2026

    Brazil

    Asalin hoton, EPA

    Brazil ta samu gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan nasarar da ta samu kan Paraguay 1-0 a wasannin neman zuwa gasar daga yankin Kudancin Amurka.

    Nasarar ta zama ta farko da mai horarwa Carlo Ancelotti ya samu tun bayan karɓar aikin horar da tawagar ta Samba.

    Ɗanwasan gaba na Real Madrid Vinicius Jr ne ya ci ƙwallon bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Sakamakon na nufin Brazil ta samu gurbi a kowane Kofin Duniya tun daga fara gasar a shekarar 1930.

    "Yanzu kociyan zai samu ƙarin lokaci domin gudanar da aikinsa. Tabbas wasan na yau ba shi ne mafi kyawu a wajenmu ba, amma mafi muhimmanci dai shi ne mu yi nasara," in ji Vinicius bayan tashi daga wasan.

    "Yanzu lokaci ne na yin murnar nasarar zuwa gasar."

  13. Senegal ta zama tawagar Afirka ta farko da ta ci Ingila

    Senegal

    Asalin hoton, EPA

    Tawagar Ingila ta fuskanci rashin nasara ta farko ƙarƙashin mai horarwa Thomas Tuchel bayan Senegal ta lallasa ta 3-1 har gida a wasan sada zumunta.

    Tawagar ta Tuchel ta yi ta fafutika baki ɗayan wasan ba tare da wani abin kirki ba, yayin da Senegal ta zama tawaga ta farko daga Afirka da ta doke Ingila a tarihi.

    Ingilan ce ta fara cin ƙwallon da Kane ya zira a raga tun a minti na 7 da take wasa, kafin Sarr ya farke ta ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

    Bayan dawowa hutun ne kuma Diarra ya ƙara ta biyu, sai kuma Sabaly da ya ci ta uku bayan ƙara minti uku a kan mintuna 90 da aka buga.

  14. Man City ta tabbatar da ɗaukar Reijnders kan fam miliyan 46.5

    Tijjani Reijnders

    Asalin hoton, Manchester City

    Manchester City ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan tsakiyar AC Milan, Tijjani Reijnders kan kuɗi fam miliyan 46.5 a kwantiragin shekara biyar.

    Ɗan asalin Netherlands din shi ne mutum na huɗu da Guardiola ya ɗauka a bana bayan Rayan Ait-Nouri da Marcus Bettinelli da kuma Rayan Cherki.

    Reijnders mai shekara 26, ya sanya hannu a ƙungiyar domin samun damar buga gasar Club World Cup da za a Amurka cikin wannan wata, inda ake sa sai fara taka leda ranar 18 ga watan Yuni a wasan City da Wydad FC.

    Ɗan wasan ya bayyana farin cikinsa da komawa City yana mai cewa "City ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a duniya, da ke da ƙwararren koci da manyan ƴanwasa da kayan aiki masu inganci.''

    "Ƙarƙashin jagorancin Guardiola, City ta lashe kofuna da yawa, kuma ian son taimaka wa wajen ci gaba da ɗaukar manyan kofuna a shekaru masu zuwa."

    Reijnders ya buga wa Netherlands wasa 22, sai dai ya kasance a benci lokacin da ƙasarsa ta doke Malta da ci 8-0 a ranar Talata.

    Ya ci ƙwallo 15 a wasa 54 da ya buga wa Milan a duka fafatawa a kakar da ta gabata, inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan tsakiyar Gasar Serie A

    Yayin da Kevin de Bruyne ke barin ƙungiyar, Reijnders zai taimaka wajen ƙarfafa tsakiyar City.

    Shi ne ɗanwasa na huɗu Man City ta ɗauka tun daga ranar Litinin zuwa yanzu:

    • Tijjani Reijnders - Daga AC Milan
    • Rayan Cherki - Daga Lyon
    • Ait-Nouri - Daga Wolves
    • Marcus Bettinelli - Gola daga Chelsea
  15. Atletico Madrid ta ɗauki golan Atalanta Musso

    Juan Musso

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid na cikin 32 da za su fafata a gasar kofin duniya ta kulob-kulob kuma tana ci gaba da shirin yin hakan ta hanyar sanar da sayen sabon mai tsaron raga.

    Ta tabbatar da ɗaukar golan Atalanta Juan Musso kan yarjejeniyar shekara uku.

    Musso mai shekara 31 ya shafe kakar wasa ta bara a kulob ɗin na birnin Madrid a matsayin aro inda a yanzu ya zama nasu. Yana kuma cikin tawagarsu da za ta fafata a gasar ta kofin duniya.

    Ya buga mata wasa 11 a dukkan gasanni na kakar 2024-25.

  16. Dortmund ta sayi Jobe Bellingham daga Sunderland

    Jobe Bellingham

    Asalin hoton, PA Media

    Jobe Bellingham ya koma Borussia Dortmund daga Sunderland kan yarjejeniyar shekara biyar zuwa 2030.

    Ɗanwasan tsakiyar mai shekara 19 ya fara taka wa Sunderland leda tun 2023, inda ya buga wasa 90 kuma ya taimaka mata samun gurbin buga gasar Premier League ta Ingila.

    Matashin ya fara sana'arsa a kulob ɗin Birmingham City bayan ya fito daga kwalejin koyon ƙwallon ƙungiyar, kafin ya shekara biyu a babbar ƙungiyar tasu.

    Cikin wata sanarwa, Bellingham ya ce yana alfahari da "babbar" alaƙar da yake da ita da magoya bayan Sunderland.

    Irin wannan hanya yayansa Jude Bellingham ya bi, daga Birmingham zuwa Dortmund, inda ya shafe shekara uku kafin ya koma Real Madrid a 2023.

  17. Carson zai bar Man City bayan wasa biyu cikin shekara shida

    Carson

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan lashe kofuna tsawon shekara shida da buga wasa biyu kacal, mai tsaron ragar Manchester City Scott Carson zai bar kulob ɗin idan kwantaraginsa ya ƙare a bazarar nan.

    Golan mai shekara 39 kuma tsohon mai tsare wa Ingila raga, na cikin tawagar City da ta lashe kofuna 11, ciki har da uku rigis da ta ci a kakar wasa ta 2022-23.

    Carson ya koma City ne a matsayin aro daga Derby County a 2019 kafin ya fara zaman dindindin a 2021.

    Ya shafe mafi yawan zamansa a City a matsayin gola na uku bayan Ederson da Ortega, inda ya buga wasan minti 117 kacal jimilla.

  18. Yaƙin Isra'ila a Gaza yana firgita ni sosai - Pep Guardiola

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Reuters

    Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yana cikin "firgici soai" sakamakon yaƙin da Isra'ila ke yi da mayaka a Zirin Gaza yayin wani jawabi da ya gabatar.

    Wata 20 kenan tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoiban 2023, inda mayaƙanta suka kashe aƙalla mutum 1,200 da kuma sace wasu 251.

    Aƙalla Falasɗinawa 54,800 aka kashe sakamakon hare-haren na Isra'ila a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya ta zirin ƙarƙashin ikon Hamas.

    "Abin da muke gani a Gaza abu ne mai ƙona zuciya. Yana ƙona jikina baki ɗaya," in ji Guardiola cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

    "Bari na bayyana ƙarara, ba maganar aƙida ba ce. Ba maganar na faɗi gaskiya ba ce ko akasin haka. Magana ce kawai ta girmama rayukan ɗan'adam, da kula da maƙwabcinka.

    "Ƙila muna jin cewa yaran a muke gani ana kashewa a asibiti ba mu jin komai saboda ya tashi daga asibiti. ZA mu iya jin cewa ba matsalarmu ba ce amma mu kiyaye saboda nan gaba za ta iya zama tamu. Yaro ko yarinyar da za a kashe nan gaba zai iya zama namu.

    "Tun daga lokacin da wannan bala'i ya fara a Gaza, 'ya'yana Maria da Marius da Valentina nake kallo. Duk safiya idan na ga jariran Gaza, abin yana firgita ni."

    Kocin ɗan asalin Barcelona a Sifaniya ba baƙo ba ne wajen bayyana ra'ayinsa na siyasa. A baya ya sha nuna goyon bayansa ga masu fafutikar neman 'yancin yankin Catalonia a Sifaniyan, inda har hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta ci tararsa saboda saka wata riga mai nuna goyon bayansu a filin wasa.

  19. Burin Osimhen na komawa Man United zai iya cika a bana

    Osimhen

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da ake rufe kasuwar saye da musayar 'yanwasa a yau Talata, ana sa ran akwai 'yanwasan da cinikinsu zai faɗa, da kuma waɗanda ake shirin fara kai musu tayi.

    Cikinsu har da ɗanwasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, wanda jaridar La Gazzetta Sport ta ruwaito cewa burinsa na komawa Manchester United ka iya cika bayan ya ƙi amincewa da gwaggwaɓan tayin da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi masa.

    Rahotonni na cewa farashin yuro miliyan 75 ne a cikin ƙunshin yarjejeniyarsa a Napoli, amma United na fatan miƙa tayin kuɗi da kuma ɗanwasanta Joshua Zirkzee domin sayen Osimhen.

    Ɗanwasan mai shekara 26 ya lashe gasar Super League ta Turkiyya a kakar da aka kammala tare da Galatasaray, inda ya buga wasa na kaka guda a matsayin aro.

  20. Maraba

    Barka da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na duniyar wasanni.

    Za mu ɗora daga inda muka tsaya a yau Talata, kuma ni ne Umar Mikail zan jagoranci kawo rahotonnin.